Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 21 of 59
Chapter 20
Zahra ta haɗiye wani abu a maƙoshi.
Firdausi tace,
"How long?"
"Almost two months."
Firdausi ta É—an kalli Zahra kafin ta sake maida kallonta kan yarinyar.
"Kin san yana da aure?"
Nan take yarinyar ta haÉ—e gira.
"A'a."
Firdausi ta nuna Zahra dake zaune shiru kamar mutum-mutumi.
"Wannan matarsa ce. Kuma yanzu ne ma suka yi wata da aure."
Ba ƙaramin mamaki yarinyar tayi ba.
"What?!"
Sai ta sake kallon Zahra sosai.
"Amma taya zan yarda?"
Firdausi bata ce komai ba sai ta shiga Instagram page ɗin Ibrahim a wayarta sannan ta miƙa mata.
Da sauri yarinyar ta karɓa.
Nan take idanunta suka sauka kan hotunan wedding É—in Ibrahim da Zahra.
Pictures masu kyau, videos, posting É—insa yana celebrating matarsa.
Baki ta taɓe cikin mamaki.
"Wallahi ni bansani ba..." tace kana gani kasan tayi mamaki. "Bai taɓa gaya min yana da aure ba."
Zahra dai tana zaune shiru tana kallonta.
"Ni ma dama ba aurensa zanyi ba." Yarinyar ta ƙarasa cikin rashin damuwa. "Kawai cin kuɗinsa nake yi."
Firdausi ta dafe kanta kaÉ—an.
"Toh dan Allah ki fita daga harkarsa. Kinga matar sa tana nan, kuma ace da dare yana fita wajen wata lokacin da yakamata yana gida?"
Yarinyar ta É—an gyara zamanta.
"Wallahi ma zan yi blocking É—insa. Amma sai ya turomin kuÉ—in da zai bani."
Zahra da tun farko bata ce uffan bane ta ce
"Nawa ne?"
Yarinyar ta kalleta.
"20k."
"Account number É—inki?" Cewar Zahra
Firdausi ta juya da sauri tana kallon Zahra.
Ita ma yarinyar mamaki ya kamata, sai kawai ta faÉ—i account number É—inta.
Nan take Zahra ta É—auki wayarta tayi mata transfer na 500k.
Kusan seconds kaÉ—an alert ya shiga wayar yarinyar.
Da sauri ta zaro ido.
"Jesus!" Zaro idanu tayi tana kallon screen É—in wayarta.
"Half million?!"
Ta miƙe tsaye tana dariya harda sallen murna.
"Wallahi nagode Anty!"
Sai ta juya da sauri tana buÉ—e WhatsApp dinta
"Yanzu ma zanyi blocking É—insa."
Nan take ta block number Ibrahim a gabansu.
"Anty ko zan iya samun number É—inki muna gaisawa?"
Zahra ta miƙe tsaye a hankali.
"Mungode."
Sai ta juya tana kallon Firdausi.
"Let's go."
Firdausi ta miƙe itama tana bin bayanta, zuciyarta cike da mamaki da kuma tausayi ga Zahra wacce duk da ciwon da take ji... har yanzu tana cikin nutsuwa da class.
Da suka shiga mota, Firdausi ta daɗe tana kallon Zahra kafin daga ƙarshe ta girgiza kai.
"Wallahi kuÉ—in yayi yawa Zahra"
Zahra na driving bata ko juyo ta kalleta ba ta ce
"Ba komai."
"Haba Zahra, 500k saboda kawai ta rabu da shi?"
Sai Zahra ta sauke numfashi a hankali.
"Ai kinji ta da kanki... yarinyar nada son kuÉ—i. Haka ne kawai zai sa ta rabu da shi gaba É—aya."
Firdausi ta ɗan taɓe baki.
"Toh amma half million fa..."
"Firdausi," Zahra ta katseta a hankali. "Idan wannan ne zai sa ta fita daga rayuwata da ta Ibrahim, wallahi ba yawa bane."
Shiru ya É—an ratsa motar, kowa da tunanin da yake yi
Can kuma Zahra ta sake magana cikin wani irin ciwon rai da ta daÉ—e tana dannewa.
"Please..." ta faÉ—a tana kallon titi. "Mai Ibrahim ya gani a jikin wannan da zai dinga binta?"
Firdausi ta kalleta.
Zahra ta girgiza kai da murmushi mai ciwo.
"Na fita da komai fa..." Wannan maganar tata ta fito ne daga zuciyar kana ji kasan taji zafi
"Kinga ni mana... na fita da kyau, ilimi, kudi, komai..." ta haɗiye wani abu a maƙoshi. "Then me yasa?"
Firdausi ta sauke numfashi.
"Ai maza kenan..." tace a hankali. "Allah kyauta."
