Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 37 of 59

Chapter 36

Ta yi ɗan tunani

“One grilled chicken with mashed potatoes… fresh orange juice.. and cheesecake later.”

“Certainly, Ma’am.” Ya tafi.

Zahra ta jingina da kujera.

Idanunta na kallon fountain ɗin da ke waje, wani irin nutsuwa ta sauko mata

Ta murmusa ita kaɗai, a ranta ta furta,

“Thank you, Allah…”

Bayan kusan awa biyu da rabi a restaurant ɗin, Zahra ta gama cin abincinta cikin nutsuwa. Ba ta yi saurin tashi ba.

Ta ɗan zauna tana kallon flowers da fountain ɗin da ke waje, tana jin yadda zuciyarta ta samu wani irin natsuwa.

“Da gaske Ya Umar ya yi tunani” Ta furta a zuciyarta

“Na buƙaci wannan hutun.”

Waiter ya dawo da bill.

Kafin ma ya ajiye, Zahra ta ciro katinta ta miƙa masa.

“Thank you, Ma’am.”

Ta yi masa murmushi kaɗan.

“You’re welcome.”

Ya tafi.

Ta ɗauki handbag ɗinta, ta gyara veil ɗinta a jikin mirror da ke kusa da ƙofar fita, sannan ta fice daga restaurant ɗin.

Da fitowarta waje…

Sanyin iska ya bugi fuskarta.

Ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon sararin sama. Murmushi ya subuce mata

Ba ta tuna rabon da ta samu irin wannan nutsuwar ba

Kalle kalle ta fara yi, ganin babu kowa fa wuce inda tayi parking motar, wani securities ta gani

Ta miƙa wayarta ga wani security guard da ke bakin parking lot din

“Excuse me… Please, can you help me take some pictures?”

Mutumin ya amsa cikin girmamawa.

“Sure, Ma’am.”

Ta miƙa masa wayar.

Ba ta shiga wani irin posing ba, hotuna masu sauƙi kawai. Wani tana jingine da motarta, wani tana tafiya a hankali

Wani kuma tana kallon flowers ɗin da ke gefen parking ba tare da kallon camera ba.

Da ya gama, ya miƙa mata wayar.

Ta duba, Murmushi ya bayyana a fuskarta.

“They’re beautiful! Thank you.”

“You’re welcome, Ma’am.”

Ta shiga motarta.

Ta kunna motar, a hankali ta bar wajen.

A hanya…

Window ɗinta a ɗan buɗe yake

Sanyin iska na shigowa.

Wata soft nasheed na tashi a stereo.

Zahra tana tuƙi cikin nutsuwa

Karo na farko cikin watanni, ta ji kamar ta dawo Zahra ta da.

Ba wadda take rayuwa tsakanin school, books da exams kawai ba…

Sai Zahra mai son fita ita kaɗai ta sha iska tayi pic ta daura a media handles dinta..

Da ta isa gida…

Mai gadi ya buɗe gate.

Ta shigo compound, ta yi parking

Kanwar Anty Binta ce ta fito da gudu.

“Anty Zahra, sannu da zuwa.”

Ta yi murmushi.

“Yauwa. Ya gida?”

“Lafiya.” Yarinyar ta amsa

Sai kuma ta karɓi handbag ɗinta.

“Na gode.”

Suka shiga parlour tare.

Abbah da Mami na zaune suna hira.

Abbah na hango ta, ya yi murmushi.

“My Baby… How was it?”

Zahra ta zauna a gefensa.

“It was amazing.”

Ya yi dariya.

“So… Ya Umar’s idea worked?”

“It really did.”

Ta amsa tana murmushi.

Mami ta ce,

“Kin gane yanzu? Mutum yana buƙatar ya huta wani lokaci.”

Ta gyada kai.

“Wallahi Mami! Na ji daɗi sosai”

Abbah ya kalleta

“I can see! Kin dawo da fara’arki.”

Ta yi dariya

“Really?”

“Very.”

Ya shafa kanta cikin ƙauna.

“Allah ya ƙara miki farin ciki ya raya mana ke

“Ameen.”

Daga haka ta mike t wuce zuwa d’akinta

Bayan ta yi sallah ta canja kaya…

Sabuwar wayarta ta ɗauka

Tun lokacin da Abbah ya siya mata wayar, ba ta gama saita komai ba

Yanzu ne ta samu lokacin da za ta dawo da duk account ɗinta dake wayan Mami

Ta shiga Instagram

Ta saka username da password.

