Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 40 of 59

Chapter 38

Washegari tun da sassafe…

Mummy ta shirya cikin wata atamfa mai tsada, handbag ɗinta na rataye a kafaɗa yayin da Batoul ke biye da ita har bakin mota

“Batoul, idan na kira ki ki ɗaga waya.”

“Okay Mummy.”

“Make sure kin saka ido, ki makale a parlon, sannan kuma ni Ina Jin zan Kai dare kafin na dawo”

“Safe journey” Batoul ta fad’a

Da motarta ta fice daga compound Batoul ta juya ta koma ciki

Mami kuwa na zaune a parlour tana kallon sunnah tv ana wani program da take so, yayin da Abbah yana office dinsa na gidan kamar yadda ya saba. Ya Umar ma yana gida saboda ranar hutunsa ce.

Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya…

Wata Napep ce ta tsaya a bakin gate.

Mai gadi ya leƙa jin an fara knocking

“Waye?”

“Asiya da Firdausi ce, mun zo wajen Zahra ne”

Da Jin sune ya buɗe musu gate suka shiga, gaishe sa suka yi sannan suka wuce ciki

Suna shiga parlour, suka tarar da Ya Umar zaune kan kujera, laptop na gabansa, yana duba wasu takardu.

Da sallama suka shiga dukkansu

“Assalamu alaikum.”

Ba tare da ya ɗago kai ba ya amsa

“Wa alaikumus salam.”

Sai bayan wasu daƙiƙu ya ɗaga idanunsa ya kalle su

“Lafiya?”

“Lafiya lau, Yaya Umar.” Cewar Asiya

Firdausi ta masa wani kallo, irin tambayar rainin hankalin da zai musu kenan

Ya gyada kai kawai, ya cigaba da abun da yake yi

Asiya tayi murmushi ta ce

“Ya Umar mun zo wajen Fatima ne”

“Zahra tana sama.”

Shi kaɗai ya faɗa, ya maida hankalinsa kan laptop ɗinsa.

Firdausi ta yi ƙasa da murya

“Wai kullum haka yake ne?”

Asiya ta danne dariya

“Mu tafi kawai.”

Suka haura sama.

Da suka shiga ɗakin Zahra Dukansu suka tsaya cak, Idanunsu yana yawo cikin ɗakin gashi babu kowa

Firdausi ta buɗe baki

“Zahra na jin dad’i gaskiya”

Asiya ta taɓa labulen

“Ni kam ban taɓa ganin ɗakin da ya haɗu haka ba, sai kace amarya?”

Kafin su ƙara magana… Ƙofar toilet aka buɗe

Zahra ta fito cikin doguwar rigarta zuwa gwiwa, Tana goge hannunta towel dake ɗigon ruwa

Da ganinsu…

Ta yi wata irin dariya.

“Asiya! Firdausi!”

Da sauri suka rungume juna.

Firdausi ta sake kallon ɗakin.

“Ke, wannan ɗakin naki ne ko an baki wani sabon apartment ne aro?”

Zahra ta yi dariya.

“Wallahi ni ma da na dawo sai da na yi mamaki, aikin Abbah ne fah

Asiya ta gyad’a kai

“Abbahnki yana ji da ke.”

Dariya Zahra tayi ta ce “Mu je wajen Mami ku gaisa sai mu dawo”

Daga haka Duk suka nufi side din Mami, suna shiga parlourn Mami…

Ta tarbe su da fara’arta kamar yadda ta saba.

“Ah, baƙin Zahra ne ko nawa?”

Suka gaishe ta cikin ladabi, ta amsa cikin fara’a.

Mama Ladi ce ta shigo kawo wa Mami fruit, Zahra ta juya ta kalleta

“Mama Ladi, dan Allah ki dafa mana lunch mana”

Mama Ladi ta yi murmushi.

“To Anty Zahran mu, farin cikin Abbahnta”

Mami ta girgiza kai tana dariya, itama murmushin tayi

Zahra ta yi murmushin kunya

Zahra ta mike tace

“Ku zo muje can”

Sosai suka zauna suka sha hira a dakin Zahra, can aka kawo musu abinci, suka zauna suka ci tare

Firdausi ta tattara plates ɗin bayan sun gama

“Asiya, bari ni na kai kitchen.”

Ta riƙe plates ɗin ta nufi stairs, Asiya ma ta mike ta kwashe cups ta bita a baya

Sai dai… Da take saukowa, ba ta lura da wani step ba, Ƙafarta ta kauce, ta yi missing step.

Kafin ta kai ƙasa… Ta faɗo jikin wani Plate ɗin ya karkata, amma bai zube ba

Ta ɗaga kai da sauri. Ya Umar ne

Ya riƙe ta kada ta faɗi

Tana daidaita tsayuwarta…

Sai ya sake ta.

