Damata Biyu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Damata Biyu Part 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 25 of 82
Alhamdulliah
15
Zuwairat Ummumaryam
Faiz ji yayi kanshi na wani juyawa, he feels kaman ya dors hannu bisa kai ya dinga ihu, he sees nothing if wata tana gaba wata tana baya, their behavior tankar yan yara haka suke behaving, inshort behavior dinsu ya fi na yara sai da ace na wawaye da kuma mara ilimi, abun mamaki shine yanda kou irin tsoron nan da yasan suna mashi da bai gan sun nuna ba, bintu na tsaye bakin kofar da amira take zaune, faiz gani yayi in har yayi sanya zasu maidashi dan iska, daga kai yayi idanuwanshi suka sauya color kaman ba nashi ba, idanuwanshi sauka sukayi kan santala santala cinyoyin amira dake gaban mota, ita bintu juyawa tayi tana cewa
"Ai sai ku sauka lafiya...am not going anywhere.. " bata karasa ba faiz yace
"Get back here... right now!!!!...." Ya dakawa bintu data juya zata bar wajen tsawa, ahankali ta juyo face dinta daddaure, tamkar bai taba dariya ba ya kalli amira yace
"Now ki koma baya..." Ya fada mats sounding so pissed off like never before
"Ba na rigata fitowa ba..." Amira ta fara fada bata karasa ba faiz ya daga mata hannu yana cewa
"I don't want to hear anything from you....now go back..." Bai karasa ba amira ta bude kofsr a fusace ta fito yayinda bintu tayiwa amira gwalo tana murmuring
"Karuwa..." Under her breath, amira heard her Amma sai tayi kaman bataji ba don already she knows she have to get immune to this name, sai da ta shiga baya bintu tazo zata bude gidan gaba, wani irin kallo fajz yayi mata yace
"Dallah malama koma baya..." Ya daka mata tsawa itama with his eyes as red as coal, baki ta turo kaman bazata koma ba ta buda baya itama ta shiga, sai da ya tabbatar da sun shiga ya juya ba ya kallesu tare da nuna both of them da yatsa, he doesn't feel that mugun so da yakewa amira because of yanda take son komawa yar rigima,
"Wallahi kunyi kadan ku maidani dan iska...ku kunsan in ba darajan aure ba babu wacce ta isheni kallo cikinku balle har ku nemi ku Raina ni....an let me make this clear from now henceforth duk yarinyar data sake tayimin kan kara sai nayi mats na rodi....I won't take this act of illiteracy and irresponsible a gidana....mota tawa ce...duk wacce ta Riga fitowa ta zauna gaba...kai infact daga yanzun baya zaku dinga Zama both of you...Kar wacce ta sake zaunar min gaban mota...sai in da ita kadai zan fita...." If you see yanda yake magana bakinshi na kumfa kasan ranshi ya mugun baci.. he sounds so bitter and angry
"If da akwai wacce take ganin she's to big to stay da wata cikin gidan nan then she should get ready to leave...I don't care.. wallahi Kuka karamin hauka wata zan karo ku Zama ku uku... Period..." Jin maganar zai karo wata yasa zuciysr bintu faduwa, no doubts she loves him more than amira, sauke idanuwa tayi yayinda ita kuma amira tana goge hawayen kukan karuwa da vintu take Kiranta, she can't explain irin zafin da zuciyarta ke mata, juyawa yayi ya nunasu da yatsa dayan bayan daya yana cewa
"Wallahi in har kuna son darajan ku ya dawo yanda yake da you have to learn to stay with each other like yanda kuke da. .if not....bazan fadi abinda zanyi maku ba...." Ya fada sannan ya juya a fusace ya tada mota yana kallon amira dake cleaning hancinta ta madubi, yaga yanda jikin bintu yayi sanyi, har suka isa family house dinshi babu mai cewa juna komai, saidsi ya kallesu ta madubi yana tuki, he feels so sad at this moment, shidai he is not strong for matsala at all, bai son hayaniya kou kadan and he prays this comes to and end, yana zuwa bakin gate din gidansu yayi horn aka bude mashi kofa, nesa yaga yaran maryam sun's wasa a sakar gida, he just pray she's not around because he have had enough drama for today, yasan muddin zasu hadu sai anyi tashin hankali don he knows zagin dayayi mata yana nan cikin ranta har yanzun, he wondered why tayi shuru bata ce komai ba, he just prayed she have stayed away from him and his family for good like he warned her to, packing yayi gefe guda yaran suka tsaya suna kallon motar, yana bude motar ya fito suka bar wajen da gudu suka koma bangaren grandma dinsu, baki ya tabe yana cewa
