Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 46 of 59
Chapter 44
Tun bayan dawowarta daga makaranta…
Zuciyar Zahra ta kasa mantawa da Saudat.
Duk sanda take cikin happy moments sai kuma hoton kayan jikin Saudat da suka tsufa ya dawo mata.
Har dare… tunani ɗaya ne kawai ke yawo a ranta.
“Ya Allah…”
“Ta yaya zan taimaka mata ba tare da ta ji kamar an raina mata ba?”
Washegari…
Bayan sun gama breakfast…
Zahra ta nufi backyard.
A can ta tarar da masu aikin gidan guda biyu suna gyara lambu.
Da suka ganta…
Sai suka yi saurin ajiye abin da ke hannunsu.
“Ina kwana Hajiya karama.”
“Lafiya.” Ta amsa cikin murmushi.
“Ya aikin?”
“Alhamdulillah.”
Ta ɗan kalli ɗaya daga cikinsu.
“Please ina son ku yi min sanitation na ɗakina.”
“Duk wardrobe ɗina a sake gyara min kayan ciki, Da shelves ma. Za ku iya?”
Nan take suka gyara tsayuwarsu.
“Za mu iya Hajiya, kafin azahar ma za mu gama In shaa Allah”
Ta yi murmushi “Thank you.”
Bayan sun gama lunch, suka raba abincin, suka Kai na dining tare da plate da spoons, sannan suka haura sama zuwa ɗakin Zahra
Nan da nan suka fara aiki, ɗaya na sharewa, ɗaya na goge mirrors.
Anty Binta ta sauke curtains ta kai laundry. Suka sake tsara tsarin shoes rack, aka share ƙarƙashin king size bed ɗinta
Suka sake jera perfumes, lotions, handcream, face mask, da duk wani kayan dake kan mirror ɗin
Suka goge glass shelves. A hankali… Ɗakin ya sake canzawa.
Ita kuwa Zahra…
Ta tsaya gaban wardrobe ɗinta, ta buɗe shi
Layuka na dresses masu tsada suka bayyana su atamfa, lace, abayas da Turkish dresses.
Ta riƙa ciro ɗaya bayan ɗaya, tana duba su sosai
“Na saka wannan sau ɗaya.”
“Wannan ma sau biyu.”
“Wannan ma ba’a san shi da ni ba both media da school”
A haka ta fara ware set by set, ba wai kuma dan sun tsufa bane, hasalima…
Da yawa daga cikinsu sababbi ne, sai dai…
Ba ta cika komawa ta sake sawa ba, musamman idan tayi hoto da shi, kuma kullum sabbin kaya ake ƙara mata.
A ƙarshe… ta ware set goma sha biyar kuma dukkansu masu kyau ne da tsada, ta naɗe kowannensu da kyau.
Ta saka su cikin wani babban fancy bag mai kyau, tayi zipping bakin bag din, sai ta ɗora a gefe
Anty Binta tana murmushi ta ce
“‘Yar Abbanta mun gama?”
Dariya tayi ta ce
“Zaku iya tafiya, thank you” daga haka suka juya suka fita
Can tana kan ware wasu veils da Jibab Mami ta leƙo
Ta tsaya tana kallon yadda ɗakin ya canza harda sheki banda kamshim da yake yi
Ta yi dariya
“Yau kuma… ’yan tsafta ne suka taso?”
Zahra ta yi dariya.
“Kai Mami…Wallahi jiya ban ji daɗi ba har dare na kasa manta da abun”
Mami ta shigo
“Me ya faru?”
Ta nuna fancy bag ɗin
“Kin ga Saudat jiya?”
“Kayan jikinta sun yi matuƙar tsufa wallahi abin ya taɓa ni.”
“Ba na so mutane su riƙa raina ta shi ya sa na ware waɗannan, zan ba ta”
Mami ta buɗe bag ɗin ta ɗauki ɗaya daga cikin kayan sai ta kalli Zahra.
“Baby… Ba su yi yawa ba?”
Zahra ta girgiza kai.
“A’a Mami.”
“Besides… ban cika saka su ba, kuma Ita ce ta fi buƙatarsu.”
