Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 18 of 28

Page 33&34

"A firgice mommy taɗago kanta tana kallon Beebah tace ke Beebah bakida hankali ne? Ya 'yar uwarki tana nuna miki saurayinta zaki faɗi maganan banza akanshi? Idan nakarajin irin wannan maganan daga bakinki saina ɓata miki rai tashi kibani waje"

Beebah tafita a É—akin, mommy tace kiyi hakuri Hassana na kinga 'yar uwar taki batada hali me kyau, bani hoton nashi nagani, Binta tace to saita nunawa Mommy hoton mommy tace kaii amma gaskiya sirikinan ya haÉ—u masha Allah ya sunanshi? Abdul inji Bintu, masha Allah Babban suna Allah yabarku tare, kuma Allah ya nunamin ranar Aurenku Ameen.

_Ahmad_

Habeeb ne yasashi agaba yayi ta mishi nasiha, Ahmad yace nagode Habeeb Allah yabar zumunci.

_HABEEB_

"Habeeb kuwa acikin zuciyarshi yana tunanin yafaÉ—awa Ahmad damuwarshi amma yana tsoron kar ayi mishi mumunan fahimta, azuciyarshi yace kai garadai nafaÉ—a mishi ko zai nema min mafita,
Wani abu yace mishi Aa karka faɗa ka riƙe sirrinka, ba lalle bane kowa yayi maka kyakkyawan zato"

Yana cikin tunanin yaji an dafashi, Ahmad ne yace "abokina kasan bana ɓoye maka komai a rayuwata? Habeeb yace eh, to kaima banason ka ɓoyemin komai inason kafaɗamin damuwarka,
na lura tin Wancan zuwannaka kana ɓoyemin wani abu"
Habeeb yace babu komai Ahmad dama wata 'yar matsalace agida amma in Allah ya yadda za'ayi solving nasu very soon.

To Allah yasa Ameen

_Bintu_

Yau ce ranan dasukayi da Abdul zaizo wajenta dan haka tasha wanka tasa atamfa ja da jar gyale sai jar takalmi tayi makeup, idan kaganta kamar kasace ka gudu.

Abdul yazo gidansu Bintu anyi mishi tarba me kyau, Bintu ta ajeshi a babbar falo suna hira sai Abdul yace

"Babe tinda nazo banga twins nakiba ki kirata mana mu gaisa".

Bintu tace tom, saita É—au waya takira Beebah tace kiseni a falon Mom, Beebah tace ok
Jim kaÉ—an saiga Beeba tasha doguwar rigar material ja itama jar gyale tasa, tana zuwa falon ta tsaya akan Bintu tace gani,

Bintu tace Abdul ne yakeso ku gaisa, tace to bagani ba! Bintu tayi shiru Abdul yace ya kike ƙanwata? Beebah tace Aa niba ƙanwar ka bace ni ƙanwar Habeeb ce, Abdul yayi dariya yace toya kike ƙanwar Habeeb? Tace lafiya

"Yace ok saiya cire kuɗi yace gashi ko ƙanwar Habeeb,
Beebah tace Aa ai gidanmu ba'a yunwar kuÉ—i.

Ta juya tayi tafiyarta Bintu tayi shiru tarasa yazatayi,
Abdul yace karki damu my dear nasan yaranta ne yake daminta karkiji komai.
A rayuwar Bintu ba abinda tatsana kamar wulaƙanci haka suka ƙarashe hiransu da Abdul tarakashi wajen motarshi tace mishi sai yaushe Kenan yace gaskiya ba rana Babe, tace dan Allah kayi hakuri da abinda twins nawa tayi maka yace ba komai babe, haka sukayi sallama yatafi tana ɗaga mishi hannu.

Tajuya tashiga cikin gida ta samu Beebah kwance suna waya da Habeeb, tana zuwa ta wupce wayar ahanun Beebah Tace "bakida hankali Ko? to yau zan koya miki hankali har Zaki wulaƙanta Abdul kuma kinsan shi zan Aura? Beebah tace bani wayata! Baza'abada ba! Ki ƙwace Beebah tafara ƙwatar Wayar suka kwashe da dambe!

_HABEEB_

Habeeb suna waya da Beebah yaji duk Abinda sukeyi yanatayi Musu magana su daina amma ina sai ihun Beebah yakeji alamun tana dakuwa, aranshi yace me hakuri fushinshi babu kyau!

Beebah bakaramin duka takesha ba awajen Bintu, gashi bakinta baya shiru, tana ta zagin Abdul, da Bintu taga Beebah ba shiru zatayi ba saita fita falo ta tsinƙa sucket na TV tashiga ɗakin da gudu...

✍️🗒️ *jiddah S mapi*

_pls share🙏🏻_
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

*dedicated to my love❤️*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.