Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 52 of 59

Chapter 50

Ana daf da kiran sallar Magrib… Zahra na zaune a ɗakinta

Ta gama shirya sabbin atamfofin da Anty Binta ta jera mata a wardrobe

Lokaci zuwa lokaci sai ta buɗe ƙofar wardrobe ɗin ta sake kallonsu tana murmushi

A daidai lokacin… Sai ta ji ƙarar motar Ya Umar ta shigo compound

Ba ta tsaya tunani ba, ta fito da sauri, tun ɗazu take jiran dawowarsa ta basa labari, ta sauko ƙasa

Tana isa harabar gidan…

Ta hangi Ya Umar yana saukowa daga motarsa

Mai aiki yana sauke wasu manyan akwatuna guda biyu daga boot din motar Ya Umar

Manya ne, masu ƙarfi kuma masu kyau wanda ake yayi kuma da tsada

Ta karasa wajen Tana murmushi

“Yaya sannu da zuwa”

Ya Umar ya kalle ta

“Baby.”

Ta ƙarasa kusa da shi, ta nuna akwatunan

“Waɗannan fa? Taru ka fara ne?”

Ya ɗan jingina da motar yana murmushi

“Naki ne.”

Ta zaro ido

“Nawa kuma?”

Ya gyada kai

“Eh”

“Abbah ne ya ce in siya miki manyan akwatuna masu kyau”

“Saboda duk kayanki za su shiga ciki”

Zahra ta dafe baki

“Ya Allah… Nagode.”

Ya Umar ya riƙe ƙugu yana kallonta.

“Duk wannan farin cikin saboda akwati?”

Ta yi dariya

“Ba ka gane ba, suna da kyau sosai, latest ne fa”

Ya girgiza kai yana murmushi

“Toh ai shikenan”

Da daddare.. Bayan an idar da sallar Isha’i…

Mami na ɗakin Zahra, ta kira Mama Ladi da Anty Binta da auran masu aikin gidan

Bayan Duk sun haɗu, Ta ce

“Ku fara shirya kayan Baby, gobe ba na son ace zaa yi ta gaggawa”

“Toh Hajiya” Suka amsa gaba ɗaya

Aka fito da manyan akwatunan biyu, aka buɗe su a tsakiyar ɗakin Zahra

Mami na tsaye tana ba da umarni

“Wannan atamfofin…”

“A jera su a wannan akwati”

“Abayas kuma a can”

“Hijabai a ware”

“Takalma a saka a pouch bag ɗinsu”

“Perfumes kada su zube.”

“Jewelleries kuma a cikin ƙaramin box din can”

Mama Ladi da Anty Binta kuwa… sai aiki suke yi cikin tsari kamar yadda Mami take faɗa

Zahra kuwa… tana auna gefen gado

Hannunta riƙe da pillow sai kallonsu take yi

Lokaci zuwa lokaci kuma sai ta tashi

“Anty Binta wannan ba a nan za a saka shi ba”

Ko kuma ta ce

“Mama Ladi Please wannan hijab ɗin kar ya yi squeeze”

Mama Ladi ta yi dariya

“Hajiya Baby… ba zamu ɓata miki ba, aikinmu ne wannan”

Mami ta kalli Zahra, ta girgiza kai

“Toh uwar mutane, kina zaune can kina bada directive”

Zahra ta yi dariya

“Ba haka ba ne, Ina dai son komai ya kasance cikin tsari”

Ya Umar kuwa ya shigo ɗakin daidai lokacin, ya jingina da ƙofa

Ya ɗan kalli yadda aka cika ɗakin da kaya, sai ya ce da dariya,

“Baby… kin tabbata school kuwa zaki koma? Ko boutique za ki buɗe?”

Duk suka kwashe da dariya..