Ya gyara rigarsa kaɗan, sannan ya kalle ta da idanunsa masu sanyi

Firdausi ta haɗiye yawu

“I’m… I’m sorry.”

Ya Umar ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, Sannan ya ce cikin murya mai nutsuwa

“Ki koyi tafiya a hankali…” Ya ɗan dakata yana kallonta

“…as a lady, bai kamata kina acting like namiji ba”Yana gama magana ya wuce ba tare da ya ƙara kallonta ba

Firdausi ta tsaya tana binsa da wani irin kallo, ta murguɗa masa baki

“Mtsss Malam sai uban zafi, shi ko Baki bai sani ba” A hankali ta faɗa.

Asiya ta cije leɓenta kada ta yi dariyar dake cinta

Zahra kuwa da saukowarta kenan

Tun da ta ga abin da ya faru, ta kasa riƙe dariyarta, ta riƙe cikinta

“Wallahi ku biyu…Ban san me ya sa, ba ku taɓa jituwa ba.”

Firdausi ta taɓe baki

“Ni ma ban sani ba, Kullum kamar ni kaɗai yake ganin mai laifi”

Zahra ta sake fashewa da dariya

“Wallahi drama ɗinku yana bani joy”

Firdausi ta gyara plates ɗin

“Ni dai bari na kai kitchen.”

Zahra ta wuce parlo Asiya na biye da ita a baya Suka zauna a parlour suna hira na ɗan lokaci, a haka Firdausi tazo ta same su

Da rana ta fara ja…

Asiya ta ce

“Ya kamata mu tafi.”

Firdausi ta gyada kai. Suka miƙe tare

Zahra ta ɓata fuska ta ce

“Allah Sarki, har naji babu ɗaɗi” sai kuma ta gyaɗa kai

Lemme talk to Mami sai ku mata sallama, wajen Mami suka nufa, bayan sun shiga parlonta da sallama

“Mami, za mu tafi.”

Mami ta yi murmushi ta ce

“Har zaku tafi? Allah ya kiyaye hanya. Bari Ina zuwa”

“Ameen” suka amsa mata suna murmushi

Ta miƙe ta wuce ciki bata wani daɗe ba ta dawo rike da nylon a hannunta, ta miƙa musu

“Ku riƙe wannan ba yawa”

Suka karɓa suna mata godiya

Daga nan Zahra ta ce,

“Ku zo mu je gaida Abbah na” daga haka suka ma Mami sallama suka fita

Har study room na Abbah Zahra ta kai su, da sallama suka shiga

Abbah ya ɗago ya yi musu murmushi

“Ah… ƙawayen Baby ne ashe”

Suka gaishe shi cikin ladabi da kunya ya amsa yana tambayar su ya gida

Zahra na kallonsa ta ce

“Abbah tafiya zasu yi shine na kawo su su gaishe ka”

“Ma shaa Allah” ya ce

Ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudin da bai dan nawa bane ya mikawa Fatima ya

“Suyi kudin mota”

Suka amsa cikin farin ciki, sannan Zahra ta raka su har bakin gate, suka yi sallama

Daren ranar…

Bayan an idar da sallar Isha’i, gidan ya yi shiru kamar yadda ya saba

Abbah bai shigo daga masallaci ba, Mami kuma tana side dinsa tana gyarawa

A parlour kuwa…

Ya Umar na zaune kan doguwar kujera, laptop ɗinsa a gabansa yana duba wasu files na office.

Sai dai… kusan minti goma kenan bai samu ya karanta ko shafi guda ba

Saboda…..

“Yaya…” Muryar Zahra ta katse masa tunani

Ya ɗaga kai.

Ta karasa ta zauna kusa da shi, ta jingina da kafadunsu, bayanta kuma na jingine da kujera tana murmushi

“Na’am.”

Ta ɗan lumshe ido.

“Yaya…”

“Eh?”

“Wai me ya sa kai da Firdausi ba ku taɓa jituwa ne?”

Ya Umar ya ɗan haɗe gira.

“Waye kuma ita?”

Dariya sosai tayi ta ce

“Wannan Black beauty friend dina mana da kullum idan ta zo sai kayi mata masifa”

Da kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce “Waye ya ce miki ba ma jituwa?”

Ta fashe da dariya

“Ni mana! Kullum idan ta zo gidan nan sai ka dinga mata irin kallon nan…”

Ya ci gaba da duba laptop ɗinsa ba tare daya kulata ba

Ta matsa kusa da shi kaɗan

“A’a… Ka faɗa min gaskiya ni dai”

“Baby…”

Ta yi saurin katse shi

“Please Yaya…”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Kin san ranar farko da kika kawo su gidan nan?”

