A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 28
Page 25&26
"Bayan wasu lokutane Mommy ta É—ago kanta tace da yayi Aure dayafi dai Habeeb wata kila ta yafe mishi idan taga yayi Auren, musamman idan yaje mata da jika, (toh fa kunji mommy da zance) Habeeb yace ok mommy baradai nagwada yi mishi maganan ko zai yadda, to Amma mommy idan ya yadda wa zai Aura sabida kinsan bashi da budurwa! Mom tayi shiru daga baya ta nisa tace ga Habeeba saina bashi ita ya Aura! Habeeba tayi shiru atake zuciyarta ta tsinke!!! To Shikenan mom bara zanyi mishi maganan anjima inji Habeeb "
Ahmad yana kwance ciwon ciki ya dameshi yasha magani ma ba sauki da kyar ya É—au wayarshi yakira abokinshi Bash,
Hello Bash dan Allah kana inane? Bash yace kanada matsala ne? Ahmad yace eh akwai matsala ok kana wani club ne? Bash bana club Ina gidana na anguwar sarki kazo ka sameni ok,
Bayan wasu mintuna saiga Bash.
"Bash yana shiga ɗakin yaga Ahmad a kwance yanata murkususu, ya ƙarata ɗakin da gudu yana tambayan Ahmad meya faru? Ahmad baya iya ko magana sai rike maranshi dayake, Meya sameka A hankali yace cikina! Bash yayi shiru yana tinani can yace "Haba gaye meyasa zaka cutar da kanka ga 'yammata a club kala kala ya zaka zauna da ciwon ciki kamar mace? Haba mana gaye karka bada ni mana" Aa Bash nadaina bazan sake kusantar wata mace ba a duniya, na riga nayi Alkawari idan ba my Teemah ba saide ciwon cikin yakasheni, to Amma ai saika ɗan sha ko kwalba ɗayane inji Bash, Ahmad yace nasha nasha banga anfaninshi ba sai ma ƙaramin cuta dayake, to Shikenan saika kashe kanka.
Yanzu me kake so Nayi maka? Ahmad yace mommy zaka kiramin awayarka inason naji muryarta dana Fareedah, Bash yayi shiru dan ya tuna Mommy tahanashi tafiya da Ahmad idan tagansu tarema hararanshi takeyi Mommy taki jininshi, amma bari dai ya gwada.
Yacewa Ahmad bani numbanta Ahmad yamishi nuni da wayarshi Bash ya É—auko wayar yaÉ—au numban Mommy yakira ta, da farko kamar baza'a É—aga kiranba sai daga baya aka É—aga.
mommy tace hello, ba'ayi magana ba! Tanata hello hello anyi shiru, Bash yakasa magana, sai can yace hello momsy ya gida? Mommy tayi shiru tsabar taƙaici tarasa me zatace mishi, dan tagane muryanshi, azuciyarta tace wannan Bash ɗin da kanshi kamar sandan mopping sainayi maganinshi,
Tace meke tafe dakai? Yace am dama momsy Ahmad ne..... Mommy tace dakata banason shashanci komai Ahmad yayi a duniyarnan dasa hannunku aciki sabida ku abokanshi ne, ku kuke bashi shawara mara kyau, mom tafashe da kuka tace Allah ya isa tsakanina daku Bashir, kun ɓatawa ɗana rayuwa nabarku dashi nikam na yafe Ahmad duniya da lahira, kuma idan kasake kirana to hukuma ne zasu rabamu dakai.
Mommy takashe wayar tana kuka me cin rai.
"Bash yayi shiru yana kallon Ahmad, wanda yake ta kukan dana sani, Yace haba gaye ya zaka tsaya kana kuka akan maganar tsohuwa kasanfa tsofinnan surutun bala'i ne dasu ka manta kawai kaÉ—ansha ko kwalba É—aya ne, idan babu kuma a frij É—in zan iya saya maka da kuÉ—ina"
*note*
(ana cewa aboki baya É“ata aboki, wannan magana ba gaskiya bace wani abokin ma ze iya kashe ko nawa ne dan ganin kaima ka É“ata rayuwarka kun zama daidai akiyaye abokai da bakai ba gindi ko kawayen dabasu da natsuwa Allah yatsaremu AmeenðŸ™Â)
Ahmad yace Aa akwai a frij ɗaukomin kwalba ɗaya, da Bash yaga Ahmad ya shanye kwalban giya me tsada ɗaya sai ya ƙara ɗauko waniyabashi haka Ahmad yayi ta ɗurawa har bacci yaɗaukeshi.
Da Bash yaga Ahmad yayi bacci saiya fita a É—akin yakira numban wata yace hello polinah kina inane? Ok kizo anguwar sarki yanzu kisame ni yabata numban gidan.
Polinah wata sheɗaniyar yarinya ce wanda ta ƙware a bariki, sau da dama Bash yanayiwa Ahmad tallanta amma yaki, itama polinah tanason Ahmad sosai kamar ranta, yau ta samu dama.
âœÂï¸Â🗒︠*jiddah S mapi*
[6/23, 12:48 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_Story/written by_
*jiddah S Mapi*
_Dedicated to my lovly friend *ELHAM*_
*KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION*
{United we stand and succed, our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.