A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 28
Page 21&22
"Tun daga Wannan ranan Hajiya Mariya tadaina yiwa Ahmad magana, Fareedah ma ba magana take mishi ba ko yayi musu magana É—auke kai kawai suke Abun duniya yayi mishi yawa ya rasa ina zesa kanshi shi fa a Azuciyarshi yanaji bata mutu ba! Haka yazama kamar wani mahaukaci duk inda yaji ance Fateemah saiya juya yaga meshi, abokansa sun kasa gane kanshi baya zuwa club yadaina bin mata ko ankirashi awaya baya É—auka sai shaye shaye yake kamar mahaukaci"
Akwai wata rana daya kira Fareedah yace tazo tasaya mishi magani Fareedah batayi magana ba sai yaga kamar ta rainashi ne haka yarike Fareedah yayi ta dukan ta.
Mommy tana dawowa taga Fareedah jiki a fashe tace meya sameki? Fareedah tace Ahmad ne ya daketa! Mommy tafita a ɗakin taje ta sameshi a kwance kan gado, mommy tace Ahmad bazaka kashe 'yar mutane ka kashe mahaifinka sannan kazo ka kashe Ƙanwarka ba, baka isa ba kayi kaɗan
Katashi kabar gidannan cikin minti goma idan kasake dawowa saina tsine maka Albarka!!!Ahmad yabuÉ—e baki zaiyi magana amma Mommy tace idan ya kuskura yayi magana Allah ya isanta haka ya tattara kayanshi yabar gidan.
Ahmad ya rame bashi da tinani saina Fateemah a halin yanzu yafara tuninin yana son Fateemah ne idan ya tuna da hakurinta da juriya, Sai yayi ta kuka kamar me, haka Habeeb yazo ya tarar dashi haka,
Yace meya sameka Ahmad yayi mishi bayanin duk abinda yafaru.
**********
*cigaban labari*
"Yaune ranar zagayowar haihuwan Bintu da Beebah an haɗa party wanda kawayensu na makaranta dayawa suka hallara, inda Bintu da Beebah suka sa anko na skirt pink da top black suka ɗaura kai da black na ɗankwali, Faɗin yanda sukayi kyau ɓata lokaci ne domin yau 'yan biyun Mommy sunyi mugun kyau kamar asace a gudu, kawayensu kuma sunsa dogon riga baki sunyi kyau suma sosai an yanka cake ansa waƙa a speaker Inda Beebah tayi ta dansewa ita da ƙawayensu Bintu sai video kawai take yi musu tana dariya."
Habeeb kuwa ya kira Beebah yace mata sweet sis ki hau watsapp kituramin hotonan da kukayi yau zansa a status É—ina tom broh bari na buÉ—e Data....
âœÂï¸Â🗒︠*jiddah S mapi*
[6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Story/written
By *jiddah S MAPI*
_dedicated to my daughter AFRAH_
_follow ne on wattpad Jiddahpretty_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.