Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 59 of 59

Chapter 57

Kalaman Saudat suka sa motar ta yi shiru na ɗan lokaci

Waƙar da ke tashi daga speaker har yanzu tana ci gaba da tashi amma babu wanda yake saurara

Zahra ta ɗan ɗaga idanunta zuwa rear-view mirror.

Black Hilux, tinted glass! Ba ta iya ganin waɗanda ke ciki.

Ta sake mayar da hankalinta kan hanya

“Maybe coincidence.”

Saudat ta girgiza kai

“I don’t think so.”

Firdausi ta ɗan juya tana kallon baya ta window.

“Where?”

“Can…” Ta nuna mata.

Firdausi ta leƙa

“Oh…” sai kuma ta yi shiru.

“Hmm…” Suhaima ta ce

“Me kuke gani ne?”

Aasiya ta amsa cikin sanyin murya

“Wata Hilux.”

“Shi me?” Suhaima ta waiwayo ta kalla. “Toh ai mota ce kawai.”

Saudat ta ce

“Ki ci gaba da kallonta.”

Suka isa wani junction, akwai hanyoyi uku.

Ba wannan ce hanyar da suka saba bi ba.

Zahra ta juya zuwa dama

“Baby…” Firdausi ta yi mamaki ta ce

“Wannan ba hanyarmu ba ce.”

“I know.” Kawai Zahra ta faɗa

“Why?”

Zahra ba ta amsa ba sai ta ci gaba da tuƙinta kawai

A cikin mirror kamar yadda suke kallo… Hilux ɗin ma ta juya zuwa dama, daidai bayansu yanzu kam…

Ko Suhaima ta daina magana

“Ya biyo mu…” Ta faɗa cikin murya mai rauni.

Babu wanda ya yi magana.

Zahra ta sake gwadawa… ta shiga wani ƙaramin layi da ma ba hanyarsu bace, ba ta taɓa ma bin layin ba tunda take a kaduna

Layin ya yi tsit.. Gidaje kaɗan ne a unguwar.

Hilux ɗin… har yanzu na biye da su.

Firdausi ta rufe fuska

“Ya Allah…”

Aasiya ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi.

Saudat kuwa ta fara karanta Ayatul Kursiyyu cikin ƙasa-ƙasa.

Suhaima ta ce cikin firgici

“Baby… they’re following us.”

Zahra ta yi ƙoƙarin ta danne tashin hankalin da ke neman bayyana a fuskarta.

“No panic.” Ta faɗa a hankali

“Nobody panic.”

Amma zuciyarta… da sauri take bugawa.

A cikin Hilux… Drivern ya yi murmushi

“She knows.”

Mutumin da ke gefensa ya ce,

“Good.”

“Let’s keep pushing.”

“Don’t get too close.”

“Not yet.”

Driver ya gyada kai

Hilux ɗin ta ci gaba da binsu cikin distance da bai yi yawa ba.

A motar Zahra…

Firdausi ta zaro wayarta “Baby, should I call Ya Umar?”

“Not yet.” Zahra ta ce

“Police?”

“Not yet.”

“Why?” Firdausi ta tambaya

“Because I’m still hoping I’m wrong.” Cewar Zahra kenan

Sai ta sake kallon mirror Hilux ɗin na nan… ba ta rage gudu ba, ba ta wuce su kuma ba

Kawai… ita dai tana binsu ne

Numfashin Zahra ya ɗan yi nauyi, ta riƙe steering wheel da ƙarfi.

A karon farko… ta fara jin tsoro.

Ba don kanta ba… sai don ’yan matan da ke zaune tare da ita.

Ta haɗiye yawu. Sannan ta faɗi cikin murya mai cike da ƙwarin guiwa, duk da cewa zuciyarta ba haka take ji ba.

“Girls…”

“If anything happens…”

“Just do exactly what I tell you.”

Ba wanda ya yi magana! Kowacce ta fahimci abu ɗaya…

Wannan ba coincidence ba ne.

Shiru ya mamaye motar, sai ƙarar engine da bugun zuciyoyinsu da ke ƙaruwa.

Zahra ta ɗan ƙara saurin motar, ba don gudu take son yi ba…

Sai don ta sake gwada tabbacin abin da suke zargi.

Da ta ƙara speed… Hilux ɗin ma ya ƙara.