Mami ta yi murmushi cike da alfahari, ta shafa kumatunta
“Allah Ya ƙara miki zuciyar taimako Fatima. Kin san sirrin arziki?”
Zahra ta girgiza kai.
“Mutum ya riƙa taimakon wanda bai da shi. Sai kiga kullum Allah zai na Kara masa ninkinsa saboda ya san hannunsa a buɗe yake.”
“Allah Ya ba ki lada.”
Zahra ta yi murmushi.
“Ameen.”
Mami ta juya ta fita.
Da yamma…
Zahra na saukowa daga sama…
Yayi dai-dai da lokacin da Ya Umar ya dawo daga office
Da ganinsa… ta yi saurin ƙarasa
“Yayaa!”
Ya yi murmushi.
“My Baby.”
Ta karasa ta kama hannunsa.
“Zo”
Ya kalleta
“Ina?”
“Zo mana zaka ji koma menene”Ba ta ba shi damar tambaya ba.
Ta ja shi har cikin parlour.
Yana kallon kofar side ɗinsa ya ce “Ki jira. Bari na yi fresh up.”
Mintuna kaɗan bayan haka…
Ya fito cikin casual wear.
Har sannan ta na zaune tana jiransa, ya zauna a gefenta
Sai ta sake kama hannunsa ta miƙe tsaye, ta ja shi zuwa dining area.
Ya yi dariya.
“Ke… Me ya same ki ne yau?”
Serving ɗinsa tayi, ta tura masa abincin gabanta, ita kuma ta ɗora haɓa a hannunta, tana kallonsa sosai.
“Yaya…”
“Hmm?”
“Yaushe za ka yi aure?”
Ya kusan shaƙewa da ruwan da yake sha. Ya kalleta.
“Not now! Not anytime soon.”
Ta haɗe fuska.
“Yaya me haka kuma? Idan ba ka da budurwa… Ni zan nema maka.”
Ya yi dariya sosai.
“Toh ke ina ruwanki?”
Ta ɗan turo baki.
“Akwai mana, babba ma kuwa”
Ya girgiza kai yana dariya.
“Toh Madam Matchmaker. Wace kika samo?”
Ta yi murmushi
“Please… ka auri Saudat.”
Ya Umar ya ɗan taɓe fuska
“Saudat? Wace ce kuma?”
Zahra ta ɓata fuska “Friend ɗina mana wannan farar nan… Wacce take zuwa nan tare da Firdausi.”
Ya ɗanyi tunani ya. D
“Oh… Ita! Toh me ya sa?”
Zahra ta ce cikin fara’a
“Saboda tana da kirki, tana da tarbiyya, kuma ina ganin za ku dace.”
Ta ɗan yi shiru
Sannan ta ƙara da murmushi.
“Kuma Kaga babu tuwanta da magana especially idan she’s not comfortable da mutum
Ya Umar ya fashe da dariya.
“Wallahi ke akwai ki da abin dariya.”
Sai kuma yayi shiru sannan ya ɗaura
“Baby… Kawarki ba ta min.”
“Kuma… She’s not my type, besides… ba yanzu zanyi aure ba maybe after four years.”
“By then, zan kai shekara talatin da biyar.”
Zahra ta haɗe fuska, ta marairaice
“Pleaseeeee…”
Ya Umar ya girgiza kai yana dariya.
“Sorry!!! No negotiation.”
Ta sake ƙoƙarin lallashinsa
“Yaya…”
Ya ɗaga hannu
“Discussion closed.”
Ta tsaya tana kallonsa da ɓacin rai irin na shagaɓɓan yara, sai ta yi tsaki a hankali, ta miƙe tsaye.
“Ni ba zan sake magana da kai ba.”
Ta juya za ta tafi.
Ya Umar ya yi dariya har da riƙe ciki.
“Baby…”
Ta ƙi waiwayowa, ta i gaba da tafiya.
Shi kuma ya girgiza kai yana murmushi.
“Wannan yarinyar…”
“Wai har ita ce zata neman min mata…
Tun bayan hirarta da Ya Umar…
Zahra ta ƙuduri aniyar nuna masa fushi.
Duk da ya san halinta sarai…
Ita kam ta ɗauki maganar da muhimmanci.
Tun da ta shiga ɗaki ta rufe bata sake fitowa ba.