Zahra ta ɗauki pillow ta jefa masa

Ya kauce, pillow ɗin ya faɗi ƙasa

Ya Umar ya ɗauke shi, ya mayar mata

“Kiyi ki bar mana gida, dama mun gaji da ke”

Zahra ta yi dariya ta ce

“Yaya Dan Allah goooo”

Ta kalli akwatunan da a hankali suke cika da kayanta, sai zuciyarta ta buga

Yanzu kam…

Gaskiya ta fara fahimtar cewa saura kwana ɗaya kacal…

Sai kuma taji wani iri kamar zata yi kuka

Bayan kusan awa guda…

Aka kammala komai

Duk sun gama jera mata su, ta kalli aikin, ta gyada kai cikin gamsuwa.

“Alhamdulillah! Haka nake so”

Mama Ladi da Anty Binta suka rufe zip ɗin manyan akwatunan, suka mayar da su gefen wardrobe

Mami ta waigo ta kalli Zahra

“Yanzu dai kin shirya”

Zahra ta yi murmushi

“In shaa Allah.”

Mami ta shafa kafadarta

“Ki kwanta da wuri! Gobe akwai abubuwa da yawa.”

“Toh Mami.”

Da Mami da masu aikin suka fita…

Zahra ta kalli akwatunan nata, ta yi murmushi ita kaɗai. Sai ta zauna bakin gadonta

Ta ɗauki wayarta, ta shiga WhatsApp

Nan take ta yi conference call da Firdausi, Asiya da Suhaima.

Ba a jima ba… Kowa ya shiga

Firdausi ce ta fara magana

“Madam Off-campus!”

Duk suka yi dariya.

Zahra ta girgiza kai.

“Ku daina fa”

“Kin gama packing?”Asiya ta tambaya

Zahra ta waiga gefen akwatunan

“An gama komai! Mami ta saka an shirya min ɗazu”

Suhaima ta yi murmushi

“Ni ma na gama, na saka kayana tun da yamma”

Firdausi ta ce

“Ni ma yanzu na rufe akwati.”

Aasiya ta ce

“Same here. Na bar saura kayan da zan sa gobe kawai.”

Firdausi ta yi dariya

“Huh? Wasa wasa dai gobe zamu koma school”

Suhaima ta amsa da dariya

“Hmm, ki Bari dai, Rayuwar girki, rayuwar wanki, rayuwar biyan bills”

Asiya ta ce

“Kuma rayuwar assignment babu mai tayaki”

Duk suka fashe da dariya.

Zahra ta ce

“Allah Ya taimake mu.”

“Ameen”Suka amsa gaba ɗaya.

Firdausi ta ce

“Ku kwanta da wuri, gobe akwai aiki”

Suhaima ta ce

“Kuma kar wani ya makara.”

Aasiya ta ƙara da cewa

“Da safe zan yi texting ɗinku.”

Zahra ta yi murmushi

“Shikenan! Good night girls.”

“Good night” Suka amsa ɗaya bayan ɗaya

Daga nan…

Kowa ya fita daga conference call

Zahra ta ajiye wayarta a gefen gadonta, ta sake kallon manyan akwatunan nata.

Sai ta sauke numfashi cikin murmushi

“Gobe…” Ta faɗa a hankali.

“Anya zan iya 24/7 ba tare da Mami, Abbah especially Yaya ba?”

Toilet ta wuce tayi alwala, tana fitowa ta kwanta kan gado ta kashe bedside lamp

Washe gari…

Tun kafin fitowar rana gidan ya riga ya cika hayaniya

Ƙarar masu aiki na kai-komo, ƙamshin arabian tea da ake dafawa, da kamshin suyan da ke yawo a cikin kitchen din suka haɗu suka ba da wani irin kamshi na natsuwa

Zahra ta koma ɗakinta ta karanta Al-Qur’ani na ɗan lokaci kafin ta fara shirin ranar

Karfe takwas na safe…

Kowa ya hallara dining

Abbah na kan kujerarsa ta kullum, Mami na gefensa, Ya Umar ya iso bayan ƴan mintuna

Mummy da Batoul ma suka zauna a ɗaya gefen teburin

Wanda ma basu gaisa ba nan suka samu aka gaisa

Sai dai Zahra ta lura Ya Umar lokaci-lokaci yana kallonta yana murmushi, ta gane saboda yau ce ranar da za ta koma off-campus tasan dole ne ma yayi missing ɗinta

Abbah ya ɗaga kai

“Baby kin gama shirya komai?”