"I don't have time for you..." Ya fada yana tsaye tare da mika, bintu ce ta fara bude kofar ta fito, amira sai faman gyara face dinta da veil dinta gudun Kar a gane she have cried, bintu na fitowa ta wuce bangaren hajiya Fatima don duk sanda zatazo she always goes there first ta fara gaidata before ta shiga bangaren hajiya kadijatu, fajz na tsaye bakin motarshi har amira ta fito, ta dan ja veil dinta kasa yanda bazaa gan face dinta da kyau ba, she knows maman faiz su biyu ne so she knows bintu is going to greet the first wife of the house, ahankali itama tabi bayan bintu don shiga bangaren hajiya Fatima, kaman daga sama taji faiz ya kama hannunta tare da changing direction dinta zuwa na bangaren mum dinshi,
"Ki wuce wajen iyami..." Ya fada mata atakaice, babu musu ta saki hannunshi ta nufi bangaren hajiya kadijatu, already hajiya kadijatu tasa an hadawa faiz swallow mai taushin gaske like he wants it, sai miyan white okro da kuma stew wanda yaji nama da kifi, amira na sallama hajiya ta amsa mata with a smile, gaidata amira tayi hajiya ta amsa sannan ta samu waje ta zauna kanta kasa, faiz kam shiga bangaren dad dinshi yayi tunda yasan he is at home, alhaji was so happy to see him, for the very first time fajz sees his love a idanuwan dad dinshi, he was asking if he is ok, if da akwai India ke mashi ciwo kou abinda ke damunshi, fajz made it clear he is now ok Kuma zai koma office as soon as possible.
Bintu kam tana shiga bangaren hajiya Fatima ta tardata itama a falo sai Maryam dake zaune tana latse latse wayarta, sallamarta yasa ta daga kai batare data amsa ba, gaidasu tayi hajiya ta amsa with a smile yayinda ita kuma Maryam tace
"Wato ke da wannan dan iskan ne kukazo shi yasa yaran nan suka dawo ciki?...I should have known better..." Ta fada tana gyara zamanta
"Anty inawuni..." Ta gaida Maryam
"Lafiya lau...." Ta amsa mashi atakaice before tace
"Yana ina..." Ta fada tana mikewa
" Yana Waje...anty dan Allah komai ya wuce...pls..." Ta fada dataga Maryam ta mike a fusace
"In baki son ranki ya bace don't talk to me..." Ta fada heading outside like a mad woman
"Wai ina Zaki....hope dai kin san an asirce alhaji ba zai taba ganin laifin wannan yaron ba..." Hajiya Fatima ta fada mata
"Ai mama kou meye sai na kalli idanuwan wannan tantiri na tambayeshi ya maimaita abinda ya fadamin....kawai don nace Kar ya zauna da karuwa sai ya zageni har uwata...ai I won't leave him at all..." Ta fada Tana barin dakin a fusace, bintu fara yarfa hannuwa tayi ba don komai ba sai don she's afraid zaayi tashin hankali wanda asalinshi is because of her, she knows itace silan duk abinda ya faru for now is all because of her, tana ganin Maryam ta fita ta kalli hajiya Fatima tace
"Mama...pls kiyi mata magana... komai ya wuce dan Allah...duk laifi nane..." Ta fada kaman zatayi kuka cikin matsanacin tashin hankali, harara hajiya ta watsa mata without even saying a word, Maryam na fita tayi bangaren hajiya kadijatu da sauri kaman zata tashi sama, da sauri bintu tabi bayanta tana kiran
"Anty pls I beg you.... ni kiyimin duk abinda kikeso...pls pls pls .." ta fada while running behind her, ai kou kallonta Maryam batayi ba don she have decided that tunda har fajz ya bude baki ya zageta sai tayi mashi abinds har ya mutu bazai manta ba, she will deal with both shi da amira in a different way.
