Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 28 of 28

Page 57&58

🔚🔚🔚🔚

"Fareedah taÉ—an saki jiki kaÉ—an da Habeeb, ahanyansu nazuwa kaduna ansha love amota musamman Beebah data rikita É—an mutane da turare,
Bayan sun iso ne kowa yafito amotar a gajiye kamar an dakesu.

Ahmad ne yanunawa Habeeb wasu gidaje tsararru kerarru haɗaɗɗu, guda uku yace "Habeeb kazaɓi gida ɗaya acikin waɗannnan"
Habeeb yace "kowannema nagode basai nazaɓa ba! Allah yasaka da alkhairi sannan yabar zumunci" Ahmad yace "Ameen"

To tinda gidan uku be kuma ajere komai naciki kala É—aya ne nizan zauna a tsakiya tinda nine karami
Dukka suka kwashe da dariya
Habeeb ne yarike hanun matarshi yace sai kun karaso.

Ahmad yace daÉ—in Abin dai baza'aci fuskarmu ba! Kowama yanada tashi.

Duka suka wuce gidansu,
Bayan sun idar da sallan mangariba da isha ne Ahmad yaÉ—auki wayarshi yakira su Habeeb da Abdul yace idan ba matsala yanason zasuyi magana agidanshi dukkansu da matansu,
Sukace ba komai.

Jim kaÉ—an saigasu sunzo suka zauna a babban falon da yake mallakin Bintu ne da Ahmad,
Bayan sun zauna Habeeb yabuÉ—e musu da Addu'a.

Ahmad ne yayi gyaran murya yace "da farko ina godiya ga Allah me kowa me komai wanda shine yayi sanadin taruwanmu anan,
Sannan ina mika godiya ga Abokaina Kuma Aminaina Wato Habeeb da Abdul, hakika kunmin inuwa wanda ba kowa bane zai iya yiwa abokinshi Awannan zamanin" Ahmad yatsunkuyar da kanshi yafara hawaye yace

"Habeeb kasan irin wahalar danayi a neman Fateemah kuma kaima ka tayani nemanta alokacin danake cikin taahin hankali,
Sai wani ikpn Allah ashe Fateema A gidanku take!!! Bamu sani ba!
Matar da Allah yarubuta zata zama matarka ashe A GIDANMU TAKE!!!
nasan kanason Fateema Habeeb Amma Allah bai rubuta kai zaka Aureta ba!
Matar da Allah ya rubuta zaka Aureta
A GIDANMU TAKE!!!

Habeeb ne yace "kayi hakuri Ahmad kadaina kuka komai yawuce kamar yanda matar dakake nema A GIDANMU TAKE!!! haka zalika matar danakeso yanzu A gidanku take!!! Ikon Allah kenan".

Abdul ne yace "godiya yakamata muyiwa Allah daya nuna mana wannan rana ba kuka ba!"

Ahmad ne yace "ku yafeni dukkanku nasan nashiga hakkin ku"
Habeeb yace kadaina irin wannan maganar Ahmad komai yawuce.
Muyi addu'a dai kawai Allah yajikan Daddy yasa mutuwarshi shiyafi Alkhairi mukuma idan namu yazo Allah yasa mucika da imani

"Ameen" cewar duk mutanen falon.

Kasancewar Amaren duk suna off hakan yasa mazajen duk suka hakura dasu,
Banda Ahmad da saida ya yayi wasa da Fateemah Bintu.

Bayan sati É—aya,
Ahmad ne naji yana yiwa matarshi sannu duk ya rikice,
Dana leka É—akin sai naga Fateemah Bintu kwance akan gado ba alamar motsi gashin kanta abarbaje,
Naga Ahmad yashiga toilet nabishi naga ruwan zafi yahaÉ—a Bahon wanka,
Naga yadawo Dali yaÉ—au 'yar mutane yayi hanyan toilet da ita, nikuma kasancewar ban kai age É—in dazan san me sukayi ba! Yasa na É—auki biro na da takadda na naÉ—aukan rohoto nayi waje sai gidan Habeeb.

Ina zuwa naga Fareedah kwance akan cinyarshi tana zuba shagwaɓa kamar wata baby shikuma yazage sai biye mata yake, nace to abun nakun na yarane, nayi gaba sai gidan Abdul da Beebah uwar kauɗi.

Ina zuwa naji abunda yafi karfina!
Beebah ce take cewa Abdul "Baby anya ba ciki ne dani ba? Kaduba kaga yanda nake Amai fa"
Abdul dayake rungume da ita yace

"Allah yasa cikine, da bawanda zai kaini Farin ciki"

Nayi gaba nace bada niba.
***********

_Bayan wasu shekaru_

Gidan Ahmad ne naga wasu kyawawan yara suna wasa su biyu mace ce dakuma namiji farare kamar Auduga.

Ahmad ne kwance atsakiyarsu yana cakulinsu sunata dariya,
Sai naga wata kyakkyawar mata tashigo tace "Hubbie wai ina su mommyy karama sukaje ne? Tin É—azufa suka fita wai wasa"

Daga baya naji wata mace tace "Ai mommy karama A GIDANMU TAKE!!!
Tin dazu suna wasa dasu Daddy karami"
Juyawar dazanyi sai naga Polina da hijabi.

Ashe wai Bash ya shiryu dayaga Ahmad ya gyara halinshi, Polina ma ta musulunta tayi Istibra'i sannan Bash wanda yanzu ake kira da Bashir ya Aureta!

Suna zaman lafiya harta haifa mishi yara 'yan biyu Haneef da Haneefah.
Suma suna zaune ne agefen gidansu Ahmad wanda shi Ahmad dakanshi ne yasaya musu.

Ahmad ne yace to Alhamdulillah yanzu dai kinji inda suke,
Tinda itama ga 'yarta tin É—azu A GIDANMU TAKE!!!

Alhamdulillah!!!
Alhamdulillah!!!
Alhamdulillah!!!

Nan nakawo karshen littafina me suna A gidanmu take!!! Kuskuren danayi ko tuntuɓen harshe Allah yagafarta mani.

Saimun haÉ—u a littafina na gaba me taken MAKAUNIYA CE!!!

*special thanks to WALIDATION S MAPI sisi forever*

✍️🗒️ *Jiddah S Mapi*

Taku ce 👍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.