Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 36 of 59

Chapter 35

Rayuwa haka ta cigaba da tafiya

Kwanaki suka zama makonni, makonni suka rikide zuwa watanni.

Tun bayan registration ɗin da Zahra ta yi na WAEC, NECO da JAMB, gaba ɗaya rayuwarta ta sauya

Duk wanda ya san Zahra tun farko zai fahimci canjin da aka samu a tattare da ita

Ba wai saboda ta daina dariya ko wasa ba… A’a. Sai dai yanzu tana da manufar da take son cimma

Kullum idan aka tashi daga makaranta, kai tsaye gida take dawowa. Da zarar ta ci abinci ta yi sallah, sai ta ɗauki littattafanta ta nufi garden ɗin gidan, wajen ya zama tamkar classroom ɗinta.

Ƙarƙashin wata babbar bishiya mai yalwar inuwa aka tanadar mata tebur da kujera. A kan teburin akwai littattafan Mathematics, English, Physics, Chemistry, Biology, Government da sauran subjects ɗinta, kowanne a jere tamkar ƙaramin library.

Sau da yawa idan mutum ya zo wuce wa ta wajen, zai same ta ne ta sunkuyar da kanta ne tana karatu, ko kuma tana rubuce-rubuce a wani jotter.

Har housemaids sun saba, da zarar lokacin cin abinci ya yi, zasu je su same ta

“Baby, Mami tace ki zo ki ci abinci.”

Sai ta ɗaga kai da ƙyar.

“Ku aje mana please, idan na shigo zan ci”

Da farko Mami na matsa mata ta shiga ciki, daga baya ta haƙura

Ta fahimci Zahra idan ta sa abu da zuciya, sai ta gama shi ake gane kanta

Wata rana da yamma…

Abbah ya fito daga office dinsa na gidan a gajiye, yana shiga compound idanunsa suka sauka kan garden, can ƙarƙashin bishiya ya hango Zahra

Ba ta ma san ya shigo ba.

Headset na kunne, biro na hannunta, calculators biyu a gefe, papers cike da calculations sun warwatse a gabanta

Abbah ya tsaya daga nesa yana kallonta

Murmushi ya bayyana a fuskarsa.

“Ya Allah ka albarkaci iliminta ka ma rayuwarta albarka” Ya furta a hankali. Bai ƙarasa wajenta ba, ya juya ya shiga main entrance din

A dining da daddare bayan suna cin abinci

Abbah ya kalli Zahra.

“Baby.”

Ta ɗago.

“Na’am?”

“Yaushe kika huta?”

Ta yi dariya.

“Ban huta ba, tukun”

Ya ɗaga gira

“Meaning?”

“Karatu nake yi.”

Mami ta girgiza kai

“Wallahi Zahra kin fara bani tsoro, ko yaushe kina garden, akwai gajiya fah, ki dinga hutawa mana.”

Zahra ta yi murmushi.

“Da zarar na gama exams ɗina zan huta sosai.”

Ya Umar ya yi dariya.

“Abbah.” Ya kira.

“Ina ganin idan Baby ta ci gaba haka, a gaba za’a ga amfanin hakan saboda ta Riga da ta Saba da hakan, dole ta yi passing.”

Abbah ya yi murmushi.

“In Sha Allah.”

Murmushi kawai tayi ta cigaba da cin abincinta

Lokaci bai tsaya ba

WAEC ta zo, Jarabawar farko…

English Language.

Tun ƙarfe shida na safe Zahra ta riga ta shirya

Abbah da kansa ya raka ta makaranta

Kafin ta sauka daga mota ya riƙe hannunta.

“Nervous?”

Ta yi murmushi.

“A little.”

Ya shafa kanta

“Ki shiga, ki rubuta abin da kika sani kada ki ji tsoro, and make sure ki fara da addu’a”

Ta gyada kai.

“In Sha Allah.”

Haka jarabawa ta ci gaba

Paper bayan paper.

Ko da yaushe idan ta dawo gida, ba za ta fara hutawa ba sai ta fara duba subject na gobe

Wata rana Ya Umar ya ce,

“Baby…”

Ta ɗago.

“Hmm?”

“Kin san akwai rayuwa bayan exam ko?”

