A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 28
Page 17&18
"Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka karɓe ta sai Emergency Room",
Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin.
Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka,
Dahaka har likita yafito daga ɗakin yacewa Daddy yana buƙatar magana dashi,
Daddy yace to.
"Bayan yashiga ɗakinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da 'yarka to kayi mata Aure, kaga idan har agidan miji take bazata rinƙa yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba.
Daddy yayi shiru yana tinani, se daga baya yace to nagode Doctor.
Doctor yace "yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya tafiya"
Bayan an sallamesu ne suka koma gida,
Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace,
Yace "Mariya bakya ganin kawai mu haÉ—a Auren Fateemah da Ahmad?
Tunda mun yadda da tarbiyanta,
To Alhaji ne dai banƙi ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga haƙƙin yarinya marainiya,
Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu,
Haba Mariya shi Ahmad É—in ba haifanshi akayi ba?
Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi.
To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya.
Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad, suma kansu basu sani ba! ********************
Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan juma'a wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad,
Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta guÉ—a. Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai,
Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu, inda suketa shaye shayensu,
Bayan juma'a aka É—aura Auren Fateemah da Ahmad, akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya,
Se dare Ahmad yadawo gida,
Daddy ya kira wayanshi yace "kasameni a falo"
Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah,
Bayan sun hallara a falonne,
Alh Kabeer yayi gyaran murya yace
"Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan, to yau Aure aka É—aura,
Auren Fateemah da Ahmad".
A razane Ahmad yaÉ—ago kanshi yana kallon Daddy,
Ya buɗa baki zaiyi magana Daddy ya ɗaga hannu yace "Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaƙanta ta"
Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka,
Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu,
Yace zaku iya tafiya.
"Tofah dahaka suka wuce É—aki kowa jikinshi a mace,
Ita kuma Fareedah murna take kamar me, suna shiga É—akin ta rungume Fateemah tana ta tsalle, ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi,
Dahaka Fareedah tafara haÉ—a mata kayanta tana cewa gobe a É—akin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you,
Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba? ,
Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci"
Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan,
Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya,
Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini.
"Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa,
Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah,
idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwaÉ—o kuma yace idan ta faÉ—a saiya kasheta,
Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira,
Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan"
"Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi, babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi, tanason tafaÉ—a ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaÉ—a wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta!"
Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali.
Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangaÉ—i,
Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki,
Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene, Fateemah tayi saurin katseta.
Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo,
Tana leƙa ɗakinshi taga ya kwanta rub da ciki.
Ai kuwa tarufeshi a,
Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa.
"Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a É—aki, haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara É—aukanta, amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah!
Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana buÉ—e kofan yaji gumm!
Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira,
Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru.
Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta buÉ—e kofan,
Wato raini yafara shiga takaninsu kenan!
tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani,
Tana zuwa taga kofanshi a rufe, taɗan buga ƙofan kaɗan.
Kamar jira yake yace waye tayi shiru, yace oya open the door
Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da rana😳ta zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan buɗe na mantaka ne wallahi,
CabÉ—i ni ta manta?
âœÂï¸Â🗒︠*jiddah S mapi*
[6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*jiddah S mapi*
_Dedicated to my lovely daughter AFRAH_
_✅ote me on wattpad Jiddahpretty_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.