Ta gyada kai

“Eh Abbah, komai ya kammalu”

“Good” Ya ce yana ɗaukar cup ɗin shayinsa

“Kada ki manta, idan kina buƙatar wani abu, ko da ƙarfe nawa ne, ki kira ni za’a miki providing kuma a Kai miki can”

Ta yi murmushi

“In shaa Allah.”

Mami ta ƙara da cewa,

“Kuma kar ki cika cin abincin waje, ki riƙa girki idan kina da lokaci, danna sanki da rashin son girki”

Zahra ta ɗan turo baki

“Mami…, girki againnn”

Duk suka yi dariya, Bayan breakfast kowa ya gama watsewa

Can Zahra ta nufi ɗakin Mami, ta tarar da ita tana wani aiki ne

Ta zauna kusa da ita

“Mami…”

Mami ta ɗago

“Na’am Fatima”

“Na yi magana da Firdausi da Asiya da Suhaima.”

“Mun yanke shawarar zama tare.”

Mami ta ɗan yi shiru

Ta kalleta cikin nutsuwa

“Kun san juna, kuma idan haka zai fi muku sauƙi, ba komai”

Amma sai ta ɗaga yatsa

“Abu ɗaya zan ce…”

“Kar zaman ƙawance ya sa a manta da karatu”

Zahra ta yi murmushi

“In shaa Allah Mami hakan ba zai faru ba”

Mami ta shafa kumatunta

“Toh Allah ya yarda”

“Ameen.”

Can around 11am, bayan Abbah ya bayar da directive… Nan take aka fara fitar da kayan abinci zuwa boot na motocin gidan

Masu aiki biyu suka fito da manyan cartons, Shinkafa, taliya, Semovita, spaghetti, macaroni, Tin tomatoes, Vegetable oil, Buckets, Mop, kayan tea da sauran abubuwan buƙata

Driver da masu aikin suka riƙa kai-komo tsakanin store da boot na motar, ana jera komai cikin tsari

Abbah ya fito ya tsaya yana kallonsu

“Ku tabbatar babu abin da aka manta”

“Toh Alhaji” Suka amsa

Zahra dake Snapchat tana chatting, ta miƙe zata buɗe window nan taga abun dake faruwa a compound, da sauri ta sake labulen ta shiga bathroom

Can bayan ta gama wanka ta fito, ta shafa lotion tare da shafa light perfume

Ta saka wata atamfa mai launin blue da pink ɗinki mai sauƙi but elegant, tayi ɗaurin ɗankwali sannan ta yafa blue veil

Ƙaramin agogonta na azurfa da bracelet ɗinta suka ƙara mata kwarjini

Ta ɗauki wayarta da handbag, ta fito ƙasa

Mami ta kalleta daga parlour

“Baby.”

Ta amsa

“Na’am Mami.”

“Ki je ki yi wa Mummy sallama kafin ku tafi”

Ba tare da gardama ba… ta gyada kai

“Toh Mami.”

A hankali ta nufi ɓangaren Mummy, ta yi knocking

“Shigo.”

Ta tura ƙofar ta shiga, ta tarar da Mummy da Batoul zaune kan sofa, da alama hira suke yi

Zahra ta yi murmushi cikin ladabi

“Barka da gida Mummy”

“Yauwa shalelen Babanta” Mummy ta amsa

Ta ƙarasa kusa da ita, ta durƙusa

“Mummy… zan tafi ne yanzu, shine na zo na yi miki sallama”

Mummy ta ɗan yi shiru

Sai ta ce,

“Allah Ya kiyaye hanya! Ki je lafiya, ki dawo lafiya”

Zahra ta yi murmushi

“Ameen! Nagode Mummy.”

Mummy ta miƙe ta nufi ƙaramin fridge da ke parlon, ta buɗe shi

Ta fito da wani takeaway mai kyau

Ta buɗe, ƙamshin danbun naman kaza da aka soya kyau ya cika parlon

Ta zuba mata yaji mai ƙamshi, hadi da garwayawa

Ta sake ɗauko wani takeaway a cike da yaji mai ƙamshi, ta rufe takeaway ɗin.

