Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 33 of 59

Chapter 32

Yarinyar ce ke saukowa daga matakala, sweet na cikin bakinta, fuskarta kuwa cike take da hawaye. Da alama ko ƙafafunta ba za su iya ɗaukarta ba, domin a hankali take saukowa kamar za ta faɗi a ƙasa.

Da sauri mutumin ya ƙaraso gabanta, kafin ma ta kai ƙarshen matakalar ya durƙusa ya ɗauke ta cak.

Sama ya É—aga ta yana dariya, sannan ya yi mata kiss a kumatu.

Nan take ta kwalla ihu na murna tana cilla ƙafafunta sama.

Ya sake yi mata wani kiss, sannan ya fara share mata hawayen da suka ɓata kyakkyawar fuskarta.

"Mamana, wa ya taɓa min ke?" Ya tambaya cikin kulawa.

Babyn ta juya ta kalli mutanen da ke tsaye a gefe. Nan take ya bi kallonta.

Wani matashiyar Mata ya kala, É—an haÉ—e gira yayi

"Khadijatou, me kika yi wa 'yata?" Ya tambaya

Tsohuwar matar da ke zaune a gefe ta yi saurin cewa,

"Kul! Kar ma ka soma. Da ba don jika ta fi 'ya ba, da na nuna maka rashin mutunci idan ka ce zaka taɓa Hadiza."

Dariya suka yi gaba É—aya. Khadijah kuma ta masa gwalo

Ya haÉ—e gira yana kallonta, yayin da har sannan yake tsaye tare Babyn

Mama ta yi murmushi tace,

"Sannu da zuwa. Toh ai sai ka ajiye shalelen naka."

Khadijah ta girgiza kai

“Ah toh! Ni kam naga ko hutawa bai yi ba, balle a yi maganar cin abinci."

Ta nuna yarinyar da ke jikinsa

"Idan ka biye wa wannan Baby ɗin taka, ba za ka taɓa hutawa ba."

"Ina ruwanku?"

Ya faÉ—a yana rungume da Fatima a jikinsa.

Khadijah ta É—auki jakarsa ta kai masa É—aki, sannan ta dawo parlon

Har zuwa lokacin yana zaune da Fatima a cinyarsa, yana ba Mama labarin tafiyarsa da yadda hanya ta kasance.

A dai-dai lokacin wata mata ta fito daga É—aya daga cikin É—akunan tare da yara biyu, mace da namiji.

Fuskarta a haÉ—e take tamkar ba ta son ganin kowa.

Da ƙaramar yarinyar ta hango shi, da sauri ta yi yunƙurin zuwa wajensa.

Sai matar ta watsa mata wani kallo mai kaifi tare da zare mata idanu.

Nan take yarinyar ta tsaya cak, ta fasa ƙarasa wa gare shi.

Matar ta kama hannunta, sannan ta ja hannun yaron da ke gefenta.

Yaron kuwa har hawaye suka fara cika idanunsa, domin yana son zuwa wajen mahaifinsa. Sai dai yana tsoron mahaifiyarsa.

Ba tare da ta ce komai ba, ta juya da su suka fita daga parlon.

Shiru ya É—an ratsa wajen. Tsohuwar matar ta sauke ajiyar zuciya.

"Wannan wani irin hali ne haka?" Ta faÉ—a cikin takaici

"Karfi da yaji ta rabaka da yaran nan, toh me amfanin zamanta a gidan nan?"

Khadijah kuwa kanta a ƙasa yake, ko magana ba tayi ba. Domin ta san ita ce silar matsalar da ke tsakaninsu

Mutumin ya É—an yi murmushi mai ciwo.

"Sai ta ci gaba da nisanta su da ni." Ya faÉ—a a hankali

"Akwai ranar da za ta yi nadamar yin hakan." Ya É—an yi shiru kafin ya ci gaba

"Amma ni ba zan taɓa buɗe baki na na mata magana ba."

