Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 1 of 59

*FARASHIN IZZAH*💅🏽💆🏻‍♀️💍💔

Daga marubuciyar BEYOND THE VEIL(LABULEN SIRRI) a baya ina amfani da jiddatulkhayr writes amma yanzu na dawo Hauwajay writes

Hauwa Jibrin Sulaiman

(Hauwajay writes)

Young talented writers association (YOTA)

*Bismillahir Rahmanir Rahim 🤍*

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah MaÉ—aukakin Sarki, Wanda Ya sake bani ikon dawowa da wani sabon labari.

Bayan irin ƙauna da goyon bayan da kuka nuna min a *Beyond The Veil*, kalmomi ba zasu isa su bayyana farin cikina ba. Na ji ku, na karɓi ƙaunarku, kuma hakan ne ya ƙarfafa ni na sake ɗaukar alƙalami domin kawo muku wani sabon tafiya.

Ina fatan wannan sabon labarin zai samu karɓuwa a zuciyoyinku kamar yadda na baya ya samu ko ma fiye da haka. Domin na rubuta shi ne da zuciya, da ji, da kuma fata cewa zai taɓa wani ɓangare na rayuwarku.

Ku kasance tare da ni a wannan tafiya…

Domin wannan ba kawai labari bane rayuwa ce, darasi ne, da kuma wani ɓoyayyen sirri da zai bayyana a hankali.

Nagode sosai da kasancewarku tare da ni. 🤍

Jiddatulkhayr writes taku ce✍🏼

_Book 1_

Prologue

Da gudu motar ta ƙusa kai dab da gate ɗin makarantar. Da sauri mai gadin ya miƙe daga zaunan da yake ya buɗe gate ɗin sanin motar, ya ɗaga hannu yana gaishe da wanda ke cikin motar, amma motar ba ta saurare shi ba. Wani irin 'brake' motar ta yi bayan ta isa dab da babban hall ɗin da ɗalibai suka taru don rubuta jarabawar WAEC.

Buɗe ƙofar baya aka yi. Sai bayan sakanni kafin ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar. Duk hankalin ɗalibai ya koma kanta,  duk da cewa idan da sabo sun riga sun saba da hakan

Sake sauko da ɗayan ƙafarta ta yi waje, wacce ke sanye da white socks da black expensive Toms shoes. Sannan a hankali ta fito daga motar. Sanye take da white mini hijab, white riga, da black trouser, uniform ɗin ya yi mata bala'in kyau wanda ya sake fitar da anihin kyanta, Zahra kenan 'yar shekaru 18

Fuskarta na sanye da black sunglasses. Ta É—an zaro glass É—in daga idonta zuwa kan hancinta, tana bin wajen da kallo.

Ta tashi daga jikin motar ta rufe, kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ɗan taka zuwa wajen driver. Kamar wacce aka sa dole ta yi magana, ta buɗe baki ta ce

''Zaka iya jira na, dan yau ba daÉ—ewa za mu yi ba''

''Shikenan, Hajiya'' ya amsa cikin girmamawa

''Hey Fatima!''

Muryar ta katse nutsuwarta.

A hankali ta juya, tana kallonsu har suka ƙaraso

Murmushi ta yi mai É—auke da confidence

"Point of correction… Asiya" ta ce cikin sanyi

"Sunana Zahra, not Fatima"

Asiya da Saudat suka kalli juna suka fashe da dariya.

"Hey Pretty!" Saudat ta ƙara

Zahra ta É—an karkatar da kai tana murmushi ta ce

"Na'am… ai a rubuce yake a fuska ta"

Sai fuskar ta É—an canza, ta koma serious ta ce

"Asiya… exams card ɗina da biro?"

"Yana cikin jakkata" Asiya ta amsa

Ta gyada kai

Wayarta ta fara ringing.

Ta ciro ta daga aljihun wandonta ta É—aga kiran. Kawayenta suka kalli juna cikin alamun tambayar yaushe kuma? Amma babu wanda ya san amsar

Saida ta gama wayan, ta sauke daga kunnen nata

"Zahra, kin canza waya ne?" Saudat ta tambaya

Wani murmushi mai É—auke da izza ya bayyana a fuskar ta

"Yaushe ake yayin iPhone 16 Pro… alhali har 17 ya fito?" Ta ɗan ɗaga gira

"Jiya Abba ya canza min"

Kawayenta suka taya ta murna.

An fara kira a shiga hall.