Firdausi ta lumshe ido

“…Ya biyo mu fahh”

Wannan karon babu wanda ya ƙara cewa coincidence ne, kowa ya gani da idanunsa.

Suna fita a wannan layin Zahra ta ɗauki wani roundabout.

Maimakon ta bi hanyar gida…

Sai ta zagaya roundabout ɗin sau biyu

Ta sake dawowa daidai inda ta fito.

Aasiya ta kalleta da mamaki

“Baby… me kike yi?”

“Testing.” Ta faɗa ba tare da ta ɗauke idanunta daga hanya ba.

Hilux ɗin…

Shi ma ya zagaya roundabout ɗin kamar yarda itama tayi sau biyun kuma daidai bayansu.

Saudat ta riƙe hannun kujera da ƙarfi

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Ta fara maimaitawa a hankali.

Suhaima kuwa idanunta suka cika da hawaye

“Ya Allah…”

Firdausi ta zaro wayarta cikin rawar hannu.

“Baby, enough! I’m calling Ya Umar.”

“Call him.” Wannan karon Zahra ba ta hana ta ba.

Firdausi ta danna sunan Ya Umar❤️

Wayar ta fara ringing.

Ring… Ring… Ring…

Bai ɗaga ba, ta sake kira

Har yanzu… No answer

“He’s not picking!” Ta faɗa cikin tashin hankali.

Zahra ta haɗiye yawu.

“Kira Abbah.”

Firdausi ta yi sauri ta koma kan sunan Abbah.

Sai dai… Call Failed.

“What?” Ta sake gwadawa

Network Error “Ya Allah…”

Aasiya ta karɓi wayarta

“Let me try.”

Ita ma ta kira. Amma sakamakon ɗaya ne.

Network ya fara ɗauke-ɗaukewa

A cikin Hilux… Drivern ya yi murmushi.

“They’re trying to call someone.”

Mutumin da ke gefensa ya ce

“Keep driving.”

“Don’t let them out of your sight.”

Driver ya ƙara matsowa kusa.

A karon farko… Nisan da ke tsakaninsu ya ragu sosai.

Zahra ta hango hakan a mirror.

Ta murɗa steering wheel cikin nutsuwa, ta hau babban titi mai cike da motoci.

“Maybe idan muka shiga traffic za su daina.” Ta faɗa amma babu Wanda ya iya amsa mata

Ga mamakinta Hilux ɗin ta ci gaba da binsu

Firdausi ta fara kuka.

“Baby…”

“I don’t like this.”

Suhaima ta riƙe hannun Saudat

“Ki ci gaba da mana addu’a plsssss”

Saudat kuwa ta fara karanta Ayatul Kursiyyu da Suratul Falaq da An-Nas cikin ƙasa-ƙasa.

Aasiya ta ci gaba da danna wayarta

“Still no network.”

Zahra ta matse steering wheel har fararen yatsunta suka bayyana

A zuciyarta tana ƙoƙarin ta kasance mai ƙarfi, amma tsoro ya fara shiganta

Sai kwatsam…

BWAAAAAH!

Hilux ɗin ta yi horn mai ƙarfi. Ta ƙara matsowa kusa da bayan motarsu.

Suhaima ta yi ihu

“Ya Allah!”

Firdausi ta waiwayo cikin firgici.

“Baby!”

Zahra ta ƙara saurin motar. Hilux ɗin ma ta ƙara.

“Baby… faster!” Firdausi ta faɗa cikin rawar murya.

“Please!”

Zahra ba ta amsa ba. Idanunta suna kan hanya.

Hannayenta kuwa sun matse steering wheel har jijiyoyin hannunta suka fito.

Ta ƙara taka accelerator

Engine ɗin motar ya yi wani irin ƙara.

Sai dai…

Hilux ɗin ba ta rage musu tazara ba. Ita ma ta ƙara gudu.

A cikin motar…

Babu mai magana.

Sai Saudat da ke karanta Ayatul Kursiyyu cikin hawaye.

Suhaima ta fara kuka

“Ya Allah ka tsare mu…”

Aasiya ta ci gaba da ƙoƙarin kiran Ya Umar.

Har yanzu…

No Service.

Ta bugi dashboard da tafin hannunta

“Damn it!”

Firdausi ta ce,

“Try WhatsApp call!”

Ta gwada.

