Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 6 of 59

Chapter 5

Bayan sun gama lectures É—insu na farko, Firdausi ce ta zo kansu da sallama a bakinta.

Zahra ta mata murmushi ta ce,

"Late comer"

Dariya tayi ta ce,

"Ba zaku fahimta ba ne. Kun san sai na gama aikin gida dukka, tunda yanzu dai Mama ba lafiya ba. A hakan ma Abdul ne yayi wanke-wanke"

Asiya ta ce,

"Wai har yanzu ne jikin nata?"

Ta ce,

"Da sauƙi fah, kawai dai saura ta gama warwarewa ne"

Zahra ta ce,

"Allah ya ƙara mata lafiya"

Ta ce "Ameen"

Firdausi ta kalli Asiya, ta É—an kalli wasu colleagues É—insu da suke gefenta, sai kuma ta kalli Zahra ta ce

"Zahra, HOD yana kiranki. Kamar akwai issues da project topic É—inki fah"

Zahra ta ce,

"Ban gane ba. Tunda ba su gane da issues ba sai yanzu da aka yi nisa da practical?"

Firdausi ta ce,

"Shi ne ai. Nima nawa wai bai gama yarda da practical ba. Yanzu dai ki tashi muje muji menene, dan yace yana neman mu"

Asiya ta ce,

"Hmm Allah ya kyauta. Amma ai hakan ba daidai bane, tun farko sai ya faÉ—a muku ai"

Zahra ta miƙe a zuciye tana kallon Firdausi kamar itace ta kawo matsalar ta ce

"Sai ki wuce muje ai. Shi ma dan muguntarsa ne yasa zai kashe min aiki."

Daga haka tayi gaba, Firdausi na binta a baya.

Sai da suka je corridor É—in offices É—in lecturers É—insu, Firdausi ta dakatar da Zahra ta ce,

"Mu zauna akan wannan kujerar"

Zama suka yi

Zahra tana kallonta ta ce,

"Toh me kuma amfanin zaman?"

Firdausi ta ce,

"Magana nake so muyi… amma kin san halin Asiya da baki. Not that tana da baƙin hali, amma zata faɗa wa Suhaima, kuma kin san Suhaima zata iya faɗa wa Saudat. Kuma kin san halin da Saudat ta tsiro, kaf department sai sun ji. Gashi ke makiya da yawa kike da su"

Zahra ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta ta ce

"Menene toh Firdausi?"

Firdausi ta ce

"Game da ke ne. Ina son sani, ya kuka yi jiya? Kin san wallahi bana jin daÉ—in yadda kika rame har haka"

Zahra na kallon Firdausi ta ce,

"At long last dai Firdausi na raka shi. Mun je, and everything went smoothly… kuma kamar dai ba shi ba, har da lallaɓa ta"

Firdausi ta ce

"Zan so da ace har zuciya ne Zahra, amma kin san menene? Gani nake yi hakan yayi ne saboda ya san kina da rauni. Kuma ya san dole zaki je saboda yadda ya san alakarki da media. Zai ce ko dan ki samu na posting zaki bi sa"

Zahra ta tsaya kallonta, ta ce

"Amma kin san har da safen nan Khalil kamar ba shi ba? Dan da gaske kamar ya canza"

Firdausi tayi dariya ta ce,

"Shikenan Zahra. Dama nima fata na hakan ta zama da gaske har ransa. Amma kar ki yi saurin yarda da shi, ki tsaya ki ga gudun ruwansa na kwana biyu"

Zahra ta ce,

"Alright, thank you Firdausi… amma dai ga dukkan alamu ya canza"

Shiru tayi tana kallon Zahra saboda tausayi take bata. Bata fahimtar mai kwanarta saboda Allah, sannan bata fatan abin dake zuciyarta game da Khalil haka ne.

Sauke ajiyar zuciya tayi ta ce,

"Zahra tashi mu koma lecture hall"

Miƙewa Zahra tayi suka fara tafiya a hankali, kowa da tunanin da take yi.

