Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 43 of 59

Chapter 41

Ana cikin raha da ɗaukar hotuna…

Sai aka ji ƙarar wata mota ta tsaya a bakin gate

Gatekeeper ya buɗe gate. Motar ta shigo a hankali

Tana tsayawa, wani dogon saurayi ya fito sanye da wata ash-colour shadda mai matuƙar kyau. Fuskarsa cike da murmushi.

A bayansa kuma wata kyakkyawar budurwa ce ta fito cikin Abaya mai launin lavender.

“Ya Ims!” Zahra ta faɗa da ƙarfi tana dariya, ko jira ba ta yi ba…

Ta ɗaga gown ɗinta kaɗan ta yi gudu zuwa wajensu

Ya Imran ya buɗe hannuwansa, ta faɗa jikinsa

Ya rungume ta kamar ƙanwarsa ta jini

“Happy Birthday, Princess.

Allah Ya ƙara miki shekaru masu albarka.”

“Ameen…” Ta amsa tana murmushi

Ya ɗan ja hancinta cikin wasa

“Duk da ke kin manta da mu,

Weekend ɗaya kika yi a gidanmu kika gudu, baki sake zuwa ba”

Ta taɓe baki

“Ni? Toh ai ku ko zuwa mana baku yi”

Ya yi dariya

“Toh shi kenan.”

A dai-dai lokacin… Iklima ta ƙaraso

“Toh ni fa? Ni ba za ki rungume ni ba?”

Zahra ta saki Ya Imran da sauri

“Iklimatyyy!”

Ta rungume ta da ƙarfi

“Na yi missing ɗinki wallahi.”

Iklima ta yi dariya

“Ni ma. Ai ban gane ki ba, na ɗauka amaryace fah”

Zahra ta ɗan bugeta a kafaɗa

“Ki bar ni.”

Dukansu suka yi dariya.

Uncle Moh ma ya fito daga motar tare da anty Maryam

Abbah ya ƙarasa wajensa

Suka rungumi juna cikin farin ciki.

“Lale marhabin.”

Su Mami ma suka je suka gaisa da su. Nan take wajen ya sake ɗaukar armashi.

Ya Imran ya ciro wani ƙaramin gift bag, ya miƙa wa Zahra.

“Wannan kuma daga gare Ni ne.”

Ta karɓa tana murmushi

“Nagode sosai.”

Ta juyo ta kalli Iklima.

“Ke ma kina ciki ko?”

Iklima ta ɗaga gira

“Eh mana. Ni ce ma na zaɓa.”

Ya Imran ya yi dariya

“Karya take.”

Suka fara gardama

Zahra ta riƙe cikinta tana dariya.

Aka cigaba da shagali

Ƙananan yara na ta gudu tsakanin balloons. Manya na hira

While Photographer bai daina aikin sa ba

Ya Umar da wasu abokansa suna ta karɓar baƙi

Mami da Anty Jiddah suna kula baki mata

Da magariba ta yi…

Baƙi suka fara sallama ɗaya bayan ɗaya

Kowa na zuwa ya sake yi wa Zahra fatan alheri.

“Allah Ya sa ki gama da duniya lafiya.”

“Allah Ya baki Miji nagari.”

“Allah Ya ba ki ilimi mai amfani.”

Ta riƙa amsawa cikin ladabi

“Ameen.”

“Nagode sosai.”

Uncle Moh ya rungumi Abbah kafin tafiyarsa.

“Da dukkan alamu Yau ka faranta mata rai.”

Abbah ya yi murmushi

“Farin cikinta shi ne farin cikina.”

Ya Imran ya ɗan murɗe kunnen Zahra cikin wasa

“Ki kula da kanki.”

Ta yi dariya

“Kash! Wannan fah cin zali ne”

Iklima ta sake rungume ta

“Ki kira ni idan kin samu lokaci, akwai gist”

Kai Zahra ta gyad’a, daga haka ta rakasu har jikin mota

Tass Baki suka gama tafiya, hayaniyar gidan ta lafa.

Balloons suna ta motsawa da iskar dare, ma’aikata suka fara tattara tebura da kujeru.

Caterers na kwashe kayan aikinsu.

Photographers suna nuna wa Abbah wasu daga cikin hotunan da suka ɗauka.

Abbah ya kalli hoton Zahra tana rungume da shi.

Sai ya yi murmushi.

“Madalla.”

“Ku tabbatar kun haɗa min komai.”

“Ba zan so a rasa ko da hoto ɗaya ba.”

“Okay sir.”

A gefe guda kuma…

Zahra ta tsaya ita kaɗai tana kallon motarta. Key ɗin na hannunta.