Ta yi dariya

“Ina so ne in gama da wannan”

Ya girgiza kai yana murmushi

“Perfectionist.”

Da suka gama WAEC…

Ba a jima ba NECO ta biyo baya.

Shi ma cikin ƙoƙari da addu’o’in iyayenta ta kammala.

Ga JAMB data yi

Wannan ne ya fi ɗaukar hankalin kowa a gidan

Abbah da kansa ya samo mata teachers na musamman da suke zuwa gida suna yi mata revision.

Ko Mummy ta yi mamakin yadda yake kashe kuɗi saboda ita. Sai dai ba ta ce komai ba

Domin duk lokacin da ta yi magana, Abbah ba ya sauraronta indai Akan Zahra ne

Ranar JAMB

Tun safe Zahra ta shirya, bayan ta gama Duk addu’o’in da zata yi ta zauna jiran Abbah. Abbah ya raka ta CBT centre.

Kafin ta shiga ya ce,

“Ki tuna da abin da kika karanta. Kar ki yi rushing. Ki karanta question sau biyu so that ki fahimci me ake cewa”

Ta yi murmushi.

“Yes, Sir.”

Ya yi dariya.

“Good.”

Ta shiga.

Sa’o’i biyu da rabi bayan haka.. ta fito.

Tun daga nesa Abbah ya gane ta, ya buɗe mata ƙofar mota tana murmushi harta karaso

“How was it?”

Ta ɗan daga ido sama kamar mai tunani tace

“Alhamdulillah! Ai Abbah In shaa Allah result din zai yi kyau

Abbah ya yi murmushi.

“In shaa Allah”

Bayan kwana biyu ne aka fara bude results din JAMB

Ranan kuma suna makaranta suna wani extra lesson, tun safe makarantar gaba ɗaya t cika da hayaniya, kowa na dubawa.

Wasu na ihu, wasu kuma fuskokinsu cike da damuwa

Zahra na zaune cikin classroom ɗinsu, ba kasafai take shiga cikin mutane ba shiyasa idan ba wai Tana tare da friends bane a compound toh zaka same ta ne a class

Firdausi ta shigo da gudu.

“Zahra!” Ta kira da sauri

“Result ya fito!”

Zahra ta miƙe tsaye

“Da gaske?”

“Wallahi.”

Mika mata wayan wata Teacher tayi ta ce

“Karba ki duba” Zahra ta karba ba tare data ce komai ba.

Hannunta ya fara rawa yayin da ta shiga portal ɗinta, password ta saka

Registration number.

Ta latsa check.

Na ɗan daƙiƙu kaɗan…

Screen ɗin ya buɗe

Idanunta suka sauka kan total score.

250 Ta zaro ido.

Firdausi ta yi ƙara

“Allahuu Akbar!”

Asiya ta rungume ta.

“Congratulations! My love”

Ko Saudat ta yi murmushi.

“Alhamdulillah, Congrats Teema”

Zahra ta kasa magana

Har sannan idanunta na kan screen.

250…

Ba mafarki take yi ba.

Firdausi ta girgiza ta.

“Ke! Wai kina jin mu kuwa?”

Nan take Zahra ta fashe da kuka

Ta rungume su ɗaya bayan ɗaya.

“Alhamdulillah…”

Shi kaɗai take ta maimaitawa

Da aka tashi makaranta taje wajen mistress dinsu ta karba waya

Abbah ta fara kira bai ɗauka ba.

Sai Ya Umar ya ɗauka.

“Baby.”

“Yaya!” Ta faɗa cikin murna.

“I got 250!”

Shiru ya yi na daƙiƙa guda.

Sai ya yi wani irin ihu.

“What?! 250?!”

Ta yi dariya.

“Yes!”

Ya Umar ya yi murmushi har kunne.

“Baby… I’m so proud of you, driver zai zo daukan ki yanzu. Abbah zai yi murna fiye da yadda kike zato.”

Zahra ta kashe wayar tana murmushi…

A haka har driver yazo ya dauke ta. Tun daga bakin gate take ta murmushi ita kaɗai. Driver ya buɗe mata ƙofa, ta fito da sauri tana rungume da handbag ɗinta.

