Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 28

Page 35&36

"Tana zuwa ɗakin tashaƙo wuyar Beebah ta rinƙa zabga mata belt tana huci, Beebah taji wuya sai zazzare ido take ihunma takasa"

Suna cikin haka Mommy tashigo ɗakin, taga Beebah a hannun Bintu sai zare ido take, ita kuma Bintu sai huci take tana zaneta, Mommy tayi saurin shiga ɗakin tana ƙoƙarin kwatan Beebah Amma takasa,
Dataga Beebah tana jujjuya idanu Alaman zata suma, tafita a É—akin da gudu tana ihu takira Baba me gadi da driver.

Tace kuzo zata kasheta ranta yaɓaci dama haka take idan ranta yaɓaci, da gudu suka shiga ɗakin, sukayi kan Bintu suna ƙwatan Beebah Amma ina Rikon da Bintu tayi mata bana wasaba!

"Da kyar da suɗin goshi suka ƙwaci Beebah, ai kuwa tanajin an saketa ta kwasa da gudu tayi cikin toilet ta kulle ƙofar"

_Ahmad_

Ajmad ne yake tambayar Habeeb meyake faruwa awayar? Habeeb yace wallahi Ahmad narasa ganewa Bintu wani irin zuciya ne da ita idan ranta yaɓaci, tanada hakuri sosai Amma idan ranta ya ɓaci ba'a gane kanta, yanzu fa dukan Beebah takeyi kamar 'yarta, Ahmad yace ay dama haka me hakuri yake idan ranshi yaɓaci ba kyau, saidai kuyi ta mata Addu'a.......

Kafin yakarasa yaji wayarshi tana kara, daya duba saiyaga sunan Abdul ne, yayi dariya yaɗau wayar, yace "hello dude ya kake?" ɗayan bangaren akace lafiya ya jikinnaka? Ahmad Yace da sauki, Albishirinka? Ahmad yace goro, nasamu matar Aure anan Adamawa, Ahmad yace kai banason ƙarya, yace wallahi nake faɗa maka kuma Aurenta zanyi insha Allah.

kaima ina maka Addu'a kullum Allah yabayyana maka Fateemahnka idan har tana raye, idan kuma bata raye Allah ya musanya maka da mafi Alkhairi,
Ameen cewar Ahmad cikin sanyin murya yayi maganar sukayi sallama.

"Abdul abokin Ahmad ne yakasance me bashi shawara ako da yaushe, bayason damuwar Ahmad ko kaɗan, sannan yana taƙaicin yaga Ahmad yana tafiya da Abokanan banza, shima yana daga cikin masu bincikowa Ahmad Fateemahn shi".

_Bintu_

Bintu takicin abinci taki yiwa kowa magana agidan, har na tsawon kwana biyu, abun yadami Mommy sosai yau ta tarasu a falon ta tanason ta sasantasu, zaman dasukeyin baya mata daÉ—i ko kaÉ—an.

kuma haka akayi dan Bintu ta sakko Beebah kuwa tabata hakuri komai yawuce.

Yau friday Bintu ce ta dami Abdul sai yazo gidansu, shikuma Abdul yana gudun wulaƙancin Beebah yace mata gaskiya yau bazan zoba Babyna, tace mishi dan me? Yace babu, tace idan badan wulaƙancin da Beebah tayi maka ba nasan bazaka ki zuwa ba!

Yace mata Aa wallahi bahaka bane, tace to kazo, da Abdul yaga ta nace yace mata to zanzo Amma sai bayan juma'a tace tom.

Haka akayi kuwa bayan juma'a saiga Abful yazo, yayi kyau yasa brown na shadda da hula brown yayi kyau sosai,
Bintu kuwa tasa Abaya pink da gyallenshi tasa flat shoe pink tayi kyau kamar asace a gudu.
Tana zuwa wajenshi yaji ƙamshin turarenta a hankali ya lumshe idonshi, ya buɗe yace
"Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan halitta"

Bintu tayi dariya har kumatunta ya lotsa tace godiya nake masoyina.

Abdul yayi dariya yace ranki ya daɗe dolene yau nayi snapping naki ko ɗayane Bintu tarufe fuskanta tace banason hoto, Abdul yayi yayi ta ɓuɗe fuskanta taƙi, ahaka ya ɗauketa hoton ta rufe fuskanta da hanunta, tana dariya.

Haka sukaci gaba da hirarsu cikin farin ciki, suna cikin hiranne Abdul yanata dariya, dan Bintu yau tana ta bashi labarai,
kawai saiga Beebah tazo wucewa,
da Alama mommy ce ta aiketa.

Bintu tayi shiru zuciyarta tana bugawa tana tsoron kar Beebah ta wulaƙanta Abdul irin na rancan.

Beebah tana isowa wajensu ta tsunkuya har ƙasa tace "ina wuni yaya Abdul"....

✍🗒️ *jiddah S Mapi*
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*dedicated to my love ❤️*

*WATTPAD*
Jiddahpretty

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.