Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 28

Page 11&12

Wow nice name inji Fareedah,

Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce, gata fara ga ido wow.

Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin karɓa ba?

Tace "banada bukatar kudinne shiyasa, duk abunda nake so mama tana bani.

"To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah"

Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki, ba abun yacewa Daddy ze tafi ba, se harara yake ta bankawa yarinyan. Gani yake kamar ita take kara delaying nasu.

Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan, ta girgiza kai tace "aa nagode abawa sauran"

Kikarɓa ni na baki ay, a hankali tasa hanu ta karba tace"nagode Allah yasaka da alheri" Ameen
*************

Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata.

To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah, har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah! ba batajin dadi a ranta, sunyi muguwar shakuwa da Fateemah..

Ta ɓangaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu, mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taɓa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina.

Abun yana taɓa zuciyar Mariya taya za'ace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan?

yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu, yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta.

To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah

A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad

"Wai kai son yaushe ne zakayi Aure? Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama.

Ba tambayanka nake ba?. Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura.

Mommy tace "udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishi"Fareedah tace "yess mommy nizan nema mishi ma dakaina.

Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt

Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba!

Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa tace"ina Fateema? "

Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin É—azu taki amata allura.

A wana É—aki take? cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar? muje nakaiki cewar wata yarinya

Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi

Da gudu tafita tana kiran mommy!

Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu, tafara tambaya lafiya?

Fareedah batayi magana ba se nuna daki take!

Mommy tace kiyi magana, dakyar tace Fateemah, wace Fateeman? Cewar Daddy.....

Nan suka shiga dakin da gudu. Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu

Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya

Ya dago kanshi yace ke me haka? Kinata kiran sunana kamar wani sa'anki

"Yaya wai kaje inji mommy"
Yaja wata doguwar tsaki yace muje

Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti😳

Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta? Dubi jikinta fa duk datti....... Zaka dauketa ne ko sai ranka ya ɓaci cewar daddy.

A hankali yaÉ—auketa yana yatsina fuska

Yariketa kamar kashi ya É—auka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi.

Har saida kanta ya bugu

Daddy yace shiga mutafi, dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni.

Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu

A haka har suka iso specialist hospital. Suna zuwa ba ɓata lokaci aka karbesu

Likitoci suka shiga ciki da ita, Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na karɓi sako, babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi, baka da imani ne?

Ahmad ya haÉ—a rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me haÉ—i na da ita da za'a hanani yin uzirina akanta? Yarinya kucaka ma da ita

Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai.

Alh kabeer yace to, nan yashiga ciki, doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo? Alhkabeer yace eh nine

Ok amma kasan da ciwon dayake daminta? Yace Aa

Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar 'yarka tana cikin matsala

"Ka taɓa zama da ita ka tambayi matsalarta? Daddy yace Aa

Tofa akwai babbar matsala! Am sorry to say, 'yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci.

✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI*
[6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to my lovly sister @walidation_

_✅ote me on_ _wattpad Jiddahpretty_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.