Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 44 of 59

Chapter 42

Zahra ta shigo ɗakinta cikin gajiya, amma har yanzu murmushin da ke fuskarta bai gushe ba, sai yanzu ta baro ɗakin Mami bayan tafiyar Anty Jay

Ta cire heels ɗinta ta jefar a gefe, ta zauna bakin gadonta tana kallon key ɗin motarta.

Har yanzu abin kamar mafarki yake mata.

Sai wayarta ta fara vibrating.

Firdausi Calling…

Ta yi saurin ɗagawa.

“Hello, Fir!”

“Zahra don’t tell me ki ce kike trending”

Firdausi ta faɗa da muryar mamaki.

“Wallahi duk social media yau ke kaɗai ake ta magana a kanki, kin zama topic of the day”

Asiya ta ce

“Ke! Shine zaki ɓoye mana wannan birthday party ɗin?”

Zahra ta yi dariya.

“Wallahi ni kaina surprise ne.”

“Ban san komai ba sai yau da na dawo gida daga gidansu Saudat

“Karya!”

Firdausi ta faɗa.

“Da gaske, har yanzu ma ban gama yarda ba.”

Asiya ta yi dariya

“Princess kenan.”

Saudat ma ta shiga conference call ɗin.

“Happy birthday once again! Allah ya ƙaro miki shekaru masu albarka.”

“Ameen.”

“Nagode sosai.”

Suka ɗan yi hira na wasu mintuna.

Kafin daga ƙarshe Firdausi ta ce,

“Ki shiga Instagram, ki ga abin da ke faruwa.”

Zahra ta yi dariya

“Toh.”

Daga nan suka yi sallama

Ta buɗe Instagram, tana shiga kuwa

Sai notifications suka fara shigowa babu ƙaƙƙautawa. 99+ Notifications.

Ta lumshe ido

“Wai me haka?”

Ta shiga home page, abin da ta gani… sai da ta buɗe baki. Ko’ina a Instagram…

Bidiyonta ne, reaction ɗinta lokacin da ta ga motar.

Lokacin da ta rungume Abbah, da lokacin da aka yanka cake.

Pictures ɗinta cikin pink gown.

Manyan pages suna repost, Blogs suna posting. Story mentions kuwa… ba ta ma iya ƙirgawa.

@Safiyya___ mentioned you in a story. @Zehra___ tagged you in a post. @Ibtisam___ mentioned you.

Notifications suna ta shigowa babu tsayawa, ta shiga comments

“Allah ya ƙara miki albarka.”

“Princess.”

“So elegant.”

“Masha Allah.”

“The reaction is priceless.”

“Father of the year.”

“She deserves it.”

Ga likes…

Suna ƙaruwa a kowane secs

Zahra ta girgiza kai tana murmushi

Sai ta shiga profile na videographer.

Ta ga ya riga ya ɗora edited version na birthday video ɗinta. Editing ɗin ya yi matuƙar kyau.

Music mai taɓa zuciya, ga Quality mai kyau, reaction ɗinta kuma ta fito sosai.

Ta yi masa direct message.

Hi.

Please can you send me the edited version? I really love it.

Ba a wuce minti biyu ba…

Ya yi reply.

Sure, Princess.

Happy Birthday once again.

Ya turo mata full video ɗin.

Ta sauke shi cikin wayarta, ta sake kallonsa sau ɗaya.

Sai murmushi ya kubce mata, ta ajiye wayar a gefen gado.

Ta miƙe tsaye, ta nufi toilet

Ta yi alwala cikin nutsuwa.

Da ta fito…

Ta shimfiɗa sallaya, tayi shafa’i da witr❤️❤️❤️

Sannan ta zauna ta fara karanta Suratul Mulk cikin natsuwa

Bayan ta kammala, sosai ta ɗaga hannuwanta sama.

“Alhamdulillah…Ya Allah, kamar yadda Ka faranta min rai a yau… da kuma kullum, Allah kada Ka sa ni in manta da Kai.”

“Ka sa wannan ni’imar ta zama alkhairi a gare ni, ka kare ni daga hassada da sharrin mutane. Fatan da Mummy ta min Allah kar kasa na aikata abun da zan kunyata iyayena”

Ya mike, had’i da naɗe sallayar.

Ta kashe babban wutan ɗakin

Bed lamp kaɗai ta bari a kunne.