Cikin daƙiƙu kaɗan…

Account ɗinta ya dawo.

Ta kalli profile ɗinta tana murmushi

Ta daɗe ba ta yi posting ba.

Followers ɗinta kuwa sai ƙaruwa suke kullum, ta shiga gallery

Ta zaɓi hotuna huɗu daga waɗanda aka ɗauke ta yau

Dukansu simple ne, babu wani pose mai yawa, Elegance kawai

Ta rubuta caption.

“Sometimes… all your heart needs is a little peace. 🤍✨ Alhamdulillah.”

Ta danna Post, ta ajiye wayar

Ba’a wuce minti ɗaya ba…

❤️ 245 Likes

Ta ɗaga gira.

“Masha Allah.”

Ta ci gaba da kallon comments.

“Absolutely gorgeous.”

“Queen energy.”

“Elegance has a name.”

“Our soft life queen is back!”

“This smile… we’ve missed it.”

“Allah ya ƙara miki farin ciki.”

“Simple but classy.”

“Fatima Zahra never disappoints.”

Ta yi murmushi, ba ta cika shiga reply ba

Sai dai idan comment ɗin addu’a ne, nan take ta rubuta “Ameen, thank you. 🤍”

Ta sake wucewa, wani ya rubuta,

“Marry me.”

Ta yi dariya ita kaɗai, ta yi scrolling ba tare da ta ba shi amsa ba, sai kuma wani comment ya ja hankalinta.

“Your dignity is what makes you different.”

Ta tsaya tana kallon comment ɗin na wasu daƙiƙu, daga ƙarshe ta yi like kawai

Domin wannan kalmar…

Ita ce ta fi bayyana wacece Zahra.

Wata irin izzah da Allah Ya ɗora mata, wadda ba ta neman ta ja hankali da ita, amma duk inda ta bayyana, mutane kan lura da ita.

Ta kashe wayarta, ta jingina da headboard ɗin gadonta tana murmushi.

Washegari tun da sassafe Zahra ta isa makaranta kamar yadda ta saba

Tun daga parking lot ɗin makarantar take tafiya cikin nutsuwarta. Uniform ɗinta fari ne ƙal, an yi masa guga yadda babu ko ɗigon wrinkle. Black shoes ɗinta suna kyalli, hijab ɗinta kuma a nannade sai shatin guga tamkar an zana.

School bag ɗinta na rataye a kafaɗarta ɗaya, a ɗaya hannun kuma tana riƙe da file. Ba ta cikin masu hayaniya.

Ba ta cikin masu tsayawa suna hira a hanya, kawai tafiya take zuwa school hall din

A tara candidates ne a babban hall domin wani bayani daga Principal da wasu external supervisors ne suka yi musu jawabi.

Bayan an gama…

Ɗalibai suka fara fita a hankali.

Hall ɗin ya cika da cunkoso.

Zahra tana tafiya a hankali tana ƙoƙarin kauce wa mutane, bayanta kuma Firdausi ce

Sai dai…

Wani dogon matashi daga science block ya fito da sauri, idanunsa na kan wayarsa.

Bam!

Ya bugi Zahra da ƙarfi. File ɗinta ya faɗi, takardu suka warwatse

Ita kanta ta ɗan ja baya saboda ƙarfin bugun. Sai dai kafin ta gama daidaita kanta…

Yaron ya kalle ta na daƙiƙa ɗaya, ya kuma ci gaba da tafiyarsa, tamkar babu abin da ya faru.

Firdausi ta zaro ido

“Excuse me!” Ta ce, Amma bai tsaya ba

A hankali Zahra ta sunkuya ta tattara papers ɗinta, ta gyara hijab ɗinta, ta ɗauki handbag ɗinta.

Sannan…

Ta ɗaga kanta.

“Kai…” Muryarta ta fito sai da bada kara ba, amma akwai wata irin izzah a cikinta da ta sa yaron ya tsaya. Ya waiwayo

Ta ɗaga hannu alamar ya dawo

Ba tare da ya san dalilin da ya sa yake jin dole ya bi umarninta ba… Sai ya dawo.

Ya tsaya a gabanta…

Ta ɗan ɗaga idanunta ta kalle shi

Ba fushi a fuskarta, amma kallon ya isa ya sa ya ji kamar ya raina kansa

Ta ce cikin nutsuwa,

“Ka bugeni.”

Ya ɗan ɗaga kafaɗa

“So?”

Firdausi ta yi yunƙurin magana.