Ko lokacin da Mama Ladi ta kawo mata fruits da juice…
Sai ta ce
“Ki ajiye a bakin kofar
Har yamma ta yi magariba ta gabato har ta shige. Har lokacin dinner ya yi…
Zahra ba ta fito ba.
A dining room, kowa ya hallara
Abbah na zaune a kujerarsa, Mami na gefensa Mummy da Batoul ma suna nan.
Ya Umar ya zauna shiru yana cin abincinsa, sai dai lokaci zuwa lokaci idanunsa na bin staircase. Yana jiran fitowar Zahra.
Amma shiru…
Ba alamar za ta sauko.
Abbah ya ɗaga kai ya zagaya dining ɗin da kallo, sai ya haɗe gira
“Baby fa?” Ba ta sauko ba?”
Mummy ta ɗaga kai daga plate ɗinta
“Da yamma dai na ga kamar ta wuce backyard da books a hannunta Maybe karatu take yi.”
Mami ta kalleta da mamaki.
“Da wannan daren? Sai ta zauna a backyard?”
Mummy ta ɗaga kafaɗa
“Ni abin da na gani kenan.”
Abbah bai ce komai ba, ya ajiye spoon ɗinsa, ya miƙe tsaye
Ba tare da ya ƙara wata magana ba… ya juya ya nufi staircase.
Ya Umar ya bi bayansa da kallo.
A zuciyarsa ya san… Wataƙila har yanzu Zahra na fushi da shi ne
Abbah ya hau sama, kai tsaye ya nufi ɗakin Zahra.
Da ya isa…
Sai ya lura ƙofar ba a rufe take ba.
Yayi knocking kafin ya tura ta a hankali, ƙofar ta buɗe.
Abin da ya gani…
Sai ya sa murmushi ya suɓuce masa.
Zahra na zaune a kan gadonta, ta baza littattafai a gabanta, Laptop a buɗe, highlighter a hannu.
Hankalinta gaba ɗaya na kan karatu, sai da ta ji ƙarar ƙofar…
Ta ɗago kai.
Da idanunta suka sauka kan Abbah…
Nan take fuskarta ta sauya, ta yi murmushi
“Abbah.”
Ya jingina da ƙofar yana kallonta.
“Har yanzu kina karatu?”
Ta yi dariya
“Exam is around the corner.”
Ya gyaɗa kai cikin tausayawa.
“Karatu yana da kyau, amma ba da yunwa ba.”
Ya miƙa mata hannu
“Help me.”
Ta haɗe gira cikin wasa
“Da me?”
Ya yi murmushi.
“Ki zo ki ci abinci kafin cikin ki ya fara kara”
Ta rufe littafin da ke hannunta.
“Alright, Abbah.”
Ta sauko daga kan gadon, ta gyara scarf ɗinta, ta ɗauki wayarta. Sai ta kashe laptop ɗin.
Abbah ya jira har ta ƙarasa, sannan suka fito tare.
Yana tafiya a hankali
Ita kuma na biye da shi. Har suka sauko staircase…
Idanun duk waɗanda ke dining suka koma kansu. Musamman Ya Umar.
Da ya ga Zahra ta sauko lafiya, sai ya sauke numfashin da bai ma san yana riƙe da shi ba.
Shi kuwa Abbah…
Ya ja mata kujera kusa da tasa
“Zauna Baby.”
Ta zauna cikin nutsuwa, Mummy ta miƙe ta fara serving ɗinta.
Zahra ta fara cin abincin a hankali.
Sai dai…
Ko sau ɗaya ba ta kalli Ya Umar ba.
Shi kuwa…
Lokaci zuwa lokaci idanunsa na komawa kanta.
Yana son ya yi magana, amma ya san halin ƙanwarsa.
Idan ta ce tana fushi…
Sai ta gama fushinta kafin ta dawo yadda take.
Kyan zuciyarta ba ta daɗe da riƙe ƙulli ba…
Amma idan ta kama, sai wanda ya san yadda zai lallabeta.
Ya Umar ya ɗan yi murmushi a a zuciyarsa ya ce ‘Ai Baby… nan da gobe za ta manta’
Karan spoons kawai kake ji saboda babu mai cewa komai…
Can… Zahra ta ɗaga kanta ta kalli Abbah
“Abbah…”
Ya amsa yana kallonta.