Ta haye kan gadonta, ta kashe shi ma, ta ja duvet har ƙirjinta.

Ba ta jima da kwanciya ba… saboda gajiyar ranar…

Bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita

Washegari…

Da misalin ƙarfe takwas na safe.

Ƙamshin tea da sandwich mai zafi ya cika dining area.

Mama Ladi da sauran ma’aikata suka gama shirya breakfast.

Abbah ya riga ya zauna sbd saurin da yake yi, Mami ma ta zo ta zauna

Bayan ɗan lokaci…

Zahra ta sauko cikin wata doguwar riga mai launin purple da farin veil scarf akanta

Ta fara gaishe da Abbah da Mami kafin ta zauna.

Sai dai su kaɗai kawai ta gani saɓanin sauran ranakun, a hankali ta ce

“Mami… Ya Mummy fa? Da Batoul, har da Yaya?”

Mami ta kalli Abbah.

Abbah ya ɗan yi murmushin manya kawai.

“Ki ci abincinki, babu komai

Zahra ta ɗan kalli fuskokinsu, ta fahimci akwai abin da ba sa son ta sani.

Sai ta yi shiru, ta fara breakfast ɗinta.

Suna cikin cin abincin…

Abbah ya sauke cup ɗinsa a hankali, ya kalli Zahra.

“Baby.”

“Na’am Abbah.”

“Yanzu an fara online screening, wace makaranta kike so? Na yi waya a miki komai tun da wuri

Zahra ta yi shiru.

Ta sauke spoon ɗinta, ta dafe haɓa tamkar mai nazari

Abbah ya sake cewa,

“Nile University? Ko Pen Resource University?”

“Kawai faɗa duk Wanda kike so”

Mami ta ce,

“Ko Baze University.”

Zahra ta yi shiru

Sai hoton Firdausi, Asiya da Saudat ya faɗo mata a rai.

Ta san ba za su iya biyan kuɗin irin waɗannan makarantu ba, dan gwara ma Suhaima, kuma bata son ta rabu da su

Sai ta ɗaga kai tana murmushi.

“Abbah… Lemme think first.”

Abbah ya gyada kai.

“No problem, ki yi tunani sosai.”

Da suka gama breakfast…

Zahra ta koma ɗakinta, tana shiga ta dauki wayanta ta zauna kan gadonta…

Ta buɗe group chat ɗinsu.

The Queens👑❤️

Ta yi typing.

Girls…

Wace school kuke planning?

Wallahi ni ina son mu tafi school ɗaya, course ɗaya ma idan zai yiwu.🥺❤️

Nan take replies suka fara shigowa.

Asiya:

Ni KASU nake tunani.

Firdausi:

Same here.

Saudat:

Ni ma KASU.

Suhaima:

Ni Daddy yana so Nile.😂

Firdausi ta yi replying.

Ke ɗin daban ce.

Mu talakawa muna KASU.😭😂

Asiya:

Wallahi idan Zahra ta ce KASU zan fi farin ciki.

Firdausi:

Please Princess ki zo mana.🥺❤️

Zahra ta yi murmushi.

Ta rubuta.

Okay…

Let me convince Abbah first.❤️

Ta kashe data, ta ajiye wayarta.

Kai tsaye… ta nufi ɗakin Mami ta buga ƙofar a hankali

“Shigo.”

Ta shiga.

Mami na zaune tana gyara wasu kaya, ta ɗago tana murmushi.

“Fatima ya ne?”

Zahra ta zauna kusa da ita, ta ɗan shafa hannunta.

“Mami… Ina son magana ne da ke”

Mami ta ajiye abin da ke hannunta.

“Ina jinki.”

“Mami… Ina son na je KASU.”

Mami ta ɗan zaro ido.

“KASU?”

“Eh.”

Mami ta yi shiru na wasu daƙiƙu.

Ta kalli Zahra sosai.

“Ke da kanki… wannan shi ne inda kike so? Ba Nile ba?”

“Ba Pen Resource ba? Ba Baze ba?”

Zahra ta girgiza kai.

“A’a! KASU nake so.”

Mami ta ɗan sauke numfashi.

“Gaskiy duk da ba na son ki yi makaranta ɗaya da Batoul.”

“Amma… gwara ki tafi can da KASU”

Zahra ta riƙe hannunta.

“Mami… I have made my mind.”