Bai shiga ba! Network ɗin kamar ya ɓace gaba ɗaya.

Gari kuwa ya fara yin duhu, saboda har Magrib ya wuce

Hasken motocin da ke kan titi ne kaɗai ke haskaka hanyar.

Traffic ya fara raguwa. Motoci sun yi kaɗan.

Wannan ne abin da ya fi ba Zahra tsoro, ta fi son titi mai cike da jama’a ba irin wannan ba.

Ta hango wani filling station a gaba, nan take ta juya zuwa ciki. Ta yi tunanin idan akwai mutane…

Wataƙila Hilux ɗin za ta wuce.

Amma… da ta shiga filling station…

Hilux ɗin ma ta biyo bayanta, ta tsaya a gefe.

Kamar tana jiran Zahra.

Firdausi ta kalli motar da idanunta suka cika da tsoro.

“They’re still here…”

Zahra ta haɗiye yawu.

Ba tare da ta kashe engine ba… Ta sake ficewa daga filling station.

Hilux ɗin ma ta biyo ta

A cikin Hilux…

Driver ya yi murmushi.

“She’s smart.”

Mutumin da ke gefensa ya ce

“But she’s getting tired.”

Ya ɗauki waya, ya tura wani short message.

“We’re close.”

Sai ya kashe screen ɗin.

A motar Zahra… ta sake kallon mirror.

Hilux ɗin ta sake matsowa kusa, kusan babu tazara.

Sai kwatsam…

BANG!

Hilux ɗin ta ɗan bugi bayan motarsu, ba bugu mai ƙarfi ba…

Amma ya isa ya sa motar Zahra ta karkace kaɗan.

Suhaima ta yi ihu.

“Ya Allah!!”

Saudat ta riƙe kujerar gabanta.

Firdausi ta fashe da kuka

“Baby!”

Aasiya ta ce da ƙarfi,

“Control it!”

Zahra ta murɗa steering cikin sauri, da ƙyar ta dawo daidaiton motar.

Numfashinta ya fara fita da sauri.

A karon farko… tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta.

Ta leƙa mirror. Hilux ɗin na sake shirin matsowa.

Idan suka sake bugunsu…

Wataƙila motar za ta fita daga hanya ko ma ta kwace daga hannun Zahra

Sai kuma daga can nesa…

Ta hango hasken wata mota mai ƙarfi tana tahowa daga gaba.

Fararen fitilunta suka haskaka titin gaba ɗaya

Motar tana ƙaratowa da wani irin gudu.

Hasken fararen fitilun motar ya ƙara kusantowa.

Zahra ta lumshe ido na ɗan daƙiƙa saboda tsananin hasken.

“Who’s that?” Firdausi ta tambaya cikin tashin hankali.

“Innalillahi wa’inna ilahir rajiun, Baby farautarmu suke yi, gashi kamar network baya son mu”

Babu wanda ya iya tanka mata

Motar tana ƙaratowa da gudu…

Duk sun gama giving up kawai motar kansu zata hau… sai dai abin mamaki…

Ba ta wuce su ba, ta yi wani irin juyawa cikin sauri

Screeeeech! Ƙarar tayoyi ta cika titin.

Motar wata ash-colour Range Rover ta tsaya a tsakiyar hanya.

Kai tsaye… Tsakanin motar Zahra da Hilux ɗin.

“Baby!” Aasiya ta yi ihu.

“Brake!”

Zahra ta taka birki da ƙarfi.

Motarta ta tsaya da ƙyar, numfashinta na fita da sauri.

Hilux ɗin da ke bayansu ma ta taka birki, amma saboda gudun da take yi…

Ta kusa karo da Range Rover ɗin.

Driver ɗin ya yi saurin kaucewa. Motocin biyu suka tsaya suna fuskantar juna.

Shiru wajen ya ɗauka sai ƙarar engines kawai.

Door ɗin Range Rover aka buɗe… wani dogon saurayi ya fito.

Black jeans ke jikinsa sai wani, white shirt.

Bai ko kalli Zahra ba, kai tsaye idanunsa suna kan mutanen Hilux.

Firdausi ta ɗan matsa gaba.

“…Shi ne.”

Suhaima ta zaro ido

“Guy ɗin nan?”

