Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 20 of 59

Chapter 19

Firdausi kuwa ta sauka ƙasa, a compound suka haɗu.

Ibrahim yana shigowa, Firdausi ta kalle shi fuska a hade.

"Ina wuni," ta faɗa a taƙaice.

Shi kuma ya kalleta da wani irin kallon, sannan ya wuce ba tare da ya amsa ba.

Ita ma ta bi shi da irin kallon nan na rashin kunya.

Wajen unguwar nasu shiru, manyan gidaje ne, babu kowa dan kowa na gidansa. Ta fara tafiya a hankali tana bin titin unguwar har ta kai bakin titi.

Da ƙyar ta samu abin hawa ta shiga, zuciyarta cike da tunanin Zahra da kuma halin da ta bar ta a ciki.

Ibrahim na shiga parlorn ƙasa, babu kowa.

Kai tsaye ya haura sama zuwa É—akinsa. Ko kallon dakinta bai yi ba, ya cire kayansa sannan ya shiga toilet yayi wanka.

Yana fitowa aka kira sallar isha'i, hakan yasa yana gama saka kaya ya sauka ƙasa. Masallaci ya wuce direct.

Bayan ya dawo ne ya tsaya a kitchen na É—an lokaci, kamar mai tunani. Sai ya É—auki plate ya wuce dining. BuÉ—e warmers É—in yayi.

Abincin da Zahra ta dafa ne a jere cikin tsari. Wani É—an numfashi ya sauke a hankali kafin ya ja kujera ya zauna.

Ya É—iba abincin kaÉ—an sannan ya fara ci a hankali. Dining É—in gaba É—aya shiru yayi masa

Lokaci zuwa lokaci idanunsa na É—agawa sama kamar yana sauraron motsi daga upstairs, amma shiru kake ji .

Sai kawai ya ci gaba da cin abincin a hankali, zuciyarsa cike da wani irin tunani da shi kansa bai gama fahimta ba.

A bangaren Zahra tun kafin Ibrahim ya dawo daga masallaci, Zahra ta riga ta ji motsinsa a cikin gidan. Ko da yake tana cikin É—akinta, amma ko da wasa bata fita ba, Duk da ta saba idan taji sawunsa tana fita..

Sai dai wannan karon... ta share.

Kwanciya tayi akan gadonta tana kallon ceiling É—in É—aki, zuciyarta na wani irin bugawa da bata saba ji ba. Duk shawarwarin da Firdausi ta saka mata a kai ne ke yawo a kanta.

"Ki nemo number É—in..." Wannan maganar ta sake dawo mata

Sai kuma ta tuna yadda Ibrahim ya kwana a waje, wani rin abu taji ya tokare mata zuciya.

Da sauri ta miƙe daga gadon ta nufi toilet.

Ruwan É—umi ta kunna sannan ta fara wanke fuskarta a hankali. Ta daÉ—e tana wanke idanunta musamman saboda kumburin da kuka ya saka musu.

"Ba zai gane ba..." Ta furta a hankali tana sake É—iba ruwa.

Bayan ta fito ne ta goge fuskarta da towel mai laushi sannan ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta.

Har yanzu idanunta sun É—an yi ja kaÉ—an, amma ba kamar É—azu ba.

Mint sweet ta jefa a bakinta sannan ta fara taunawa a hankali. "Ko muryata ba zai gane ta canza ba..."

Wani tsaki ta ja a hankali saboda yadda take ƙoƙarin acting kamar komai lafiya ne alhalin zuciyarta na cin wuta.

Wardrobe ta buɗe. Wani English wear mai matuƙar ɗaukar hankali ta zaɓa.. milk colour fitted gown mai taushi wanda ya zauna a jikinta kamar an yi shi saboda ita. Gashinta ta gyara cikin simple style sannan ta saka ɗan turare mai sanyin ƙamshi.

Da ta gama shiryawa, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta. Kamar a ita ba.