Har yanzu ba ta yarda cewa duk wannan nata ne ba, ta shafa bonnet ɗin motar a hankali, ta yi murmushi.

Sai ta ɗaga idanunta zuwa sararin sama

“Alhamdulillah… My Perfect Rabb” Ta faɗa a hankali

A zuciyarta…

Ta yi addu’ar Allah Ya sa ta kasance ’ya mai anfani ga iyayenta, kamar yadda suke ƙoƙarin ganin farin cikinta a kowane lokaci.

A parlour…

Mami, Ya Umar, Zahra da Anty Jiddah suna zaune suna kallon hotuna da videographer ya fara tura musu a laptop.

Lokaci zuwa lokaci…

Dariya na tashi

Musamman idan aka ga reaction ɗin Zahra lokacin da ta fara ganin motar.

Ya Umar ya riƙe cikinsa yana dariya

“Wallahi Baby, fuskar nan taki ta cancanci a saka frame.”

Zahra ta turo baki.

“Yaya… banso! Kuma ai Ni ban san kuna recording ba”

Mami ta yi dariya

“Shi ya sa reaction ɗin ya yi kyau.”

A dai-dai wannan lokacin…

Suka ji ƙarar wata mota ta tsaya a compound.

Ba wanda ya kula sosai, sai dai…

Bayan ƴan daƙiƙu.

Bang!

Aka buɗe ƙofar parlour da ƙarfi.

“Ashe Yau za’a yi bura’uba!”

“Wannan wace irin iskanci ce haka?! Da son kai kiri kiri a fili?!”

Muryar Mummy ce ta ratsa parlon gaba daya, kana Jin yadda tayi magana kasan ba karamin ɓacin rai take ciki ba

Har sai da Zahra ta firgita, ta juyo da sauri

Mummy ta shigo tamkar guguwa

Fuskarta a haɗe. Idanunta sun yi jawur.

Batoul kuma na bayanta.

Tun suna kan hanya suka ji labarin abin da yake faruwa a gidan

Amma ganin komai da idanunsu…

Shi ne ya ƙara hura musu wutar zuciyarta

Da Batoul ta hango Zahra cikin doguwar pink gown ɗinta, har yanzu tana riƙe da key ɗin sabuwar motar…

Sai hawaye suka cika mata ido.

“Mummy…” Ta faɗa da muryar kuka

“Wai da gaske…”

Mummy ta yi wani irin tsaki.

Ta nuna Zahra da yatsa.

“Saboda ke ne za a yi wannan almubazzarancin? Saboda ke ne za’a yi uban taro gaki ’yar goal ko?”

Zahra ta tsaya cak, ta rasa me zata ce

Kawai idanunta suka cika da ƙwalla

Ta matse key ɗin da ke hannunta.

Anty Jiddah zata tashi Mami tayi saurin rike ta

Muryar Mummy ta sake tashi cikin sananin fushi haɗi da zallar kishi

“Yau saboda ke aka tara dangi?”

“Aka yi party?”

“Aka yi cake?”

“Aka kawo mota?”

“Wai me kika fi sauran yaran gidan nan ne?!”

Batoul kuwa ta fashe da kuka.

“Wallahi ba adalci ba ne.”

“Ni da nake university…”

“Ba a taɓa yi min rabin wannan ba.”

Zahra ta ɗaga kai a hankali.

Ta buɗe baki kamar za ta yi magana… Sai kuma ta fasa.

Ta juya da sauri tana kallon Mami da Ya Umar cikin ruɗani

Gabanta ya fara bugawa, ba don ta ji tsoron Mummy ba…

Sai don ba ta taɓa ganin ta cikin irin wannan matsanancin fushi ba.

Thank God… Kafin Mummy ta ƙara cewa wani abu…

Sai aka ji takun tafiya daga corridor

Abbah ya fito.

Fuskarsa ta canza gaba ɗaya

Ya tsaya yana kallon Mummy.

Sai ya ce cikin sanyin murya, amma mai cike da iko

“Ke! Dalla ki rage ma mutane murya.”

Mummy ta juyo tana huci

“Me?”

Abbah ya matso gaba kaɗan.

“Na ce ki rage murya.”

“Mutanen gidan nan suna hutawa, kar ki zo ki dame mu, ki damu da maƙwabta, kada ki tashe mana gida da ihu.”

Parlour ɗin ya yi tsit.

Ko Batoul ta daina kukan da take yi

Mummy ta tsaya tana kallonsa.

Fuskarta cike da mamaki da takaici.

Abbah kuwa bai ɗaga murya ba.

Amma yadda ya faɗi kalaman…

Ya isa ya sa kowa ya yi shiru

Ya juya ya kalli Zahra, muryarsa ta lafa

“Baby… calm down! Babu Mai taɓa ki ya kwana lafiya “

Sai ya sake mayar da kallonsa kan Mummy dake uban hararansa,

Idanunsa cike da gargadi.

