Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 41 of 59
Chapter 39
Mummy na zaune a ɗakinta ita kaɗai
Ƙofar balcony ta ɗan buɗe, iska mai sanyi na shigowa tana kaɗa labulen ɗakin
Wayarta na manne a kunnenta
Muryarta ta yi ƙasa sosai, tamkar ba ta son ko bango ya ji abin da take faɗa balle kuma wani
“…na faɗa maka kar ka damu.” Ta ɗan yi shiru tana saurare.
“A’a… ba yanzu ba” Ta sake yin shiru
Sai kuma ta ce
“Zan sake kiranka idan na tabbatar”
A dai-dai lokacin… Knock! Knock!
Ta ɗago kai. Kafin ta yi magana…
Aka buɗe Ƙofar a hankali, Ya Umar ne
Da ganinsa… Sai ta yi wata irin razana
Da sauri ta sauke wayar daga kunnenta, ta katse kiran ba tare da ta yi sallama ba, ta ajiye wayar gefenta cikin sauri
Sannan ta ɗago tana kallonsa
Idanunta cike da wani irin ruɗani da ta yi ƙoƙarin ɓoyewa.
Ya Umar ya ɗan haɗe gira.
“Mummy…?”
Ta gyara zamanta
“Me ya kawo ka?”
Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu sannan ya ce cikin ladabi,
“Na zo ne…na ba ki haƙuri, game da abin da ya faru ɗazu.”
Mummy ta kau da kai, ba tare data kalle shi ba, sai ta ce cikin sanyin murya,
“Na ji.”
Ya jira ko za ta ƙara magana amma ta yi shiru
Ya sake cewa,
“Mummy, wallahi ba….”
Ta katse shi
“Na ce na ji.”
Sai ta ɗan ɗago kai
“Ka je ka kwanta, mu yi magana gobe.”
Ya Umar ya kalleta cikin mamaki.
Ba wannan amsar yake zato ba, yawanci idan ya zo wajen Mummy, ko da tana fushi, sai ta yi magana masifa especially idan Akan Zahra ce
Amma yau… tamkar tana son ya fita daga ɗakin da wuri, sai Sannan reaction dinta daya shigo ya dawo masa, ya dan kalle gefenta sai kuma ya ce
“Toh…Sai da safe.”
Ta gyada kai kawai, ba ta ƙara cewa komai ba
Ya Umar ya juya ya fita, haɗi da kulle mata kofar, yana kulle kofar
Mummy ta sauke numfashi a hankali
Ta ɗauki wayarta, ta kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu sai ta lumshe idanunta… ba tare da ta sake kiran lambar ba.
Washegari…
Tun bayan data idar da sallar Azahar, Zahra ta shiga ɗakinta ta shirya cikin wata doguwar abaya mai launin maroon, tayi rolling veil, ta ɗauki handbag ɗinta black tare da sanyawa fararen kafarta black flat shoe, sannan ta sauko ƙasa
Mami ce ta fara hangota
“Ina kuma za ki?”
Zahra ta yi murmushi
“Gidansu Saudat zan je, Mami.”
Mami ta gyada kai
“Allah ya kiyaye hanya, amma kar kiyi yamma”
“Ameen, Toh Mami”
Tana fita compound driver ya taso “Fita ne Hajiya?” Kai kawai ta gyada masa
Malam Bala ya buɗe mata ƙofa ta shiga, daga nan suka fice daga gidan
Tafiya sosai suka ɗanyi, sannu a hankali suka bar manyan tituna suka shiga cikin unguwannin cikin gari, titunan sun yi ƙunci dakyar motoci ke iya bi ta wajen
Gidaje suna manne da juna, ga gidajen kananu
Yara na ta wasa a bakin hanya, wasu mata kuma na zaune a ƙofar gidajensu suna hira.