Ya jingina da kujera "Kamar yadda take so, zan bar komai ya tafi a hankali."

Khadijah ta miƙe a hankali, kanta a kasa zata wuce

Ya É—an matso gaba yana cewa,

"Please ki shiga da ita, bari na watsa ruwa."

Ta ƙaraso kusa da babyn zata sauke ta, Babyn ta makyalkale shi da shagwaɓa

"Abbah... bana son zuwa wajen Mami." Dariya ya yi a hankali, yana girgiza kai

Mami ta yi murmushi ta ce,

"Sai ki yi ta zama mana ina ruwa na, karfi da yaji Abbahn ki yasa baki girma”

Sai tsohuwar matar ta ce cikin salon umarni mai É—an zolaya

"Ke dai je ki kwanta mana Khadijah, tun safe kike aiki fah, yanzu ki huta, ki bar shi da mai sunansa kawai tunda ita bata son kowa sai shi."

Khadijah ta É—an yi murmushi cike da kunya, ta gyada kai.

"Toh." Daga haka ta juya ta nufi ciki a har sannan kuma kanta a kasa yake

Shi kuma ya sauke numfashi, ya ce,

"Bismillah." Nan take ya miƙe tsaye, ya ɗauke da Fatima har sannan

Ya goya ta a bayansa tana manne masa kamar ba za ta bar shi ba, yana lallashinta da muryar da ya saba kwantar mata da hankali

A haka ya kaita har wajen Granny, sannan ya sauke ta a hankali

Asalin Labarin…….

Alhaji Muhammad Nasir attajiri ne na gaske, mutum mai tarin arziki wanda ya yi suna a duniyar kasuwanci. Sunansa ba a Najeriya kaɗai aka sani ba, har ma a faɗin nahiyar Africa ya yi kaurin suna saboda basira da ƙwazon da Allah Ya hore masa.

Asalinsa É—an jihar Bauchi ne, amma shekaru da dama da suka gabata ya dawo da zama garin Kaduna, inda ya gina rayuwarsa da kasuwancinsa.

Ya rasa mahaifinsa tun yana ƙarami, kuma mahaifiyarsa ce ta tsaya tsayin daka wajen rainonsa da karatunsa. Da addu'arta da jajircewarta, Allah Ya sanya masa albarka har ya zama ɗaya daga cikin manyan attajiran ƙasar.

Alhaji Muhammad yana da mata biyu.

Matarsa ta farko ita ce Hafsat.

Allah Ya albarkace su da yara biyu, namiji da mace; Umar da Fatima, wacce aka fi sani da Batoul. Sunan mahaifiyarsa ce

Sai dai Hafsat tana da wata irin É—abi'a ta raina mutane. Ko kai waye, ba ta cika É—aukar kowa da muhimmanci ba. Har mahaifiyar sa ba ta tsira daga halinta ba, ga uban gadara

Wannan ne ya sa Alhaji Muhammad ya ƙara aure.

Ya auri Khadija, kyakkyawar Bafulatana daga jihar Adamawa. Ita ma Khadija ta taso cikin gata da daula, don haka ba ta da ɗabi’ar raina mutane ko wulakanta mutum, ahasalima mutunce mai son kowa da kuma kyauta

Tun bayan shigowarta gidan ne zaman lafiya ya fara yin ƙasa.

Da farko Hafsat ta yi fushi matuƙa har ta bar gidan. Sai dai daga baya ta dawo da kanta, amma ta ɗauki wani mataki da ya daɗe yana ci wa Alhaji Muhammad tuwo a ƙwarya, ta hana yaranta kusantar mahaifinsu.

Ko Umar, wanda a baya kusan kullum yana tare da mahaifinsa, sai da ta raba su.

Hakan ya yi wa Alhaji Muhammad ciwo sosai a zuciya. Sai dai daga baya Allah Ya azurta shi da kyakkyawar diya daga Khadija.