Kallon agogo tayi, Almost tara na dare, sai kuma gabanta ya faÉ—i.

"Har yanzu bai leƙo ni ba..."

Maganganun Firdausi ne suka fara dawo mata.

"Namiji idan ya ga mace tana rushewa saboda shi..." Wani numfashi ta sauke.

Ta miƙe zata fita, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta tsaya cak.

"Anya zan iya?" Wani soro ne ya ratsa ta.

Sai kuma last text É—in da Firdausi ta turo mata ya faÉ—o mata a rai.

"Control yourself first kafin ki gano komai."

Wannan ne ya bata wani ƙarfin guiwa.

Ta dafe ƙirjinta a hankali sannan ta buɗe ƙofar ta fita, Direct ɗakin Ibrahim ta shiga.

Ta same shi zaune bakin gado, waya na hannunsa yana dannawa hankali kwance kamar babu wata damuwa a duniyarsa

Da ya É—aga kai suka haÉ—a ido, sai ya É—an tsaya kallonta.

Kafin ya ce wani abu, Zahra ta karya muryarta cikin shagwaɓa ta ƙarasa kusa da shi.

"I missed you..."

Ta faɗa tana zaunawa kusa da shi kamar ƙaramar baby.

Ibrahim ya É—an É—aga gira yana kallonta.

"Tun safe?"

Ta É—an turo baki.

"Hmmm."

Wani murmushi ya suɓuce masa.

"Amma ai kina fushi da ni ko?"

Ta É—an girgiza kai.

"Who said?"

Sai ta kwanta jikinsa a hankali tana riƙe hannunsa.

"Please kar ka sake bace min haka."

Maganar ta bugi zuciyarsa kai tsaye.

Nan take ya saki jikinsa da ita gaba É—aya.

"Sorry..." Ya furta a hankali yana shafa bayanta.

Zahra ta runtse idanunta.

Duk da zuciyarta ke mata zafi, ta danne komai.

A daren sosai suka sha love kamar ma babu wata matsala tsakaninsu. Ibrahim na mata hira, tana dariya tana responding yadda ya kamata, alhalin zuciyarta na wani irin aiki a ɓoye.

Wani lokaci ma sai ta tsaya tana kallonsa tana mamakin yadda yake iya zama normal haka.

Bayan wani lokaci ne suka kwanta

Zahra tayi pretending kamar bacci ya É—auketa.

Ibrahim ya gyara mata kwanciyarta a hankali, har blanket ya ja ya rufe mata jikinta.

Ta ji yadda ya É—auki wayarsa.

A hankali ya sauka daga kan gadon yana rage murya.

"Hello..."

Sai kuma shiru....

"Yes... I sent the 50k already."

Zuciyar Zahra ta buga da ƙarfi.

Ta ci gaba da pretending kamar bacci take.

Daga can muryar mace ta É—an fito kaÉ—an daga wayar amma bata ji sosai ba.

Ibrahim yace,

"No... don't worry about it."

Shiru ya sake yi yana saurare.

Sai kuma ya É—an yi murmushi kaÉ—an.

"You worry too much."

Wata magana aka sake masa. Sai yace,

"I'll see what I can do tomorrow."

Daga haka ya kashe wayar.

Zahra ta ji ƙafafunsa sun dawo kusa da gado.

Sai ya kashe light É—in É—akin sannan ya kwanta kusa da ita.

Ita kuwa zuciyarta har lokacin bugawa take yi kamar zata fito.

Can wajajen ƙarfe biyu na dare Zahra ta buɗe idanunta a hankali, Ibrahim na bacci.

Ta tsaya tana kallonsa na wasu seconds kafin daga ƙarshe ta miƙe a hankali. Wayarsa dake gefensa ta ɗauka.

Da hannunta na rawa ta kamo yatsansa sannan ta manna akan thumbprint É—in. Nan take wayar ta buÉ—e.

