Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 47 of 59
Chapter 45
Ranar Lahadi ce.
Tun bayan sallar Asuba, gidan ya kasance cikin nutsuwa. Ba a jin hayaniyar zuwa makaranta ko shirye-shiryen fita aiki kamar sauran ranakun mako.
Bayan sun gama breakfast…
Zahra ta ɗan yi ta kai-komo a parlour
Kallo ɗaya za ka yi mata ka san akwai abin da take son faɗa. Sai dai tana neman lokacin da ya dace.
Ya Umar na shirin fita zuwa gymnasium ya ɗan yi training
Da ta hango shi… ta ƙarasa gare shi da sauri tana kwala masa kira
“Yaya…”
Ya waigo.
“My Baby.”
Ta karasa da sauri ta tsaya gabansa tana murza yatsunta
Ya ɗan yi murmushi
“Lafiya?”
Ta sauke numfashi.
“Na zo na ba ka haƙuri.”
Ya Umar ya ɗan haɗe gira.
“Haƙuri? Na me?”
Ta ɗan sunkuyar da kai
“Saboda na dame ka da maganar aure.”
Ya Umar ya fara dariya a hankali.
Ya ɗora hannunsa a kanta.
“Baby… ba komai, Ni nama manta.”
Ta ɗago tana kallonsa.
“Da gaske?”
“Da gaske.” Ya amsa mata
Sai ta yi murmushi, Nan take fuskarta ta sake.
Sai kuma ta ce,
“Yaya…”
“Ina da wata ƙaramar magana.”
“Uhum? Ina ji”
“Za ka kai ni gidan Saudat? Ina son kai mata wasu kaya.”
Ya Umar ya kalleta na ɗan lokaci.
Sannan ya gyada kai
“Toh, ba matsala. Idan kin shirya…”
“Ki sanar da ni, sai mu tafi”
Fuskarta ta cika da annuri.
“Thank you, Yaya.”
Ta juya da sauri, ta nufi sama, shi kuma ya juya ya fita..
Ranar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, har zuwa yamma…
Zahra ta gama duk abin da take yi, tanq zaune tana duba wayarta…
Sai ta ji knocking, ta ɗaga kai tana kallon kofar sannan ta tashi, ta buɗe
Ya Umar ne. Ya jingina da ƙofar.
“Ready?”
Ta yi saurin gyada kai
“Yanzu?”
“Eh.”
“Idan kin shirya… Mu tafi.”
“Okay.” Ta yi murmushi.
Da sauri ta koma cikin ɗakin, ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin.
A corridor ta kwala kira
“Anty Binta.”
Mai aikin gidan ta amsa da sauri.
“Na’am Zahra”
“Kin ga fancy bag ɗin nan da ke ɗakina?”
“Eh.”
“Don Allah ki kai shi wajen motar Yaya, ki saka a boot.”
Anty Binta ta amsa cikin ladabi.
“Toh Hajiya Zahratyy”
Nan take ta shiga ɗakin.
Ta ɗauko babban fancy bag ɗin da ke cike da kayan da Zahra ta ware wa Saudat, ta sauko da shi a hankali.
Ta kai shi inda motar Ya Umar take.
Ya Umar ya buɗe boot, ya karɓa daga hannunta sannan ya saka ciki
“Nagode.”
“Babu komai Alhaji.”
A can sama kuwa…
Zahra ta sake shiga ɗakinta.
Ta canza kaya, ta aka wata doguwar abaya mai launin dusty rose, ta ɗaura matching veil dinsa
Ta ɗan shafa turare, ta ɗauki handbag ɗinta, ta kalli kanta a mirror.
Ta gyara veil ɗinta kaɗan, sannan ta fito.
Kai tsaye ta nufi ɗakin Mami.
Ta yi sallama.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Mami ta ɗago kai.
“Ina za ki kuma?”
“Zan bi Ya Umar. Za mu je gidan Saudat.”
Mami ta yi murmushi.
“Toh! A dawo lafiya.”
“In shaa Allah.”
Ta sunkuya, ta rungumi Mami.
Sai ta fito. Da ta sauko ƙasa…
Ta tarar da Ya Umar ya riga ya kunna motar.
Yana zaune yana jiranta.
Da ya ganta… Ya buɗe mata front seat.
Ta shiga, ta ɗaura seat belt.
Ta yi masa murmushi.
“Sorry na ɓata maka lokaci.”
Ya girgiza kai.
“Ba ki ɓata min komai ba.”
Mai gadi ya yi saurin buɗe babban gate.
Motar ta fita daga gidan
A hankali Ya Umar ya ɗauki hanyar unguwar da Saudat suke zaune…
Zahra na zaune gefensa, zuciyarta cike da farin cikin cewa yau za ta faranta wa ƙawarta rai ba tare da ta ji an tausaya mata ba
Bayan kusan mintuna talatin da barin unguwarsu…
Ya Umar ya rage gudun motar
Suka shiga ƙunƙuntar layukan cikin gari.