Saudat ta haɗiye yawu

“What?!…”

Zahra kuwa… ta kasa cewa komai sbd saurayin nan ne data taɓa mari, Wanda tace bata kaunar sanin komai daga garesa

Yana tsaye a gabansu…

Kamar wanda ya shirya tsayawa shi kaɗai

Mutumin ya ɗaga hannu alamar su tsaya

Sai ya yi magana ba tare da ya waiwayo motar Zahra ba ya ce

“Lock the doors” Muryarsa ta fito da ƙarfi

“Don’t come out.”

Zahra ta yi shiru, ba ta san dalilin da ya sa ba… Amma wannan karon… kawai samun kanta tayi da take bin umarninsa

Ta danno central lock.

Click.

A cikin Hilux… Driver ya yi tsaki.

“Damn.”

Mutumin da ke gefensa ya ce,

“I told you someone was watching.”

Driver ya buɗe ƙofar motar.

“Move him.”

Saurayin ya ɗauki matakai biyu gaba, kwata-kwata bai nuna tsoro a tattare da shi ba

Ya ce cikin sanyin murya,

“Enough!!! Leave them.”

Driver ɗin Hilux ya yi dariya

“Who are you?”

Saurayin ya amsa ba tare da ya ɗaga murya ba.

“The wrong person to test tonight.”

A cikin motarsu Zahra… Firdausi ta kalli Zahra da sauri

“Baby…”

“Waye shi?”

Zahra idanunta suna kansa.

A karo na farko… ba ta da amsar wannan tambayar

Sai dai zuciyarta ta fara bugawa da wani irin sauri, ba wai saboda tsoro ba… saboda wani abu da ba ta taɓa ji ba.

Mutumin da ta ɗauka matsala ne… Shi ne kaɗai yake tsaye tsakaninsu da matsalar da zasu faɗa

Iskar dare ta kaɗa rigar saurayin.

Har sannan yana tsaya cak yana jiran su fito daga Hilux ɗin, ba wata alamar tsoro tattare da shi. Sai nutsuwa mai ban mamaki.

Driver ɗin Hilux ya fito ya rufe ƙofar da ƙarfi.

Bang!

Ɗayan mutumin ma ya fito daga bayan motar. Dukkansu sanye da baƙaƙen kaya, gashi suna cikin mask, Fuskokinsu cike da tsaurin ido kuma

Firdausi ta saki wata ƙaramar ƙara

“They’re three…”

Saudat ta fara karanta Ayatul Kursiyyu da ƙarfi fiye da da.

Aasiya kuwa ta ce

“Ya Allah ka kawo mana ɗauki.”

Saurayin ya ɗan juya kansa kaɗan, bai kalli Zahra ba

Amma ya yi magana cikin murya mai ƙarfi.

“Zahra!!!” Karo na farko da ta ji ya kira sunanta cikin irin wannan yanayin.

Ta amsa a hankali

“…Yes?”

“Ki saurare ni da kyau.”

Ta haɗiye yawu.

“If I tell you to drive…”

“Don’t look back.”

“Just go.”

Zahra ta yi shiru, gabanta ya faɗi

“Amma kai fa?”

Bai amsa tambayar ba, sai ya sake maida hankalinsa ga mutanen

Driver ɗin Hilux ya yi dariya

“Hero kenan? Ka matsa gefe.”

Saurayin ya girgiza kai.

“No.”

“Last warning.” Mask Man ɗin ya ce

“No.”

Shiru ya biyo baya na wasu seconds

Sai ɗaya daga cikin mutanen ya fara takowa zuwa gare shi.

A hankali, kuma cikin isa.

Saurayin ya tsaya a inda yake, ko motsi bai yi ba

Zahra ta riƙe steering wheel, ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ke mata zafi ba

Wannan mutumin… ba ta san ko sunansa ba, ba ta san komai game da shi ba.

Amma yana tsaye ne yana haɗa rayuwarsa cikin haɗari… kuma for that matter saboda ita.

Firdausi ta ce cikin kuka,

“Baby… mu tafi.”

Zahra ta girgiza kai

“I can’t…”

Suhaima ta ce,

“Idan suka kama shi fa?”

Babu wanda ya amsa mata

Can nesa…

Aka fara jin ƙarar wata mota tana tahowa da gudu

Saurayin ya ɗan kalli gefen hanya, sai ya yi murmushi a hankali

Mutanen Hilux ba su lura da komai ba, har sannan duk hankalinsu yana kansa

Sai kuma…

Hasken wata mota ya bayyana daga nesa… yana ƙaratowa da matuƙar gudu

Vroooom!