Motar ta tsaya a gaban wani ƙaramin gidan haya mai tsohon gate
Driver ya sauka ya buɗe mata ƙofa,
Zahra ta sauka, ta ɗan ɗaga kanta tana kallon gidan
Ba wani babban gida ba ne…
Amma an ana ƙoƙarin tsaftace gidan duk da yanayin rayuwar da suke ciki
Ta ƙarasa bakin ƙofar da sallama
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Wata dattijuwa mai fara’a ta fito zata hanyar kitchen
Tana ganin Zahra… Sai fuskarta ta cika da murmushi nan take
“Ah… Zahra! Maraba da zuwa, ’yata.”
Zahra ta sunkuyar da kai cikin girmamawa tana murmushi
“Ina wuni, Mama?”
“Lafiya lau, Alhamdulillah.”
“Ya gida?”
“Lafiya.”
Mama ta matsa gefe
“Shigo mana Saudat tana ciki.”
“Nagode.”
Zahra ta shiga, parlourn gidan ƙarami ne, babu komai a cikinta sai tabarma ce shimfiɗe a ƙasa, tare da wasu ɗa pillows a gefe.
Ko da ta shiga… ba ta nuna komai a fuskarta ba
Ta yi sallama cikin fara’a
“Assalamu alaikum.”
Da jin muryarta… Saudat ta fito da gudu daga ɗaya daga cikin ɗakunan
“Zahra!”
Ta ƙaraso da sauri ta rungume ta
“Kai! Ban yi tunanin za ki zo ba.”
Zahra ta yi dariya
“Me ya sa ba zan zo ba?”
Suka zauna a kan tabarmar
Sai ga Mama ta shigo da ruwa a cikin wani cup kana gani kasan cup din ya jima sosai
Ta ajiye gabanta
“Ga ruwa, ’yata.”
Zahra ta yi murmushi
“Nagode sosai, Mama.”
Mama na fita…
Saudat ta ɗan matsa kusa da ita
“Zahra… karki sha.”
Ta yi mamaki
“Me ya sa?”
Saudat ta sauke numfashi
“Ba irin ruwan da kika saba sha ba ne kar wani abu kuma ya same ki”
Zahra ta kalli cup ɗin
Sai ta ɗago ta kalli Saudat, ta yi murmushi
“Waye ya ce miki ban sha?”
Ba tare da ta ƙara magana ba… Ta ɗauki cup ɗin
Ta ce Bismillah a ranta, sannan ta sha. Ko kaɗan ba ta nuna wata alama ta ƙyama ba, amma ba kadan ba taji kamar tana son tayi amai
Saudat ta kasa ɗauke idanunta daga kanta
“Zahra…”
“Me?”
Ta yi murmushi kawai.
Bayan sun ɗan yi hira… Zahra ta kalli kawarta
“Toh…Kin fara shirye-shiryen university kuwa?”
Nan take fuskar Saudat ta sauya, ta sunkuyar da kai
Na wasu daƙiƙu ba ta ce komai ba
Daga ƙarshe ta ce cikin sanyin murya,
“Gaskiya… ba na jin zan ci gaba da karatu”
Zahra ta haɗe gira
“Me ya sa?”
“Kin san halin da muke ciki. Mama ba za ta iya ba, Ni ma ba zan matsa mata ba.”
Shiru ya ratsa tsakanin su
Sai Zahra ta kama hannunta
“Saudat…”
Ta ɗago kai tana kallonta
“If you’re willing to read… I’m willing to help you.”
Saudat ta zaro ido
“Kina nufin…”
Zahra ta katse ta da murmushi
“Eh! Registration, school fees, abin da zan iya… Za mu yi tare.”
Saudat ta ci gaba da kallonta
Kafin ta ankara… Hawaye suka cika idanunta
Ta faɗa jikin Zahra ta rungume ta da ƙarfi ta fashe da kuka.
“Na gode… Wallahi ban san ya zan saka miki ba.”
Zahra ta shafa bayanta a hankali
“What are friends for?”
Mama ce ta shigo a lokacin
Da ta ga Saudat na kuka a jikin Zahra…
Ta firgita
“Lafiya kuwa?”
Saudat ta share hawayenta
“Mama… Zahra ce… ta ce za ta taimaka min na ci gaba da karatu.”
