A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 28
Page 13&14
"Alh 'yarka tana cikin matsala" zai fi maka sauki ka kirata ka lallaɓata, ta faɗa maka meke damunta, sabida hakki ne a kanka.
To fa nan Daddy yafara share zufa, yanason yace ba 'yarshi bace, amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci.
"Yace toh doctor nagode" yanzu ya ake ciki? Doctor yace "a halin yanzu de an É—aura mata ruwa, saura na rubuta muku magungunan da zaku saya"
Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya, yana ta tsaki wannan wani irin abune? Bamu santa ba! Ba dangi ba! Ba 'yan uwa ba! Amma ahanani yin komai chewww....
Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi.
"Dan Allah karka dame ni Bash, ka kyaleni na huta wannan wana irin Bala'i ne?" naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka? ÆŠittt ya kashe wayar.
Zo nan my son! "To"
Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin, to Daddy ya karɓi papern yana tafiya yana tsaki.
Fareedah kuwa takasa zama, da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata? tin suna amsawa har sukayi shiru
*****************
Da ahmad yakawo maganin suka É—unguma gaba É—aya suka shiga É—akin, suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfaÉ—o, Fareedah tayi gudu ta rungumeta.
"Ita kuma Fateemah ta lumshe ido"
Ahmad kuwa yau kamar ido ya faÉ—o tsabar harara *nace oho de*
Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace "da sauki" tom Allah yakara sauki tace "Ameen"
Daddy Yace idan kika É—an samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce, tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita.
A take Ahmad ya É—ago kanshi yana kallon Daddy, yace "Daddy wani gida zata wuce? "
Wani gida kake ciki? Cewar Daddy, nan yai shiru yana kallonsu.
*************
Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace "Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaÉ—awa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki", to Daddy.
Mommy tace "Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare", ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida, to Daddy
Da kyar Fateemah take tafiya, sabida tanajin jiki. Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali.
Bayan sun É—au hanya suna tafiya ne "Fateemah tafarajin Amai,
A hankali tace inajin Amai!
Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai, yai shiru kamar bai jita ba, ta sake cewa "yaya Amai takeji", nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake.
Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe, tofah nan yaja birki ya tsaya.
Yace "fitah" sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita, ya sake cewa "nace kufita"
Fareedah tace "haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama".
Zaku fitane ko sai na ÆÂata muku rai, ya daka musu tsawa!!.
Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama, da kyar Fareedah ta riketa suka fita, suna fita a motar Fateemah ta faÉ—i dan bata da karfi ko kaÉ—an.
Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen
_wattpad_
Jiddahpretty
âœÂï¸Â🗒︠*jiddah S mapi*
[6/23, 12:46 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*jiddah S mapi*
_Dedicated to my lovely sister walidation_
✅ote me on wattpad
*Jiddahpretty*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.