Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 28

Page 23&24

"Beebah ta buÉ—e data ta turawa Habeeb hotonan su da videos É—in dasukayi, habeeb yana ganin videon yace mata wow sweet sis kunyi kyau gaskiya tace thank you broh,
Se mangariba dab suka gama partynsu suka raka duk ƙawayensu kowacce tashiga motarta suka tafi, Bintu ce ta kwashe musu gift dasuka samu daga wajen ƙawayensu tashiga musu falon mommy dashi".

Ahmad yau ya tashi da tsananin ciqon kai inda yayi ta birgima yana riƙe da kanshi, dakyar yasamu yasha magani yaɗan samu sauƙi, ya zauna a gefen gado yana tinani azuciyarshi yace "da ace my teemah tana nan data bani magani da kanta nasha, komai nayi mata zatayi hakuri dani wayyo my teemah ina kike dan Allah ki bayyana min kanki nasan kina raye baki mutu ba! Ki fito dan Allah naganki zan nuna miki soyayyar dabaki taɓa jin labarinshi ba ko a Novel.

Haka ya karashe tunanin shi ya tashi ya shiga wanka, bayan yafito daga wankane yashafa mayukanshi masu kamshi ya taje gashin kanshi me laushi kamar na indiyawa, ya buÉ—e wardrobe nashi yaÉ—auko wani riga pink colour da bakin wando ya É—auko picap baki yasa ya dubi kanshi a madubi yaga ya rame sai de yayi fari sosai, a hankali ya rufe idonshi yace oh god help me out.

"Habeeb bashi da damuwan daya wuce damuwar abokinshi Ahmad, kullum idan ya zauna sai yayi tagumi yana tinanin ta ina zai fara taimakawa Ahmad, har Mommy tagano yanayin shi da daddare suna zaune a falo suna kallo, Bintu tana É—an danne danne awaya ita kuma Bebbah ta kwantar da kanta akan cinyar Habeeb tana mishi rigima wai sai yayi mata tsifa, Mommy tace Habeeb inason in tambayeka wani Abu mana? Yace to Mom ina jinki Mommy tace meya sameka ne naga tin ranan daka dawo daga Kaduna kashiga damuwa ko wani Abunne yasamu Ahmad? "

Habeeb yace gaskiya mom Ahmad yana cikin matsala nan yafara faɗa mata duk abunda ya faru Amma ya ɓoye mata yanda Ahmad ya yar da Fateemah,
Ba Mommy ba har 'yan biyu saida sukayi hawayen tausayin Ahmad, Mommy tace yanzu shi Ahmad É—in yana ina? Habeeb yace yanzu de yana gidanshi acikin kadunan Amna yace min bazai iya zama a Kaduna ba gaskiya ze tafi Dubai yayi zamanshi acan, Mommy tace to yayi Aure mana wata kila idan ita Hajiya Mariyan taji zata yafe mishi, Habeeb yace gaskiya mom Ahmad A halin yanzu ko yayi Aure to matar daya Auran agaskiya GANGAR JIKINSA TA AURA dan zuciyar Ahmad tana wajen Fateemah

mommy tayi shiru tana tunani......

✍️🗒️ *jiddah S mapi*
[6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S mapi*

_dedicated to Eeshart💕_

*🌈KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION*

_{united We stand and succed; our ambition is to Entertain & motivate the mind of readers}_

*WATTPAD*
@Jiddahpretty

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.