“Nan gida ne, ba kasuwa ba

Kuma ba zan yarda da hayaniya ba.”

Shiru ya mamaye parlour na wasu daƙiƙu.

Mummy ta tsaya cak tana kallon Abbah kamar zata dake sa

Fuskarta ta yi ja saboda tsananin fushi

Numfashinta na fita da ƙarfi

Sai kuma ta yi wani ɗan dariyar takaici

“Toh kenan…” Ta faɗa tana girgiza kai

“Shi ke nan! Har za ka raina ni a gaban mutane? Ka faɗa min maganganun banza marasa kan gado a gaban ‘ya’yan cikina”

Abbah bai motsa ba, yana kallonta da mamaki

Mummy ta ci gaba,

“Wallahi ba zan zuba ido ina kallon wannan banbancin da kake yi ba.”

“Ba zan taɓa yarda ba.”

“Batoul ma sai an yi mata.”

“Ko za’a yi tashin duniya ne”

Ta ɗan dakata tana cizon leɓenta.

“…kuma sai na ɗauki mummunan mataki a kan abin da yake faruwa a gidan nan.”

Parlour ɗin ya sake yin tsit.

Abbah kuwa…

Sai ya yi murmushi

Murmushin mutumin da ya gaji da jin irin waɗannan barazanar.

Ya ɗan gyara tsayuwarsa .

“Bismillah.” Ya faɗa a nutse

“Haka muke son ji.”

Mummy ta zaro ido tana kallonsa.

Abbah ya ci gaba da magana cikin nutsuwa

“Kuma ki saurara da kyau, Hafsat.”

“Wannan shi ne karo na ƙarshe da zan yi miki magana cikin natsuwa.”

Idanun Mummy suka ƙanƙance.

Abbah ya ɗora da cewa,

“Idan ba ki yi hankali ba…”

“Zaman ki ya zo ƙarshe a gidan nan.”

Kalmar ta sauka kamar tsawa haka nan a kunnenta

Mami ta ɗan runtse idanunta

Anty Jiddah ma ta ɗan kalli Abbah cikin mamaki.

Batoul kuwa ta tsaya tana kallon mahaifinta, ta kasa ko motsi.

Mummy ta yi wani irin dariya mai cike da takaici.

“Ni?”

“Za ka kore ni?”

Ta girgiza kai.

“Toh shi ke nan! Ko ba yanzu ba, amma ku jira.”

Ta nuna Zahra da yatsa.

“Wacce kuke ɗagawa sama.”

“Wacce kuke ganin ita ce cikakkiya.”

“Ita ɗin nan…”

“Sai ta jawo muku abin kunya.”

“Ku tuna maganata.”

Ta juya da wani irin huci

Fuuuu! Ta nufi staircase ba tare da ta sake waiwayowa ba.

Takalmanta na bugun matakala da ƙarfi saboda fushi.

Batoul ta share hawayenta

Ta yi saurin binta a baya ba tare da ta ce komai ba.

Har suka ɓace daga ganin mutanen parlour

Na ɗan lokaci…

Ba wanda ya yi magana.

Sai Anty Jiddah da ta girgiza kai a hankali

“Allah ya kyauta”

Mami ta sauke numfashi

Ita dai ba ta ce komai ba.

Ya Umar kuwa…

Tun lokacin da Mummy ta fara wannan hayaniyar…

Kunyar abin da ya faru ta riga ta kama shi

Ya shafa goshinsa, ba tare da ya ce komai ba…

Ya juya a hankali

Ya fita daga parlour.

Zahra ta bi bayansa da kallo.

Ta san wannan shirun na Ya Umar…

Shi ne mafi girman alamar cewa zuciyarsa ta yi nauyi.

Abbah ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, sai ya buɗe su.

Ya kalli Zahra da Mami.

Ya tilasta murmushi.

“Yau ranar farin ciki ce.”

“Ba zan bari wani ya ɓata mana ita ba.”

Amma duk da kalamansa…

Kowa da ke parlour ya fahimci cewa maganar da Hafsat ta yi ko kadan bai dace ba, a haka kowa ta watse

Misalin ƙarfe tara na dare…

Gidan ya yi shiru gaba ɗaya.

A parlourn Abbah…

Shi da Ya Umar ne kaɗai suke zaune.

Kofunan shayi ne a gabansu, amma babu wanda yake sha.

Abbah ya jingina da kujerar da yake kai.

Ya kalli Ya Umar yana murmushi.

“Umar.”

“Na’am, Abbah.”

