Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 28

Page 47&48

"Ahmad gudu yake akan titi kamar zai tashi sama, Abdul ne yayi mishi magana yace, haba Dude wannan wani irin gudu kakeyi? Baka tsoron muyi hatsari? Ko kuma mu bugu da bishiya? Shiru Ahmad yayi mishi,
ganin haka yasa Abdul yaja bakinshi yayi shiru, sabida yasan halin abokinnashi"

Bintu kuwa acikin zuciyarta haushin wanda yake tuka motar takeji, mutuminnan wani irin mugu ne? Yana gani muna cikin motar amma yake irin wannan gudun? Duk yanda akayi wannan baisan darajar mutum ba, mugu azzalimi, duk acikin zuciyarta take wannan maganar.

Beebah kuwa duk gudun da akeyi batama saniba sabida hankalinta duk ta tattarashi akan Ahmad, gayen yamatuƙar tafiya da imaninta,
Haka har sukayi parking awani waje me kyau, saman wajen an rubuta "Adamawa special photos" Ahmad yanayin parking ya buÉ—e motar yafita ko juya bayanshi baiyi ba, yana fita su Bintu ma suka fito, dukansu suka shiga cikin É—akin da ake É—aukan hoto, suna zuwa sukayiwa me hoton bayanin yanda akayi, yace musu ba matsala za'asan yanda za'ayi.

Duk maganar dasukeyi Ahmad ya sunkuyar da kanshi baya kallon kowa, har suka shirya dukansu, Bintu da Beebah sunsa anko na riga da skirt atamfa suka É—aura kansu, sunyi kyau bana wasa ba,

Me hotone yafara É—aukansu hoto, dukansu, idan An É—auka É—aya saisu janza kaya.

An É—auki Beebah da Ahmad tarike wuyanshi, sai kuma akace za'a É—auki Bintu da Ahmad.

Ahmad yana zaune akan kujera tunda aka fara É—aukan hoton bai É—aga kanshi yakallesu ba, saidai yakalli me É—aukan hoton,
Bintu ce zasu É—au hoto da Ahmad sai me hoton yace saikin rike wuyanshi idan har kunaso kar mutane sugane, Bintu ce taÉ—an sunkuyo kaÉ—an tarike wuyan Ahmad, jikinsu ne yayi shocking atake! Bintu tasake shi da sauri tayi baya, shima Ahmad yaji wani shocking ajikinshi harya kusa faÉ—owa kasa.

"Me hoton ne yace ku muke jirafa".

Bintu ta iso wajen jiki amace tarike wuyan Ahmad aka É—aukesu hoto, ana gama É—auka suka tara kayansu aka tura musu hotunan awaya.

A hanyansu ne nakomawa gida motarsu tasamu matsala, Ahmad ne yace duk su fito, Beebah uwar kauÉ—i itace tafara fitowa daga motar, sai Abdul yabi bayanta, sai Bintu ce karshe,
Ahmad ne yace wata tabamu É—ankwalinta mana zamusa awani waje. Beebah ce tahaÉ—a face alamun koza'a kasheta bazata bada ba! Bintu ce tacire É—an kwalin kanta ta mika mishi tace gashi.

Ahmad Azuciyarshi yace ashe tanada hakuri bara kawai mu gaisa da ita, É—ago kanshi yayi dan su gaisa saiyaga ta sunkuyar da kanta tana gyara gyellen ta, sai kawai yaÉ—auke kai, ita kuma tana Gama gyaran gyalle tajuya zata kalleshi taga ya É—auke, saita basar,
Ahmad kuma tin É—azu addu'a yake acikin zuciyarshi domin tin jiya yakejin tsinkewar zuciya.

Bintu ce ta É—ago kanta tanason yiwa Beebah magana daidai lokacin Ahmad ma yaÉ—ago kanshi.

Suna haÉ—a ido, Bintu tafara jujjuya ido alamun akwai matsala, Ahmad ne yafara ja da baya yana nuna Bintu, ita kuma Bintu ta tsala ihu tace "ku taimakeni zai kashe ni" Abdul ne yariketa da karfi yana tambayanta meya faru?

Ta juya da karfi tafara gudu akan titi tana ihun ataimaketa, Abdul da Beebah ma suka rufa mata baya suna binta da gudu,
Ahmad kuma ya bushe awajen sai nuna waje É—aya yake da yatsa!

Gudu take Akan titi bata lura da yanda motoci suke wucewa.
Abdul da Beebah sai binta suke suna kiran sunanta Bintu!!! Bintu!!! Bintuu!!!

daidai wani dutse bintu tafaÉ—i kasa sabida ta gaji, tana faÉ—uwa kanta ya bugu da dutse atake kan yafara jini,
Daidai lokacin Abdul da Beebah suka iso wajen, suna zuwa Abdul ya ɗauketa yatare Napep yace Asibitin specialist, suka shiga me Napep yakaisu. Suna zuwa aka karɓi Bintu akayi Emergency Room da ita.

_Ahmad_
Shikuma Ahmad yakai minti talatin hanunshi asama yana nuna waje É—aya, bakinshi kuma yana rawa kamar mejin sanyi, saida yaÉ—an fara dawowa natsuwarshi kafin ya buÉ—e mota yakama hanyan Kaduna, ko waiwayar Adamawa be karayi ba!

"Abdul ne yaje gidansu Bintu yafaÉ—awa mommy abinda yake faruwa, aruÉ—e mommy tafito tashiga motar suka nufi Asibitin".

_Bintu_
Bata dawo hankalinta ba har yanzu likitocine akanta,
Beebah kuwa sai kuka take kamar ranta zai fita, Azuciyarta kuma tana Addu'an Allah yasa ba Aljanu bane suka shafi Bintu,
Domin ita tana matsifar tsoron me Aljanu.

_Ahmad_
Allah Allah yake yakarasa garin Kaduna, yama rasa me zai fara tinani a halin yanzu? Fateemahn shi yagani ko kuma idonshi ne yake mishi gizo? To Amma idan Fateemah ce ai zatayi mishi magana, to amma ita wannan tagudu, anya itace Fateemahn shi? Kodai kamane kawai? Komadai menene idan naÉ—auko Mommy da Fareedah zasu san komai,
Yanata magana shi kaɗai kamar taɓaɓɓe, idan yatuna yanda tarike wuyanshi sai yayi murmushi....

✍️🗒 *Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

*Dedicated to my love*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.