Ta gyada kai

“Eh.”

“Da ta shigo… Ba ta yi sallama yadda ya kamata ba.”

Zahra ta zaro ido

“Really?”

“Eh.”

“Na yi mata magana cikin ladabi.”

“Ta kuma ba ni amsa cikin salon rainin wayo.”

Zahra ta tuna

Sai ta fara dariya.

“Ai Firdausi haka take idan ta ji kunya.”

Ya Umar ya ɗaga gira

“Ni ban san kunya ba, abin da na sani shi ne mutum ya san yadda zai yi magana.”

Ta riƙe cikinta tana dariya

“Shi ya sa kullum idan kun haɗu…

“…ku ke kallon juna kamar za ku yi faɗa?”

Ya Umar ya ɗan murmusa

“Ba faɗa ba ne. Character correction ne”

Zahra ta fashe da wata irin dariya

“Wallahi Yaya… kai ma akwai taurin kai, halinku ne daya”

Ya ware idanu yana kallonta

“Me abun dariya anan?”

“Ta yi missing step yau saboda kai ne maybe, kasan haka ake a india fah”

“It’s Okayy?”

“Eh mana”

Ta kwaikwayi fuskarsa da maganarsa

“‘Ki koyi tafiya a hankali… as a lady…”

Ta kwaikwayi yadda ya faɗa har da haɗe gira.

Ya Umar ya kasa riƙe dariyarsa

“Baby… Allah kin raina ni.”

“Ni? Aa rufamin asiri”

Ta ci gaba da dariya tana ɗan bugun kafaɗarsa da tafin hannunta

A dai-dai lokacin… aka bude Ƙofar parlour, Mummy ce ta shigo

Sai yanzu ta dawo daga fitarta na safe

Tun daga ƙofar… Idanunta suka sauka kan Zahra da Ya Umar

Ta tsaya cak Fuskarta ta canja

Ba tare da ta ce komai ba… ta ƙarasa gabansu da sauri.

Tas!

Sautin marin ya amsa cikin parlour gaba daya

Zahra ta rikice ta dafe kumatunta da sauri, ta ɗaga idanunta cikin mamaki

“M… Mummy…”

Mummy ta nuna ta da yatsa.

“Dan ubanki, kar na sake ganin kina manne wa ɗana! Shegiya! Yarinyar sai shegen son maza”

Ya Umar ya miƙe tsaye da sauri.

“Mummy! Kiyi haƙuri mana amma wannan words din yayi karfi”

Mami ta fito daga corridor da sauri, da alama marin ne taji ta fito

Da ta ga Zahra riƙe da kumatunta… Idanunta suka sauya nan take, ta ƙarasa cikin sauri

Ta tsaya gaban Mummy

Murya a sanyaye, amma cike da tsauri ta ce,

“Don’t dare you. Kar ki sake daga hannu ki buga min ’ya!!! Abin ya isa haka. Ni ban taɓa dukan miki ɗa ko ɗiya ba”

Parlour ya yi shiru

Ya Umar ya tsaya kamar an dasa shi, kunyar abin da ya faru ta hana shi magana.

Mami ta kama hannun Zahra a hankali, ta ja ta zuwa bayanta

Sannan ta kalli Mummy dake mata wani banzan kallo

“Zahra fa yarinya ce, kar ki manta shekara goma sha bakwai take yanzu, Idan kina ganin laifi ne ta yi dariya da Yayanta da suka taso tare tun tana ƙarama… to ni ban ga wannan laifin ba dan kallon Uba take masa”

Ta ɗan dakata

Sannan ta ci gaba da cewa,

“Idan kina maganar tarbiyya ne… Ki fara lura da Yayarta da take fita sai can dare ta dawo, ki fara daga nan kamar zai fi miki a matsayin uwa”

Mummy ta matso gabanta

“Har kin isa kina yi min magana haka?”

Mami ta ce a nutse,

“Na faɗi abin da na ga ya dace ne”

Mummy ta nuna Zahra.

“Toh ki ja wa ’yarki kunne. Kar na sake ganinta tana manne wa ɗana.”

Mami ta yi murmushi mai sanyi.

“Idan kin isa… Ki raba ɗanki da ita mana.”

Mummy ta ce

“Na dai faɗa miki next time mataki zan dauka kafin ta lallata min d’a”

Mami tayi dariya

“Tabbas’yar shekara 17 itace ake cewa zata lalata d’an 27 yrs! We’ll Allah ma ya tsare min ‘ya dan nasan tarbiyyar dana bata”

Mummy ta cije leɓenta cikin takaici.