“Na gama magana da L-Cars.”

Ya Umar ya ɗaga kai.

“Da safe za su zo su ɗauki motarka.”

“Su kai showroom.”

“Sannan su kawo maka sabuwar Rolls-Royce Phantom Series II.”

Ya Umar ya yi shiru na wasu daƙiƙu

Sai ya girgiza kai a hankali.

“No, Abbah.”

Abbah ya ɗan haɗe gira.

“Ban gane ba.”

Ya Umar ya yi murmushi.

“Ni ina son motata.”

“Wannan ta ishe ni.”

Abbah ya ce,

“Amma me ya sa?”

Ya Umar ya ɗan gyara zamansa.

“Abbah…Idan saboda an saya wa Zahra mota ne za a canza mini tawa…”

“Zan ji kamar duk abin da aka yi mata sai an yi mini makamancinsa.”

Ya ɗan yi murmushi

“Bayan kuma motar da nake amfani da ita ma ta fi sabuwar tata tsada.”

“Dama a gidan nan… Ita ce kadai bata da mota. Yanzu kuma ta samu”

Abbah ya yi shiru yana kallon ɗansa

A hankali murmushi ya bayyana a fuskarsa.

“Na yi niyya ne in faranta maka rai.”

Ya Umar ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa.

“Toh shikenan Abbah, Nagode.”

“Allah Ya ƙara girma.”

Abbah ya yi murmushi

“Ameen.”

Sai dai kafin ya ƙara magana…

Wayar Ya Umar ta fara ringing.

Ya zaro ta daga aljihunsa

Da ya ga sunan da ke kan screen…

Mummy Calling.

Ya miƙe tsaye

“Abbah, bari in je.”

Abbah ya gyada kai

“Alright, Good night”

Ya Umar ya nufi ɓangaren Mummy.

Ya buga ƙofa a hankali.

“Shigo.” Muryanta ya ratsa kunnensa

Ya shiga.

Mummy na zaune bakin gado.

Fuskarta babu alamar walwala balle rahama

Yana zama bata, ba ta bari ya yi magana ba.

“Munafuki!”

Ya Umar ya ɗan zaro ido

“Mummy…”

Ta ɗaga hannu ta dakatar da shi

“Kar ka kira ni da Mummy. Ni ka ɗauka ba na ganin abin da kake yi?”

“Kullum kana can da su, Baka ɗauke ni Uwa ba…”

Ya Umar ya girgiza kai, bai bari ta karasa ba ya ce

“Wallahi ba haka ba ne.”

“Tohh….” Ta katse shi.

“Daga yau… saurara da kyau.”

“Idan ka sake bin side ɗin ubanka da Mami… ko ka tsaya kana hira da su ballanta gaisuwa”

“Ko ka zauna tare da su…”

“To ka ɗauka… zan iya yafe ka”

“Kuma Allah Ya isa tsakanina da kai.”

Kalmar ta tsoki zuciyarsa kamar mashi, ya zaro ido, nan take ya fara zufa

“Mummy… Don Allah!”

“Me ya sa za ki ce haka? Su fa iyayena ne! Ta yaya zan daina gaishe su?”

Mummy ta harare shi.

“Saboda su ne zaka wani rikice min? Kalle ka fah harda wani uban zufa dake sassako maka”

Lallai kuwa…

Ya Umar bai ma san lokacin da zufa ta fara keto masa a goshinsa ba

Zuciyarsa ta cika da ruɗani.

A ransa yana ta maimaita

“Ta yaya zan rabu da Abbah? Ta yaya zan daina gaishe shi? Ta yaya zan yi kamar Mami ba ta wanzu ba?”

Ya haɗiye yawu, saboda wannan abune mai kamar wuya ga uban Baki data masa

“Mummy… Don Allah ki saurare ni.”

Amma Hafsat ko kallonsa ba ta yi, ta nuna masa ƙofa.

“Tashi ka fita”

“Na gaji da jin maganarka.”

Ya kasa motsi.

Ta sake ɗaga murya.

“Na ce ka bace min a ɗaki! Kafin na ƙara fushi.”

Ba don yana so ba…

Ya Umar ya miƙe a hankali.

Ya kalli mahaifiyarsa da idanun da suka cika da damuwa.

Sai dai ta juya fuskarta gefe.

Ko kallonsa ba ta sake yi ba.

Cike da nauyin zuciya…

Ya buɗe ƙofar

Ya fita.

Yana tafiya a corridor…

Hannunsa dafe a kansa.

A karon farko…

Ya ji kamar an ɗore shine tsakanin wuta da inuwa, biyayya ga mahaifiyarsa… ko kuma ƙaunar mahaifinsa

#FARASHIN IZZAH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.