Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 39 of 59

Chapter 37

“Omo Dude kace da Kai aka zo mana” daga haka ya sake zahra yayi wajen Ya Umar

Parlour ya cika da annashuwa , kowa na tambayar juna

Aunty Maryam ta kawo masu fresh juice

Uncle Moh kuwa ya kasa daina kallonta.

“Muhammad ya raini shalelensa har ta girma haka?, yanzu ta bar Baby kenan”

Ya Umar ya yi dariya.

“Uncle… Wallahi har yanzu Baby ce!Kuma za ta ci gaba da zama Baby.”

Zahra ta yi gwalo.

“Exactly.”

Suka sake yin dariya.

Bayan sun yi hira na kusan awa guda…

Ya Umar ya miƙe.

“Toh Uncle… Ni zan wuce.”

Nan take Zahra ta miƙe

“Yaya…”

Ya yi murmushi.

“Weekend ne fa.”

Ta yi frowning face dinta

“Ka kula da kanka.”

Ya shafa kanta.

“Ke ma.”

Sannan ya fita, ta bisa a baya, tare da Ya Imran

Har ƙofar mota Zahra ta raka shi, shagaɓa take masa shi kuma yana biye ta har ya lallabata ta hakura,

Da motar Ya Umar ta fice daga compound…

Zahra ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonta har ya ɓace daga ganinta.

Ya Imran ya koma ciki, jin shiru yasa iklima fito wa

Iklima ta ɗan turo ta da kafaɗa tana dariya

“Kin gama rakiyar kenan?”

Zahra ta murmusa

“Ya Ims ma ai idan zai tafi haka nake rakarsa.”

“Ke dai.”

Hannunta ta riƙa suka koma cikin gidan

Bayan sallar Juma’a…

Parlour ya sake cika.

Uncle Moh ya dawo daga masallaci tare da Ya Ims.

Aunty Maryam kuwa ta gama haɗa abinci. Kamshin tuwon shinkafa da miyar taushe ya mamaye gidan.

“Zahra!”

Aunty Maryam ta kira.

“Na’am, Aunty.”

“Zo ki taimaka min.”

Da sauri ta nufi dining.

Ko da wasa ba ta cikin yaran da idan basu gida su nuna cewa basu aiki a gida dan haka ba zasu iya ba a waje

Plate-plate ta fara jera wa, spoons, cups

Aunty Maryam ta tsaya tana kallonta

Ta yi murmushi.

“Wallahi Mami ya raini ’yarta da tarbiyya.”

Zahra ta yi dariya

“Abbah yana cewa idan mutum bai iya yi wa kansa aiki ba, duk dukiyar duniya ba ta isa ta amfane shi ba.”

“Allah ya ƙara masa lafiya.” Cewar Anty Maryam

“Ameen.” Ta amsa

Bayan Duk sun hallara

Ita ce ta fara zuba wa Uncle Moh ruwa, Sai Ya Ims, sai Iklima sannan Aunty Maryam.

Uncle Moh ya girgiza kai

“Wannan yarinya ba ta canzawa har yanxu da kwazonta”

Murmushi Zahra tayi basu san takura kanta take yi ba

Ya Ims ya yi dariya

“Baby Zahra ce fa.”

Ta taɓe baki

“Ya Ims… Daina kirana Baby.”

“Kin girma ne?” Ya tambaya yana dariya

Ta haɗe hannu a ƙirji

“Very much.”

Iklima ta fashe da dariya

“Ai idan Abbahnki ya zo nan yanzu zai ce ‘Baby’…”

“…za ki amsa.”

Duk suka yi dariya.

Zahra ta yi kamar za ta mare ta, ta bar dining din da sauri Tana dariya

A can gida kuwa…

Wata farar Hilux ce ta tsaya a compound.

Mai gadi ya buɗe gate mutane huɗu suka fito

Dukkansu cikin kayan aiki.

Mama Ladi ta fito daga kitchen tana kallonsu.

“Malam… Su waye?”

Mai gadin ya ɗaga kafaɗa.

“Ni ma ban sani ba.”

A dai-dai lokacin…

Mami ta sauko daga staircase ta back door, ta kalli mutanen.

“Sannunku.”

“Sannu, Hajiya.”

Ɗaya daga cikinsu ya yi gaba.

Ya miƙa mata wata takarda.

Ta karɓa ta duba.

Sai ta ɗaga kai.

“Ku biyo ni.”

Daga haka suka bi bayanta zuwa sama.

Ita ce Mama Ladi ta tsaya tana binsu da kallo.