Yara birjik na wasa a bakin hanya kamar ko da yaushe
A hankali…
Ya Umar ya faka motar a gaban gidan Saudat.
Ya kashe motar, ya waiwayo ya kalli Zahra
“Mun iso ko Madam?”
Ta gyada kai.
“Thank you, Yaya.”
Ta buɗe ƙofar motar ta sauka, ta ɗan kalli gidan.. kamar yadda ta bar shi kwanakin baya… Haka yake.
A tsakar gidan ana jin muryoyin yara suna wasa Zahra ta yi murmushi
Sai ta ɗaga murya
“Aliyu!”
Ba jimawa…
Ƙaramin yaron ya leƙo daga cikin gidan
Da ya hango Zahra… Fuskarsa ta washe
“Laa ke ce!”
Ya yi gudu ya ƙaraso.
“Ina kwana.”
“Lafiya lau Aliyu.”
“Ya gida?”
“Alhamdulillah.”
Ta nuna masa motar
“Zo mana.”
Ya biyo bayanta
Da suka isa bayan motar…
Ya Umar ya sauko ya buɗe boot.
Fancy bag ɗin mai girma ya bayyana.
“Ka taimaka ka ɗauka sai ka shiga da shi ciki, ko?”
“Toh.” Ya amsa da
Ya Umar ya fito daga motar ya karasa wajensu, ya ɗaga bag ɗin ya miƙa masa
Aliyu ya karɓa da hannaye biyu
Sai da ya ɗan karkata saboda nauyinsa.
Ya Umar ya yi dariya.
“Zaka iya ɗauka kuwa?”
Aliyu ya gyara riƙonsa
“In shaa Allah zan iya.”
Zahra ta yi dariya
“Idan ya yi maka nauyi ka faɗa fah”
Ya girgiza kai da sauri.
“A’a. Zan iya.”
Suka nufi ƙofar gidan tare, suna shiga tsakar gidan…
Mahaifiyar Saudat ce ta fito daga ɗaki tana riƙe da ɗan ƙaramin buta.
Da idanunta suka sauka kan Zahra… Nan take fuskarta ta cika da fara’a.
“Lale Maraba”
Zahra tayi murmushi ta gaishe ta cikin mutuntawa
“Ya kika baro iyayenki”
“Lafiya ƙalau.”
Mama ta ɗago idanunta.
Sai ta hango Ya Umar tsaye a bakin ƙofar gidan yana jingine da motarsa
Nan take ta gyara tsayuwarta cikin girmamawa.
“Sannu da zuwa.”
Ya Umar ya ɗaga kai Kai kalle tsohuwar Matar, sai kuma ya ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi ya karasa bakin kofar ya ce
“Yauwa Mama. Barka da warhaka, Fatan an wuni Lafiya”
“Lafiya lau.”
Mama ta yi murmushi.
Ya Umar yana juya ya koma cikin motarsa ganin unguwar babu wata privacy
Saudat ta fito daga cikin ɗaki bayan jin muryoyin su
Da ta ga Zahra.. ta yi wani irin murmushi
“Zahra!” Ta ƙaraso da sauri, ta rungume ta.
“Ban yi tsammanin za ki sake zuwa da wuri haka ba.”
Zahra ta yi dariya
“Na ce bari na zo na ganki.”
Aliyu kuwa…
Har sannan yana riƙe da babban fancy bag ɗin.
Ya ɗan ɗaga shi yana kallon Saudat, sai kuma ya kalli Zahra
“Anty Ina zan ajiye wannan”
Zahra ta murmushi
“Sorry ka shigar da shi ciki, na Saudat ne.”
Saudat ta haɗe gira cikin mamaki
“Nawa kuma?” Ta kalli Zahra
Zahra ta yi murmushi kawai
“Mu shiga ciki…”
Saudat ta bi bag ɗin da kallo. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri.
Ta san Zahra ba ta taɓa zuwa hannun empty ba, amma jakkan kuma fah
Ya kai abban fancy bag ɗin cikin parlour yana haki saboda nauyinsa
Ya ajiye shi a gefen tabarmar da ke parlour.
Sai ya waigo yana kallon Zahra.
“Anty anan zan ajiye?”
Zahra ta gyada kai.
“Eh! Nagode sosai Aliyu.”
Ya yi murmushi
“Babu komai.”
Daga haka ya juya ya fita zuwa tsakar gida
Idanun Saudat suka koma kan bag ɗin. Sai kuma ta kalli Zahra.
Ta haɗe gira cikin mamaki
“Zahra… Mene ne wannan?”