Ranar da aka haife ta, tamkar an sauke wani sabon farin ciki ne a rayuwarsa.

Saboda tsananin son da yake yi wa mahaifiyarsa, sai ya sake sanya wa yarinyar sunanta, wato Fatima Zahra.

Tun daga ranar, Zahra ta zama abar so ta musamman a wajensa. Ita ma Zahra ba ta son kowa kamar mahaifinta.

Tun tana ƙarama ya saba da ɗaukar lokacinsa gaba ɗaya yana tare da ita.

Shi ke yi mata wanka, shi ke kai ta makaranta, shi ke É—aukota, shi ke kwantar da ita barci

A wurin Zahra, Abbah ba mahaifi kaÉ—ai ba ne, aboki ne, masoyi ne, kuma duniya ce a gare ta

Lokacin da Umar ya fara girma, ya fara fahimtar cewa abin da mahaifiyarsu ke ƙoƙarin dasa musu game da mahaifinsu ba daidai ba ne. A hankali ya fara janye jikinsa daga gare ta, ya koma kusantar mahaifinsa.

Tun daga lokacin, kusan kullum shi da Zahra za a same su a É—akin Abbah

Wannan ya sa wata irin shakuwa ta musamman ta shiga tsakaninsu,. Shakuwa mai ƙarfi da ta zarce ta 'yan uwa kawai, kamar wasu ‘yan biyu

Duk abin da Zahra take so, to Ya Umar ma zai so shi. Abin da ya bata mata rai, shi ma zai bata masa rai.

Sannan akwai mutum guda da bai taɓa iya ƙin wani abu da Zahra take so ba... wato Abbah….

A haka rayuwa ta ci gaba a gidan Abbah har Zahra ta girma. A lokacin tana ajin SS2, kuma ta taso cikin tsananin so, kulawa da gata.

Tun tana ƙarama, dukiya ba komai bane a wajen ta. Saboda ta taso tana samun duk abin da take buƙata, kuɗi a wajenta tamkar wani abu ne na yau da kullum.

Zahra ba ta da É—abi'ar raina talakawa ko kyamar marasa hali. Akasin haka ma, tana da zuciya mai tausayi da son taimakon mutane, sai dai tana da wani irin Izzah Wanda a koda Yaushe Mami ke mata magana akai

Sai dai Mummy ta gwada mata cewa ai mahaifinta attajirine dan haka idan bata izzah za’a rainata kuma ba zata sabo karbuwa ba a wajen mutane

Tun tana yarinya take son tsafta, wanka da kwalliya. Wannan ɗabi'ar tata ce ta sa kusan duk kuɗin aljihu da Ya Umar da Abbah suke ba ta suna ƙarewa ne a kan turaruka, kayan kwalliya da sauran abubuwan da take so.

Tun tana da shekara goma sha biyar ta fara amfani da social media. Saboda kyawunta, salon rayuwarta da kuma yadda take son fita solo dates lokaci zuwa lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara samun mabiya da yawa har ta zama sananniya a shafukan sada zumunta. hakan ne yasanya zahra bata kaunar rai ni ko kadan

A wannan lokacin ne kuma ta haÉ—u da Asiya, Firdausi da Saudat.

Dukkansu sun samu gurbin karatu ne ta hanyar scholarship.

A farkon haÉ—uwarsu, Saudat ta fi shan wahala a cikinsu. Yadda take shiga makaranta da kuma irin tufafin da take sakawa ya sa mutane da dama suna guje mata ko kuma su raina ta.

Kasancewar yawancin ɗaliban makarantar 'ya'yan masu kuɗi ne, hakan ya ƙara sa Saudat ta ji ba ta cikin su

Suhaima ce kadai a cikinsu iyayenta suke da kudi Wanda tun farko itama a makarantar suke tare da zahra

Zahra kuwa a hankali ta ja Saudat a jikinta saboda tana bata tausayi

Ba Saudat kaɗai ba, hatta Asiya da Firdausi, Zahra ta kasance tana taimaka musu a duk lokacin da suka buƙaci taimako.