Ta miƙa mata su

“Ga wannan, zai tai maka miki musamman yajin, idan kuma kina bukatar wani abu just let me know”

Zahra ta karɓa da hannuwa biyu, fuskarta cike da mamaki

“Nagode sosai Mummy Allah Ya saka da alheri.”

Mummy ta gyada kai kawai

“Allah Ya kiyaye.”

Zahra ta sake yi musu sallama, ta juya ta fita

Ƙofar na rufewa…

Batoul ta juya tana kallon Mummy da mamaki

“Mummy…Gaskiya ban gane ba, kamar kin yarda da su yanzu”

Mummy ta jingina da kujera

Wata siririyar dariya mai cike da ma’ana ta kubce mata

Ta girgiza kai a hankali

“Lallai Batoul… har yanzu yarinya ce ke”

Batoul ta haɗe gira

“Mummy?”

Mummy ta ɗan matsa kusa da ita, ta rage muryarta

“Ke dai…”

“Ki jira abin da zai faru nan ba da daɗewa ba”

“Tsarauniya zata zama….”

Ta yi murmushi mai cike da wani sirri

Batoul ta zuba mata ido. Gabanta ya ɗan faɗi, ta san wannan murmushin…

Ba ya zuwa da alheri…..

Sai dai ba ta san me Mummy ta shirya ba amma koma menene she’s happy with it

Zahra ta sauko daga benen cikin nutsuwa, murmushi ne kwance a fuskarta. A hannunta kuwa tana riƙe da ƙaramin takeaway ɗin yajin da danbum naman da Mummy ta ba ta

Tun kafin ta ƙarasa parlon, ta hango Abbah, Ya Umar da Mami zaune suna jiranta

Da ta iso, ta ɗaga takeaway ɗin tana murmushi

“Mummy ce ta bani”

Abbah ya kalli abin da ke hannunta. Har ya buɗe baki zai ce,

‘Don’t use it… ki kai ɗakin Mami ki barsa acan’

Sai idonsa ya sauka kan Ya Umar da ke tsaye a wajen. Nan take ya haɗiye maganar, bai ƙara cewa komai ba

Maimakon haka, ya yi murmushi kawai

“Let’s go?”

Ya Umar ya miƙa mata hannunsa

“Slay Mama”

Ba tare da wata-wata ba Zahra ta saka hannunta cikin nasa

Mami ma ta miƙe daga kujerar da take zaune

“Ni kuma bari na wuce ɗaki.”

Ta ɗan matso kusa da Zahra, ta shafa kanta cikin tausayi da kauna irin ta Uwa

“Baby, Allah Ya tsare hanya, Ya ba ku sa’a”

Ta ɗan dakata kafin ta ƙara da murmushi

“Kuma… kar ki canza halin da kuma sanki da shi, kiyi amfani da nasihan da muka miki”

Nan take Zahra ta zaro ido tana kallonta

“What?” Sai ta ɗan matso kusa

“Mami… ba da ke za a je ba ne?”

Mami ta yi dariyar da bata son ta saka Zahra Jin wani iri

“Eh mana”

Da sauri Zahra ta kwace hannunta daga na Ya Umar.

“Ai shi kenan!” Ta juya da sauri ta nufi Mami

“Mami, mu tafi tare!”

Mami ta yi dariya tana buɗe mata hannu, Zahra kuwa ta rungume ta tamkar ƙaramar yarinya. Abbah da Ya Umar suka kalli juna suka yi murmushi.

Ya Umar ya girgiza kai yana dariya.

“Wallahi Mami, ni dai na rasa matsayina. Da zarar Zahra na nan, ni ba ni da wani amfani.”

Zahra ta leƙo daga jikin Mami ta masa gwalo.

“Exactly!”

Suka cika parlon da dariya, har Abbah da ba kasafai yake yin dariya da ƙarfi ba sai da ya saki dariyar da ta sa yanayin moments dinsu ya ƙara cika da farin ciki

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.