Zahra ta yi kamar ba ta ji ba. Ta yi murmushi kawai
Sannan ta miƙe tsaye.
“Ki gyara fuskarki, ki zo ki raka ni waje, kar Yayana ya yi ta jira.”
Saudat ta ɗan yi mamaki amma ta miƙe, ta shiga ciki ta ɗauki hijabinta ta saka
Da ta fito… Zahra ta kalleta daga sama har ƙasa, ta ɗan taɓe baki cikin wasa.
“Joor… Ki sake gyara fuskarki mana, kin fito kamar za ki yi kuka.”
Saudat ta saki murmushi
“Ke ma dai…”
Ta koma cikin dakin ta gyara fuskanta da kyau sannan ta canza hijab, ta sake fitowa
“Yanzu fa?” Ta tambaya
Zahra ta yi murmushi
“Perfect.”
Ta juya ta fara tafiya, Saudat ta bita a baya, da suka kai bakin ƙofar parlourn
Saudat ta tsaya. “Zahra!”
Ta waiwayo
“Kin manta kayan nan fa.”
Zahra ta girgiza kai.
“A’a. Ban manta ba.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci. Sannan ta ce cikin murmushi
“Naki ne.”
Saudat ta tsaya cak, kamar ba ta ji daidai ba.
“Nawa?”
Zahra ta gyada kai
“Eh. Naki”
Saudat ta zuba mata ido, ta kasa magana balle motsi, Kamar an dasa ta a wajen
Zahra ta yi murmushi ta koma baya, ta kamo hannunta.
“Mu je mana.”
Har sannan Saudat ba ta iya cewa komai ba. Idanunta suka fara cika da ƙwalla, amma ta haɗiye su.
Zahra ba ta ba ta damar yin magana ba, ta jawo ta har suka fito tsakar gida.
Mama na zaune bakin ƙofa.
Da ta ga su… ta yi murmushi
“Har za ku tafi?”
Zahra ta sunkuya cikin ladabi
“Eh! Mama”
Mama ta ɗaga hannu.
“Toh Allah kiyaye hanya, an gode”
“Ameen.”
Suka ƙarasa bakin gate.
Ya Umar na jingine da motarsa yana duba wayarsa.
Da ya ji takunsu… Ya ɗago kai.
Zahra ta yi murmushi.
“Yaya… ana gaishe ka.”
Ya Umar ya ɗan yi mamaki. Mamakin Zahra kawai yake yi, wato wannan ma another plan of her ne, amma bai nuna komai ba
Ya gyada
“Yauwa. Ya studies”
“Lafiya lau.”
Saudat ta sauke kanta ƙasa cikin kunya. “Nagode.”
Zahra ta buɗe ƙofar motar, sai ta waiwayo.
“Toh…”
“Bye. Za mu tafi yanzu “
Saudat ta yi saurin sake cewa,
“Amma…Kayan nan fa?”
Zahra ta yi murmushi
“Idan kin shiga ciki… za ki gani, Nace naki ne”
Ba ta ƙara ba ta damar magana ba, ta rufe ƙofar motar
Ya Umar ya kunna motar. A hankali suka bar unguwar.
Saudat kuwa… Ta tsaya nan wajan ta kasa motsi, har sai da motar ta ɓace daga ganinta
Ta sauke numfashi, ta juya a hankali ta nufi cikin gida…
Yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri.
Dan ba ta san me Zahra ta bar mata a cikin wannan babban bag ɗin ba.
Tun daga bakin ƙofa idanunta suka sauka kan babban fancy bag ɗin da ke ajiye a tsakiyar parlour.
Kamar yana jiranta ta ƙarasa kusa da shi, ta durƙusa.
Hannunta na ɗan rawa
“Me Zahra ta saka a ciki ne?”
Ta buɗe zip ɗin a hankali. Tana ɗaga murfin… Sai ta tsaya cak.
Ta zaro Idanunta
“Innalillahi…”
Ta ɗaga rigar farko
Sabuwar atamfa ce mai matuƙar kyau, ta ajiye ta gefe
Ta sake ɗaukar wata, doguwar abaya ce mai tsada
Ta ci gaba da cirowa ɗaya bayan ɗaya tana irgawa
Har ta rasa ƙirgawa.
ɗan karamjn Parlour ɗin ya fara cika da kaya masu tsada
Wasu har label ɗinsu bai cire ba.
Saudat ta kasa magana ta rufe baki, sai kuma ta yi wata irin ƙara.
“Mamaa!!”
“Mama ki zo da sauri!”
Muryarta ta sa Mama ta fito da gudu daga kitchen ta shigo parlon
“Lafiya? Me ya faru?”
Da ta shigo parlour… sai ta tsaya cak.
Idanunta suka kai kan kayan da suka bazu ko’ina.