“Bana son makaranta mai nisa da gida.”

Mami ta san akwai wani dalili da Zahra yasa ta nace, amma ba ta matsa mata ba

Sai ta shafa kanta.

“Allah Ya sa abin da kika zaɓa shi ne mafi alkhairi.”

“Ameen.”

Bayan fitarta daga ɗakin Mami…

Kai tsaye ta nufi inda Abbah yake, ta buga ƙofar a hankali

“Come in.”

Ta shiga.

Abbah na duba wasu files, da ya ganta…

Sai ya cire glasses ɗinsa.

“My Princess, kin gama tunani?”

Ta yi murmushi.

“Eh.”

“Wace school?”

“KASU.”

Abbah ya yi shiru.

Ya jingina da kujerarsa.

“KASU kuma Baby?”

Eh.”

Ya haɗe gira kaɗan.

“Me ya sa? Ke da za ki iya zuwa kowace university?”

Zahra ta ɗan yi murmushi.

“Abbah Ina son ta ne, kuma bana son nisa da gida.”

Abbah ya ci gaba da kallonta.

Ya san Zahra, ba ta da halin nacewa abu sai idan ta yanke shawara

Sai ya yi murmushi

“Kin tabbata?”

Ta gyada kai

“One hundred percent.”

Abbah ya ɗan yi dariya.

“Toh shi ke nan, za a miki process na KASU.”

Fuskar Zahra ta cika da annuri

“Thank you, Abbah!”

Ta yi saurin rungume shi, ya shafa kanta yana dariya.

“Allah Ya sa alkhairi.”

“Ameen.”

Ya juya zata fita, sai kuma ta juyo.

“Abbah…”

“Yes?”

“Ina Yaya?”

Abbah ya ɗan kalli agogo.

“Gaskiya ban san inda yake ba.”

“Ni ma ban gan shi ba tun safe.”

Zahra ta gyada kai.

“Maybe ya tafi office.”

Ta yi murmushi

“Sai anjima.”

Ta fita daga side ɗin da sauri, tana isa ɗakinta…

Abu na farko da ta yi… ta kunna data

Ta shiga group chat.

Girls!!!!!!🥹❤️❤️

Abbah ya yarda.

KASU it is.🥹🎉

Nan take group ɗin ya kaure da murna.

Firdausi:

Yeeeeeehhhhhh!!!😂❤️

Asiya:

Allahuuu Akbar!!!🥹❤️

Saudat:

Finally!❤️

Suhaima:

Welcome to KASU girls.😂🤍

Zahra ta jingina da pillow tana murmushi.

A karo na farko…

Ta fara jin daɗin cewa wata sabuwar rayuwa na gab da buɗewa gare su baki ɗaya.

Tun safe har la’asar ta yi amma…

Babu alamar Ya Umar.

Ba wanda zai ce ya gan shi a gidan

Ko da yamma ta yi, har aka yi magariba… har lokacin bai dawo ba.

Zahra ta riƙa leƙa ta window lokaci zuwa lokaci ko zata gansa, duk ƙarar mota da ta ji…

Sai ta ɗaga kai da sauri tana tunanin ko Ya Umar ne, amma duk ba shi ba ne.

Sau biyu ta kira wayarsa, bai ɗaga ba

A karo na uku… sai aka katse.

Da ta sake kira kuma.. wayar a kashe

Sai gabanta ya fara bugawa.

“Ya Allah… save my brother”

Gidan ya yi tsit

Mummy da Batoul suna zaune a parlour.

Kowacce da wayarta a hannu, ba sa magana.

Sai dai lokaci zuwa lokaci suna kallon juna.

Aka buɗe kofar parlour

Abbah ne ya shigo daga waje.

Ya cire hularsa yana miƙa wa ɗaya daga cikin masu aikin compound

Kafin ya zauna…

Sai Zahra ta fito daga corridor, da alama ita ma fitowarta kenan daga ɗaki.

Da ta ga Abbah…

Ta ƙarasa da sauri

“Abbah…”

Ya ɗago yana kallonta.

“Yea Baby.”

Ta haɗe gira.

“Har yanzu ban ga Yaya ba.”

Abbah ya ɗan tsaya yana kallon damuwar dake fuskanta

“Gaskiya… Ni ma ban gan shi ba.”

Zahra ta cije leɓenta.

“Na kira wayarsa da farko bai ɗaga ba, yanzu uma a kashe take.”