Dalibai suka fara tururuwa zuwa tantancewa don kafin shiga Hall É—in

Amma Zahra… ta kama hanyar wani office dake wani ɓangaren

"Ke! Baki ganin sauran É—alibai suna shiga hall ne?" wani sabon malami ya tsawata mata

Cak ta tsaya, ta juya,ta naÉ—e hannunta, ta gyara tsayuwarta

Ta kallesa kai tsaye cikin idanu cike da kwarin gwiwa.

"Ba zaki bi hanyar hall É—in bane?" ya sake tambayarta

A hankali ta buÉ—e baki, kamar waccan ake wa dole ta ce

"Excuse me… kaga nayi kama da wacce zata yi exam a cikin wancan hall ɗin?

With thousands of people?

Babu iska… babu fanka?"

Malamin ya kasa amsawa sabar shock daya shiga

Ta juya, ta fara tafiya cikin izzah kamar ba Malami bane ya tsayar da ita ba

Wani malami daga baya ya ce,

''Kyale ta… a office take nata exams, special student ce"

Bayan awa biyu… ɗalibai suka fara fitowa daga hall ɗin jarabawar, harda kawayenta a cikin wanda suka fito

Ita kuma… ta fito daga office ɗin cikin nutsuwa

Ta ci karo da wani malami da tun farko taji bata kaunarsa sbd yadda yake kallonta

"Ahh… Pretty girl ce" ya faɗa yana murmushi

"Har kin gama?"

Ta kallesa sau É—aya sannan ta É—auke kai ta ce

"Eh" daga haka ta wuce abinta..

"Mu tafi" ta faÉ—a wa kawayenta bayan ta isa inda suke kiranta

"Ina da modelling anjima. Ina son na je gida na huta… it's been a while da nayi posting a Instagram"

Suka shiga mota, ta zauna a gaba

"Ka ja motar da gudu… bana son slow motion" ta umarci driver

Motar ta fice da gudu kamar yadda ta bada umurni

Suna cikin tafiya bayan sun shigo wani unguwa wanda kallo É—aya zaka masa ka fahimci tabbas wannan suna fama da rayuwa, dai dai wani layi ta ce

"Tsaya", drivern yayi parking. Ta sauka ta zaga ta buÉ—e boot.

Ta É—auko wani babban leda.

Ta shiga wani lungu, ƙaramin gida mai nuna ana wahalar rayuwa a cikinta nan ta shiga

Ta yi sallama, ƙaramin yaro ya fito da gudu yana ganinta ya fara tsalle da dariya yana

"Anty!"

"Shhh…" ta ce tana murmushi

Ta ajiye ledar hannunta, ta ce

"Je ka kira mamanka, ka nuna mata laidar idan ta fito"

Ba tare da jiran godiya ba… ta juya ta koma mota.

Suka ci gaba da tafiya har suka sauke kawayenta kowacce a gidansu

Da suka isa gida, ta sauka. Wani mutum mai kimanin shekara 65 ne tsaye a compound yana shirin shiga mota, ga waya kuma ƙare a kunnen sa. Da gudu ta je ta rungume shi.

Ya sauke wayarsa ya sumbaci goshinta ya ce

''Baby, ya exams É—in?''

Ta ce

''Alhamdulillah, Abbah na''

Ya ce

"Allah ya ba da sa'a. Bari zan fita, idan na dawo sai mu yi magana"

Ta gyaÉ—a kai tana murmushi haÉ—i da masa bye bye

Ta shiga cikin compound.

Wata mata mai kimanin Mid 50s ce tsaye cikin tsadadden kaya, wani saurayi wanda zai kai 30yrs ne tsaye gefenta, da budurwa mai 22yrs wanda take tunkarar su

Ta kalli saurayin da gudu taje ta rungume shi. Ya É—aga ta sama yana dariya

"Wai yaushe Zahra zaki yi kiba ne? Ji fa ko nauyi baki da shi!"

Ta ce

"Toh wa ya ce maka ina son kiba?"

Ta kalli matar da fuska a haÉ—e,

"Mummy, ina wuni."

Ta amsa a takaice, "Lafiya"

Ta kalli budurwar,

"Anty Batoul" amma ko alamar ta kalleta bata yi ba sai ma gaba data wuce abinta

Ta kalli Yaya Umar ta ce,

"Yaya, bari na shiga ciki"

Yana murmushi ya ce ''Ki je ki huta"

Mummy ta harba mata kallo mai nauyi yayin da ta wuce

Ta ce

"Dan ubanka idan baka daina taɓa yarinyar nan ba sai na saɓa maka, wawa kawai"

Ya ce

"Mummy me aibun hakan?"