Ta so ta tambaya… Sai kuma ta fasa.

Ta juya ta koma kitchen wajen aikinta tana kwalawa Binta kira

A gidan Uncle Moh kuwa…

Da yamma suka fita garden

Ita da Iklima suna zaune a kan swing.

Ya Ims yana ta tsokanarsu

“Kai Iklima. Ki tambayi kawarki.”

Iklima ta kalle shi.

“Me?”

“Har yanzu tana ƙin samari ne?”

Zahra ta harare shi.

“Ya Ims.”

Ya yi dariya

“Me na ce?”

Iklima ta haɗa baki.

“Wallahi kuwa. Last time wani ya ce yana son ta… Bai gama maganar ba ta bar wajen.”

Ya Ims ya riƙe ciki yana dariya

“Da gaske?”

Zahra ta taɓe baki

“Ni ban ga abin dariya ba. Karatu nake yi.”

Ya Ims ya ɗaga hannu.

“Okay, okay. Doctor Fatima Zahra.”

Ta gyara masa.

“Professor.”

Duk suka fashe da dariya.

Yamma sosai yayi

A hankali iska mai sanyi ta fara kaɗawa

Uncle Moh ya fito daga parlour.

Ya tsaya yana kallonsu.

“Har yanzu ba ku gaji da hirar ba?”

Ya Ims ya ce,

“Daddy, yau Zahra ta dawo mana. Ai babu ita babu Hutu”

Uncle Moh ya yi murmushi.

“Haka nake so.”

Ya juya ya kalli Zahra.

“Ki ji daɗin weekend ɗinki.”

Ta gyada kai.

“In shaa Allah, Uncle.”

Ta sake jingina da kujerar swing.

Fuskarta cike da annashuwa

Washegari… (Asabar)

Tun bayan sun gama breakfast…

Uncle Moh ya shigo parlour yana juya mukullin motarsa a hannunsa. Ya tsaya yana kallon yaran.

“Toh… Wa zai fita da ni?”

Iklima ta ɗaga hannu da sauri.

“Ni!”

Ya Ims ya ɗaga hannu shima.

“Ni ma.”

Uncle Moh ya juya ya kalli Zahra.

“Ke fa?”

Zahra ta yi ɗan murmushi

“Inda za mu je ne ban sani ba.”

Ya yi dariya.

“Surprise.”

Ta taɓe baki.

“Uncle… Dama ba na son surprises.”

“Dole yau ki tafi to” ya ce

Aunty Maryam ta fito daga kitchen tana dariya.

“Wallahi tun safe yake cewa idan Baby Zahra ta tashi za su fita.”

Uncle Moh ya ce,

“She has been studying for months, yau hutunta ne.”

Ya Ims ya tafa hannu.

“Exactly! Muje mu nuna mata Kaduna.”

Zahra ta yi dariya.

“Kamar ban san Kadunan ba.”

Iklima ta rungume hannunta.

“Please mana.”

Ta kalli Uncle Moh sai ta yi murmushi.

“Okay.”

Cikin mintuna talatin…

Kowa ya shirya.

Uncle Moh ne ke driving. A gaba Ya Ims ya zauna.

A baya kuwa… Iklima da Zahra.

Tun daga cikin mota hirarsu ba ta tsaya ba.

Ya Ims na ta juyowa yana tsokanar Zahra.

“Baby… Har yanzu kina da waɗancan snack din da kullum kike ɓoyewa?”

Ta zaro ido.

“Ya Ims! Ka manta ka sace min dukka ne?”

Ya fashe da dariya

“Wannan ƙaryar ce.”

Iklima ta nuna shi

“Ni shaida ce.”

Dariya ta cika motar. Har Uncle Moh ya ce,

“Ku bar yarinyar nan mana.”

Ya Ims ya ce,

“Daddy ai ita ce favorite ɗinka na lura .”

“Saboda ta cancanta.” Uncle Moh ya faɗa ba tare da tunani ba

Ya sa Zahra ta yi murmushin kunya.

Wani katafaren recreational park suka fara zuwa. Suna shiga…

Iklima ta ja hannun Zahra.

“Zo!”

Suka fara zagayawa, suna ɗaukar hotuna suna dariya.

Ya Ims kuwa yana ta musu photobomb a baya.

“Ya Ims!”

Zahra ta yi ihu “Ka bari mana.”

Ya yi dariya.

“Ai wannan hoton ya fi kyau idan ina ciki.”

Bayan sun gama…

Sai Uncle Moh ya kai su wani restaurant

Da suka zauna… Waiter ya kawo menu.