Suna komawa cikin hall, zaman su ke da wuya sai ga Saudat a kansu ta ƙaraso tana murmushi.

Kamar haÉ—in baki, har Suhaima data shigo yanzu babu wanda ya kulata.

Zahra kam ma hawa IG tayi tana kallon yadda bloggers suke tagging É—inta.

Can Saudat ta miƙe ta bar wajen.

Suhaima ta bita da kallon harara ta ce,

"Munafuka kawai"

Zahra ta ce,

"Amma me yasa kuke haka ne?"

Asiya ta ce,

"Ai tazo ta kwashe kayanta a gidan da muke wai zata dawo hostel. Ita bata son zaman off campus. Amma kin san yadda tayi playing É—inmu, wani gida aka kama mata ita kaÉ—ai"

Asiya ta ci gaba da cewa,

"Ni fa problem dina da ita yadda ta canza ne. Musamman ga Zahra. Kullum bata da abin yi sai maganarta. Ko ta manta sanda aka kawo ta level 1 ne? Idan da ba Zahran ta wanke ta ba, akwai wanda zai kalleta ne?"

Zahra ta ce,

"Enough please. Tun yanzu zaku fara sa ma kanku ciwon kai? Ai maganar tayi yawa"

Firdausi tayi dariya ta ce,

"Dake ai mu kece da har magana zata sa mana ciwon kai"

Duk suka yi dariya.

Bayan ta koma gida, duk sammaminta zata ga Khalil, tunda shi 2pm yake tashi ita kuma yau tayi evening lectures ne. Amma shiga compound data yi taga babu mota ne, abin ya bata mamaki.

Bayan ta sauka ta juya tana kallon mai gadi ta ce

"Sannu Baba"

Ya ce,

"Yauwa, sannu Hajiya. Ai É—azu ma kinyi baki nace kina makaranta"

Ta ce,

"Baki kuma? Ko sun faÉ—a maka su waye ne?"

Ya ce,

"A’a gaskiya basu faɗa min ba, amma sun ce zaku yi waya."

Ta ce,

"Tohm shikenan. Dan Allah Baba, mai gidan ya zo kuwa?"

Ya ce,

"A’a, tun da ya fita da safe bai dawo ba tukunna"

Tayi shiru, sai kuma ta ce,

"Na gode"

Daga haka ta nufi cikin gidan.

Sama ta wuce. Bayan ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da yin alwala. Ta zo tayi sallar La’asar sannan ta wuce kitchen.

Girki ta É—aura.

Bayan ta gama ta sake share gidan duk da babu wani datti. Ta baÉ—e gidan da turare sannan ta wuce sama.

Tana shiga WhatsApp É—inta sau taga Firdausi na online. Kawai ta danna mata kira.

Yana shiga ta É—aga. Bayan sun gaisa sai kuma tayi shiru.

A hankali ta ce,

"Firdausi baya gida, kuma nasan maybe sai ya kai yadda ya saba kaiwa. Bana son na fara kai magana gida ne amma abin ya fara yawa, musamman yadda kinsan a gidanmu ba kowa yaso auren ba"

Firdausi ta ce

"Ki kwantar da hankalinki. Maybe ana Magrib zai zo, tunda kema kinga changes É—insa. Kawai ki daina daga hankalinki balle kiyi ta ramewa"

Ta ce,

"Thank you Firdausi"

Daga haka ta kashe kiran.

Sai kuma ga wani kiran Firdausi ya kuma shiga. Ta É—aga.

Firdausi ta ce,

"Kina jina?"

Ta ce,

"Eh"

Ta ce,

"I think gobe ki shirya ki tafi gidan su. Kije ki gaishe da mahaifiyarsa, idan da hali ma ki mata girki"

Ta ce,

"Toh thank you. School É—in fah?"

Ta ce,

"Ai gobe lecture É—aya gare mu, kuma 2 to 4 ne. Sai ki tafi da wuri idan yaso daga can sai kizo lecture É—in."