Da shiga parlour…

“Abbah!” Ta kira da ƙarfi cikin farin ciki.

Abbah da ke zaune yana duba wasu takardu ya ɗago kai. Kafin ya ce komai, Zahra ta ƙarasa ta rungume shi.

“Alhamdulillah, Abbah!”

Ya rungume ta yana murmushi.

“Congratulations, Baby.”

Ta ɗago tana kallonsa cikin mamaki.

“Kun sani?”

Ya yi dariya.

“Ya Umar ya riga ya kira ni.”

“250…” Ya girgiza kai cike da alfahari.

“I’m proud of you.”

Ta ce “Kash Ya Umar daya daka bari na fara fada ai” dariya kawai Abbah yayi

Mami ma ta miƙe ta rungume ta.

“Allah ya ƙara basira. Allah sa matakin nasara ne”

“Ameen, Mami.”

Ya Umar kuwa yana jingine da bango yana tafa hannu.

“Baby ta yi mana abin kirki.”

Batoul ta taɓe baki ta kalli gefe.

Mummy kuwa…

Tun farkon shigowarta take kallon Zahra ba tare da ta daga ido Akan ta ba

Abbah ya miƙe tsaye.

“Baby.”

Ta ɗago.

“Ina da wani abu a gare ki.”

Ta yi mamaki.

“Na me?”

Ya yi murmushi.

“Ki je ki buɗe drawer ɗin office na

Ta ɗan haɗe gira.

“Office? Abba?”

“Yes. Ki dauko box din cikin”

Ta nufi office ɗinsa da sauri.

Da ta buɗe drawer ɗin…

Wani farin akwati mai ɗauke da tambarin Apple ne ya bayyana

Ta tsaya cak.

Hannunta ya kai a hankali ya ɗauke shi

Bugun zuciyarta ya ƙaru.

Ta buɗe…

Sabuwar iPhone ce, sabuwar fita.

Har yanzu tana cikin wrapping ɗinta.

Zahra ta zaro ido.

“Abbah…”

Ta fito da gudu daga office ɗin.

“Abbah!” Ta kira tana dariya.

“Mine?”

Abbah ya gyada kai yana kallonta cikin ƙauna.

“Yours.”

“Congratulations!!! Wannan kyautarki ce saboda ƙoƙarin da kika yi.”

Zahra ta yi ihu.

Ta sake rungume shi da ƙarfi.

“Thank you, Abbah! Thank you so much.”

Ta yi ta kissing goshinsa kamar yadda ta koya mata

Abbah yana dariya.

“Easy, Baby. Za ki karya min ƙashi.”

Parlour gaba ɗaya dariya ake yi.

Sai dai…

Mummy da Baroul, Wanda yanzu yabi jinin jikin su duk sanda su Mami suka fito suma sai su zo suga abun dake faruwa

GTa kalli wayar

Ta sake kallon Zahra

Sannan ta kalli Abbah.

“Alhaji.” Ta kira cikin sanyi

Ya amsa.

“Hmm?”

“Wato saboda ta ci JAMB ne za ka siya mata wayar da ko manya ba su da ita?”

Abbah ya kalleta.

“Eh.”

Ta yi wata ƙaramar dariya.

“Toh! Ni dai ban ga abin burgewa ba 250 ɗin nan ai ba ita kaɗai ta ci ba.”

Zahra ta sauke kanta ƙasa.

MMurmushin da ke fuskarta ya ɗan ragu.

Abbah ya ɗan yi shiru

Sai ya kalli Mummy kai tsaye.

“Hafsat…” Muryarsa ta sauya.

“Shame on you.”

Parlour ya yi tsit.

Ya ci gaba

“Kina kishi da ’yar cikinki?”

Ya girgiza kai cikin takaici

“Wallahi ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba.”

Mummy ta buɗe baki.

“Kishi?”

Abbah ya katse ta

“Yes…. Kuma abin kunya ne a gareki Yarinya ta yi abin kirki, maimakon ki ƙarfafa mata gwiwa… amma kina neman yadda za ki kashe mata farin ciki.”