Muryarta ta soma nuna damuwa.

“Abbah… ko lafiya?”

Abbah ya yi murmushin kwantar da hankali.

“Baby… Umar ba ƙaramin yaro ba ne.”

“Wataƙila wani meeting ne ya tsayar da shi.”

“Ko kuma ya yi tafiya ta gaggawa but zai dawo ai, In shaa Allah.”

Ta gyada kai

Amma damuwar da ke fuskarta ba ta ragu ba.

“Okay…”

Ta juya za ta Kama hanyar ɗaki, sai kuma ta tsaya.

Tamkar wani abu ya zo mata a rai, ta waiwayo a hankali, Idanunta suka sauka kan Mummy.

Ta yi shiru na ɗan lokaci, Kafin ta ƙarasa kusa da inda take.

“Mummy…”

Mummy ba ta ma ɗago kai daga wayarta ba.

“Hmm.”

Zahra ta haɗe hannayenta waje ɗaya, cikin ladabi ta ce,

“Please…”

“Kin ga Ya Umar yau ne?”

Mummy ta ɗaga kai a hankali, ta kalleta daga sama har ƙasa

Sai ta yi wani murmushi mai cike da ba’a.

“Ubanki ne shi?”

Zahra ta ɗan zaro ido.

Mummy ta ci gaba.

“Idan ba ki gan shi ba… ba zaki iya rayuwa bane saboda shi ɗin numfashinki ne ba? Ko yanzu kin koma mai bin Maza ne?”

Zahra ba ta ce komai ba, ta sauke idanunta ƙasa.

Ta fara murza yatsun hannunta cikin rashin sanin abin cewa.

Batoul ta ɗan ɗaga kai ta kalleta, ta wasu daƙiƙu…

Babu wanda ya sake magana.

Sai Zahra ta girgiza kai a hankali.

“Nothing…” Ta faɗa cikin sanyin murya.

“Sorry, Mummy”

Ba tare da ta sake kallon kowa ba… ta juya a hankali… ta nufi staircase.

Takunta ba irin na Zahra mai cike da kuzari ba ne

Ko tafiyarta kaɗai ta nuna damuwar da take ciki.

Abbah ya bi bayanta da kallo.

Ya fahimci sarai cewa duk da kalamansa na kwantar mata da hankali… Yasan hankalinta ba’a kwance yake ba

Ko kallon direction din Mummy bai yi ba, balle ya gwada yaji me ta ce, dan yaga da gayya take abubuwanta

Ita kuwa Mummy…

Sai ta mayar da hankalinta kan wayarta

Bayan da Zahra ta shige ɗakinta

Har yanzu tambaya ɗaya ce kawai ke yawo a zuciyarta.

“Ina Yaya yake…?”

Har can dare babu Yaya, Kowa ya koma ɗakinsa.

Hasken corridor ne kaɗai ke bayyana, yayin da gidan ya yi shiru masu aiki ma duk sun kwanta

Sai dai… Zahra tama kasa kwanciyar, damuwar Ya Umar ta ƙi barin ranta

Bacci kuwa haka yaki dukarta, ta juya dama, ta juya hagu, amma bacci ya ƙi zuwa.

A ƙarshe… ta sauko daga kan gadonta, ta saka slippers ɗinta a hankali.

Ta buɗe ƙofar ɗakin, ta fita

Kai tsaye… ta nufi ɓangaren ɗakin Ya Umar.

A zuciyarta tana addu’a.

“Ya Allah, ka sa ya dawo.”

Da ta isa bakin ƙofar sai ta lura ba a rufe ta sosai ba.

Ƙofar a ɗan buɗe take, ta tura ta da hankali sannan ta bubbuga

Knock… Knock…

“Yaya…”

Shiru… ta sake tura ƙofar.

Data leƙa ciki, nan take idanunta suka sauka kansa.

Yana kwance a kan gadonsa, da alama bai daɗe da dawowa ba.

Har yanzu bai canza kaya gaba ɗaya ba, riga ce babu a jikinsa, wayarsa kuwa a gefe take

Yana kallon ceiling cikin zurfin tunani.

Da ya ji ƙarar ƙofar.. sai ya ɗago kai.

Idanunsu suka haɗu, ya ɗan zaro ido.

“Baby?”

