A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 28
Page 51&52
"Washe gari"
Mommy ce tacewa su Beebah sushiga mota zasu koma Gombe, Beebah tace "yanzu mommy kina ganin idan muka bar garinnan ba damuwa? Kituna fa mun saba da mutane anan,
Bakya tunanin muje can mushiga wata rayuwa? "
Mommy ce ta dakatar da ita da hannu tace "Beebah bakisan damuwan dazamu shiga anan idan har muka Zauna yafi nacan bakoh? "
Beebah ce tace "Mommy wace irin damuwa zamu shiga?
Kodan Bintu bata buÉ—i baki tayi magana bane haryanzu?
Mommy kika sani ko iskokai ne suka shafeta?"
Mommy ce tacewa Beebah wannan maganar taki ɓatamin lokaci kawai kike,
Kishiga mota kawai mutafi.
Beebah ce tashiga motar badan taso ba!
Bwyan sun shiga mota gaba É—ayansu,
Driver yaÉ—auki hanyar barin garin Adamawa,
Beebah kuka takeyi sabida ko sallama basuyi da kawayenta ba,
Mommy ce take bata hakuri tana lallashinta har tayi shiru.
_Ahmad_
Suna idar da sallahn Asuba suka kama hanyan Adamawa,
Amma mommy tace subi flight na safe,
Suna zuwa Airport, daidai lokacin da aka fara sanarwa ashirya jirgi zai tashi,
Daidai lokacin Ahmad ya tuna cewar ya manta wayarshi agida.
Kuma bai kashe ba!
Yacewa Mommy "mom inason in koma gida na manta wayana"
Mommy tace haba Ahmad baka ganin jirgi zai tashi yanzu ne?
Yace mommy matsalar ay wayar ba'a kashe ba!
Za'ayi ta kirana aji switch off,
Mommy tace kodai karya kayimin ne Ahmad?
Yace haba mommy taya za'ayi nayi miki karya,
Mutafi ma kawai,
Haka suka shiga jirgi sukayi tafiyarsu.
_Adamawa_
Sauri suke suga sun bar gari yola, daidai zasu fita a fire away from yola, Habeeb yacewa mommy,
"Mom munyi babban mantuwa"
Mommy tace me muka manta?
Yace mommy mun manta da Abdul, baizo yabamu takaddan sakin Bintu ba!
Mommy kar mubar garinnan da Aure akanta,
Mommy tace hakane fa kuma, yanzu kiramin shi awaya ka tambayeshi ina yake,
Habeeb yaciro waya yakira Abdul,
Yacewa Abdul ina kake?
Abdul yace ina Airport,
Habeeb yace me kakeyi a Airport?
Ina jiransu Ahmad ne yau zasuzo, ok gashima sun karaso.
Ok idan kaÉ—aukesu kasamemu a fire away mana akwai wata muhimmiyar magana dazamuyi,
Abdul yace to bari sai nazo.
Ba'a daÉ—e dayin wayar Abdul da Habeeb ba, saiga su Ahmad sun karaso,
Abdul ne yaÉ—aukesu amotershi, yace musu suyi hakuri zasu biya ta Fire away kafin su dawo
Su Ahmad sukace ba komai,
Ahmad ne yacewa Abdul idan mun dawo gidansu Bintu zaka kaimu,
Abdul yayi mamaki sosai, ganin Ahmad dasu mom nashi sunzo wai yakaisu gidansu Bintu,
Gashi abunda yafaru jiya.
Sai kawai ya kawar da zancen.
_Bintu_
Ita tarasa waÉ—annan wasu mutane ne? Tin jiya a asibiti sukeyi mata magana,
Ita bata sansu ba!
Hasali ma tanason ta tambayesu meya kawota nan?
Wannan wani gari ne? Amma takasa Tambaya,
Dataga sun shiga mota zasu tafi wani gari, azuciyarta tace Alhmdllh zasu kaini garina, may be ma satoni sukayi,
Da Wannan tinani taji karan tsaiwar mota.
Tana juya baya taga wani mutum yafito daga wajen zaman driver,
Daga baya taga an buÉ—ewa wata
Mezata gani? Sai taga mommy tafito a motar, daga baya saiga Fareedah.
Bubbuga motar datake ciki tafara Alamun tanason tafita.
_Not Edited_
_✅ote & comment pls_
âœÂï¸Â🗒︠*Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*Jiddah S Mapi*
_Dedicated to my fans_
*بسم الله الرØÂمنالرØÂيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœÂðŸÂ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ÂðŸÂ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.