Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 28

Page 7&8

A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi

Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani

Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar

'Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai 'yan biyun da Sam basa Kama da juna?"

"meyasa ku mutane
Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza'a taba cewa ke kika hada ba" saikuma tsaya

"Gsky bana son irin wannan tambayar"

Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba

"Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba...." inji Nabeela

"Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana" hajiya ta mayar mata

"Bintu wuce mutafi"
Tafada cikin bacin rai

"To mommy" cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma É—aga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta

*AHMAD*

Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru

"Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame" inji Habeeb

"Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah" inji Ahmad

"Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta" inji Habeeb

"Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe"

Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace

Beebah bataga fuskar tambaya ba

Sai takarasa wajen Bintu tace "Bintu yanaga ran mommy a bace"

"babu komai sis" inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata É—auka da sauki

"Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace"

"Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu

"Ko zaki dake nine to?" cewar Beebah

"Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan" Bintu ta mayar mata

"Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa" inji mommy

Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi Æ´an mintuna ba

"Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo" cewar mommy

"Yee mommy dagaske kik?"cewar beebah

"Dama nataba miki karyane?"

Nan wayan mommy yafara ringing

"Yawwa ga shima yana Kira"

amsawa tayi takara a kunnenta

"Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben" saikuma ta kashe wayar

"Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo" mommy tafaÉ—a musu

"Kai amma naji haushi mommy" cewar beebah

Mommy tace "Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu'a Allah yakawo shi lafiya"

"Ameen" cewar bintu

_See me next page_

_wattpad_
Jiddahpretty
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story by_
jiddah S mapi

_dedicated to fateemah sardauna_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.