Ta ce,

"Tohm shikenan, hakan ma zan yi"

Tana kashe waya ta fara jin kiran sallah.

Ta miƙe ta wuce toilet tayi alwala, ta zo tayi Magrib.

Wasa gaske har kusan 11pm babu Khalil balle labarinsa.

Kamar ta kirasa amma ta daure zuciyarta. Tayi alƙawarin ba zata kira ba.

Ta gama duk wani activities É—inta na dare ta kwanta.

Yau bata jin zama ta jira dawowarsa.

Har ta kwanta ta tuna ƙofar a buɗe take. Ta miƙe taje ta saka key sannan ta koma ta kwanta.

A haka bacci ya É—auke ta.

Wajen sha É—aya da rabi sai gashi ya zo gidan.

Mai gadi ya buÉ—e masa gate. Ya shiga yayi parking.

Ya kura ac motar ya jingina da seat É—in sannan ya kirata.

Ya ce,

"Na ƙarasa gida"

Ta ce "Hope kai kaÉ—ai ne?"

Ya ce "Ai ni ba yaro bane"

Ta ce,

"Good. Bayani nake so kamin akan hoton da yake trending jiya a media."

Yayi shiru yana saurarenta.

Ta ce,

"I’m talking to you, kamin shiru"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

"Ban san me zan ce ba. Bana son kuma na fara miki karya. Tunda kinga hotuna na da Zahra ne ai shikenan. Bana son wani ciwon kai yanzu"

Ta ce,

"Hmmm shikenan, na kyale ka"

Ya ce,

"Better please"

Daga haka ya kashe motar tasa ya daura kansa a steering. Sai kuma ya buÉ—e motar ya sauka.

A hankali yake tafiya irin nasa na kasaita.

Bayan ya haura sama ya wuce É—akinsa yayi wanka ya saka kayan bacci sannan ya fito ya nufi É—akin Zahra.

Ya kai hannu ya murɗa ƙofar yaji a kulle.

Abin ya bashi mamaki sosai, dan yasan Zahra bata kulle É—aki.

Sake kai hannu yayi ya murɗa da ƙarfi, yaji a kulle.

Juya-juya ya fara yana kalle-kalle.

Kansa ya kulle.

Bata zo gida bane ko kuma ta kulle É—akin ne kawai?

Ai bai san sanda ya sauka ya tafi can ƙasa ba. Ya buɗe ƙofar parlour ya wuce compound.

Ganin motarta yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya koma É—akinsa.

Bayan ya kwanta abin yayi ta bashi mamaki yadda ta kulle É—akin, a haka bacci ta É—auke sa.

Washe gari…

Bayan ta tashi, wani yunwa ce ta addabeta.

Tana idar da sallah ta wuce kitchen.

A kitchen É—in ma take Azkar meanwhile tana girkinta.

Tana ji ya shigo amma ta daure zuciyarta.

Ta juya tana kallonsa bayan ya leƙo kitchen ɗin.

Kamar babu komai haka ta ce masa,

"Ina kwana, fatan ka tashi lafiya"

Ya ce "Lafiya Zahra"

Kamar tayi shiru sai kuma taji ba zata iya ba.

Ta ce,

"Jiya baka zo gida da wuri ba. Wai nikam me kake tsayawa ne yi a wajen Noory? Ni fah yanzu banda wani lokacin ganin ka sai da safe. Mun koma kamar wasu strangers."

Ya ce,

"Dan Allah kimin shiru. Yau ne na saba kaiwa wannan lokacin? Ko kuma yanzu da asuban fari kike son tono faɗa? Baki da ikon tambayata daga ina nake, amma ni ina da ikon tambayarki. Kaiii… fita ma idan naga dama sai na hana ki, shikenan. Amma ke baki da wannan right na tambayata, Okay?"

Wani shiru tayi ganin completely ya sake komawa wannan Ibrahim É—in nasa.

Hawaye ya cika idonta.

Ta sauke indomie É—inta ta zuba ta fara ci.

Bayan ta gama ta wuce parlour ta kwanta.