Dattijuwar ta tsaya cak
Idanunta suka cika da ƙwalla.
Ta ɗaga hannayenta sama.
“Allah… Ya saka miki da alheri, ’yata. Allah Ya buɗe miki ƙofofin alkhairinsa sannan ya baki abokin rayuwa Nagari”
“Ameen” Cewar Saudat
Zahra ta yi murmushi cikin kunya
“Adduan nan yafi komai ai Mama, Nagode kuma a cigaba da mana addua”
Kai kawai ta gyada ta gama zama speeches sai kuma ta kira wani ƙaramin yaro
“Aliyu!”
Yaron ya shigo da gudu.
“Na’am, Mama.”
“Ga kuɗi nan Je ka siyo mana alale.”
“To Mama.” Daga haka ya fice daga parlon, Mama ta wuce ciki
Bayan ɗan lokaci…
Yaron ya dawo da alalen a wani kwanon roba
Mama ta ajiye a gabansu
“Ki ci ’yata, namu abincin ba lalle ki iya ci bane”
Zahra ta ɗan yi murmushi
“Nagode.”
Ta ɗauki kaɗan, a hankali ta fara ci
Ba saboda tana jin yunwa ba…
Sai don kar su ji kamar ta raina abin da suke da shi, kuma bata so tasa suji wani iri da effort dinsu
Duk da haka… da ƙyar ta iya cin rabinsa, amma fuskarta cike take da murmushin dole
A zuciyarta kuwa…
Ta sake godewa Allah daya azurta Abbahnta sannan karo na biyu data sake jin ta tsane talauci kuma bata fatan ko kaddararsa ya same su
Can bayan sun sha hira….
Ta ɗauki handbag ɗinta ta miƙe tsaye
“Toh Saudat, zan wuce.”
Saudat ma ta miƙe
“Da wuri haka?”
Zahra ta yi murmushi
“Ina son na isa gida kafin yamma.”
Ta ɗan buɗe handbag ɗinta
Ta ciro wani farin envelope mai kauri ta kama hannun Saudat, ta sanya mata shi a hankali
Saudat ta haɗe gira
“Wannan kuma?”
Zahra ta girgiza kai
“Karki buɗe yanzu, ki je ɗaki tukuna idan na tafi”
Saudat ta kalleta cikin mamaki
“Zahra…”
Ta katse ta da murmushi
“Make sure kin je kin yi online screening, an fara registration, ba na son ki bari lokaci ya ƙure”
Saudat ta ji wani iri
Ta matse envelope ɗin da hannunta
“Amma…”
“A’a” Zahra ta sake katse ta.
“Ki ɗauke shi a matsayin taimakon da zaki ma ƙawarki.”
Hawaye suka sake taruwa a idanun Saudat, ta gyada kai
“In shaa Allah ba zan ba ki kunya ba tunda kina so nayi karatu, Allah ya biya ki Zahra”
Mama ta fito daga ɗaki daidai lokacin
Da ta ga envelope ɗin a hannun Saudat, ta fahimci abin da ya faru.
Ta dafe ƙirjinta.
“Kaii ‘yar nan…”Ta ƙaraso gabansu
“’Yata…Wallahi ban san irin godiyar da zan yi miki ba.”
Zahra ta yi saurin kama hannunta cikin ladabi.
“Haba Mama Kada ki ce haka.”
“Ku ci gaba da yi min addu’a kawai.”
Mama tayi murmushi
“Allah Ya saka miki da gidan Aljannah, Allah Ya ƙara wa iyayenki lafiya da arziki.”
“Ameen Ameen, Nagode”
Zahra ta amsa cikin nutsuwa.
Ta rungumi Saudat na ƙarshe
“Ki kira ni idan akwai wani abu.”
“In shaa Allah.”
Ta yi sallama da Mama.
Sannan ta juya ta fita.
Har bakin gate Saudat da Mamanta suka raka ta.
Driver ya yi saurin buɗe mata ƙofar motar. Ta shiga
Ya rufe ƙofar cikin girmamawa.