“Na’am, Baby.”
Ta ɗan ajiye spoon ɗinta
“Ka ce Ya Umar ya yi aure.”
Nan take…
Kowa ya ɗaga kai ya kalleta.
Batoul ta haɗe gira tana mata wani kallo
Mummy ta dai baka gane me fuskanta yake nufi sai dai expressionless
Mami kuwa ta kalli Zahra tana murmushi, tana jiran jin abin da zai biyo baya.
Shi kansa Ya Umar…
Sai da ya kusan haɗiye abincin ba tare da ya tauna ba. Ya ɗaga kansa yana kallon Zahra
Abbah ya yi murmushi.
“Toh Baby?”
Zahra ta gyara zamanta.
“I mean it fa Abbah. Kace dole ya yi aure soon.”
Ta nuna Ya Umar da spoon ɗinta.
“Ko kuma ya bar maka gida. Saboda ai ya girma.”
Ya Umar ya dafe goshinsa a hankali
“Innalillahi…”
Abbah ya kasa riƙe dariyarsa, sosai yake kyasawa, ya girgiza kai
“An yi faɗa da Yaya kenan?”
Zahra ta girgiza kai da sauri.
“A’a. Kawai ya yi aure, Idan ma ba shi da budurwa…”
Sai ta ɗan yi murmushi.
“Ya zo na zaɓa masa Mata, wallahi… She’s very beautiful, Abbah.”
Wannan karon… Abbah ya fashe da dariya
Ya riga ya fahimci inda maganar ta dosa
Mami ta jingina da kujera tana kallon Zahra cike da nishaɗi
Mummy da Batoul kuwa… Sai kallonta suke yi
Zahra ta sake kallon Abbah.
“Abbah! Ba ka faɗa masa ba fa, ai gashi nan, yana jin ka.”
Abbah ya share hawayen dariyar da ta taru a gefen idonsa.
Sannan ya juya ya kalli Ya Umar
“Umar.”
Ya Umar ya ɗago kai
“Na’am Abbah.”
“Kanwarka tace ka yi aure, kuma idan ba ka da matar… tace ta samo maka.”
Ya Umar ya sauke numfashi, sai ya yi murmushi
“Gaskiya Abbah… ba ni da ra’ayin yin aure yanzu, Ina da abubuwa da yawa a gabana. Ina so na gama settling ɗinsu. Sai daga baya nayi”
Abbah ya gyada kai cikin fahimta.
“Okayy”
Sai ya juya ga Zahra
“Baby.”
Ta ɗaga kai.
“Aure ba abin gaggawa ba ne, a hankali ake zuwa har Allah Ya kawo lokacin kuma baza a tilasta mutum ya yi aure ba…”
“Musamman idan har bai shirya ba, Idan lokaci ya yi… Shi da kansa zai yi.”
Zahra ta ɗan turo baki.
Fuskarta ta nuna ba ta gamsu ba.
Amma… bata yi gardama ba.
Mummy ta yi wani ɗan murmushi mai cike da ba’a.
“Ai yau na ga abin da bai ishe ni ba. Kowa dai ya tattaru akan kula da Umar.”
Ba wanda ya bi maganarta. Abbah bai ko kalleta ba.
Mami ma ta ci gaba da cin abincinta cikin nutsuwa.
Zahra kuwa…
Ta ɗan girgiza kai.
“Okay, Abbah.”
Ba don ta yarda da abin da ya faɗa ba… Sai don ta fahimci babu wanda zai goyi bayan shirinta a wannan lokacin.
Sai ta koma cin abincinta cikin nutsuwa, amma a zuciyarta…
Ta riga ta yanke hukunci.
“Wannan maganar ba ta ƙare ba sai na nemo wata hanya”
Ya Umar ya sace kallonta, ya girgiza kai yana murmushi
Bayan an gama dinner… Kowa ya miƙe daga dining
Abbah ya nufi parlonsa kamar yadda ya saba.
Ya Umar ya tsaya yana magana da ɗaya daga cikin masu aikin gidan.