Uncle Moh ya miƙa wa Zahra.

“Princess, Order whatever you want.”

Ta girgiza kai.

“Uncle, komai kuka ci ni ma shi zan ci.”

Ya kalleta yana murmushi

“Har yanzu ba ki canza ba.”

Aunty Maryam ta kan faɗa masa kullum… _“Wannan yarinya ba ta da son wahalar da mutane.”_

Ana cikin cin abinci…

Sai wata yarinya ƙarama ta zo kusa da teburinsu, ta tsaya tana kallon ice cream ɗin da Iklima ke ci.

Zahra ta lura da ita, ba tare da ta ce komai ba… ta kira waiter.

“Please… Another one.”

Sai gashi ya zo da ice cream, ta karba ta miƙa wa yarinyar.

Yarinyar ta zaro ido.

“Nawa?”

Zahra ta yi murmushi.

“Naki ne.”

Yarinyar ta yi murmushi sosai.

“Thank you.”

Ta gudu wajen mahaifiyarta.

Uncle Moh ya kalli Zahra.

Ya girgiza kai.

“Kin gaji wannan halin daga wajen Muhammad.”

Ya Ims ya yi dariya.

“Baby ba za ta taɓa ganin ƙaramin yaro ba ta wuce.”

Zahra ta ɗan sunkuyar da kai.

“Abbah na yana cewa…”

_“Idan Allah ya ba ka fiye da abin da kake buƙata, akwai haƙƙin wani a ciki.”_

Uncle Moh ya ce

“Allah ya ƙara masa lafiya.”

“Ameen.”

Sai can wajen yamma suka dawo gida. Kowa ya gaji.. amma fuskokinsu cike suke da annashuwa

Da suka shiga parlour…

Iklima ta faɗa kan kujera.

“Wallahi na gaji.”

Ya Ims ya yi dariya.

“Ke kika fi gudu ai da wasan banza, ba dole ba”

Zahra kuwa ta zauna tana kallon hotunan da suka ɗauka.

Suka dinga dariya suna tuna yadda Ya Ims yake lalata musu pictures.

A haka suka ƙarasa weekend ɗinsu cikin farin ciki…..

Meanwhile kuma a wannan ranan a

Compound ɗin gidan Alhaji Muhammad Nasir ya cika da zirga-zirga

Wata babbar mota ce ta tsaya a bakin gate, daga cikinta wasu ma’aikata suka fito ɗauke da kayan aikinsu. Wasu na riƙe da measuring tape, wasu kuma da manyan cartons, yayin da wasu ke tura trolley ɗauke da kayayyaki.

Mama Ladi ta leƙo daga kitchen tana mamaki

“Subhanallah… yau kuma me ake yi ne a gidan nan?”

Sai dai babu wanda zai bata amsa.

Mami ce ta fito daga parlour cikin nutsuwa. Ta gaishe su, sannan ta ja su zuwa sama.

Da suka isa gaban ɗakin Zahra…

Ɗaya daga cikin mutanen ya buɗe notebook ɗinsa.

“Hajiya, nan ne?”

Mami ta gyada kai.

“Eh. Amma ku kula sosai. Ba na son ko ƙarce ya samu wani abu.”

“In shaa Allah.”

Nan take aka fara aiki.

An fara cire labulen ɗakin, sai carpet.

Sannan aka fara kwashe tsoffin kayan furniture ɗin a hankali.

Mami ta tsaya bakin ƙofa tana kallonsu.

Wani ya tambaye ta,

“Hajiya, wannan dressing mirror ɗin fa?”

Ta ɗan yi tunani.

“A’a… ku cire shi ma.”

Bayan wasu mintuna…

Ɗakin gaba ɗaya ya koma fanko.

Ko Mami da ta saba ganin ɗakin kullum, sai da ta yi mamaki.

“Allah Sarki…” Ta faɗa a hankali.

“Ashe haka ɗakin yake idan babu komai.”

Ana cikin haka…

Wata mota ta sake shigowa compound.

Ta tsaya, aka fara sauke sabbin kaya

Ga wani king size bed, wardrobe mai sheƙi, Reading table, Bookshelves, Dogayen wall mirrors, Sofas, Flowers, Frames, Lighting.

Komai ana shigarwa cikin tsari

Mami ta shiga ɗakin a hankali bayan an gama jera manyan kayan.

Ta tsaya cak, idanunta suka kan ko’ina cikin ɗakin, paint na bangon da aka sauya, sabbin curtains, carpet mai laushi.

