A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 28
Page 45&46
"Mommy ce tayi kan Beebah dagudu tana ihu, ganin haka yasa Bintu tayi sauri ta É—auko goran swan a frij tazo aka shafawa Beebah afuska, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana buÉ—e idonta tafara tambayan Habeeb, yaya me naji kana cewa? Kamar naji kace kanason Hassana kuma da Aure? Kamanta mu 'yan biyu ne da ita? Ko ka manta ciki É—aya muka fito da ita? Allah yasa dai wasa kake, duk tabayoyin datake mishi tanayine cikin hawaye sannan ta Zubawa Habeeb ido,
Mommy tayi shiru tanayi wa Habeeb kallon tuhuma.
Da Habeeb yaga duk shi suke kallo, ciki kuwa hadda Bintu, sai kawai yafara kame kame, yajuya yafita a É—akin.
_Ango_
Abokansa ne suke ta zagin Abu wai an raina musu hankali, yaza'ayi ranar Aure a nemi Amarya arasa, Abdul yatsaya yakasa yin komai sai gyara gari yake tin É—azu da goge zufa,
Yakira numban Bintu yafi sau 20 ba'a É—aga ba! Azuciyarshi yace kodai yaudarana dama takeda niyan yi?
Ahmad ne yadafa kafaɗan Habeeb yace "kadaina tunani dude" insha Allah gobe Zamuje gidansu Amaryar tafaɗa mana meyake faruwa, domin kasan lamarin Aure yanzu, kowa yana kokarin yaga an ɓata,
Abdul ne yace "Haba Ahmad kana gani fa yarinyannan tadinga wulaƙanta ni a idon duniya, Aure wasane? Hakafa ranan kamu ta tafi tabar wajen saida ɗayar 'yan biyunta tazauna awajen, yanzu kowa yazata Beebah ce Matata!... Wani irin magana ne kake faɗa dude? Kana nufin wannan ba itace kake Aura ba? Kuma ai naga pre-wedding pics ɗin da ita akai.
Abdul ne yayi mishi bayanin duk abinda akayi, Ahmad yayi shiru yana tunani can yace "Amma Abdul ka tabka kuskure Babbah! Meya kaika É—aukan hoto da 'yan biyun wacce kake Aura kuma kace Ba itace matarka ba! Kana ganin mutane baza suyi maka mumunan fahimta ba? agaskiya ka aikata Babban kuskure!
Abdul yace "hakika Ahmad na aikata kuskure to amma tayaya zan wanke wannan kuskuren danayi"?
Ahmad yace mafita É—ayane garemu shine kaje gobe ka É—auko matarka koma muje tare, kacewa kanwarta ta É—auko duk kayan da kukayi hotunan dashi saimu tafi tare dukanmu huÉ—u, Ita matarka saitasa kayan da wancan tasa ranar dazakuyi hoton koda shike ai su 'yan biyu ne, bazasu rasa kaya kala É—aya ba,
Idan munje wajen É—aukan hoton, ni saina É—auka da Beebah kai kuma ka É—auka da matarka, sannan muÉ—auka dukanmu huÉ—u, kaga zamu juya kan mutane, ba kowa ne zai gano bakin zaren ba, idan aka tambayeka saikace ai Bintu itace matarka!
Abdul wani sanyi yaji azuciyarshi, yacewa Ahmad to insha Allah haka za'ayi, nagode da wannan shawarar.
Suka sallami abokanansu suka basu hakuri, kowa yawatse.
_washe gari_
Ahmad ne da Habeeb suka buga wanka, sunsa anko gaba ɗayansu shadda ne fari da zubin baƙi, sukasa hula baƙi da takalmi baƙi sai agogo baƙi, bakaramin kyau sukayi ba, suka shiga motar Ahmad baƙi, suka ɗau hanya sai gidansu Bintu.
Suna zuwa Abdul ne yashiga daga ciki dan Ahmad yace shi baze shiga ba! Yana jiransu awaje, Abdul yana shiga ya gaida mommy afalo, mommy take bashi hakuri tace kayi hakuri Abdul wata 'yar matsala aka samu, shiyasa kaga ba'a kai maka Bintu ba! Abdul yace ba komai, mommy ce ta tashi afalon taje takira Bintu aÉ—akinsu, Bintu ce ta tashi tasa dogon riga, gaba É—aya ta rame tin jiya take cikin kuka da tinani tarasa meyake mata daÉ—i.
Goga powder tayiwa fuskarta tasa baƙin kwalli acikin Idonta tayafa baƙin gyale, ta fesa turare ajikinta masu kamshi, tasa flat shoe, duk abinda takeyi Beebah na kallonta tace ko zamuje ku gaisa ne? Beebah tace no, tace dan Allah muje, Beebah data tuna dukan rannan saita diro akan gadon tace bari nasa hijab sai naje mu gaisa.
"Suna zuwa falon Beebah tafara tsayawa abaya baya dan tasan rashin kunyan datai tamishi jiya, shi kuma saiya basar yace ya kike kanwar Habeeb? Beebah tace lafiya ya gajiya? Yace babu,
Abdul ne yayi gyaran murya yace amm Hassana da Hussaina? Sukace na'am yace wata alfarma nazo nema awajenku, duk da Bintu yanzu ita matatace amma dole na nemi alfarma,
Sukace ba matsala kafaÉ—a muji in Zamu iya,
Yace dama inason ku É—ibo kaya waÉ—anda kukayi anko,
da wanda mukayi pre-wedding pics dashi, yanzu zamuje ayi sabon hoton sabida wancan akwai matsala"
"Bintu ce tace ita bazatayi hoto ba! Abdul yadinga haɗata da Allah taki, da Abdul yafusata yace look Bintu karkiga dan inasonki kice zaki wulaƙanta ni, yanzu miji nake awajenki umarni nake baki kitashi ki ɗebo kayanki zamuje ayi sabon hoto! Yafaɗa cikin fushi.
Bintu ce tahaÉ—a rai ta tashi tashiga É—aki ta É—ebo kayan dana Beebah,
Beebah ce takarɓi kayan ta tafi sawa a mota, ita kuma Bintu tashiga cikin ɗakin mommy domin sanar da ita.
_Ahmad_
Shikuma ya zauna yanata jiransu amma har yanzu basu fito ba! Ganin haka yasa yajuya kanshi yadaina kallon kofar gidansu Bintun, dayaji karar buÉ—e kofar saiya juya yaga Beebah ce takesa kayansu aciki, tace ina wuni? Yace lafiya, daga cewa lafiya be kara komai akaiba kuma be sake juya bayanshi ba, yayi readyn jan mota idan sun fito.
Beebah ce tashiga cikin motar tazauna tana kallon side view na Ahmad.
Abdul da Bintu Kuwa sunata rigiman fitowa.
Bintu tace sai Abdul ne zai fara fitowa shikuma Abdul yana tsoron kada yashiga gaba ta gudu, shima yace sai ita zata fara fita.
Da kyar Bintu tayadda tafara fitowa rai aɓace taje ta buɗe motar tashiga wajen da Beebah take.
Shikuma Ahmad ko juyawa ya kallesu baiyi ba, yana ganin Abdul yashiga,
ko gama rufe marfin motan baiyi ba! Yaja motar cikin fishi yafara watsa gudu akan titi....
_✅ote, comment and share plsðŸ™ÂðŸÂ»_
âœÂï¸Â🗒 *Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written by
*Jiddah S Mapi*
_Dedicated to my Facebook fans_
*بسم الله الرØÂمنالرØÂيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœÂðŸÂ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ÂðŸÂ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.