Hajiya kadijatu da amira na falo suna dan hira, tunda amira ta shigo bata daga kai ba kanta kasa, she's so down today, kawai kaman daga sama sai taji ana
"Ina wannan shegen yake!!!..." Taji kaman daga sama, her heart skip saboda tsoro, she knows who's voice it is, it's the voice da take ji a nightmares dinta these days, she's so scared of this voice, tamkar fitsari zai kufce mata haka ta fara ji, she was trembling kaman baby dayaga monster for the first time, kawai she wants to run far away from to avoid disgrace, hajiya kadijatu couldn't believe her ears don tunda suke Maryam bata taba mata rashin kunya ba dukda she knows side din mom dinsu suke duk sanda wani dan misunderstanding ya shiga tsakanin su, tana ganin hakan ta wajen yanda suke mata wani irin kallo Amma not for once ta bude baki tayi maganar banza inda take so she's so shocked jin abinda tace
"Maryam is something wrong with you...." Hajjiya kadijatu ta fada tana mikewa tsaye,
"Nothing is wrong with me....ina faiz yake. Yau kou ni kou shi gidan nan... tunda har fajz ya bude baki ya zageni kawai don ba fada mashi gaskiya banga abinda zai hanani cin uwarshi ba yau....kawai daga na fadawa yaro Kar ya zauna da karuwa...karuwar ma wacce take da shege gida...shine zai zageni ...am I his mate da zai zageni...." Ta fada ontop of her voice cikin matsanacin ihu, kou kadan bata gan amira that is trembling a gabanta ba, idanuwanta sun rufe da kou kadan vata gan wacce ke zaune ta fara hawaye ba, bintu was so speechless jin yanda Maryam ke magana hannu ta fada dorawa a kai tana
"Haba anty. Haba dan Allah....haba pls . " Take ta maimaitawa, amira Kuka kawai take kanta kasa, ,salati hajiya kadijatu ta farayi tana clapping hannuwanta, it's as if she's dreaming
"Maryam...so you came here to insult me....wato an turoki don ki cimun mutunci..." Ta fada sounding so pissed off
"Ba wajenki nazo ba.. ai kina sane ta zageni ya zagi uwata. What did you tell him...ai uwa bata fi uwa ba...kuma karuwa bazata .." bata karasa ba gaze dinta ya sauka kan amira da kanta ke boye cikin veil tana Kuka
"Oh...here she is....ga karuwar nan...ashe you're here... Ashe ga mara asalin nan wacce ta Saida kanta kan titi..." Each statement she make tana dungurin amira dake Kuka, hajiya kadijatu nufota tayi tana
"Leave here right now...kafin in bata maki rai.." ita kuma bintu fita waje tayi tana kiran
"Yaya...yaya!! " da karfinta ta dafa cikinta, fajz da ya danyi relaxing a bangaren dad dinshi yayinda alhaji na latse latse wayarshi, he heard the shout from afar saboda yanayjn ginin, kallon dad dinshi yayi yace
"Daddy did you hear anything?..." Ya fada idanuwanshi waje
"Nope..." Alhaji ya amsa mashi, bintu was calling him and moving towards the apartment so the next call came louder than na farkon, da sauri fajz ya mike shima alhaji ya mike, kou shoes bai saka ba ya fito sai ga Bintu da face dinta cike da hawaye sai hakki take saboda condition dinta, tana ganinsu ta dan duka tare da dafe bayanta tana cewa
"It's anty Maryam...tana bangaren iya...mi..." Ai bata karasa ba faiz yayi bangaren mum dinshi da gudu alhaji ya kama bintu yana cewa
"Seat here..." Ya fada yana bin bayan faiz shima da gudu.
A bangaren hajiya kadijatu abun baiyi Dadi ba sam don da hajiya kadijatu ta gajj da irin zagin da Maryam takewa amira sai ta wankawa Maryam, ai nan Maryam tace da wa aka hadata in ba amira ba, she descended on her hot hot ta fara jibgarta yayinda amira didn't do anything to help herself instead she keeps hiding her head dukda Maryam aim for nothing but her head, now she knows she means business, she really means to kill her don bugun is not coming in light at all, hajiya kadijatu sai ihu take tana cewa
"Kashe yar mutane zakiyi..." Ta fada cikin tashin hankalin da ta dade bata shiga ciki ba, she was beating Maryam too from the back, fajz ji yayi his legs are not taking him faster than he wants, shima alhaji da duk sauran karfin shi ya bi bayan faiz, itama bintu kou kadan bata zauna ba dukda alhaji yace ta samu waje ta zauna saboda how she's breathing binsu tayi da gudu tana kuka, kusan lokaci guda fajz da alhaji suka shiga bangaren hajiya, ai kaman mahaukaci faiz yayi flinging Maryam daga kan amira, she fell on center table dake tsakiyar falon hajiya, she fell so hard that sai da ta saki kara lokaci guda, kanta fajz yayi looking so fierce like never before, da sauri alhaji yabi bayan faiz yana cewa
"Barni daita.. barni da mara kunya..." Ya fada yana maida fajz gefe yayi kan Maryam data mike tsaye da kyar kaman she's dreaming, idanuwanta sun fito waje.