Ta bar shi tsaye ta wuce gaba abinta kamar zata wajen mota

Sai kuma ta juya tabi bayan Zahra zuwa babban parlorn nasu

Zahra kamar yadda ta saba tafiya haka take yi kamar ba zata yi ba

Mummy ta tsaya a wurin, idanunta na bin hanyar da Zahra ta bi har ta ɓace mata

Fuskarta a É—aure, amma ba irin na fushi kaÉ—ai ba ne

A hankali ta ja numfashi

Sannan ta juya, ta nufi kujerar da take zaune a baya, ta zauna a hankali kamar wacce wani abu ya ɗauke mata ƙarfi

Ya Umar daya biyo ta a baya ya kalleta da mamaki

''Mummy… lafiya?''

Ba ta amsa masa ba

Sai ta É—aga hannu a hankali, tana masa alamar ya yi shiru

Wani irin shiru ne ya sake mamaye falon

Mummy ta kai hannu cikin designer bag É—inta, ta ciro wayarta

Na ɗan lokaci… ta tsaya tana kallon screen ɗin kawai

Kamar wacce ke yanke shawara mai nauyi ko kokonton abin da zata yi

Sannan ta danna wani number.

Wayar ta É—auki lokaci tana ringing

A ƙarshe aka ɗaga. Ba gaisuwa

Sai Mummy ta ce cikin murya mai sanyi da ba a taɓa jin irinta a bakinta ba

"Ta dawo"

Shiru daga ɗayan ɓangaren.

Sai muryar da ta fito mai nauyi

"Kin tabbata?"

Mummy ta rufe idonta na sakanni

"Bangane ba, abin da idanu na suke faÉ—a min ai ba karya bane"

Yaya Umar ya É—an matsa kusa da ita, yana kallonta cikin ruÉ—ani

"Mummy… wa kike magana da shi?"

Ta É—aga masa hannu da sauri ba tare da ta kalle shi ba

"Ka fita"

Ya tsaya cak, ya ce

"Mummy......"

"Na ce ka fita!"

Muryarta ta É—an daki É—akin, amma ba kamar fushin yau da kullum ba

Wani irin tsoro ne ke ɓoye a cikinta

Yaya Umar ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya juya ya fita a hankali.

Tana ganin ya fita

Mummy ta sauke wayar daga kunnenta a hankali.

Amma ba ta kashe call É—in ba.

Muryar daga ɗayan ɓangaren ta sake fitowa

"An riga an faÉ—a miki cewa wannan rana za ta zo"

Numfashinta ya É—an rikice.

Ta ce a hankali,

''Na yi tunanin… mun gama da wannan''

Ƙaramin dariya mai sanyi ta fito daga wayar

''kina wasa sosai, amma komai yana dab da lalacewa''

Hannun Mummy ya fara rawa kaÉ—an

Ta riƙe gefen kujera da ƙarfi.

''Me kuke so wannan karon?''

Shiru na É—an lokaci.

Sai amsar ta zo a hankali… amma da nauyi

"Ba abin da muke so ba... abin da ita ta tuna"

Kalmar ta tsaya mata a rai.

"Ita ta tuna?"

Muryar ta ce

"Kuma idan ta tuna... Mun san abin da zai biyo baya"

Call É—in ya katse.

Falon ya sake yin shiru.

Amma wannan karon… shiru mai nauyi ne, harta zuciyarta yayi mata nawi. Mummy ta zauna ba motsi.

Idonta ya tsaya wuri guda. A hankali ta furta

''Ya Allah…''

Sai ta É—aga kai tana kallon hanyar É—akin Zahra dake upstairs

Idonta cike da wani abu ba ƙiyayya ba, ba soyayya ba…

Sai dai tsoro.

Tsoron da ta daɗe tana ɓoyewa.

Ta ce ƙasa-ƙasa

"Da gaske… kin manta komai ne… ko kina wasa ne da mu?"

A Bangaren Zahra kuwa, tana hawa sama ta nufi wani É—aki

Zahra na shiga É—aki ta faÉ—a kan tsadadden gadonta, ta lumshe idanu.

Aka buɗe ƙofar toilet, Mami ta fito tana murmushi,

''Yau kuma a gajiye kika shigo kenan?''

Ta ce,

''Yes Mami… kuma masu aikin nan ba su gama abinci ba, yunwa nake ji wallahi''

Mami ta ce,

''Alright, bari na hado miki oat ki sha kafin a gama''

FARASHIN IZZAH…

Ku biyo mu don jin cigaban labarin Fatima Zahra, wacece ita? Wake shigowa rayuwarta...

#Jiddatulkhayr writes

#08110615256

https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

*FARASHIN IZZAH*

Jiddatulkhayr writes

Book 1

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.