Bai ma gama faɗin sunan ba… sai ya ga ta ƙaraso da sauri, ta faɗa jikinsa.

Ta rungume shi da ƙarfi.

Nan take… Ta fashe masa da kuka

“Yaya…”

“Meyasa zaka yi min haka?”

Ya Umar ya rikice.

“Subhanallah…”

“Baby…”

“Me ya faru?”

Ta girgiza kai tana kuka.

“Na kira ka.”

“Wayarka a kashe.”

“Duk throughout ban gan ka ba.”

“Na tsorata sosai.”

Ya Umar ya lumshe idanunsa.

Kalaman Mummy na jiya suka dawo masa. Sai ya ji zuciyarsa ta yi zafi

A hankali…

Ya janye ta daga jikinsa.

Ya share mata hawayen da suka zubo.

“Shhh…”

“Ki daina kuka.”

“Nothing happened.”

Sai ya miƙe tsaye.Ya ɗauki wata farar riga ya saka.

Sannan ya kamo hannunta

“Zo.”

Suka fito daga ɗakin.

suka isa parlour, ya zaunar da ita kan kujera.

Shi kuma ya zauna kusa da ita.

Ya riƙe hannunta cikin kulawa.

“Baby.”

Ta ɗago idanunta masu ja saboda kuka.

“Hmm.”

Ya ɗan yi murmushi.

“Da farko…”

“Ina son ki san wani abu.”

Ta yi shiru tana saurarensa.

“Ba daidai ba ne…”

“Ki riƙa shiga ɗakina haka nan.”

Ta haɗe gira.

“Me ya sa?”

Ya Umar ya yi murmushi.

“Saboda yanzu kin girma. Eh, ni muharraminki ne, kuma ba wani abu ba ne, amma ba ina son ki saba da shiga ɗakin namiji ba tare da izini ba.”

“Ki saba da kiyaye hakan, duk inda kika je, ko da kuwa ɗan uwanki ne.”

Zahra ta yi shiru, ta fahimci abin da yake nufi, sai ta gyada kai cikin biyayya.

“Okay… ba zan sake ba.”

Ya shafa kanta.

“Good girl.”

Sai ta sake kallonsa.

“Amma… Meyasa baka dawo ba?”

Ya Umar ya ɗan kau da kai.

Ba zai iya gaya mata gaskiya ba

Don ba ya son ta san abin da ya faru tsakaninsa da Mummy.

Sai ya tilasta murmushi wa fuskansa

“Meeting ne. Wani emergency meeting, ya ɗauki lokaci sosai.”

Ta haɗe gira

“Shi ya sa baka ɗaga kirana ba?”

Ya sauke idanunsa.

“Na yi busy sosai da na gama kuma… wayata ta mutu, ban samu damar caji ba sai yanzu.”

Zahra ta ɗan yi shiru.

Sai ta ce da ƙaramar murya,

“Da ka kira ka ce min ai, wallahi na damu.”

Ya Umar ya ji wani irin tausayinta.

Ya ɗan matsa kusa da ita.

“Sorry, na yi kuskure.”

“Ba zan sake ba.”

Ta turo baki irin na yara cikin shugaba ta ce

“Promise?”

Ya ɗaga hannunsa.

“I promise.”

Sai ta yi murmushi

Ya Umar ya miƙa mata tissue dake aljihun, to goge fuskarki

Ta karba ta goge tana kallonsa

“Yanzu kin yi murmushi har naji dadi”

Ta yi dariya kaɗan.

“Ka fi so ina yi murmushin ne?”

“Exactly.”

“Shi ya sa ba na son ganin kina kuka.”

Ya ɗan murɗe mata kunne cikin wasa.

Ta ɗan ture hannunsa.

“Ouch”

Daga nan… Ya raka ta har bakin staircase.

“Yanzu…kije ki kwanta, gobe za mu yi magana.”

Ta gyada kai.

“Good night, Yaya.”

“Good night, Baby.”

Ta juya ta haura sama.

Har sai da ta shige ɗakinta.

Ya Umar ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, ya lumshe idanunsa.

A zuciyarsa…

Ya san ƙaryar da ya yi mata ta ceci zuciyarta na ɗan lokaci

Amma bai san har yaushe zai iya ɓoye mata abin da ke faruwa ba.

Da wannan tunanin ya juya a hankali, ya koma cikin ɗakinsa.

#FARASHIN IZZAH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.