Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 55 of 59
Chapter 53
Da yamma ta yi liss, kowacce ta kama abin da take yi.
Firdausi da Aasiya suna kitchen suna wanke kwanukan abincin da suka ci, Suhaima da Saudat kuma suna gyara ɗakinsu, yayin da Zahra ta fito ta zauna ita kaɗai a ƙaramin balcony ɗin apartment dinsu.
Iska mai sanyi na kaɗa veil.
Wayarta na hannunta, amma ba chatting take ba.
Kallon sararin sama kawai take yi.
A can wani ɓangaren gari…
A cikin wani katafaren office mai cike da kayan alatu, wata mata ta zauna cikin kujerar fata, tana jujjuya wani glass a hannunta.
Fuskarta ba ta nuna komai.
Sai wayarta ta ɗauki ƙara. Ta ɗaga.
“Na’am.”
Muryar wani namiji ta fito daga ɗaya ɓangaren.
“Mun tabbatar yarinyar ta koma School Villa.”
Ta lumshe ido.
“Good.”
“Yanzu me kike so mu yi?”
Ta ɗan yi shiru kafin ta ce cikin sanyin murya,
“Ku ci gaba da sa ido kawai.”
“Ba za mu ɗauki wani mataki ba?”
Ta yi wani ɗan murmushi mai cike da ma’ana.
“Ba yanzu ba…”
Ta miƙe tsaye tana kallon waje ta cikin glass window.
“Lokacin da ya dace… ita da kanta ba za ta fahimci yadda komai ya fara ba.”
Tana kai wa nan ta kashe wayar
Washegari da safe.
Da ƙarfe bakwai da rabi, Zahra da ƙawayenta suka fito daga School Villa, kowacce ɗauke da jakarta, suna ƙoƙarin samun Napep kafin lecture na ƙarfe takwas.
Abin mamaki, yau ma babu ko guda.
Firdausi ta yi ajiyar zuciya
“Da alama yau ma trekking za mu yi.”
Zahra ta haɗe fuska
“Wallahi ban shirya ba.”
Kafin su fara tafiya, hayaniya suka fara ji tana tashi daga bakin babbar hanyar shiga campus.
Mutane suka fara taruwa, wasu ɗalibai suna gudu zuwa wajen.
“Me ya faru?”
“Wani accident ne wai!”
“Napep ce ta bugi wani student!”
Nan take Zahra da ƙawayenta suka kalli juna, suka nufi wajen tare da sauran mutane.
Da suka isa, taron ya yi yawa, ga wata Napep ta kife a gefe
Wani ɗalibi yana kwance a ƙasa cikin ciwo, mutane da yawa kuwa sun tsaya suna kallo kawai, babu wanda ya san abin da zai yi.
A dai-dai lokacin ne aka ji ƙarar wata baƙar mota mai tsada tana tsayawa a gefen hanya
Door ɗinta aka buɗe
Wani dogon saurayi cikin farar shirt mai sauƙi da baƙar wando ya fito da sauri.
Ba tare da ya kula da hayaniyar mutane ba, ya kutsa cikin taron.
Ya durƙusa kusa da wanda ya ji rauni, ya fara duba yanayinsa cikin nutsuwa.
“Someone call the emergency unit. Hurry!”
Muryarsa cike take da kwarin gwiwa.
Cikin daƙiƙu kaɗan, ya haɗa wasu ɗalibai suka ɗaga wanda ya ji raunin cikin tsari, suka saka shi a motarsa domin a garzaya da shi asibiti.
Kafin ya shiga motar, idanunsa suka ɗan zagaya taron kamar akwai abun da yake nema
Na ɗan lokaci kaɗan…
Idanunsa da na Zahra suka haɗuwa, kallonta yake yi while ita accidentally nema ta kalle sa ta ɗauke kai ba tare data san tama kalle sa ba
Amma kafin komai ya faru ko wani yayi noticing, ya shiga motar
Sake haɗa ido suka yi, wannan karan tayi noticing saboda yadda aka sauke glass din motar kasa, sai kuma lokaci guda aka ɗaga sama haba ɗaya kuma tinted ne
Motar ta ja da sauri ta bar wajen
Zahra ta tsaya tana kallon hanyar da motar ta bi.
Ba ta san ko waye ba
Ba ta ma san sunansa ba
Sai dai saboda wani dalili da ita kanta ba ta fahimta ba…
Taji tana son sanin wanene shi.. kuma kamar bata yarda da shi ba…
Bayan lectures na ranar suka ƙare, Zahra da ƙawayenta suka fito daga lecture hall suna hira.