Zahra ta hana ta da ɗan kallon gefe.

Sannan ta maida idanunta kansa.

“Saboda na yi shiru… ka ɗauka za ka raina ni ne?”

Yaron ya haɗe gira

“I didn’t do it intentionally.”

Ta yi ɗan murmushi.

“Really?” Ta ɗan matsa kusa da shi.

“Toh idan ba da gangan ka yi ba…ina kalmar I’m sorry?”

Ya yi shiru.

Mutane suka fara tsayawa

Wasu na kallonsu

Ta ci gaba.

“Ko a gidanku ba a koya maka cewa idan ka yi wa mutum laifi, ko ba da gangan ba, ka nemi afuwa?”

Yaron yayi folding hannayensa

“Ba zan taba miki yadda a school din nan suke miki ba, na buge ki ne kuma nace ba intentionally bane”

Zahra ta gyara file ɗinta Sannan ta ce,

“Listen carefully!! Humility is a choice”

“But manners… are compulsory”

Ta ɗan dakata.

“Okay dan bana magana? Na taba rokon wani akan suyi respecting dina? Mutunci ba ya nufin mutum ba shi da bakin magana bane”

Sai ta nuna sa da ɗan yatsarta

“Kada ka sake kuskuren raina wani saboda ya zaɓi nutsuwa”

Yanzu gaba ɗaya wajen ya yi tsi Ana kallon ikon Allah

wani Teacher da yake wucewa ya tsaya, ya kalli yaron.

“Young man…Aren’t you going to apologize?”

Yaron ya sauke kai.

“I’m… sorry.”

Zahra ta gyara handbag ɗinta.

Ta ce “it’s okay! At least now…”

“…you’ve learnt something.”

Ta juya cikin nutsuwa, kafin ta yi taku uku… sai ta tsaya ba tare da ta waiwayo ba

Ta ce,

“Next time …respect people before they demand it.”

Ta ci gaba da tafiyarta.

Babu wanda ya sake cewa komai.

Firdausi ta bi bayanta tana murmushi da suka yi nisa… ta riƙe hannun Zahra.

“Wallahi da ni ce… sai na mare shi.”

Zahra ta yi dariya kaɗan

“Mari?”

Firdausi ta gyada kai.

“Eh mana.”

Zahra ta girgiza kai.

“Mari yana warkewa.”

Ta ɗan yi shiru

Sannan ta ƙarasa da wata irin nutsuwa.

“Amma kunyar da mutum zai ji idan aka tuna masa tarbiyyarsa… ita tana daɗewa.”

Firdausi ta tsaya cak.

Ta kalli Zahra.

Sai kawai ta fashe da dariya.

“Wallahi Zahra… ke daban ce.”

Zahra ta yi murmushi kawai

Ta ci gaba da tafiyarta

Bayan kammala dukkan jarabawanta…

Rayuwar Zahra ta ɗan sauya.

Ba wai saboda ta samu wani sabon abu ba… Sai don karo na farko cikin watanni da dama, ta samu lokacin da za ta huta.

Da safe za ta taimaka wa Mami da wasu ƙananan abubuwa a gida musamman gyaran part din abbah ko girkin Abbah

Wani lokaci kuma ta zauna da Abbah suna hira a library.

Idan Ya Umar yana gida kuwa…

Sun dunga hira, ko kuma yayi ta tsokanarta kamar ba kanwarsa ba sai ka dauka mate dinta ce yadda suke yi

Ko da ta je makaranta ma…

Ba don karatu bane take zuwa sai don dama classmate dinta suna ss2 ne dama

A haka rayuwa take tafiya.. Kwanaki suka koma makonni, wata rana da rana…

Zahra na zaune a parlour tana kallon wani documentary tare da Abbah.

Wayarta ta fara vibrating.

Firdausi Calling…

Da ta ɗauka…

Tun kafin ta yi magana…

Firdausi ta yi ihu

“Zahraaaaa!

WAEC result is out!”

Zuciyar Zahra ta buga

Ta yi saurin miƙewa tsaye.

“Really? Yaushe aka sake?”

“Wallahi! Na duba nawa yanzu!”

Ba ta sake jiran wani abu ba ta katse wayan, Tana kallon Abbah tace

Abbah waec result is out”

Ko amsar da zai bata ba ta jira ba ta gudu zuwa study room

Laptop ɗinta ta buɗe

Candidate number

PIN

Check Result.

Numfashinta ya tsaya, ta danna.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.