Gabanta ya faÉ—i, da sauri ta shiga recent calls.

Last call É—insa...

"Pretty ❤️"

Wani irin mashi ne ya soki zuciyarta.

Da sauri ta kwafe number É—in zuwa wayarta, hannunta har rawa yake yi saboda tashin hankali.

Bayan ta gama, ta fita daga contacts É—in ta kashe wayar gaba É—aya sannan ta mayar inda ta É—auka.

Sai ta É—auki wayarta ta turawa Firdausi number É—in nan take.

"This is the number."

Daga haka ta kwanta a hankali, abin mamaki kuwa, nan take bacci ya É—auke ta saboda gajiyar tunani da tashin hankali.

Da safe suka tashi tare.

Kamar kullum suka yi sallah.

Ibrahim ma babu alamar damuwa a tattare da shi. Har lokacin yana treating Zahra normal. Wannan ne ma ke ƙara rikita mata kai.

Bayan sun gama shiryawa suka sauka breakfast.

Farida ta haÉ—a musu tea da bread da omelette.

Ibrahim na cin breakfast É—insa yana É—an duba wasu files a tablet.

Zahra kuma tana ci a hankali tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci.

"Yau kina da lectures da yawa?" ya tambaya.

"Hmmm." Ta ce masa

"Kar ki gaji da yawa."

Kai ta gyada masa kawai.

Bayan sun gama, suka fito tare. A compound ya tsaya yana kallonta.

"Take care."

"You too."

Sai ya É—an matso ya sumbaci goshinta a hankali kafin ya shiga motarsa.

Zahra ta tsaya tana kallonsa har ya fita...

Tana isa makaranta kuwa, bata ma shiga department É—insu ba.

A wani department ta tsaya ta kira Firdausi.

Da sauri Firdausi ta É—aga.

"Kin iso?"

"Eh." Zahra ta ce

"Ina kike?"

Zahra ta gaya mata wajen.

"Toh ki tsaya ina zuwa."

Bata jima sosai ba sai ga Firdausi ta iso da sauri. Ta buÉ—e motar Zahra ta shiga.

Tana zama, Zahra ta juya tana kallonta.

"Meya faru bayan na baki number É—in?"

Firdausi tayi murmushi kaÉ—an.

"Ki bari."

"Firdausi..." zahra ta kira sunanta

"After school zaki ga abin da nayi." Cewar firdausi

Zahra ta haÉ—e gira.

"Don Allah ki gaya min yanzu mana."

Firdausi ta girgiza kai.

"Nope. Yanzu let's go for lectures first."

Sai ta É—an kalli Zahra.

"Kuma please ki haÉ—a kanki yau, kar aje Ana lectures kina tunani"

Wani numfashi Zahra ta sauke kafin ta tada motar.

Haka suka wuce lectures tare.

A hall É—in ma Zahra ta fi jiya É—an nutsuwa saboda yanzu tana jin akwai wani abu da zata gano.

Firdausi kuwa lokaci zuwa lokaci tana kallon wayarta tana replying messages a ɓoye.

Break time suka haÉ—u da Asiya da Suhaima.

Suhaima tace,

"Yau kam Zahra ta dawo normal."

Asiya tayi dariya.

"Wallahi jiya tsoro ta bani."

Zahra tayi murmushi kawai.

Daga baya suka wuce masallaci suka yi sallah tare.

Bayan sun idar ne suka zauna a harabar masallacin na É—an lokaci, iska mai sanyi na bugunsu yayin da students ke wucewa suna ta hira.

Amma duk da Zahra na zaune tare da friends É—inta...

Zuciyarta na jiran abin da Firdausi zata gaya mata ne kawai.

Suka koma suka yi last lecture É—insu kafin aka tashi.

A hanya suna tafiya tare bayan sun yi sallama da Asiya da Suhaima, Zahra ta juya tana kallon Firdausi.

"But kin san wannan wani number ne ba na ranan ba?"

