Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 28

Page 37&38

"Abdul ya saki baki yana kallon Beebah a Azuciyarshi yace wataƙila ma sabon salon iskancine takoya zatayi mishi, taƙara cewa ina wuni yaya Abdul, Abdul yace lafiya kanwar Habeeb ya kike ya gida? Tace lafiya lau yaya, Yace ina zuwa haka? Beebah tace Mommy ce ta aikeni G.R.A zan kai aika, yace ok dama nima tafiya zanyi me zai hana na sauƙe ki acan? Tace tom nagode,
Abdul sukayi sallama da Bintu yashiga motar Beebah ma tashiga suka tafi"

A hanya Abdul yake tambayar Beebah yace
"ƙanwar Habeeb meyasa kika sauya alokaci ƙanƙani? " Beebah tanason tayi mishi rashin mutunci Amma tana tsoron karya faɗawa Bintu takara shan dukan mutuwa.

Tace mishi babu komai

yace "ok"

yaje ya ajeta a G.R.A yayi tafiyarsa.

_Ahmad_

"A kwana biyun da Habeeb yazo wajenshi yaɗan samu sauƙin abunda yake daminshi, Amma har yanzu bai dawo daidai ba, yau yaɗan buɗe data yace bazi yaɗan ganin Abunda yake tafiya a social media, yana buɗe datan yaɗan aje wayar sabida messages ɗin sugama shigowa, bayan wasu 'yan mintuna yaɗauki wayar yana duba messages na abokai da kuma 'yan uwanshi saiya shiga message na Abdul wanda yaga hotone yatura mishi, yana buɗewa yaga hoton wata faran yarinya doguwa tsiririya ta rufe fuskanta tana dariya da Alama batason hotonne aka ɗauketa,
Duk yanda yaso yaga fuskarta yakasa"

YabuÉ—e voice chat É—in da Abdul yayi mishi yaji Abdul yace "dude ga hoton matana danake Auran" Ahmad yayi mishi reply da Allah yasa ka Aureta dude, yatura mishi.

_Bintu_

"A duniya ba abinda takeso sama da Mommy dakuma Abdul yanzu har maganan Aure yashiga, domin Abdul yaturo iyayenshi anyi magana,
ansa rana,
wata biyu masu zuwa, idan an É—aura Aure kuma a kaduna zasu zauna".
*************

"Yau Da daddare mommy tashiga ɗakin Habeeb Tanason tambayarshi maganin ciwon kai, Amma me? Tana zuwa ɗakin taga Habeeb yarungume hoto yana kuka Kamar ƙaramin yaro, be maji shigowarta ba!

"A hankali tajuya tafita a ɗakin ta tsaya a window tana leƙanshi, sai kuka yake harda sheshsheƙah, yana kukan yatashi yaje wajen kayanshi, ya ɗauko wani frame pink colour me kyau yasa hoton aciki ya buɗe kayanshi yasa frame ɗin ya fesawa kayan turare ya juya yashiga toilet".

Mommy tana tsaye tana kallon ikon Allah, nan ta tuna wata rana datazo takamashi yana kallon hoto, yana ganinta yayi sauri ya ɓoye hoton abayanshi,

Mommy tagaza ganewa Habeeb wani irin mutum ne? Idan tace ya kawo matar daze Aura sai yace mata "A GIDANMU TAKE" tarasa gane me kalman yake nufi.
Amma koba komai yau saitaga hoton dayake ɓoyewa ko ta halin ƙaƙa!
Tajuya tayi tafiyarta takoma falo.

Habeeb yana shiga toilet ya wanke fuskarshi yayi alwala yazo yayi sallah, yana idarwa yatafi falon mommy yana zuwa yatarar da ita da 'yan biyunta suna hira, yafara murmushi yace kaga Mommy da 'yan biyunta, mommy tace eh wallahi Habeeb Amma meya sameka naga kamar kayi kuka? Habeeb yace wallahi mommy yau bacci nayi tayi, Mommy tace ok.

"Da safe Mommy takira Habeeb awaya tace yazo falo zata aikeshi, Habeeb yana zuwa
Mommy tace GRA zakaje ka karɓomin saƙo yace tom Mommy, Habeeb yana fita agidan Mommy taje ɗakinshi ta buɗe kayanshi daidai inda taga jiya ya ajiye hoton,
Tana ganin hoton ta É—auka ta tafi É—akinta dashi, tana zuwa É—aki ta buÉ—e frame É—in.

Ta É—auko hoton tana gani.

Amma me? Tana kallon hoton jikinta yafara rawa hanunta yakasa rike hoton kawai sai hoton yafaÉ—i.
itama tabi bayan hoton a sume...

*Share, vote and comment🙏🏻*

✍️🗒️ *jiddah S mapi*
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to My love_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_jiddah S mapi_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.