Wani lokaci kuɗi take ba su, wani lokacin kuma tana saya musu abubuwan da suke buƙata ba tare da ta jira sun roƙe ta ba.

Saboda haka, a hankali dangantakarsu ta ƙara ƙarfi

Har ya kai ga ba sa kallon Zahra a matsayin kawa kawai.

A wajensu, Zahra Yaya ce, abokiya kuma 'yar uwa wacce a kodayaushe take tsayawa a bayansu…..

Kana kallonta ka san a matuƙar gajiye take

Tana zaune a kujerar baya a motar, hankalinta gaba É—aya ya tafi wani wuri. Idanunta na kan titin da suke bi, tana kallon komai ta cikin window ba tare da ta lura da abin da ke kewaye da ita ba

Envelope ɗin result ɗinta kuwa tana riƙe da shi tamkar wani abu mai daraja.

Ba ta ma lura da lokacin da aka buÉ—e gate É—in gidansu aka shiga da motar ba.

Sai da motar ta tsaya sannan ta É—ago kai

Kallon harabar gidan ta yi na ƴan daƙiƙu, sannan wani faffadan murmushi ya mamaye kyakkyawar fuskarta

Tun kafin driver ya gama buɗe mata ƙofa, ta buɗe da kanta ta fito. Da gudu kuwa ta nufi cikin gidan

Tana shiga parlon, ko kallon wanda su ke ciki ba ta yi ba.

Kai tsaye ta nufi inda Abbah yake zaune.

"Abbahhh!" Ta kira cikin farin ciki kafin ta faÉ—a jikinsa.

Dariya ya yi yana rungume ta.

"Da alama Baby na yau ma ta sake cin first position."

Dariya ta yi tana gyara zamanta a jikinsa.

"Sure, my Abbah."

Mummy ta ja tsaki. Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe ta fita daga parlon

Ya Umar da ke zaune kusa da Abbah ya haÉ—e gira.

"Shine ba za ki kula da ni ba kenan?"

Ta juya tana kallonsa.

"Ka tsaya mana, bari na gama da Abbah na farko”

Daga haka ta miƙa masa envelope ɗin.

Abbah ya karɓa ya buɗe yana dubawa.

Da ganin sakamakon, murmushi ya bayyana a fuskarsa.

"Excellent." Ya furta yana kallonta da alfahari.

Nan take Zahra ta miƙe tsaye.

Ta dafa kugunta tana kallon Ya Umar.

"Yaya..."

"Na'am."

"Me za ka ba ni a matsayin gift?"

Dariya ya yi "FaÉ—i komai."

Ta ɗan ɗora yatsa a haɓa tana tunani.

Sai kuma ta ce,

"System nake so."

Ko ƙyaftawa bai yi ba

"Consider it done. In sha Allah kafin gobe zan saya miki."

Wani irin farin ciki ya bayyana a fuskarta.

Mami ta yi dariya.

"Eh lalle, Ya Umar. Kai dai ka ci gaba da bata ta”

Abbah ya jefa mata wani kallo.

Nan take ta yi shiru tana murmushi.

Zahra kuwa ta karɓi result ɗinta daga hannun Abbah ta kai wa Ya Umar.

Batoul ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai, ba tare da ta ce komai ba ta wuce ɗakinsu da sauri, tana shiga ta tarar da Mummy zaune

"Mummy! Kina ji Yaya kuwa?” Ta faɗa cikin fushi.

Mummy ta É—ago tana kallonta

"Me kuma ya faru?"

"Yaya wai zai saya wa Zahra system gobe."

Wani irin tsaki Mummy ta ja.