Firdausi ta haÉ—e gira.

"How?"

Sai Zahra ta fara bata labarin yadda ta sake duba recent calls ɗin Ibrahim da daddare, inda ta ga "Pretty ❤️" maimakon "Lovie Dovie."

"Wannan ma wata Pretty ce..." ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya.

Firdausi ta tsaya cak tana kallonta.

"Subhanallah..." Na É—an lokaci ta rasa abin cewa.

Sai kuma ta sauke numfashi tace,

"Shiga mota."

Zahra ta ce "Inda zamu je?"

"Zaki gani." Cewar firdausi

Zahra bata ƙara magana ba ta shiga motar. Ita dai gaba ɗaya ta kosa taga me Firdausi take ta ɓoyewa haka.

Bayan kusan mintuna talatin na tafiya, Firdausi tace mata inda zata juya.

Har suka isa wani babban park mai kyau da manyan restaurants da wajen shakatawa.

Parking Zahra tayi suka sauka.

Firdausi ta É—auki wayarta ta kira wata.

"Hello... mun iso."

Sai tayi shiru tana sauraro. Can ta ce

"Okay."

Ta kashe wayar sannan ta juya tana kallon Zahra.

"Mu shiga."

Cike da mamaki Zahra ta bi bayanta.

Suka shiga cikin wani cool down restaurant mai nutsuwa da ƙamshin coffee da perfume mai daɗi.

A wani corner na wajen wata budurwa ce zaune tana danna waya.

Kyakykyawa ce, eh... amma ko kaÉ—an bata isa ta fito da wani abu na musamman a gaban Zahra ba. Zahra ta fita da komai.. class, kyau, nutsuwa, da wani irin presence da ke sa mutum ya tsaya kallonta.

Yarinyar ma tun da suka ƙaraso wajenta idanunta suka tsaya akan Zahra.

Suka yi sallama sannan suka zauna.

"Ya only you?" Firdausi ta tambaya.

"Eh."

Bayan sun gaisa ne Firdausi ta gyara throat É—inta kaÉ—an.

"Kin san Ibrahim?"

Yarinyar ta gyada kai.

"Eh mana."

"Wane Ibrahim?"

Ta É—an yi murmushi.

"Ibrahim Khalil."

Zahra ta haɗiye wani abu a maƙoshi.

Firdausi tace,

"How long?"

"Almost two months."

Firdausi ta É—an kalli Zahra kafin ta sake maida kallonta kan yarinyar.

"Kin san yana da aure?"

Nan take yarinyar ta haÉ—e gira.

"A'a."

Firdausi ta nuna Zahra dake zaune shiru kamar mutum-mutumi.

"Wannan matarsa ce. Kuma yanzu ne ma suka yi wata da aure."

Ba ƙaramin mamaki yarinyar tayi ba.

"What?!"

Sai ta sake kallon Zahra sosai.

"Amma taya zan yarda?"

Firdausi bata ce komai ba sai ta shiga Instagram page ɗin Ibrahim a wayarta sannan ta miƙa mata.

Da sauri yarinyar ta karɓa.

Nan take idanunta suka sauka kan hotunan wedding É—in Ibrahim da Zahra.

Pictures masu kyau, videos, posting É—insa yana celebrating matarsa.

Baki ta taɓe cikin mamaki.

"Wallahi ni bansani ba..." tace da gaske. "Bai taɓa gaya min yana aure ba."

Zahra dai tana zaune shiru tana kallonta.

"Ni ma dama ba aurensa zanyi ba." Yarinyar ta ƙarasa cikin rashin damuwa. "Kawai cin kuɗinsa nake yi."

Firdausi ta dafe kanta kaÉ—an.

"Toh dan Allah ki fita daga harkarsa. Kinga matar sa tana nan, kuma ace da dare yana fita wajenta."

Yarinyar ta É—an gyara zamanta.

"Wallahi ma zan yi blocking É—insa. Amma sai ya turomin kuÉ—in da zai bani."