“Ke… Kin raina ni ma, kar kiyi wasa zaman gidan nan ma ya gagare ki”

Mami ta girgiza kai.

“A’a! Ba ni da lokacin gardama da ke, amma bari na tuna miki da bokanki na aiki ai da tuni kin cire Ni ke kuma kin zauna a dakin ki”

Daga haka ta juya ta kalli Zahra ta kama hannunta, ba tare da ta sake waiwayowa ba…

Ta wuce da ita zuwa ciki

Ya Umar ya tsaya a wurin yana kallon Mummy

Ya sauke ajiyar zuciya

“Mummy…”

“Wallahi bai kamata….

Ta ɗaga masa hannu.

“Karka ce min komai. Ai kai ne ka jawo min

Ya rufe baki

Ya san duk wata magana a lokacin ba za ta canja komai ba

Ya tsaya yana kallon hanyar da Mami da Zahra suka bi…

Yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa saboda marin da aka yi wa ƙanwarsa ba tare da wani laifi ba, uwa Uba manyar maganganun da Mummy ta dangan ta wa zahra

Mami ba ta tsaya ko’ina ba…

Kai tsaye sai ɗakinta.

suna shiga… Ta rufe ƙofar a hankali

Har yanzu Zahra riƙe take da kumatunta, ba marin ne ya fi mata ciwo ba…

Kalaman Mummy ne suka fi tsaya mata a rai.

“Tana son maza…”

Kalmar ta ci gaba da yawo a kunnenta.

Mami ta juyo ta kalleta.

Da ganin yadda idanunta suka cika da ƙwalla…

Zuciyarta ta taɓu “Zo nan…”

Ta buɗe hannuwanta

Zahra ta ƙarasa da sauri ta faɗa jikinta. Nan take ta fashe da kuka.

kuka irin na wanda aka taɓa zuciyarsa

Mami ta rungume ta sosai.

Hannunta na shafa bayanta a hankali.

“Shhh… Ya isa haka, Karki ƙara kuka haka”

Sai dai Zahra ta ƙara manne mata.

“Mami…” Muryarta na rawa.

“Ni ban yi komai ba ta mare ni

“Na sani.” Mami ta amsa ba tare da wata-wata ba

“Wallahi na sani.” Ta ɗago fuskarta tana share hawayen Zahra da yatsunta

“Kinga ni.”

A hankali Zahra ta ɗaga idanunta.

“Kin ji tsoron abin da ta faɗa akan ki rabu da Yayanki?”

Ta girgiza kai kaɗan

Sai kuma ta gyada

“Gaskiya… Na ji.”

Mami ta yi murmushi mai cike da tausayi

“To ki cire wannan tsoron daga zuciyarki! Kin ji?”

Ta yi shiru.

Mami ta ci gaba

“Ya Umar yayanki ne. Jinin Abbahnki ne

Kun taso tare tun kina jaririya

Ba yau kuka fara hira ba

Ba yau kika fara dariya da shi ba”

Ta ɗan shafa kanta

“Saboda haka…”

“Kar ki bari maganar kowa ta sa ki fara jin kamar ba daidai bane dan kina kallonsa a yayanki

Kin fahimce ni?”

Zahra ta goge idanunta.

“A’a Mami… amma Ina tsoron kada ya ji haushi.”

Mami ta ɗan yi murmushi.

“Ya Umar?”

Ta gyada kai.

“Wallahi shi ne mutum na ƙarshe da zai ji haushinki! Na san shi Yana sonki fiye da yadda kike zato.”

Ta ɗan ɗaga haɓarta.

“Don haka… Kada ki canja yadda kike mu’amala da shi saboda abin da aka faɗa yanzu, ki ci gaba da girmama shi, ki ci gaba da ɗaukarsa a matsayin yayanki.”

Zahra ta sauke numfashi

Sai ta jingina kanta a kafaɗar Mami

“Mami…”

“Hmm?”

“Nagode.”

Mami ta sumbaci goshinta

“Ba zan taɓa bari wani ya karya miki zuciya ba matuƙar ina numfashi.”

Sai ta ɗan ja baya ta kalleta

“Wuce ki wanke fuskarki. Ba na son Abbahnki ya shigo ya ga idanunki sun kumbura.”

Da jin sunan Abbah… Sai Zahra ta yi murmushi

“Idan ya gani fa?”

Mami ta yi dariya.

“Toh ni zan shiga uku domin zai fara tambayata ko me ya sa na barki kina kuka.”

Dukansu suka yi dariya.

Mami ta share mata sauran hawaye, ta gyara mata hulanta

Ta rungume ta sau ɗaya kafin ta juya zuwa toilet domin ta wanke fuskarta.

FARASHIN IZZAH

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.