Sai ta É—an matsa kusa da Zahra.
"Kuma ki daina comparing kanki da wata mace saboda namiji. Wallahi babu inda yarinyar nan ta kai ki."
Zahra tayi shiru kawai tana driving. Sai dai zuciyarta bata daina mata zafi ba.
A haka ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauka, Firdausi ta riƙe hannunta.
"Please ki kwantar da hankalinki yanzu. At least kin ga ita É—in ba wani serious abu bace."
Kai Zahra ta gyada mata.
"Text me idan kin isa gida." Cewar firdausi
"Toh." Ta amsa
Firdausi ta sauka ta shiga gida.
Zahra kuwa ta juya motarta ta nufi gida, zuciyarta cike da abubuwa mabambanta... ciwo, haushi, da kuma wani irin son Ibrahim da bata iya cirewa daga ranta duk da abun daya ke mata
Da Zahra ta isa gida, parking tayi a hankali kafin ta kashe motar.
Na É—an lokaci bata fito ba.
Hannunta na kan steering, idanunta kuma a lumshe.
Yanzu kam komai ya canza.
Ba kamar kwanakin baya ba da take kuka kawai tana jin tsoro. Yanzu tana da tabbaci. Tabbacin da ya zauna mata a zuciya kamar dutse.
Ibrahim yana fita wajen wata mace.
Wani numfashi ta sauke kafin daga ƙarshe ta buɗe motar ta fito.
A hankali ta shiga ciki.
Farida ce a kitchen tana gyaran kayan girki. Jin motsinta yasa ta leƙo.
"Sannu da zuwa Hajiya."
Zahra ta amsa da murmushi kaÉ—an.
"Yawwa Farida."
"Tea zan haÉ—a miki?"
"A'a."
Daga haka ta wuce sama.
Yau bata ji buƙatar kuka ba kamar kullum. Sai dai zuciyarta ta yi wani irin sakayau
Direct É—akin Ibrahim ta shiga.
Komai nasa tsaf kamar yadda ya bari da safe. Turarensa har yanzu na tashi a ɗakin. Ta ƙarasa slowly ta zauna bakin gadon.
Idanunta suka sauka kan pillow É—insa.
Sai ta tuna yadda yake kallonta da soyayya... yadda yake rungumeta... yadda yake saka ta jin kamar ita kaÉ—ai ce a duniyarsa. Sai kuma ga gaskiyar nan.
Murmushi tayi.
Wani irin murmushi mai ciwo.
"Amazing..." Ta furta a hankali.
Wayarta ta É—auka ta shiga gallery É—insu. Pictures É—in da suka É—auka ranar dinner É—insu suka bayyana.
A É—aya daga ciki Ibrahim ya rungumeta yana kallonta kamar babu wata mace a duniya sai ita.
Zahra ta daɗe tana kallon picture ɗin kafin daga ƙarshe ta kashe screen ɗin.
"Ai actor ne..." Ta miƙe a hankali ta nufi wardrobe ɗinsa.
Ta buÉ—e.
Shirts É—insa neatly arranged. Watches. Perfumes.
A hankali ta É—auki wata shirt tasa ta matso kusa da hancinta.
Ƙamshinsa.
Zuciyarta ta sake bugawa.
Duk da komai...
har yanzu tana sonsa.
Wannan ne abinda ya fi bata tsoro, sai ta mayar da shirt É—in ta rufe wardrobe.
A dai-dai lokacin ta ji ƙarar gate, ta tsaya cak.
"Ibrahim..."
Da sauri ta fito daga É—akin ta wuce nata.
Kafin ya shigo sama, ta riga ta zauna kan bed tana duba wani handout kamar mai karatu.
Bayan wasu seconds ta ji motsinsa a parlorn sama.
Sai muryarsa.
"Zahra?"
Ta É—aga kai kamar yanzu ta lura da dawowarsa.
"You're back?"
Ya shigo É—akin yana cire agogon hannunsa.
"Hmmm."
Ya tsaya yana kallonta.
Tun daga lokacin da ya shigo yake jin akwai wani abu different a tattare da ita.
Too calm.
Ba irin Zahra É—in da zai shigo ta fara tambayarsa ina ya je ba.
Ba irin wacce idan ya ɗan ɓata mata rai take showing it instantly ba.
Yau... ta yi shiru.
"Kina lafiya?" ya tambaya yana matsowa kusa da ita.
Murmushi tayi.
"I'm fine."
Ya É—an haÉ—e gira kaÉ—an.
"Sure?"
Kai ta gyada masa.
"Hmmm."
Sai ta ci gaba da kallon handout É—in hannunta.
Ibrahim ya tsaya kallonta na wasu seconds.
Wani irin uneasy feeling ne ya ratsa shi.