Mami ta sauke ajiyar zuciya

Ya Umar kuwa ya yi shiru kawai yana kallon wani waje

Mummy ta miƙe tsaye

“Ku ci gaba.” Ta faɗa cikin fushi

Sannan ta fice daga wajen

Tana fita… Zahra ta sake murmushi

Ta buɗe wayar tana kallonta tamkar mafarki

“Abbah…” Ta faɗa a hankali

“So Beautiful.”

Ya yi dariya.

“Kin so kenan?”

“So?” Ta rungume wayar a ƙirjinta.

“I love it.”

Ranan wani Saturday da yamma

Ya Umar ya tafi garden

Ya tarar da Zahra tana ta solving Mathematics

Har ta manta da lokaci ya tafi

Ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu, sai ya ƙarasa.

“Baby.” Ta ɗago kai.

“Yaya.”

Ya zauna kusa da ita

“Kin gama da sabon duniyar naki ne?”

Ta yi dariya

“Almost.”

Ya ciro envelope daga aljihunsa ya miƙa mata.

“Take.”

Ta karɓa

Da ta buɗe…

Idanunta suka faɗa kan check din kudin

“Two hundred thousand?” Ta zaro ido tana kallonsa

“Yaya?”

Ya jingina da kujera

“Yes.”

“Na me?” Ta tambaya

Ya yi murmushi.

“Tomorrow…” Ki je solo date.”

Ta haɗe gira

“Solo date?”

“Eh! Kina stressing kanki sosai.”

“Ki fita, ki ci abin da kike so, ki yi shopping idan kina so, ki huta. Then ki dawo.”

Zahra ta yi dariya, ta matsa ta rungume shi

“Thank you! Allah ya saka da alkhairi.”

Ya shafa kanta.

“Ameen.”

“Amma fa… Kar ki kashe duka dan na sanki”

Ta yi dariya sosai

“No promises, dan ka san wacece Zahratyy”

Su biyun suka fashe da dariya.

Washegari…

Tun da sassafe Zahra ta farka cikin farin ciki

Bayan ta idar da sallar Asuba, ta zauna kan sallayarta tana karanta morning zikr ɗinta cikin nutsuwa. Ta ɗauki lokaci tana zikiri da addu’o’i, kafin daga bisani ta shafa addu’ar, ta naɗe sallayar ta ajiye a mazauninta.

Ta miƙe ta nufi balcony ɗin ɗakin. Ta ɗan buɗe labulen gilashin, hasken safiya ya shigo yana gauraye da hasken dakin, ga AC mai dadi da ƙamshin diffuser da ke ci gaba da fitar da ƙamshi cikin ɗakin

Tana tsaye tana kallon lambun gidan ne aka yi knocking sau uku a hankali.

“Come in.”

Ƙofar ta buɗe ba tare da hayaniya ba. Mai aikin gidan ta shigo cikin uniform mai kyau da safar hannu, tana jan ƙaramin cleaning trolley da ke ɗauke da kayan gyaran ɗakin.

“Assalamu alaikum, Hajiya.”

“Wa’alaikumus salam.” Zahra ta amsa ba tare da ta juyo ba.

“Fatan mun tashi Lafiya hajiya”

“Lafiya lau. Kin tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau, Alhamdulillah.”

“Good.” Cewar Zahra

“Hajiya, zan gyara ɗakin?”

“Go ahead.” Zahra ta bata amsa

“To, Hajiya.”

Ba tare da ɓata lokaci ba ta fara aikinta. Ta fara da gyara king size bed ɗin, ta shimfiɗa duvet ɗin daidai ba tare da ko da ɗan lanƙwasawa ba, ta jera decorative pillows cikin tsari, ta gyara labulen da aka buɗe kaɗan, sannan ta share duk wani ƙurar da ka iya sauka a saman furniture da glass surfaces.

Daga nan ta buɗe wardrobe kaɗan, ta ɗauko kayan da aka cire jiya ta kai su laundry basket, sannan ta maye gurbin slippers ɗin da sababbi masu tsafta da aka tanadar.

Sai ta ɗauko luxury room mist ta feshe sasanninta kaɗan-kaɗan. Nan take ɗakin ya cika da wani ƙamshi mai sanyaya zuciya, ba mai kaifi ba, irin wanda ake jin daɗinsa

Bayan nan ta shiga toilet.

