Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 28

Page 49&50

"Mommy suna zuwa Asibiti Beebah ta taso tazo wajenta, mom ce ta tambayeta meya sami Bintu? Beebah tace wallahi mom nima ban sani ba, Amma inada tabbacin Aljanu ne suka shafeta! Mom tace ke Beebah banason iskanci, kifaÉ—amin meya sameta ko kodai wani Abun Abdul yayi mata? Beebah tace wallahi mommy ba abinda aka mata kawai tana ganin Abokin Abdul damukaje É—aukan hoto dashi tafara ihu wai ataimaketa zai kasheta"

Mommy tace ina yake Abokinnashi? Mom tun lokacin data fara ihu yatsaya awajen yana nunata ko magana beyi ba
To mukuma munbita, mun barshi awajen,
Zuciyar mommy ce tayi matsifar tsinkewa!!! Atake ta tsunkuya dan wani hajijiya takeji,
Tacewa Beebah kiramin Abdul yakaini inda kukabar mutumin,
Beebah ce tace tom mommy lafiya?
Mommy tadaka mata tsawa!
Kiramin Abdul nace,
Beebah ce tabar wajen da sauri dan ganin yanayin mommy.

_Ahmad_
Gudu yake akan hanya, burinshi kawai ya iso KD dan jiyake kamar ba mai amotar, dayaga motar bata mishi gudu sai kawai yaÉ—au waya yakira Habeeb, yace mishi dan Allah ka nemamin jirgi yanzunnan, Habeeb ne yace ok kasameni a Airport, Ahmad yajuya motarshi yakoma Adamawa zuwa Airport,
Yana zuwa yatarar da Habeeb harya karɓa mishi pass,
Yamika mishi hannu suka gaisa,
Yace yau ba surutu sauri nake,
Habeeb abun yabashi mamaki taya za'ayi Ahmad yayi sauri haka? Duk yanda akayi akwai matsala.
Mangariba cif yashiga garin KD,
Yana sauka a Airport yafita da sauri yatari Napep,
Yawuce sai gidan Mommynshi,
Yana zuwa me gadi yahanashi shiga,
Yarokeshi, megadin yace bazan yadda na rasa aikina ba Ahmad! Hajiya tace duk ranan dakazo nabuÉ—e maka kofa abakin Aikina,
Amma Alfarma É—aya zanyi maka
Shine kazauna anan yanzu Fareedah zatazo dan hajiya ta aiketa,
Idan tadawo saika faÉ—a mata sakonka..

Be gama magana ba, saiga motar Fareedah ta kunno kai,
Tana ganin Ahmad ta É—auke kanta tana kokarin shiga gida,
Ahmad ne yayi mata Alama da hannu, yahaÉ—a hannunshi waje É—aya Alaman yana neman Alfarma,
Hakika Fareedah taji tausayin Ahmad yau, ganin duk yanda yabi ya rame yayi baƙi kamar bashi ba!

Saita buÉ—e mishi É—ayar kofar tayi mishi Alama dayazo,
Ahmad ne yasauke ajiyar zuciya,
Yatashi yaje yashiga motar,
Yana shiga megadi yabuÉ—e mata get tawuce ciki,
Acikin gida ta tarar da mommy tana zaune tayi tagumi kamar kullum.
Tana fita amotar tabuÉ—ewa Ahmad shima yafito.

Mommy kamar daga sama taga Ahmad acikin gidanta kuma amotar Fareedah,
Tashi tayi ta iso inda suke,
Tana zuwa ta fesawa Fareedah mari har guda uku, kana tace
"Fareedah bakida hankaline? Kokin manta me nace miki? Ko kin fini son Ahmad É—inne? "

Fareedah tayi shiru.

Ahmad ne duk jikinshi yayi sanyi,
Har yayi dana sanin zuwa,
Yatsuguna kasa zai fara magana mommy tace idan kasake kace uffan Allah ya isa!
Fita kabarmin gida,
Ahmad ne yafara kuka yace "Mommy nayadda zan fita nabar miki gidanki, Amma ina neman wata Alfarma? "

Mommy tace "Banason jin komai daga Bakinka Ahmad kaficemin agida"
Wannan karon Fareedah ma tasa baki a rokon mommy,
Fareedah kuka Ahmad kuka,
Kuma dukansu a tsunkuye suke,
Mommy ce taga sun mugun bata tausayi, sai kawai itama tafashe da kuka ta tsunkuya tarike hanunsu ta É—agasu ta rungume,
Ahmad yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya,
Rabonshi dayaji É—umin jikin mommy tin lokacin da Daddy yarasu,
Sun kai minti talatin ahaka kafin mommy tace kafaÉ—amin abinda yake daminka Ahmad?

Ahmad ne yace "Mommy naga Bintu a Adamawa"

Mommy ce tayi saurin rufe bakinshi da hannunta,
Tace shiiii banason karya, karkayimin karya don kanason in soka,
Ahmad yace mommy na rantse da Allah Bintu nagani, harda goshin sallahn ta

Mommy tayi shiru, taya za'ace wanda yamutu ya dawo?
Kodai Ahmad yasamu taɓin Hankali ne sanadin shaye shaye?

Can tace idan har da gaske kake gobe zamuje Adamawan in tabbatar,
Idan naje kuma naga karya kakemin, tofa bani bakai Ahmad,
Yace mommy nayadda idan ba ita bace Karki kara yimin magana
Kuma nima bazan sake zuwa inda kike ba! Fareedah tazama shaida.

Mommy tayadda da sharuÉ—anshi sukasa niyyan gobe da safe zasu tafi Adamawa.
******

Mommy sunje wajen dasu Beebah sukabar Ahmad Amma basu ganshi ba!
Mommy taruÉ—e tafita a hayyacinta,
Da kyar suka kama hanya suka tafi Asibiti,
Suna zuwa daidai Lokacin Bintu ta farfaÉ—o.
Amma wani ikon Allah sai kallonsu take kamar bata sansu ba!
Idan sunyi mata magana saita fara kuka,
Likita ne yace sun duba sunga ba wani matsala zasu iya tafiya gida.

Suna zuwa gida mommy takira Habeeb É—akinta,
Tacewa Habeeb

"gobe zamubar garinnan"

Kakiramin Abdul yazo muyi magana.

Habeeb ya ruÉ—e yace, Mommy meyasa zamubar garinnan? bayan nanne mahaifarmu?
Mommy tace banason dogon surutu Habeeb kayi Abinda na umarceka.

Habeeb yayi shiru, can yace kuma Mommy kikace gobe?

Mommy tace da Asuba ma kuwa...

_✅ote, comment and share pls_

✍️🗒️ *Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to all my fans_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.