Bai san me yasa ba... amma wannan shirun nata ya fi basa tsoro fiye da surutunta
Daren ranar kuwa, bayan sun yi dinner cikin nutsuwa kamar komai lafiya, Zahra ta wuce É—aki ta kwanta da wuri.
Ibrahim kuwa ya daÉ—e a parlorn sama yana danna waya.
Sau biyu yana kiran Pretty... amma busy yake nuna masa, canza dayan number ta yayi yana kira ya shiga, nan ya gane kamar tayi blocking dinsa ne. Ya haÉ—e gira.
"What's wrong with this girl?"
Ya sake kira.
Still no answer.
Wani ɗan haushi ne ya taso masa. Tun da ya san yarinyar, bata taɓa ignoring calls ɗinsa haka ba.
Sai ya tura mata message.
"What's going on?"
Blue tick ta yi amma babu reply.
Yanzu kam abin ya fara bata masa rai. Da ƙyar ya jira kusan minti talatin sannan ya miƙe ya ɗauki key ɗin mota.
A hankali ya leƙa ɗakin Zahra, ya same ta kwance kamar mai bacci.
Sai ya fita.
Kusan ƙarfe goma sha ɗaya ya isa unguwar da Pretty ke zama. Parking yayi a waje sannan ya fito.
Da farko knocking yake yi amma babu wanda ya buɗe, ya kira ta. Ta ƙi ɗagawa.
Har zai juya cikin haushi sai kuma ƙofar ta buɗe.
Pretty ta fito.
Sai dai yau ba irin yadda take tararsa da fara'a ba.
Tsaye tayi a bakin ƙofa hannu a ƙirji tana kallonsa.
"What?"
Ibrahim ya haÉ—e gira.
"What kind of attitude is this?"
Ta yi wata dariya mai raini.
"Attitude kuma? Bayan ka ɓoye min kana da mata?"
Wani irin mamaki ya kama shi.
"What?"
"Oh please." ta katse shi. "Ka yi aure har wedding pictures full Instagram amma kana pretending single wajen mutane?"
Ibrahim ya tsaya kallonta.
A karo na farko ya rasa abin cewa, Dakyar yace "Who told you?"
Pretty ta taɓe baki.
"Does it matter?"
Ya matso kusa da ita.
"So wannan ne yasa kika fara ignoring dina ?"
Ta yi dariya.
"Ibrahim ka raina ni ne?"
Ya dafe kansa.
"Listen..."
"A'a." ta katse shi da sauri. "Ni ba drama zan yi ba. In fact, thanks for the money."
Ya É—ago kai da sauri.
"What money?"
Ta yi murmushi tana É—aga waya.
"Half million fa. Your wife is classy Wallahi"
Gabansa ne ya faÉ—i.
"Wait... Zahra ta zo nan?"
"Not just her. Har da kawarta."
Wani irin shiru ya ratsa shi.
Pretty ta cigaba,
"Kuma wallahi matar ka ta bani respect. Ba irin yadda nake tunanin zata zo tana zagi da iskanci ba."
Ibrahim ya haÉ—e fuska sosai.
"Ta ce miki me?"
"Nothing much." Pretty ta taɓe baki. "Kawai ta roƙe ni politely na fita daga harkarka."
Sai ta ɗan tsaya kafin ta ƙara da,
"Kuma gaskiya... ban san kana da mata mai kyau haka ba."
Wannan maganar ta sake É—aga masa hankali.
"Pretty..."
"Please." Ta É—aga masa hannu. "Ni ban son problem. Kuma daga yau kar ka sake zuwa nan."
Sai ta ƙara kallonsa sama da ƙasa.
"Kuma honestly? Ka ci sa'a."
Tana gama faɗar hakan ta juya ta shiga ciki ta rufe ƙofa.
Ibrahim ya tsaya a wajen kamar an dasa shi, zuciyarsa cike da mamaki, haushi, da kuma wani irin shock.
Zahra ta gano komai knn? Kuma mafi damuwa... bata nuna masa komai ba.
Wani numfashi ya sauke yana shafa kansa kafin daga ƙarshe ya juya ya koma mota.
Duk hanyar dawowarsa gida jikinsa babu ƙwari, a karo na farko tun bayan aurensu... Ya fara jin tsoron nutsuwar Zahra.
Lokacin da Ibrahim ya isa gida dare ya riga yayi sosai.
A hankali yayi parking a compound É—in gidan kafin ya kashe motar, ya É—an dauki lokaci bai fito ba.
Kalaman Pretty ne ke ta dawo masa.
"Your wife is classy..." Sai kuma yadda ta ce:
"Ka ci sa'a."
Wani numfashi ya sauke yana dafe goshinsa, Yanzu kam ya tabbatar Zahra ta san komai.