Ta kasa motsi, ta kalli Saudat, ta sake kallon kayan.
“Subhanallah… Wannan duka fa?”
Saudat ta kasa cewa komai. Sai ta nuna bag ɗin da hannu.
“Mama… Zahra ce ta ba ni.”
Mama ta zaro ido.
“Duk wannan?”
Saudat ta gyada kai.
Hawayenta suka fara zuba.
“Wallahi ban sani ba, ta ce na raka ta waje, tana tuna mata da bag ɗin… Sai ta ce Naki ne.’”
Muryarta ta katse, ta fashe da kuka, ta zauna ƙasa tana rufe fuskarta.
“Mama… Me ya sa take min haka? Me na taɓa yi mata?”
Mama ta zauna kusa da ita
Ita ma idanunta sun cika da ƙwalla.
Ta ɗauki ɗaya daga cikin kayan, ta shafa shi da hannu, ta girgiza kai
“Ya Allah Ka saka mata da alkhairi. Ka buɗe mata ƙofofin rahamarka, ka ƙara mata lafiya, ka ƙara mata arziki mai albarka, ka kare ta daga idon hassada. Ka sanya farin ciki ya zama abokin rayuwarta.”
“A duk inda ta sa ƙafa… ka sanya alkhairi ya biyo bayanta.”
Saudat na kuka. Mama na addu’a.
Wannan moments ɗin ya cika da wani irin yanayi na godiya da taɓuwar zuciya.
Zahra ba kawai ƙawarta ba ce.
Ta kasance wata ni’ima da Allah Ya aiko mata a lokacin da ba ta zata ba.
Can sai Saudat ta share hawayenta da bayan hannunta, ta miƙe tsaye da sauri.
“Mama… Wayata.”
Mama ta nuna mata kan ƙaramin tebur.
“Can.”
Ta yi saurin ɗauko wayarta.
Hannunta har yanzu na rawa, ta shiga contacts.
Ta danna sunan Princess Zahra 👑❤️
Nan take wayar ta fara ringing
A ɗaya ɓangaren kuwa…
Motar Ya Umar na tafiya cikin nutsuwa, sun kusa isa gida
Zahra na zaune a front seat tana kallon titi ta window.
Wayarta da ke cikin handbag ta fara ringing, ta ciro ta.
Da ta ga sunan Saudat… Sai ta yi murmushi.
Ta ɗaga wayar.
“Hello, Saudaty.”
A can ɓangaren…
Saudat ta kasa magana, sai kuka kawai take yi.
Zahra ta ɗan ɗaga gira
“Hello! Saudat Are you okay?”
Har yanzu… Shiru sai sautin kukanta
Zahra ta ɗan yi dariya a hankali
“Ke kuma me ya sa kike kuka?”
Daga ƙarshe Saudat ta samu damar magana.
“Za… Zahra…”
“Meye haka?”
“Meye na yi…”
“Da har kika yi min wannan alkhairin?”
Muryarta na rawa, kuka na katseta
Zahra ta jingina da seat, ta yi murmushi mai taushi
“What are friends for?”
Saudat ta sake fashewa da kuka.
“Wallahi…”
“Ban taɓa ganin irinki ba.”
“Allah Ya saka miki.”
“Allah Ya saka miki da gidan Aljannah.”
“Allah Ya ƙara miki arziki.”
“Allah Ya sa duk wanda ya yi miki hassada…”
“Ya kasa ganin daidai”
Zahra ta yi murmushi.
“Ameen.”
Sai ta ce cikin tausasawa,
“Saudat! Please ki daina kuka. Kin ji?”
“Kayan ba wani abu ba ne. Kuma… kar ki ce ba zaki saka ba”
Saudat ta yi saurin girgiza kai.
“A’a. Wallahi ba zan taɓa ba ki ba, Nagode sosai.”
Zahra ta yi dariya.
“Shi kenan.”
“Yanzu ki yi murmushi.”
“Kuma ki saka ɗaya daga cikinsu idan za ki zo school.”
Saudat ta yi murmushi cikin kuka.
“In shaa Allah.”
“Bye.”
“Bye Princess.”
Da ta kashe wayar…
Ta sake rungume wayar a ƙirjinta
Wani irin natsuwa ta mamaye zuciyarta
Ya Umar ya ɗan kalli Zahra
“Ta yi farin ciki kenan?”
Zahra ta yi murmushi tana kallon wayarta
“Sosai.”
Ya Umar ya girgiza kai cikin gamsuwa
“Allah Ya saka miki.”
“Ameen.”
Ta amsa a hankali.
Sai ta mayar da wayarta cikin handbag.
FARASHIN IZZAH
500 ne ta wannan acc din 7084571222, Hauwa Jibrin, Opay
shaidar biya ta nan 08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.