A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 28
Page 43&44
"A zuciyar Ahmad yace ay Amarya ko bata da kunya, ranar Aurenta tana ɗan jin kunyar mutane Amma ita ta zage sai tiƙa rawa taje agaban Abokan Ango? Kai wannan abu da alamar tambay"
Beebah kuwa acikin zuciyarta tance kai wannan gayen ya haÉ—u ana gama kamu zan tambayi numban wayarshi, duk nan yafisu wanka, duk maganar dasuke acikin zuciyarsu be hanasu taka rawa a filin ba, har MC yace to mun gode Allah yasakawa amarya da ango dakuma babban abokin ango.
Haka suka juya suka tafi, an gama kamu dab mangariba kowa ya watse.
Ahmad ne yacewa ango yanason yabishi hotel É—in daya sauka sabida sunada magana me muhimmanci, Abdul yashiga motarshi suka wuce Hotel.
_Bintu_
Bintu tace ita wallahi daga kamu ba abinda za'a karayi a Aurenta na bidi'a.
Washe gari ranar jumma'a ranar da za'a É—aura Auren Abdul Muhammad da Bintu Umar, shirye shirye ake na musamman, kawayen mommy sunzo daga wani gari 'yan wanka ne kuma hajiyoyi ne.
Bintu kuwa tasa leshi jaa me kyau tayi makeup kamar asace agudu, Beebah ma ba'a barta ba wajen kyau, kawayensu ma sunyi kyau sosai. Kawayen mommy suma leshi suka É—inka garin mata dashi, idan kashiga gidan saika raina kanka.
2:30pm cif aka É—aura auren Bintu da Abdul akan sadaki dubu É—ari lagadan ba ajalan ba, Anyi Aure an kammala komai da mangariba abokan ango sukazo su É—auki amaryarsu.
Tofa nan akeyinta Habeeb dayaga za'a tafi da Bintu yadinga suma kamar me farfaɗiya, har mutanen wajen suka fara mamaki, mommy ce tacewa Bintu takoma gida, Beebah ce tazama amaryan karya taje tashiga mota aka tafi da ita, bayan mutane sun watse ne mommy takira Habeeb cikin ɗakinta da Bintu ta ajiyesu, mommy ce tace Habeeb? Yace na'am tasake cewa Habeeb? Habeeb yace na'am Mommy tasake cewa Habeeb? Yace na'am, Mommy tace sau nawa nakira sunanka? Yace sau uku, mommy tace tom nataɓa kiran sunanka sau uku? Yace Aa tace inason kafaɗamin gaskiya. Meye a tsakaninka da Bintu?..
Habeeb yayi shiru sai kawai yafara kuka, mommy tace ba kuka natambayeka kayi ba, idan har nina haifeka kafaÉ—amin Abinda yake ranka?
Habeeb yace Mommy inasonta ne!!! Kuma Aurenta nakeso nayi!!!
Tass tass tass kakeji Bintu ce taɗago ta dallawa Habeeb mari tana huci... Bakada hankali ne yaya? Ko kafara shaye shaye ne? Ko ka sami taɓin hankaline? Ko bakasan ciki ɗaya muka fito dakai bane? Duk waɗannan tambayoyin tana yinsu ne cikin hawaye.. Yaya kai mahaukaci ne bakada hankali, sai yau na tabbatar da haka kanka ya taɓu.
Ke Bintu kece me taɓin hankali bani ba! Kece kanki yasami matsala bani ba! Ina matsayin yayanki zaki kirani mahaukaci? Kece mahaukaciya! Yana magana yana hawaye,
Kinsan iron son danake miki? Kinsan baƙin cikin danake ji idan naganki da saurayi? Kinsan yaya nake kwana acikin kwanakinnan da Auranki ya iso? Kinsan yanda nakeji kamar na kashe Abdul idan naganku tare? Duk nasan baki sani ba.
"Mommy ce ta tsaya awajen ba bakin Magana sai zazzare ido datakeyi kamar wata taɓaɓɓiya, idan wannan yana magana tajuya ta kalleshi idan wannan yanayi ta juya ta kalleshi tarasa ya zatayi da duniyarta tarasa ina zatasa kanta ayau, jitake kamar ta tara kayanta tabar gidan kafin su fara mata tambayoyi, juyawa tayi zata bar musu ɗakin taga mutum akwance kasa ba alamar numfashi! Beebah ce kwance kasa, wanda ta daɗe da dawowa ta dalilin faɗa dasukayi da Abdul bayan ankaita gidanshi ta tsigeleshi tayi gaba abinta, tana dawowa shine ta tarar da abinda yafi karfin kunnenta. Jin kalaman Habeeb yasa tafaɗi ta suma!
Mommy ta tsala ihu ta iso wajen da Beebah take kwance ƙasa!...
_✅ote comment and share pls_
âœÂ︠*Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*Jiddah S Mapi*
_Dedicated to all my fans_
*بسم الله الرØÂمنالرØÂيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœÂðŸÂ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ÂðŸÂ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.