Mummy da Batoul kuma suka haura sama ba tare da sun ce komai ba.
Mami kuwa har ta nufa hanyar ɗakinta sai kuma ta waiwaya tana kallon Zahra ta
“Baby.”
Zahra da ke shirin hawa sama ta juya.
“Na’am, Mami?”
“Zo ki same ni a ɗakina.”
“Toh Mami.”
Mintuna kaɗan bayan haka…
Zahra ta tura ƙofar ɗakin Mami.
Ta yi sallama, ta shiga
Mami na zaune kan ƙaramin sofa tana jan tasbaha.
Ta ɗaga hannu
“Zo ki zauna.”
Zahra ta ƙarasa ta zauna a ƙafafun Mami kamar yadda ta saba tun tana ƙarama.
Mami ta shafa kanta cikin tausayi.
Sai ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Baby.”
“Na’am.”
“Na san zuciyarki.”
“Kuma na san kina son haɗa alkhairi ne”
Zahra ta yi murmushi, amma ba ta ce komai ba.
Mami ta ci gaba
“Amma akwai wani abu da nake son ki fahimta.”
Ta ɗan gyara zamanta
“Ba a wuce gaba wajen haɗa aure.”
Zahra ta ɗaga kai tana kallonta.
Mami ta ce a hankali
“Idan aka yi aure kuma aka samu matsala… ba wai namiji da matar kaɗai za su ji zafi ba, duk wanda ya shiga tsakani ma zai shiga damuwa”
Ta ɗan yi shiru. Sannan ta ci gaba.
“Misali…”
“Idan Saudat ta fito da wani hali da ba a sani ba, Ya Umar zai yi kuka da ke Ni, gani zai yi kinsa ni kuma kin boye masa
“Idan kuma… Allah Ya kiyaye…”
“Ya Umar ne ya fito da wani hali…Saudat ce za ta yi kuka da ke Ne, gani zata yi kin boye mata. Kuma hakan na bata zumunci”
Saboda haka…
“Ki bar kowa da ƙaddarar da Allah Ya rubuta masa. Idan Allah Ya rubuta matarsa ce… Ko babu wanda ya haɗa su, za su haɗu”
Tayi shiru Tana kallon fuskarta, sai kuma ta daura
“Idan kuma babu aure tsakaninsu ko duniya ta haɗu… ba za su zaɓa zana mata da miji ba.”
Zahra ta yi shiru
Tana sauraron Mami cikin nutsuwa, sai kuma ta ɗan haɗe gira.
“Mami…”
“Taya kika san Saudat ce?”
Mami ta yi wani murmushin manya. Ta ɗan ja kumatun Zahra
“Da ba ni na haife ki ba… Sai ki yi min wannan tambayar.”
Zahra ta fara dariya.
“Ashe kin gane?”
Mami ta amsa tana murmushi.
“Har tun lokacin da kika fara wannan maganar. Na riga na fahimci inda kika dosa.”
Zahra ta sauke kanta ƙasa cikin kunya, tana dan murza yatsunta.
“Sorry Mami.”
Mami ta ɗago haɓarta.
“Kada ki ba ni haƙuri. Ki dai koyi darasi.”
Zahra ta gyada kai.
“Na fahimta Kuma ba zan sake cewa komai ba.”
Mami ta yi murmushi cikin gamsuwa.
“Better! Allah Ya miki albarka, ya ƙara miki hikima.”
“Ameen, Mami.”
Zahra ta miƙe tsaye, ta sunkuya ta yi wa Mami kiss a kumatu.
“Good night.”
“Good night, Baby.”
Ta juya, ta fita daga ɗakin.
Yayin da Mami ta bita da kallo…
Sai ta yi murmushi ita kaɗai.
Ta san Zahra tana da zuciyar taimako.
Sai dai kuma…
Har yanzu tana cikin shekarun da zuciya ke rinjayar tunani.
Shi ya sa ta ga dacewar ta koya mata cewa…
Ba kowace ƙauna ce ake mayarwa aure ba, kuma ba kowace matsala ce mutum zai shiga tsakani ba
#Farashin izzah
500 ne ta wannan acc no 7084571222, Hauwa Jibrin Opay
Shaidar biya ta wannan 08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.