"Sai mu gani dan ubansa idan ya isa” Ta faɗa tana haɗe fuska

"Idan ni na haife shi, sai ya saya mata mu gani”

Batoul ta zauna bakin gado

"Mummy ko ni fah bai taɓa saya min ba. Sai Zahra da ko secondary ba ta gama ba”

Mummy ta kalleta.

"Ki yi shiru."Ta faÉ—a cikin takaici.

"Idan Zahra ce, bai isa ya ce zai saya mata ba."

Batoul ta haÉ—e fuska tana jin haushin yadda a duk lokacin da Zahra ta nemi wani abu, kamar umarni ne ga Abbah da Ya Umar

Can da yamma.

Ya Umar ya shirya fita ne domin ya cika alƙawarin da ya yi wa Zahra na siyo mata system

Yana saukowa daga É—akinsa ne sai ya tuna da wani abu,

Mummy ta ce idan zai fita cikin gari akwai abun da zai siya mata, don haka ya juya ya nufi ɓangarenta

Yana isa bakin ƙofar ɗakin ya yi knocking kaɗan sannan ya shiga.

Mummy na zaune kan gado tana duba wayarta.

Tana ganinsa sai ta haÉ—e fuska.

"Mummy” Ya kirata a hankali

Ta amsa da wani irin kallo kawai.

Ya ƙarasa ciki.

"Mummy, kin ce min idan zan fita zan siyo miki wani abu ko?"

Bai ma gama maganar ba.

Sai ta miƙe tsaye tamkar wadda take jira ya yi magana.

"Toh ashe ka tuna da ni kenan?" Ta fara cikin ɓacin rai.

Ya Umar ya tsaya yana kallonta.

Ta ci gaba da magana

"Ba Zahra kaÉ—ai ka sani ba? Kullum Zahra, Zahra, Zahra!"

"Idan ta yi atishawa kai ne farkon wanda zai damu. Idan ta nemi abu, kai ne farkon wanda zai miƙe. Ni da na haife ka kuwa kamar ba ka gani na ita kadai kake gani balle a ce Batoul kuma”

Ya Umar ya sauke numfashi ya ce

"Mummy..."

Ta É—aga masa hannu.

"Karka min magana." Ta katse shi.

"Yanzu saboda ta ci wani banzan position ne za ka kashe mata kuɗi ka siya mata system. Ni ka taɓa siya min wani abu da irin wannan kuɗin?"

Shiru ya yi yana mamakin ko Kai zaiwa Mummy bata gani idan har zai kashewa zahra, sai tace baya mata komai, kamar ba shi bane last week ya tsiya mata wani jewelry gold

Ta cigaba da masifar.

"Ka ɗauki yarinyar nan ka ɗora ta a kai. Komai nata daban. Komai nata musamman. Ko Batoul da ta fito cikina ba ta taɓa samun rabin abin da Zahra take samu a hannunka ba."

Ya Umar ya sauke kansa.

A hankali ya ce,

"Mummy, ki yi haƙuri idan na ɓata miki rai."

Amma kamar ma ya tunzurata nr

Ta ci gaba da magana tana kai-komo cikin É—akin da karfi, da ganin ba za ta saurare shi ba, sai ya sake cewa,

"Wallahi Mummy ba haka bane..."

Ta juya a fusace. "Ban ce ka fita ba?"

Shiru ya yi yana mamakin Yaushe tace ya fita

Sai ta nuna masa ƙofa.

"Ka fita ka bar min É—aki."

Ya Umar ya kalleta na É—an lokaci

Daga ƙarshe ya girgiza kai kawai.

"Toh Mummy, Allah ya huci zuciyarki."

Bai jira amsa ba.

Ya juya ya nufi ƙofar.

Yana fita...

Bang!

Ta buga ƙofar da ƙarfi a bayansa.

Ya Umar ya tsaya na ɗan daƙiƙu a wajen.

Sai ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi.

Daga nan ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya sake waiwayowa ba

#FARASHIN IZZAH

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.