Kuma abinda ya fi dagula masa kai... yadda take acting normal.
Ba kuka. Ba faÉ—a. Ba tambaya. Nothing Nothing
Komai nata cikin nutsuwa, wannan ne ya fara tsoratar da shi. A hankali ya fito daga motar ya shiga ciki.
Gidan gaba É—aya shiru, ya haura sama direct.
Da ya buÉ—e É—akin su, light É—in bedside lamp kaÉ—ai ke kunne.
Zahra na kwance gefe guda na gadon, blanket ya rufe rabin jikinta. Daga gani bacci take cikin nutsuwa
Ibrahim ya tsaya bakin ƙofa yana kallonta, na wasu seconds bai motsa ba.
Wata irin damuwa ce ta tokare masa zuciya.
"Why didn't she say anything..." Ya furta a hankali.
A hankali ya ƙarasa ciki ya cire agogon hannunsa sannan ya zauna bakin gadon. Idanunsa na kanta.
Ko yanzu ma... tana da kyau sosai.
Beautiful. Soft. Calm. But ya maganar contract???
Sai zuciyarsa ta ƙara nauyi.
Ya tuna yadda ta zo É—akinsa jiya da daddare ta rungumesa tana cewa ta missing É—insa, ashe duk a lokacin tana sane
Wani irin guilt ne ya cika masa ƙirji.
A hankali ya miƙa hannu ya gyara mata gashin daya rufe kan fuskarta.
Zahra bata motsa ba.
Shi kuwa ya daɗe yana kallonta kafin daga ƙarshe ya miƙe ya shiga toilet yayi wanka.
Bayan ya fito, ya kashe sauran lights É—in É—akin sannan ya kwanta kusa da ita.
Sai dai...
Bacci ya ƙi zuwa masa.
Kowane lokaci sai ya tuna Zahra na zaune a gaban Pretty cikin nutsuwa.
Yana tunanin:
Ta yi kuka ne?
Ta ji zafi ne?
Me yasa bata tambaye shi ba?
Ya juya yana kallonta a hankali.
Har lokacin tana bacci.
Sai ya É—an matsa kusa da ita ya rungumota ta baya.
Wani numfashi ya sauke a hankali yana lumshe ido.
"Sorry..." Ya furta ƙasa-ƙasa.
Bai ma san ko saboda me yake bada haƙurin ba.
Saboda ya cutar da ita?
Can cikin dare, Zahra ta buÉ—e idanunta a hankali. ÆŠakin gaba É—aya duhu ne sai hasken bedside lamp mai dan haske.
Ibrahim na bacci sosai, hannunsa har yanzu rungume da ita, ta tsaya na É—an lokaci tana kallonsa. Wani irin ciwo ya sake tokare mata zuciya.
"Me yasa..."
Ta furta a hankali cikin ranta kafin ta cire hannunsa daga jikinta a hankali kar ya farka, ta miƙe slowly daga kan gadon.
Wayarsa na gefen pillow, gabanta na bugawa ta É—auka
Kamar jiya, ta kamo hannunsa a hankali ta manna yatsansa akan thumbprint É—in.
Nan take wayar ta buÉ—e, da sauri ta shiga messages
Gabanta ya sake faÉ—uwa ganin latest message daga Pretty.
"Ko karyan da kayi min ba zan kara yarda da Kai ba. Don't ever text me again."
Sai kuma wani.
"I'm done. Focus on your wife."
Zahra ta daÉ—e tana kallon screen É—in, wani rin sanyi ne ya ratsa zuciyarta... wani mixed feeling ne da bata iya fassara wa
A hankali ta shiga chat É—in gaba É—aya.
Ta karanta yadda Ibrahim ke mata magana cikin sweet words.
Yadda yake tura mata kuÉ—i.
Yadda yake tambayarta ta ci abinci ko a'a.
Wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, sai dai bata yi kuka ba, wannan karon ba kuka take ji ba...
Daga ƙarshe ta yi blocking number ɗin Pretty daga wayarsa sannan tayi deleting gaba daya
Sai kuma ta tuna.
"Lovie Dovie..."
Da sauri ta shiga search, nan kuwa number É—in ya fito
Hannunta ya fara rawa.
Da sauri ta É—auki number É—in ta tura zuwa wayarta.
Na wasu seconds ta tsaya kallon screen É—in.
Zuciyarta na mata nauyi sosai.
"Mutum nawa ne...?" Ta furta a hankali.
Sai kuma ta kashe screen É—in wayar ta ajiye masa ita daidai inda ta É—auka.
A hankali ta dawo ta kwanta.
Wannan karon bata sake kallonsa ba, ta juya baya gare shi tana lumshe idanunta.
#Jiddatulkhayr writes
#08110615256
https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t
Book 1
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.