Zahra ce ta fara magana tun da suka zauna.

"Nawa ne?"

Yarinyar ta kalleta.

"20k."

"Account number É—inki?"

Firdausi ta juya da sauri tana kallon Zahra.

Ita ma yarinyar mamaki ya kamata.

Sai dai ta faÉ—i account number É—inta.

Nan take Zahra ta É—auki wayarta tayi mata transfer na 500k.

Kusan seconds kaÉ—an alert ya shiga wayar yarinyar.

Da sauri ta zaro ido.

"Jesus!"

Har ihu tayi tana kallon screen É—in wayarta.

"Half million?!"

Ta miƙe tsaye tana dariya harda sallen murna.

"Wallahi nagode Anty!"

Sai ta juya da sauri tana buÉ—e WhatsApp.

"Yanzu ma zanyi blocking É—insa."

Nan take ta block number Ibrahim a gabansu.

"Anty ko zan iya samun number É—inki muna gaisawa?"

Zahra ta miƙe tsaye a hankali.

"Mungode."

Sai ta juya tana kallon Firdausi.

"Let's go."

Firdausi ta miƙe itama tana bin bayanta, zuciyarta cike da mamaki da kuma tausayi ga Zahra wacce duk da ciwon da take ji... har yanzu ta zauna cikin nutsuwa da class.

Suka koma suka yi last lecture É—insu kafin aka tashi.

A hanya suna tafiya tare bayan sun yi sallama da Asiya da Suhaima, Zahra ta juya tana kallon Firdausi.

"But kin san wannan wani number ne ba na ranan ba?"

Firdausi ta haÉ—e gira.

"How?"

Sai Zahra ta fara bata labarin yadda ta sake duba recent calls ɗin Ibrahim da daddare, inda ta ga "Pretty ❤️" maimakon "Lovie Dovie."

"Wannan ma wata Pretty ce..." ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya.

Firdausi ta tsaya cak tana kallonta.

"Subhanallah..."

Na É—an lokaci ta rasa abin cewa.

Sai kuma ta sauke numfashi tace,

"Shiga mota."

"Inda zamu je?"

"Zaki gani."

Zahra bata ƙara magana ba ta shiga motar. Ita dai gaba ɗaya ta kosa taga me Firdausi take ta ɓoyewa haka.

Bayan kusan mintuna talatin na tafiya, Firdausi tace mata inda zata juya.

Har suka isa wani babban park mai kyau da manyan restaurants da wajen shakatawa.

Parking Zahra tayi suka sauka.

Firdausi ta É—auki wayarta ta kira wata.

"Hello... mun iso."

Sai tayi shiru tana sauraro.

"Okay."

Ta kashe wayar sannan ta juya tana kallon Zahra.

"Mu shiga."

Cike da mamaki Zahra ta bi bayanta.

Suka shiga cikin wani cool down restaurant mai nutsuwa da ƙamshin coffee da perfume mai daɗi.

A wani corner na wajen wata budurwa ce zaune tana danna waya.

Kyakykyawa ce, eh... amma ko kaɗan bata isa ta fito da wani abu na musamman a gaban Zahra ba. Zahra ta fita da komai—class, kyau, nutsuwa, da wani irin presence da ke sa mutum ya tsaya kallonta.

Yarinyar ma tun da suka ƙaraso wajenta idanunta suka tsaya akan Zahra.

Suka yi sallama sannan suka zauna.

"Ya only you?" Firdausi ta tambaya.

"Eh."

Bayan sun gaisa ne Firdausi ta gyara throat É—inta kaÉ—an.

"Kin san Ibrahim?"

Yarinyar ta gyada kai.

"Eh mana."

"Wane Ibrahim?" Cewar firdausi

Ta É—an yi murmushi.

"Ibrahim Khalil."

#jiddatulkhayr writes

08110615256

https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t

YOTA

Book 1

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.