A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 28
Page 53&54
"Habeeb ne yaga alamunta, dasauri yabuÉ—e mata marfin motar tafita.
Sai gani sukai Bintu ta tashi dagudu taje tarungume wata kyakkyawar mata da 'yarta,
Bintu kuma acikin zuciyarta daÉ—i takeji tunda gasu mommy da Fareedah, tana ganin mommy tana hawaye tafara tambayanta mommy meya faru kike kuka?
Ko Daddy ne ba lafiya?
Alamun mamaki ne yabayyana afuskar su Mommy da Fareedah,
Har Ahmad ba'a barshi abaya ba! Wajen mamakin tambayoyin da Bintu take.
Basu tashi jin mamaki ba, saida Bintu tace "Mommy waÉ—ancan mutanen satoni sukayi ko? Allah yataimakeni dannaji yana waya da wani wai a filin jirgi, dabaku zo dawuri ba, dasunana gawa!!! "
Wannan maganar ya girgiza mommy
[6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*Jiddah S Mapi*
_Dedicated to my Eeshart much love habibtyâ¤ï¸Â_
*بسم الله الرØÂمنالرØÂيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœÂðŸÂ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ÂðŸÂ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*WATTPAD*
Jiddah S Mapi
Page 55&56
"Bintu kuka tafara kamar ba gobe, ita gaskiya batason Ahmad bata kaunarshi, idan ta tuna zagin dayai tamata lokacin datake gidansu sai taji ta tsaneshi,
Hasalima tsoron shi takeji, wanda yayi niyan kasheka Amma kayadda kaci gaba da zama dashi? Wata zuciyar tace mata karkiyi haka, ta sanadin ki babansu yarasu idan kikace bakya sonshi ai kinyi butulci.
Kiduba irin son da kanwarshi take miki"
Mommy tace ke muke sauraro,
Duk É—akin sunyi shiru bakajin komai sai kukan Bintu,
Ta ɓangaren Ahmad kuma ji yake kamar yaje ya rungumeta! Ya tsani yaga tana hawaye zafi yakeji acikin ranshi.
Bintu tace "bazan iyaba!!!" wlh Mommy bazan iyaba!!!!
Ahmad ne yafara É—aga hanunshi sama alaman zaiyi roko,
Mommy ta dakatar dashi.
Mommynsu Habeeb ne tace "menene bazaki iyaba Bintu?"
Bintu tace "bazan iya musu daku ba!"
Alhamdulillah inji duk mutanen É—akin,
Ahmad ne yace mommy inada magana,
Mommy tace muna jinka.
Yace mommy inason kuzama shaida
Kamfanina na takalma da jakunkuna nabarwa Fateemah halak malak yazama nata!
Sannan akwai gidajena dake G.R.A a Kd guda biyu wanda nayi niyan zamu zauna da Fateemah aciki, sannan idan Fareedah tayi Aure zasu zauna da mijinta a É—ayan
Yanzu ma haka
Za'ayi, shikuma Abdul zan siya mishi gida agefen namu duk muzauna tare!
Mommy tayi murna sosai sannan Habeeb da Abdul sunyi godiya sosai
Su Ahmad kuma sunce gobe zasu koma, yayinda akasa ranan Aurensu Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah, sannan Ahmad da Bintu sati mai zuwa idan Allah yakaimu
******
yau akeyin ta! yaune ranan É—aurin Auran su Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah!
Amare sunyi kyau
sabida sunyi dilki
Idan kagansu kamar daga kasashen larabawa!
Musamman Bintu data zama kamar 'yar india.
Yau za'ayi lunching
Amare dukka uku sunsa Dogayen riguna pink color me yalki da bakin roses suka É—aura kansu,
Me yi musu makeup na musamman aka É—auko inda ta fesa musu kwalliya kamar ba gobe!
Idan kaga waÉ—annnan Amaren zakace babu Amaren dasuka kaisu kyau.
"Babban hall aka kama musu, inda akayi decoration na wajen da kayan ƙyaleƙyale na zamani,
Kujeru uku me zaman mutum bibbiyu akayiwa kwalliya irinna gidan sarauta!
_Ahmad, Habeeb da Abdul_
Suma ba'a barsu abaya ba wajen kyau,
Sunsa Fararen shadda me ɗauke da zibin baƙi ajiki,
Takalmi baƙi sukasa, sai agogo ma baƙi da bakaken hula.
Subhanallah!!!
Idan kaje kaga yanda aka tsara wajen da ƙawayen Amare da Abokanan ango da Amaren da angwayen,
Sai ka raina kanka!
Abinci kuma kamar ba dafawa akai ba! Drinks kuma babu kalan wanda babu,
Amare sun zauna akan kujerun da aka kayata dominsu,
Da angwayensu.
Kuyi imagine yanda Amaren da angwayennan zasu bada light Awajen.
An jera kawaye kamar cinnaka sunyi layi dukkansu da anko,
dogayen rigane marun color sukayi anko sun É—aura kai da peach na roses.