Firdausi ce ta fara magana.
“Wallahi har yanzu mutumin nan na safe bai fita a raina ba.”
Suhaima ta gyada kai
“Ni ma. Yadda ya taimaka ba tare da ya tsaya jiran a yaba masa ba… abin ya burge ni.”
Aasiya ta ce,
“Da alama ba irin samarin campus ba ne.”
Saudat ta yi murmushi.
“Toh Zahra fa? Ita dai ko magana ba ta yi a kansa ba.”
Dukkansu suka kalli Zahra.
Ita kuwa ta ɗaga kafaɗarta
“Ya yi abin kirki. Allah ya saka masa.”
Firdausi ta yi dariya
“Shi kenan? Kawai?”
“Eh.”
“Ko ba ki son sanin ko waye?”
“No.”
“Why?”
“Saboda bai shafe ni ba.”
Suhaima ta girgiza kai tana murmushi
“Ke dai kin sha bamban.”
Suna cikin hirar ne wayar Zahra ta yi ƙara.
Unknown Number.
Ta ɗan kalli screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta ɗaga.
“Hello?”
Shiru.
Ta sake cewa
“Hello?”
Har yanzu babu amsa.
Sai aka katse kiran.
Ta ɗan haɗe gira
“Waye kuma wannan?”
Firdausi ta ce
“Maybe wrong number.”
“Probably.”
Ba ta ƙara tunanin maganar ba.
Ta saka wayar cikin jakarta, suka ci gaba da tafiya.
A wani ɓangaren garin…
Matashin nan yana tsaye a bakin tagar ofishinsa.
Wani mutum ya shigo ya miƙa masa file.
“Sir, ga takardun da kuka nema.”
Ya karɓa ba tare da ya ɗaga kai ba.
Mutumin ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce,
“By the way… an ce yau kun sake ceton rayuwar wani student.”
Ya ɗan yi murmushin gefen baki.
“Anyone would have done the same.”
Mutumin ya girgiza kai.
“No, sir… not everyone.”
Ya sake mayar da hankalinsa kan file ɗin.
“Anything else?”
“A’a, sir.”
“Toh za ka iya tafiya.”
Da mutumin ya fita, ya buɗe file ɗin.
A saman shafin farko an rubuta wasu manyan haruffa
F************h
Idanunsa suka tsaya a kan rubutun na wasu daƙiƙu.
Sai ya rufe file ɗin a hankali. Fuskarsa ba ta nuna komai.
Washegari da rana, bayan sun gama lectures na ƙarshe, Zahra da ƙawayenta suka dawo School Villa cikin Napep.
Suna shiga compound, Zahra ta tsaya cak.
“Wait…”
A tsakiyar bakin apartment ɗinsu mota ce mai matuƙar kyau take parke
Firdausi ta zaro ido
“Wayyo… wa ya kawo min wannan?”
Kafin wani ya amsa, aka ji muryar wani saurayi
“Baby!”
Ta juya da sauri
“Ya Umar!”
Da murmushi ta ƙarasa wajensa.
Ya Umar ya miƙa mata mukullin motar yana jujjuya shi a yatsansa.
“Ga abin da aka ce a kawo kafin ƙafafun wani su tsage.”
Firdausi, Aasiya, Saudat da Suhaima suka fashe da dariya.
Zahra ta karɓi mukullin tana dariya
“Thank you!”
Ya Umar ya nuna mata motar
“Abbah ya ce daga yau ba trekking.”
Ta rungumesa cikin shagwaɓa
“Allah ya ƙara maka lafiya.”
Ya yi murmushi
“Ki gode wa Abbah, ni delivery boy ne kawai.”
Ta ɗaga wayarta nan take ta kira Abbah.
Da ya ɗaga ta ce,
“Abbah! Thank you so much!”
Daga can ya yi dariya.
“Ki kula da ita. Kuma ki mai da hankali kan karatunki.”
“In Sha Allah.”
Ta sake gode masa, sannan ta kira Mami, ita ma ta yi mata godiya tare da yi mata addu’a.
Su Firdausi suka karasa suka gaishe sa, ba tare daya kalle su ba ya amsa
Asiya ta ce
“Ya Umar, ka ceci rai ai, idan ba haka ba ai wata zata sha wahala”
Murmushin gefen baki yayi ba tare daya ma kalleta ba
Bayan Ya Umar ya tabbatar da komai lafiya, ya yi musu sallama ya koma.