Da motar ta fara tafiya…
Saudat da Mamanta suka ci gaba da daga mata hannu har sai da motar ta ɓace daga ganinsu.
Da suka fita daga ƙunƙuntar unguwar suka hau babban titi…
Zahra ta jingina bayanta da seat
Ta saki wani dogon numfashi.
“Alhamdulillah…”
Ta lumshe idanunta na wasu daƙiƙu
Sai a lokacin ta ji kamar numfashinta ya dawo yadda ya kamata
Tun tana gidan Saudat…
Ta yi ƙoƙarin kada ta nuna wani abu da zai sa su ji ba daɗi, amma sosai take jin tashin zuciya
Ta buɗe idanunta ta kalli tagar motar, a hankali ta yi murmushi
A zuciyarta ta yi addu’a,
“Ya Allah… Ka yalwata musu arzikinka, Ka sauƙaƙa wa Mama, Ka kuma ba Saudat ikon cika burinta.”
Mai gadi ya buɗe gate cikin girmamawa, bayan yaji horn din motar gidan ne
Driver ya yi parking a wajen da ake parking motocin gidan, kafin ya fito ya buɗe mata ƙofa…
Sai suka hango Abbah.
Yana tsaye a gefen wata motarsa tare da wasu ma’aikata biyu, da alama yanzu ya dawo daga office ne
Da ya hango Zahra a bayan motar
Sai ya ɗaga hannu.
“Tsaya.”
Driver ya yi saurin kashe motar
Zahra ta buɗe ƙofar ta fits
Da murmushi ta nufi wajen Abbah.
“Abbah na…”
Ta daura kanta kafadarsa tana gaishe shi
“Lafiya lau, Baby” Ya amsa cikin fara’a.
Ya shafa kanta kamar yadda ya saba
“Kin dawo?”
“Eh.”
“Ya gidansu Saudat?”
Ta yi murmushi
“Lafiya. Mun yi hira sosai.”
Ya gyada kai cikin gamsuwa.
“Alhamdulillah.”
Ta ɗan ɗaga gira.
“Abbah…”
“Uhum?”
“Za ka shiga ciki ne?”
Ya girgiza kai
“A’a. Sai dai ina son ki yi min wani aiki.”
Ta yi saurin amsawa
“Toh.”
Ya ciro wallet ɗinsa
Ya fito da katinsa, sannan ya miƙa mata.
“Ki je Dubai supermarket. Akwai wasu abubuwan da nake buƙata.”
Ta karɓi katin tana kallonsa cikin mamaki
“Ni?”
“Eh.”
Ta yi dariya
“Toh me ya sa ba za ka aika driver ko Ya Umar ba, ka manta ban Iya selecting ba”
Abbah ya ɗan yi murmushi.
“Saboda ina so ke ce ki zaɓo min su.”
Tayi murmushi
“Da alama dai yanzu Abbah ya fara yarda da aike na”
Ya yi dariya.
“Kin yarda?”
Ta gyada kai
“In shaa Allah.”
Ya juya ya kalli driver.
“Ka mayar da ita. Sannan ku wuce supermarket ɗin da na gaya maka, Baby ke kuma ki duba WhatsApp dinki”
Driver ya gyada kai
“Toh, Alhaji.”
Zahra ta sake kallon Abbah
“Toh ni zan tafi.”
“Allah ya tsare.”
“Ameen.”
Ta koma ta shiga motar.
Driver ya kunna motar
Motar ta juya ta sake fita daga compound…
Yayin da Zahra ke zaune a bayan mota tana mamakin irin aikin da Abbah ya aike ta yi. Dan bai taba aikanta ba
Ta jingina da seat tana murmushi a hankali.
“Abbah ma sai ya ce ni ce zan zaɓa masa kaya…”
Ta girgiza kai cikin dariya.
Bayan motar Zahra ta fice daga compound…
Abbah ya juya ya kalli mutanen da tun ɗazu suke jiran umarninsa.
“Okay…Ku fara.”
Kamar an saki tsuntsaye… Kowa ya kama aikinsa
Wasu suka fara sauke manyan cartons daga wata delivery van.