Nan da nan bacci ya kwashe ta.

Can kuma ta farka.

Ta kalli agogo kawai ta miƙe ta wuce sama.

Tana zuwa zata wuce, a wall mirror dake manne a corridor akan drawer, wayan Ibrahim ne ke ringing amma volume É—in an rage sosai.

Ta ƙarasa wajen wayar a hankali ta ɗauka.

Ta jima tana kallon saving É—in da aka yi ma wanda yake kira har ya yanke.

A take kuma aka sake kira.

Ta É—aga kiran ta kai kunne ba tare data yi magana ba.

Wacce ke ɗayan ɓangaren shagwaɓa ta fara yi:

"Haba sweetheart, me nayi maka ne kwana biyu ka guje ni? Shekarar jiya fah haka kaki zuwa, jiya ma haka. Baka sanin yadda rashinka yake saka min ciwo ba"

Zahra kam mutuwar tsaye tayi a wajen, ta kasa motsi.

Ita kuwa a ɗayan ɓangaren, jin shiru yasa ta ce,

"Wai nikam ina kake zuwa ne ma kwana biyun nan? Ko dai wata ka fara bi sweetie ban sani ba?"

Idon Zahra ya cika da ƙwalla.

Bata san ya aka yi ba, bata san yaushe ya fito ba, bata san ya aka yi yazo gabanta ba.

Kawai ji tayi mutum ya sa hannu ya karɓe wayar daga kunnenta.

Ya kashe kiran sannan ya kai fuskarsa daf da tata yana kallonta.

Ita kam dishe-dishe ma take kallonsa.

Ya ce,

"Wannan shine result É—in É—aukan wayan mijin"

Daga haka ya juya ya bar wajen.

Ta duƙa nan ƙasa. Ai baccin ma data ke ji ta nema ta rasa

Ta fashe da kuka. Can kuma ta koma cikin É—akinta.

Bata san how long ta kai ba tana wannan kukan.

Kawai ɗaga kai tayi ta kalli agogo har ƙarfe 9 yayi.

Ta miƙe ta wuce toilet tayi alwala. Ta zo ta shimfiɗa sallaya tayi raka’a huɗu sannan ta sallame.

Ji tayi ba zata iya kai abinci gidan nasu ba ma.

A yadda take ji zata iya kona gidan da kanta a ciki.

Ambaton Allah kawai take yi.

Wayarta ce ta fara ringing.

Kamar baza ta kula ba, sai kuma ta miƙe ta tafi ta ɗauka.

Ganin Firdausi ce yasa tayi picking call É—in.

Bayan sun gama gaisawa, Firdausi ta ce,

"Dama na kira naji ko zaki kai abincin?"

"Hmmm…" kawai Zahra ta iya faɗi.

Firdausi kuma sai yanzu data ce "hmm" ne ta fahimci kamar Zahra ma kuka take yi.

Ta ce,

"Zahra ban gane ba… kuka kike yi ne?"

Zahra ta ce,

"A’a Firdausi… kawai dai na fasa kai abincin ne."

Firdausi ta ce,

"Noo, ki tashi ki kai. Dan hakan shine mutuncinki, kuma ta nan ne zaki fara sayen zuciyar mahaifiyarsa"

Zahra ta ce,

"Ba zaki gane bane…"

Firdausi ta ce,

"Tunda aka yi auren nan Zahra, bayan sanda kuka je tare baki kuma zuwa ba. At least ki fara nuna mata cewa itama uwa ce. Wallahi zata ji daɗi, kuma matsalarki zata zo da sauƙi."

Zahra ta ce,

*Tohm… bari na daura."

Ta bawa Firdausi amsar ne ba wai dan zata yi É—in bane, sai dai dan Firdausi ta kyale ta.

Dan bata buƙatar magana a halin yanzu.

#Farashin izzah

#jiddatulkhayr writes

#08110615256

https://chat.whatsapp.com/IjVCBxrVY1Z4pH5IZhshvA?mode=gi_t

*FARASHIN IZZAH*

Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.