Firdausi ta ce
“Princess ta samu abin hawanta.”
Suhaima ta yi dariya
“Yanzu ba za mu ƙara jin complain ɗin trekking ba.”
Zahra ta yi murmushi
“Exactly.”
Da dare, bayan sun ci abinci suka ɗan huta, kowacce ta ɗauki littattafanta.
“Mu fita reading area?” Aasiya ta tambaya
“Let’s go.” Zahra ta amsa.
Suka nufi wurin karatu da ke cikin School Villa, inda ɗalibai da dama ke zaune cikin nutsuwa suna karatu.
Kowacce ta mayar da hankalinta kan littattafanta.
Lokaci ya ja sosai kafin suka gama.
Da kusan ƙarfe goma na dare suka dawo side dinsu a gajiye.
Kowacce ta shiga ɗakinsu, ta yi shirin kwanciya.
Zahra na zaune kan gadonsu tana duba wayarta.
Can…
Wayarta ta yi ringing.
Ta kalli screen
Unknown Number.
Ita ce lambar nan da ta kira ta jiya.
Ta haɗe gira
“Again?”
Ta ɗaga kiran a hankali
“Hello?”
Shiru.
Ta sake magana
“Who is this?”
Sai ta ji kamar numfashin wani a ɗaya ɓangaren…
Amma babu kalma ko ɗaya bai ce ba
Kafin ta sake cewa komai…
Call Ended.
Zahra ta ci gaba da kallon screen ɗin wayarta na wasu daƙiƙu
“Waye ne haka?”
Ba ta sake kiran lambar ba, ta kashe screen ɗin wayar, ta ajiye ta a gefen gadon
Sai dai a wannan karon…
Wani irin rashin nutsuwa ya ɗan shiga zuciyarta
Ta girgiza kai
“Idan da gaske yana da magana ai zai yi.”
Ta kashe fitilar bedside lamp ɗin, ta lulluɓe jikinta da duvet.
Cikin ƴan mintuna kaɗan bacci ya ɗauke ta.
Washegari.
Tun da safe, Zahra ta farka cikin farin ciki.
Yau babu maganar trekking.
Bayan sun yi sallah, suka shirya kamar yadda suka saba.
Da suka fito compound, idanun kowa suka koma kan sabuwar motar Zahra
“Wow!”
“Wallahi motar nan ta haɗu.”
“Sabuwar model ce fa.”
Wasu ɗalibai suka tsaya suna kallonta.
Firdausi ta yi murmushi.
“Princess, yau kin zama celebrity na biyu.”
Zahra ta yi dariya
“Ku shigo mana.”
Su biyar suka shiga motar.
Zahra ta ɗaura seat belt, ta kunna motar cikin nutsuwa.
“Everybody ready?”
“Yes!”
A hankali ta fice daga School Villa.
A hanya, Suhaima ta ce
“Wallahi yau na ji daɗin”
Saudat ta yi dariya
“Ni ma. Allah ya saka wa Abbah.”
Firdausi ta ce
“Yau ma za ki ce ƙafafunki za su tsage?”
Dukkansu suka yi dariya.
Zahra ta harare ta
“Very funny.”
Da suka isa campus, Zahra ta faka motar a parking area.
Da suka fito, wasu ɗalibai suka riƙa kallon motar, wasu kuma Zahra.
A yayin da suke tafiya zuwa faculty…
Sai Zahra ta ji wayarta ta yi vibration.
Ta ciro ta.
Unknown Number. Ta tsaya na ɗan lokaci.
Firdausi ta lura
“Ba za ki ɗaga ba?”
Zahra ta latsa answer
“Hello?”
A wannan karon… an yi magana.
Muryar namiji ce, mai nutsuwa
Ba ta da ƙarfi, ba ta da rauni.
“Good morning.”
Zahra ta haɗe gira
“Who is this?”
An yi shiru na daƙiƙa biyu.
Sai ya ce,
“Ki yi haƙuri da kiran da na yi jiya…”
Kafin ya ƙarasa maganar…
Sai wata mota ta danna horn kusa da su.
“Pooon!”
Hayaniyar ta hana Zahra jin abin da ya faɗa
“Hello?”
Ba a sake cewa komai ba, kiran ya katse.
Ta sauke wayar tana kallonta cikin mamaki.
Firdausi ta tambaya
“Wai waye ne?”
Zahra ta girgiza kai.
“Ban sani ba… amma wannan karon ya yi magana.”
“Me ya ce?”
“Ban ji komai sosai ba.”