Wasu kuma suka shiga ɗauko kayan ado.
Cikin mintuna kaɗan…
Farin compound ɗin ya fara sauya kamanni
An ɗaure manyan balloons fari, gold da sky blue a jikin pillars, bakin parlour da kuma hanyar shiga gidan
Flower stands masu kyau aka jera a gefuna
Wata ƙungiyar decorators kuwa na ta gyara wajen cikin sauri da ƙwarewa
Mami ta fito daga parlour
Da ta ga yadda ake ta kai-komo…
Sai ta yi murmushi
“Allah ya sa Baby ta yi farin ciki.”
Abbah ya amsa da murmushi.
“In shaa Allah, ai Allah yasa tana zuwa na mayar da su can far supermarket kafin su dawo an gama komai”
Ana cikin haka bada jimawa ba…
Aka ji ƙarar wata babbar mota tana shigowa
Sabuwar mota ce fill… Latest version.
Har yanzu nylon na jikin wasu sassan cikinta
Da aka sauke ta daga carrier…
Aka fara yi mata ado.
Manyan ribbons masu launin gold da blue aka ɗaura a kanta
Aka zagaye ta da balloons masu tsari
Da kallo ɗaya…
Za ka fahimci cewa an tanade ta ne domin mutum na musamman.
Ya Umar ya fito yana kallonta.
Ya yi ɗan busa iska
“Abbah… wannan kuma?”
Abbah ya yi murmushi kawai
“Ka bari za ka gani.”
Ya Umar ya girgiza kai yana dariya
“Baby za ta haukace da murna.”
Mami ta amsa cikin fara’a.
“Allah ya sa.”
A gefe guda kuma…
Wasu ma’aikata suka shigo ɗauke da wani babban banner.
Da aka buɗe shi…
Sai kyakkyawan hoton Fatima Zahra ya bayyana a tsakiyarsa
A sama an rubuta da manyan haruffa masu kyau
“Happy Birthday To Our Precious Princess, Fatima Zahra.”
A ƙasa kuma aka ƙara da saƙo mai taɓa zuciya
“May Allah bless your new age with happiness, barakah, success and endless joy. We love you today and always.”
Abbah ya tsaya yana kallon banner ɗin
Fuskar sa cike da gamsuwa.
“Nan…” Ya nuna gefen garden.
“A nan za a kafa shi”
Nan take suka ɗauke shi suka kafa a inda ya nuna.
A lokaci guda…
Wata mota ta sake shigowa
Caterers ne.
Suka fara sauke manyan food warmers ɗaya bayan ɗaya
Ƙamshin abinci ya fara gauraye da iskar compound.
A wani gefe kuma…
An sauko da wata katafariyar birthday cake mai hawa uku.
An yi mata ado cikin launukan fari, gold da sky blue.
An rubuta a kanta da golden icing
“Happy 17th Birthday, Princess Zahra.”
Mami ta dafe baki.
“Subhanallah… lallai Yau Dear ka nuna min kafi kaunar Zahra da ni, in ba haka ba yaushe duk ka shirya wannan ban sani ba”
Abbah ya yi murmushi
“Ba ta cancanci ƙasa da haka ba ne. Ke ma idan kishin zaki fara da ita sai na sani”
Dariya tayi ba tare data ce komai ba
Da komai ya kusa kammaluwa…
Abbah ya kira mai gadi
Gatekeeper ya ƙaraso da sauri
“Na’am, Alhaji.”
Abbah ya kalle shi sosai
“Da zarar driver ya dawo da Baby…Kada ka buɗe musu gate nan take.”
Mai gadin ya gyada kai cikin kulawa.
“Toh, Alhaji.”
“Ka fara zuwa ka sanar da ni sai bayan na ba ka umarni… sannan ka buɗe gate.”
“Na gane. Ba za a samu kuskure ba, In shaa Allah.”
Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa.
“Madalla.”
Mai gadin ya koma bakin gate
Shi kuwa Abbah ya ɗan yi wa compound ɗin kallo.
#FARASHIN IZZAH
#Hauwajay writes
#08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.