Komai ya haɗu da juna cikin kyau da tsari irin na young lady

Ta lumshe idanunta tana murmushi.

“Ma shaa Allah…Wallahi dear yana son yarinyar nan, Alhamdulillah Allah Nagode maka”

Mama ladi ma ta shigo a hankali.

Da ta ga ɗakin… Sai ta dafe baki.

“Hajiya! Wannan ɗaki kuwa…”

Mami ta yi murmushi.

“Ko ni kaina ban yi tunanin zai yi haka ba.”

Mama Ladi ta yi dariya.

“Zahra fa?”

Mami ta girgiza kai.

“Wallahi idan ta dawo, sai ta yi tunanin ba ɗakinta ba ne.”

Dukansu suka yi dariya.

A can gidan Uncle Moh kuwa…

Weekend ɗin Zahra ya kasance cikin annashuwa.

Tun safe ita da Iklima suna kitchen suna taimakawa Aunty Maryam.

Da rana suka fita ɗan yawon gari da kafa tare da Ya Ims.

Suna tsokanar juna, suna dariya.

Da yammacin Lahadi…

Ya Umar ya zo ɗaukarta.

Tun daga ƙofar gida Iklima ta rungume ta.

“Wallahi ban so ki tafi ba.”

Zahra ta yi dariya.

“Ni ma. Amma zan sake zuwa.”

Ya Ims ya girgiza kai

“Karki manta da mu idan kin shiga university.”

Ta taɓe baki.

“Ya Ims… Ku ne za ku manta da ni, but not me”

Uncle Moh ya shafa kanta.

“Allah ya tsare hanya.”

“Ameen.” Ta amsa

Aunty Maryam ta rungume ta sosai

“Ki gaida Abbahnki da Mami.”

“In shaa Allah.”

Bayan sun yi sallama…

Ta shiga motar Ya Umar.

Har sai da suka fita daga layin gidan kafin Iklima ta daina daga mata hannu.

Tafiyar gaba ɗaya cike take da hira.

Ya Umar yana ba ta labarin wasu abubuwan da suka faru a office.

Ita kuma tana ba shi labarin yadda suka yi weekend.

Har ba su ankara ba…

Motar ta shiga compound bayan Mai gadi ya buɗe musu gate.

Da sauri Zahra ta fito.

“Mami!” Ta kira tana dariya.

Babu amsa. Ta yi mamaki.

“Ko ina suke ne?”

Ya Umar ya yi murmushi kawai.

“Ki shiga mana.”

Ta wuce parlour.Ba ta ga kowa ba.

Sai Farida ta fito daga kitchen.

“Anty Zahra… sannu da zuwa.”

“Yauwa Anty Binta, ina Mami?”

“Tana sama.”

Ta gyada kai.

“Okay.”

Ba tare da ta tsaya ba… Ta nufi staircase.

A hankali take hawa tana ɗan gajiya saboda tafiya. Da ta kai corridor ɗin sama…

Sai ta tsaya. Ta haɗe gira

“Eh?”

Idanunta suka sauka kan ƙofar ɗakinta…

A buɗe take. Kuma akwai muryoyin mutane daga ciki.

Ta ƙarasa a hankali.

Da ta tsaya bakin ƙofar…

Abin da idanunta suka gani… Ya sa ta kasa ko ƙiftawa

Numfashinta ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙu.

Idanunta suka fara yawo a hankali cikin ɗakin.

“…”

“Ya Allah!…”

Kalmar data iya furtawa a hankali kenan

Da farko ta yi tunanin ko tayi kuskure ne ta shiga wani ɗakin ne

Sai ta sake kallon calligraphy ɗinto dake bakin ƙofar.

Ita ce. Amma…Komai ya sauya.

Bed da ta saba gani ba ita bace.

Sabuwar carpet mai laushi ce ta mamaye tsakiyar dakin gaba ɗaya.

Gadon da ta kwana a kai shekaru ya sauya zuwa wani katafaren bed mai matuƙar kyau, an shimfiɗa farin bedsheet mai haɗe da sky blue duvet, pillows ɗin kuwa an jera su cikin tsari tamkar na hotel.

Sabbin curtains masu launin blue da white suna sauka a hankali, iska daga AC tana ɗan motsa su.

Reading table ɗinta ma ba ita bace.

An maye gurbinta da wata babba, an tsara littattafanta cikin shelves masu kyau.

Doguwar mirror tana gefe.

Flowers masu kyau suna ƙawata kusan kowane kusurwa.