Ta saka wayar cikin jaka
“Mu je, lecturer zai shigo.”
suka ci gaba da tafiya.
Ba wanda ya lura a cikin su..
A ɗayan gefen parking area, wata baƙar mota tana tsaye.
Wanda ke cikinta ya kalle su na ɗan lokaci.
Da ya ga sun shiga cikin faculty, ya kunna motarsa ya tafi ba tare da kowa ya lura da kasancewarsa ba.
A kwana a tashi… Lokaci ya ci gaba da tafiya…
Kafin ma su ankara, kusan wata ɗaya kenan da zuwansu Campus
A cikin wannan wata ɗaya, rayuwarsu ta sauya gaba ɗaya.
Su biyar sun zama kamar ƴan uwa, lecture tare, karatu tare, cin abinci tare, dariya tare
Har ma idan ɗaya ba ta gida, sai gidan ya yi musu wani iri, musamman idan Zahra ta tafi weekend .
Sai dai akwai abu ɗaya da bai taɓa canzawa ba…
Zahra….
Har yanzu ba ta iya aikin gida ba
Ko wanke plate ɗinta ba ta iya yi yadda ya kamata ba, ballantana kuma wanki
Sau da yawa idan ta cire kayanta ta kai laundry, kafin ta dawo sai ta tarar Saudat ta haɗa da nata ta wanke musu gaba ɗaya
Da farko Zahra ta sha faɗa
“Saudat, na ce ki daina wanke min kaya mana.”
Saudat sai ta yi murmushi.
“Ba komai ai, tare da nawa na haɗa ai”
“Kullum haka kike fa, ni dai wani iri nake ji Saudat”
“Toh me ya sa zan bar naki?”
Har ma a weekends, Zahra kan dage ita za ta kai wajen waki
Amma idan ta shiga bathroom ta fito ko ta fita.. sai ta tarar a riga an gama. Daga ƙarshe ta gaji da magana, ta bar ta kawai.
Yau Lahadi ce
Babu lectures.
Tun safe gidan ya cika da annashuwa
Firdausi na kitchen tana soya ƙwai
Aasiya na haɗa tea.
Suhaima da Saudat na ta hira a falo
Zahra kuwa ta fito daga ɗakinsu tana miƙa
Ta kalli kowacce
“Girls…”
Suka waigo
“Na gaji da zama a gida wallahi.”
Firdausi ta yi dariya
“Toh me kike so?”
“Mu fita mana!”
“Where?”
“Anywhere… just to have fun.”
Aasiya ta tafa hannu
“Finally! Wannan shawarar ta yi.”
Suhaima ta ce,
“Cheers”
Saudat ta yi murmushi
“Ni ma.”
Zahra ta miƙe tsaye
“Okay then. Everybody… one hour. Mu shirya.”
“Deal!”
Nan take kowacce ta nufi ɗakinsu, bayan sunyi breakfast
Cikin ƙasa da awa ɗaya…
Kowacce ta fito cikin shiga mai kyau.
Firdausi na sanye da ash-colored abaya
Aasiya ta saka navy blue maxi gown da black veil, tana ɗauke da ƙaramin handbag.
Suhaima na cikin wine-colored jilbab mai matuƙar kyau.
Saudat kuma, duk da kayan nata ba su da tsada, ta fito cikin blue gown mai tsafta da blue veil, kyau da tsarinta suka ƙara fito da ita.
Daga ƙarshe…
Ƙofar ɗakin da Zahra suke ta buɗe
Ta fito cikin wani elegant mocha-colored flowing dress da premium chiffon veil, sanye da farin da black sneakers masu tsada, luxury wristwatch a hannunta da ƙaramin designer handbag.
Kamshin turarenta ya mamaye falon tun kafin ta ƙaraso.
Firdausi ta zaro ido
“Princess…”
Aasiya ta yi dariya
“Ke kullum sai kin kashe mutane da dressing ne”
Suhaima ta ce
“One thing about you yadda kike Kara ɗaga mana darajarmu a media”
Saudat ta yi murmushi tana kallonta
“Masha Allah.”
Zahra ta juya a hankali tana kallon kanta a mirror.
Ta yi murmushi
“So… are we ready?”
“Yes!”
Ta ɗaga mukullin motarta tana jujjuya shi a yatsa.
“Ladies… let’s go have some fun.”
Da dariya da hayaniya suka fito daga gidan, Zahra ta buɗe motarta, suka shiga ciki, sannan suka fice daga School Villa cike da farin ciki
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.