"Shege ni ka tura..." Ta fada alaman ita sam bata yarda ba, wani irin mari alhaji ya dauketa dashi yana cewa
"Irin tarbiyar da nayi maki kenan..." Alhaji ya fada sounding so furious at her, faiz was so fuming his dad is around da yau bai gan abinda zai hanashi nuna mats he is the man ba, zai nuna mata age dinta is just a number
"Ashe baki da kunya baki san darajata ba..." Alhaji ya fadawa maryam dake dafe da cheeks dinta
"Ga mara kunyar nan yaje ya auri karuwa..."Maryam ta fada kaman zatayi kuka bata samu goyon baya ba
"Kece karuwa...uwarki ce..." Faiz ya fara fada out of control wani irin kallo hajiya dake rungume da kan amira tayi mashi,
"Daddy kana jinshi.... you hear him...tou wallahi wannan karuwar bazata zauna a danginmu ba..."
"You can do nothing.... you're nothing but a zero behind a decimal point...babu abinda Zaki iyayi.... stay away from my affairs..." Faiz ya fada yana nunata dukda dad dinsu yana tsakiyar su,
"Shut up and get out of here.. " alhaji ya fadawa fajz Amma instead sai ya gyara zamanshi praying his dad will just leave right now ya samu aikata abinda ke ranshi,
"Ai I have made your affairs my business tunda you have decided to drag the name of this family into mud kuma an zuba maka ido...kai kasan karamin mashayi da kai kayi kadan kaja dani. . this whore must leave our family...daddy ai you taught us to do right...so now am doing right by fighting the nonsense that is happening..." Ta fada idanuwanta waje, alhaji yasan Maryam tana da rigima sosai Amma not to this extent da zata dinga kallon idanuwanshi tana magana any how,
"Mi kike wulakantawa haka...ni kike tozartawa ki nunamin ban isa dake ba Maryam ..."alhaji ya fada sounding so angry than ever, shuru tayi tana huci tana kallon faiz, shima kallon ta kawai yake, he just feel like smarshing her kawai, he just can't stop thinking of her beating his wife, his love, his happiness, wato dai da gaske take sai ta rabashi da amira,
"Daddy so laifi nayi don ina son kanina yayi abinda ya kamata"
"Who are you...ke kije kiji da damuwar ki Mana....stay away from me and my family..." Fajz ya fada mata
"Banza mashayi...who even knows if kai kayi mats cikin wajen....daman a jininku abun yake.. " Maryam ta fada da linage dinsu, alhaji sake dauketa yayi da mari yana cewa
"Before I open my eyes ki jirani a bangarena..." Ya daka mata tsawa, da gudu ta fita tana cewa
"Kawai don mashayi nan ya auro karuwa sai ku dinga dukana.... wallahi sai kowa ya san she's a whore. "Ta fada tana fita daga bangaren hajiya kadijatu tare da bangaje bintu dake tsaye kusa da bakin kofar, her elbow goes straight into bintus tummy wanda hakan yasa ta saki wani irin kara sosai, alhaji bin Maryam yayi da gudu don he saw yanda ta bangaje ta, da sauri hajiya ta bar wajen amira saboda yanda bintu ta fada ihu, she slowly move to the ground and hold her waist tana mikawa iyawa hannu daya, fajz da ya rasa inda zai saks kanshi saboda bakin ciki da tashin hankali yace
"Wane irin gulma ne wannan... You caused everything that's happening here right now..." Ya fada in I don't care attitude, sabuwar kara bintu ta saki don kadan abinds takr ji bai bari taji abindsa fajz ya fada ba, iyami yasan something is wrong don yanda ta rike mata hannu ya nuna she's in so much pain, ahankali hajiya ta taimaka nata ta kai kasa kawai sai ta baje legs dinta ta waresu sosai ta dafe cikinta gami da dafe bayanta ta fara hura iska da karfi tana
"Iyami cikina...iyami....bayana... iyami cikina!!!!mutuwa zanyi...na shiga uku..." Ta fada wani irin zufaena geto mats, da gudu fajz ya karasa inda take jikinshi na rawa don now he knows this is so serious,
"Wayyo bintu what's wrong...me ya faru...na shiga uku....iyami Kinga what Maryam have done to me kou...kin dai gani kou iyami..." Fajz ya fada jikinshi na rawa, alhaji dayabi Maryam a guje ne ya sake dawowa da gudu yaga Bintu kwance kasa tana ihu,
"Go get the Dr. Or ...take her to the hospital..." Alhaji ya fada cikin matsanacin tashin hankali, da gudu fajz ya dauki bintu dake Kuka sosai sukayi waje hajiya da alhaji suka bishi, yana gudu yana cewa
"God pls... God pls...rabbi pls...." Kawai yake maimaitawa, hajiya ce ta bude mashi gidan baya ya saka bintu ta shiga motar da sauri tana warware dankwalin dake kanta tana yafawa jikinta tare da jinginar da bintu jikinta, fajz dake furta kowacce irin adua ya shiga bakinshi ya tada mota suka bar gidan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.