Marble floor ɗin ta goge har yana walkiya, ta wanke wash hand basin da toilet bowl, ta goge shower glass ɗin har ya yi kamar babu komai a kansa. Ta canja hand towels da sababbi, ta sake jera toiletries ɗin daidai gwargwado, sannan ta tabbatar fresh flowers da ke kan vanity ba su yi yanƙwane ba.

Da ta gama, ta fito ta tsaya cikin ladabi.

“Hajiya, na gama.”

A wannan lokacin Zahra tana zaune kan armchair tana duba saƙonnin wayarta.

Ta ɗaga kai ta bi ɗakin da kallo. Komai ya koma kamar an sake shirya shi ne daga farko.

“Very neat. Thank you.”

“Babu komai, Hajiya.”

“Ki gaya wa Aunty Binta ta tabbatar an shirya min green tea kafin na sauko.”

“In shaa Allah, Hajiya.”

“Thank you.”

Ta ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa, sannan ta ja cleaning trolley ɗinta ta fita, tana rufe ƙofar a hankali ba tare da ta yi ƙara ba.

Tana fita, Zahra ta sauke wayarta, ta sake shakar ƙamshin da ya mamaye ɗakin, sannan ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fito

Ta tsaya gaban wardrobe tana zaɓen kaya.

Daga ƙarshe ta fito da wata doguwar gown mai launin sky blue, mai sauƙin kyau amma cike da elegance.

Ta haɗa ta da farin veil mai laushi

Ƙaramar agogon gold ta ɗaura a hannunta. Ta ɗauki handbag ɗinta.

Ta kalli kanta a mirror.

Murmushi ta yi.

“Not bad.” Ta ɗauki waya ɗinta.

Ta sauko ƙasa…

Perfume ɗinta mai sanyin ƙamshi ya cika wajen.

Mami da ke zaune a parlour ta ɗago ta kalleta.

“Allah ya tsare.”

“Ameen, Mami.”

Ta ƙarasa ta sumbaci goshin Mami.

Abbah ya ɗago daga newspaper ɗinsa.

“My Baby.”

Ta juya tana murmushi.

“Yes, Abbah?”

“Enjoy yourself.”

Ta yi dariya

“I will.”

Ya Umar ya jefa mata key ɗin motarsa.

“Drive safely.”

Ta kama key ɗin

“Roger that.”

Batoul ta bi ta da kallo har ta fita, ta taɓe baki

“Kullum princess.”

Da fitowarta compound, driver ya yi yunƙurin buɗe mata ƙofa.

Ta yi murmushi

“No, thank you I’ll drive myself.”

Ta shiga motarsa cikin nutsuwa, ta daidaita mirror, ta ɗaura seat belt

Ta kunna motar.

A hankali ta fita daga gidan

A stereo kuwa…

Wata soft instrumental nasheed ce ke tashi a hankali.

Zahra ta jingina da seat tana tuƙi cikin natsuwa, ko da ta tsaya a traffic light, mutane da dama suna kallonta

Ba wai saboda motar ba…

Sai saboda yadda take da wata irin nutsuwa da kwarjini gashi dama famous ce, kuma ta sauke glass din dukka

Bayan kusan mintuna talatin…

Ta isa wani luxury restaurant da take yawan zuwa idan tana son ta huta ita kaɗai

Parking ta yi cikin tsari, ta fito daga motar.

Tana shiga restaurant ɗin, ɗaya daga cikin staff ɗin ya yi saurin ƙarasowa.

“Welcome back, Ma’am.”

Ta yi murmushi kaɗan.

“Thank you.”

“Your usual seat?” Ya tambaya

“Yes.” Ta amsa

Ya jagorance ta zuwa wani gefen restaurant ɗin da ke kallon glass wall, inda ake iya ganin flowers da fountain na waje.

Shi ne wurin da ta fi so, ta zauna.

Handbag ɗinta ta ajiye a gefenta, ta cire wayarta, ta ɗan duba Instagram. Sai ta ajiye

Ba ta zo social media ba yau, ta zo ne ta huta.

Waiter ya ƙaraso.

“Your order, Ma’am?”

Farashin izzah

Hauwajay writes

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.