Ƙarar engine ɗinta ta mamaye wajen.

Mutanen Hilux suka juya gaba ɗaya suna kallonta.

Saurayin kuwa…ya ɗan yi murmushi

Screeech!

Wata baƙar Mercedes G-Class ta tsaya da ƙarfi a gefen hanya.

Kafin kowa ya ankara… ƙofofinta suka buɗe, mutane huɗu sanye da baƙaƙen suit suka fito cikin sauri

Driver ɗin Hilux ya haɗe gira

“Move.”

Ɗaya daga cikin sabbin mutanen ya ce cikin sanyin murya,

“Kar Wanda yayi motsi”

Nan take yanayin ya sauya.

Mutanen Hilux suka fara kallon juna, kamar sun fahimci cewa abin zai iya fin ƙarfinsu.

Saurayin ya juyo ya kalli Zahra, Idanunsu suka haɗu.

Shi kuwa ya nuna mata da hannu.

“Go.”

Zahra ta girgiza kai.

“No…”

Ya ɗan ɗaga murya.

“Zahra.”

“Drive.”

“This is not the right place.”

Muryarsa ta sa ta yi shiru, ta ji kamar ba za ta iya musu ba.

Firdausi ta riƙe hannunta

“Baby… please.”

Aasiya ta ce

“Mu tafi.”

Saudat kuwa tana ci gaba da addu’a.

Da ƙyar… Zahra ta kunna motar, sai dai kafin ta motsa…

Ta sauke glass ɗin window kaɗan.

Ta kalli saurayin

“…Who are you?”

Saurayin ya yi murmushi kaɗan, murmushin farko da ta taɓa gani a fuskarsa.

Sai ya ce cikin sanyin murya,

“Not today.”

“One day…”

“You’ll know.”

“Now go.”

Zahra ta kunna motar, amma kafin ta taka accelerator

PAAH!

Ɗaya daga cikin mutanen Hilux ya ɗauko wani ƙarfen rod ya buga wa saurayin da ƙarfi.

Ya ja da baya mataki biyu.

Fuskarsa ta ɗan canza saboda zafin ciwon, amma bai fāɗi ba.

“Dee!” ɗaya daga cikin mutanen G-Class ya yi ihu yana nufarsa.

Saurayin ya ɗaga hannu ya hana shi.

“I’m fine…”

Amma bai gama rufe baki ba…Jini ya fara zuba daga gefen goshinsa.

Zahra ta zaro ido

“Oh my God!”

Ba tare da ta sani ba ta buɗe ƙofar motar za ta fito.

Firdausi ta riƙe hannunta.

“Baby! No!”

“He’s bleeding!” Ta faɗa cikin rawar murya.

Saurayin ya ɗago ya kalleta.

Ko da jini ke bin gefen fuskarsa… sai da ya yi mata murmushi kaɗan.

“Go…”

Muryarsa ta yi rauni.

“Please…”

“For your safety.”

Idanun Zahra suka cika da ƙwalla, gabanta ya yi wani irin faɗuwa.

Mutumin da ta taɓa mara… Mutumin da take masa kallon psycho… Yana zubar da jininsa saboda ita.

“Please… don’t do this…” Ta furta a hankali.

Sai ya girgiza kai.

“Drive, Zahra.”

“That’s all I want.”

Mutanen G-Class suka kewaye shi suna kare shi.

Zahra ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi saboda wani mutum da ba ta taɓa ba muhimmanci ba yau shike risking life dinsa sbd ita

Da ƙyar ta taka accelerator. Motar ta fara tafiya.

Sai dai idanunta suna kan side mirror…

Har sai da ta ga saurayin ya durƙusa a hankali, yana riƙe da kafadarsa mai jini…

Kafin motar ta ɓace daga gare shi

Yanzu wasan zai fara!!! Wanene Ibrahim Khalil? Wannan saurayin daya taimakawa Zahra wanene shi? Ya aka yi yasan Zahra Tana cikin tsananin Neman taimako? Waya saka su wannan aikin? Wanene Ahmad daya shigo rayuwar Zahra a karshen book 1?

Toh ku gyara zamanku da kyau dan wasan yanzu zai fara!!!

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.