Sumafa ba'a barsu abaya ba! Wajen kyau.
Beebah ce taga ba'a kira Amare ba har yanzu gashi kawaye sai caskalewa suke afili,
Sai kawai tamike Abdul yasan hali,, yasan mezatayi
Yarike hanunta ta janye hanunta tafara tafiya tan rawa.
Daidai lokacin aka sake wakan
"Ahmad shanawa"
Me taken agirgiza baya baya a karkaÉ—a ayi kamas
Beebah ce tafara girgiza jikinta tana rawa kamar ba Amarya ba!
Kowa ya juya yana kallonta rawa take tana juya jiki kamar hawainiya.
Da Abdul yaga yanda take girgiza jikinta sai ya tashi shima yabi bayanta,
Suka fara rawa atare dama Abdul ma ba daganan ba!
MC. Yakira Amaren dukkansu da angwayen suka shiga fili.
Ahmad yarike hannun Bintu.
Sune agaba!
Suna shiga tsakiya Bintu ta wapce hanunta tafita!
Ahmad yatsaya yana kallon ikon Allah.
Bintu kuwa acikin Zuciyarta idan ta tuna abinda Ahmad yayi mata sai taji ta tsaneshi,
Batason Ahmad!!!
Ta tsaneshi Amma bazata iya musu da mutanen dasuka taimaketa ba!
Da yanzu tana gidan marayu, batasan ya rayuwarta zai kasance ba!
Tana cikin tinani taga Ahmad ya iso wajenta,
A hankali ya tsunkuya ya rike hannayenta duka biyu.
Ya sassauta murya
Yanda ba wanda zaiji daga ita sai shi
Yace "Wifey meyasa kikemin haka? Kodai baki yafe min bane? Kisani fa Allah ma muna mishi laifi ya yafe bale mutum É—an Adam,
Dan Allah na roke ki, ki taimakawa rayuwata
Kece farin cikina
Rabona danaji farin ciki acikin rayuwata tin ranan da wancan abun yafaru,
Daga ranan Na daina ganin haske a rayuwata, ki tausayamin my Teemah.
Inasonki!!!
Inasonki!!!
Inasonki!!!
I love you with all my heart,
Zan iya rasa rayuwata idan kika gujeni.
My teema inason ki manta komai mu gina sabon rayuwa,
Wallahi idan kika gujeni bazan taɓa gane hankalina ba!
YafaÉ—a cikin hawaye.
Bintu dataga yana mata kuka gashi mutane sunata kallonsu, saita fara kokarin tayar dashi.
Shi kuma yazauna akasa yaki tashi sai hawaye dayake kamar Amarya,
Ganin haka yasa Bintu tace "na yafe maka duk abinda kamin, kuma bazan taɓa manta halaccin da iyayenka suka min ba! Ahmad na yafe maka duniya da lahira"
Ahmad ne yafara dariya kuma yana hawayen farin ciki.
MC. Ne yafara magana yace "ana neman duk Amaren da ango a fili, suzo su nuna mana farin cikin Dasuke ciki ayau.
Ahmad ne yarike hanun Bintu, Habeeb yarike Hanun Fareedah, Abdul kuma yarike hanun Beebah,
Tafiya suke suna É—an rawa, yayinda mutane suka sa tafi suna ihu.
Wakar biki yayi biki akasa musu, inda suka fara rawa Amma banda Bintu data tsaya tana dariya.
Ahmad dayaga zata badashi afili, sai ya rike kwankwason ta yafara rawa,
Bintu kamar kasa ya tsage tashige tsabar kunya.
Tafara kokarin cire hanunshi ajikinta
Amma ina yaki saima kara janyota jikinshi dayake.
Dataga haka saita fara kuka tana tureshi.
Ahmad ne ya rungumeta afilin yasa bakinshi daidai kunnenta yace "Haba wifey mutane fa suna kallonmu ki daina kukannan kinji wifey"
Tafi sukaji anayi musu, Ahmad yasaketa!
Taga ba kowa afili daga ita sai shi su Beebah sun tafi!
Dj ne yasake musu wakan Romantic,
Bintu kamar gunki sai juye juye tafara,
Ahmad ne yarike kwankwasonta yana rawa da ita.
Dj yace atafa musu
Akasa tafi Awajen.
Dahaka har aka gama lunching kowa yashiga motan mijinshi aka wuce dasu gidansu Beebah.
Suna zuwa Bintu ko cire takalmi batayi ba! Ta kwanta akan gado tana nishin gajiya,
Beebah ce tace "dama ya lafiyar kura bale takama zawo"
Bintu tace yanzu nice kuran Beebah? Nafa lura kin fara rainani a 'yan kwanakinnan, dan kinga zakiyi Aure ko?
To bara nafaÉ—a miki har yanzu ke yarinyace awajena ehen.
Fareedah tace "wayaga Babba kema ai ba Auran kikayi ba! Tare dai zamusan komai"
Bintu tace wannan magana taki tafi karfina!