Lighting ɗin ɗakin kuwa…

Sai ya sa kamar ba ɗakin da ta saba shiga ba ne.

Ta shiga a hankali…

Tamkar mai tsoron taka wani abu.

Hannunta ta kai kan gadon.

Ta shafa bedsheet ɗin.

Ta juya tana kallon ko’ina.

“Ya Allah…” Har yanzu muryarta ƙasa take.

“Nan ne dakina kuwa?”

Dariya ta ji daga bayanta.

Da sauri ta waiwayo.

Mami ce tsaye bakin ƙofa, hannuwanta a haɗe a ƙirji, murmushi ya ƙawata fuskarta.

“Kin gama kallo?”

Zahra ta zaro ido.

“Mami…”

Ta sake kallon ɗakin.

Ta sake kallon Mami

“Mami…”

“Me ya faru da ɗakina?”

Mami ta yi dariya.

“Ki tambayi Abbahnki.”

Da jin sunan Abbah…

Zahra ta juya da gudu.

“Mami! Abbah yana ina?”

“Study.”

Ba ta jira ta ƙara cewa komai ba.

Da gudu ta fita.

Veil ɗinta na ɗan zamewa saboda gudun.

Ta sauko stairs biyu-biyu.

“Abbah!”

Ta kira tun kafin ta isa ƙasa.

A study ɗinsa…

Alhaji Muhammad Nasir yana zaune yana duba wasu files.

Da jin muryarta…

Ya ɗago kai.

Ko bai ga fuskarta ba…

Ya san reaction ɗin da take ciki.

Ƙofar ta buɗe da sauri. Ta shigo tana haki kaɗan.

“Abbah…”

Ta tsaya gabansa.

Idanunta cike da mamaki.

“Na ga…” Ta kasa ƙarasa maganar.

Ya ajiye file ɗin hannunsa.

Ya ɗaga mata hannu.

“Zo nan.”

Da sauri ta ƙarasa.

Ta durƙusa gabansa kamar yadda ta saba.

Ya shafa gefen fuskarta.

“Kin so?”

Ta ɗaga kai da sauri

“So?”

“Abbah…? Haba…Na rasa ma abin da zan ce.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci.

Sai kawai ta rungume shi da ƙarfi.

“Thank you…My Abbah.”

Ya lumshe idanunsa yana murmushi

“Wannan ƙaramin sakamako ne.Na farin cikin da kika saka ni.”

Ta ɗago tana kallonsa.

“Amma…Abbah… Me ya sa duk wannan?”

Ya yi murmushi.

“Saboda kin cancanta.”

Ta girgiza kai.

“A’a… yayi yawa.”

Ya ɗan ɗaga gira.

“Yayi yawa?”

Ta gyada kai.

“Eh.”

Ya yi dariya “Baby…”

“Ko da zan ba ki duniya gaba ɗaya…Wallahi zan ga kamar ban yi miki komai ba.”

Hawaye suka cika idanunta. Na farin ciki Ta sake rungume shi.

“Allah ya bar min kai, Abbah.”

“Ameen.”Ya sumbaci goshinta.

“Allah ya sa kullum ina ganin murmushinki.”

“Ameen.”

A dai-dai lokacin…

Ya Umar ya shigo parlour ɗin yana jingine da ƙofa.

Tun da ya ga Zahra ta rungume Abbah ya riga ya fahimci ta ga ɗakin.

Ya yi murmushi.

“Baby.”

Ta waiwayo.

Da gudu ta nufe shi

“Yaya!”

Ta rungume shi shi ma.

“Ka sani ko?”

Ya yi kamar yana tunani.

“Ban sani ba.”

Ta ɗan doke ƙirjinsa.

“Ka daina.”

Ya yi dariya.

“Toh…Na sani.”

“Amma ba ni na shirya ba.”

“Abbah ne.”

Ta ce da sauri.

“Na sani.”

“Sai dai kai ma ka taimaka.”

Ya ɗaga hannu

“Little bit. Just the shelves “

Ta yi murmushi.

“Nagode.”

Ya shafa kanta.

“Kawai ki ci gaba da saka mu proud”

Ta gyada kai cikin nutsuwa.

“In shaa Allah.”

A saman staircase kuwa…

Mummy da Batoul na tsaye suna kallon abin da ke faruwa a kasa

Batoul ta taɓe baki

“Princess ta dawo.”

Mummy kuwa…

Ta ci gaba da kallonsu cikin wani irin shiru, ba tare da ta ce komai ba

#Farashin izzah

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.