Kinga namayi bacci,
Dukka suka kwashe da dariya.
_Ahmad_
Jinshi yake kamar wani sabon halitta, suna zuwa gida yakwanta akan gado yafara tunanin wai yau Fateemarshi ce tazama mallakinshi? Yanzu gobe war haka suna tare da ita amatsayin mata da miji,
Can't wait to see yafaÉ—a da murya.
Habeeb dake gefe yace "Wai me kake faÉ—a ne Ahmad?"
Wallahi ina ganin kamar karya ne wai gobe nida my Teemah a É—aki É—aya kan gado É—aya?
Can't wait to see wallahi cewar Ahmad,
Habeeb ne yaji zuciyarshi tabuga!!!
Yanzu gobe Bintu a É—akin Ahmad zata kwana? Kuma kan gado É—aya?
Dasauri yafara faÉ—in Astaghfurullah Ashe yanzu ita matar wani ne.
Ahmad ne yaga yanayin shi yace "lafiya Habeeb?"
Habeeb yace lafiya lau ba komai
Kai dai kafiye zumuÉ—i,
Ahmad yace ba dole nayi zumuÉ—i ba!
Rabona fa da mace tun muna tare da Bash.
Habeeb ne yayi dariya yatashi yashiga toilet da niyan Alwala.
Beebah ce tacewa su Bintu ku baza kuyi sallah bane?
Bintu tace nifa bana sallah tin jiya!
Fareedah ma tace ita sai jibi zata fara.
Ita kuma Beebah yau period nata yazo!
(Tofa kunga Amare da period ranan biki)
*Washe gari*
Mommyn Habeeb da Mommynsu Ahmad ne suka tarasu babvan falo,
Sukayi musu nasiha me tsima zuciya.
Daga karshe Mommyn Beebah takira dukka Amaren a É—akinta, tayi musu nasiha irin na zaman Aure
Sannan ta basu wasu sirrikan yanda zasubi da mazajensu.
Ta É—auko wasu turare acikin jakanta, tace "ga wannan ku tabbatar sai idan zaku kwanta kafin ku shafa kada ku kuskura kushafa idan zaku fita anguwa"
Turaren matan Aure ne!
Sukace "to"
Suna fita bayan kofa Beebah ta makale ta buÉ—e turaren tashafa kafin ta rufe tafita.
Taje tasamu kowa yahaÉ—a kayanshi, musu suke, wai mommynsu Ahmad tace a motar haya zata tafi bazata bi motar mijin kowa ba!
Sunyi sunyi tabisu amotar Ahmad taki,
Haka suka hakura, kowacce tashiga motar mijinta
Suka É—au hanyar Kaduna garin gomna.
Bintu ce take kukan rabuwa da mommy acikin motar,
Ahmad juyawa yake yana kallon yanda tarufe ido tana zuba kuka kamar karamar yarinya.
A hankali yarike hanunta me laushi da tsantsi yafara wasa dashi,
Ta sauke ajiyar zuciya jin hanunshi cikin nata yana murzawa!
"Beebah kuwa uwar kauÉ—i, tana shiga Abdul yazuba mata ido Yana kallonta, jin kamshin turaren data shafa yasashi lumshe ido.
Tazauna agefenshi kamar mutuniyar kirki,
Yace matso!
Tayi shiru tana kallonshi, gashi Idonshi arufe amna yana mata magana.
Yasake cewa matso mana
A hankali ta matso wajenshi
Yarike hanunta yace "wani irin turare kika shafa?"
Tace "turare nane"
Yace ban yadda ba! KifaÉ—amin gaskiya,
Tace gaskiya nafaÉ—a maka,
Yace "ok".
"Fareedah kuma tana shiga motar
Ta sunkutar da kanta tana wasa da yatsun hannunta,
Habeeb yace "kisaki jikinki ni mijinki ne"
âœÂï¸Â🗒︠*Jidda S Mapi*
[6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*Jiddah S Mapi*
_Dedicated to all my fans_
*WATTPAD*
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرØÂمنالرØÂيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœÂðŸÂ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ÂðŸÂ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Godiya dubu ga masoyana masu bibiyar littafin Agidanmu Take!!! Banso labarin tazo muku a short story ba! Amma ya na iya Haka Allah yatsara, nagode da nuna soyayyarku gareni, banyi tsammanin first Novel É—ina zan samu masoya har haka ba! Sai gashi Allah yasa nasamu, alhmdllh ina godiya gareshi sannan ina godiya gareku*
*Special thanks to mrs sardauna bazan manta dake ba!*
*godiya ga Eeshart tnx for your comment i really appreciate*
*Bazan manta dakai ba! Aliyu Ibrahim*
*Much love to my Sister walidation S Mapi*
*Ina miƙa gaisuwata da kuma godiyata ga ɗaukakin jama'ar kungiyar KAINUWA dashen Allah*
*kuna raina kanne na! Walidation S Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil*
*Godiya ga É—aukakin jama'ar group na Agidanmu Take!!! Bazan manta da kuba!*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.