Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 49 of 59

Chapter 47

Bayan sun yi sallama da juna…

Zahra ta juya tana kallon Saudat.

“Come with me.”

Saudat ta ɗan haɗe gira

“Ina?”

“Zan kai ki gida mana tunda hanyar mu ɗaya ce”

“A’a Zahra, zan hau Napep, hanyar mu ko kaɗan ba hanya ɗaya bace

Zahra ta harare

“Saudat ki zo. Kar ki sa na sake maimaita magana.”

Firdausi ta yi dariya

“Ki bi ta kawai, kin san idan ta yanke shawara ba ta saurara”

Asiya ma ta gyada kai

“Exactly.”

Saudat ta yi murmushi cikin kunya

“Toh.”

Su huɗu suka nufi parking lot.

Da suka isa Firdausi da Asiya suka tsaya

Firdausi ta yi wa Zahra bye

“See you tomorrow.”

“In shaa Allah.” Ta amsa

Asiya ta rungume Zahra

“Drive safely.”

“You too.”

Saudat ta tsaya tana jiran Zahra ta buɗe motar, da remote ta buɗe. Ta waiwayo

“Shiga.”

Saudat ta buɗe front seat, ta shiga cikin kunya

Zahra ta zagaya ta shiga driver’s seat, ta ɗaura seat belt.

Ita ma Saudat ta ɗaura nata

Ta kunna motar, a hankali suka fita daga campus

Tana driving cikin natsuwa, bayan kusan mintuna arba’in…

Ta isa gida bayan ta ajiye Saudat gidansu, Mai gadi ya buɗe mata gate, ta shigar da motar ta faka a inda ta saba.

Da ta sauko…

Mama Ladi ta karɓi handbag ɗinta.

“Sannu da zuwa Maman Babanta”

Dariyar da bata yi Nita bace tayi

“Oh ni Zahra mai suna iri iri”

Mama Ladi data yi gaba ta fara dariya

Ta shiga cikin gidan, kai tsaye parlour ta nufa.

“Ohh Daddy’s princess is tired”

“Must you always complain? Ai dama haka makaranta yake. Dan ma ke kina yi ne cikin gatanki”

Mami ce ta amsa daga can

Da ta leƙa…

Sai ta ga Mami tsaye cikin kitchen. Apron a ɗaure a gabanta.

Wasu kayan miya a kan island.

Tana haɗa ido da Zahra, ta yi murmushi

“Baby.”

“Na’am Mami.”

“Zo ki zo mu yi girki.”

Zahra ta tsaya cak, ta kalli kitchen ta sake kallon Mami.

Sai ta haɗe fuska kamar ƙaramar yarinya

“Mamiiii…”

Mami ta ɗaga gira.

“Lafiya?”

Zahra ta turo baki gaba

“Kai Mami, ba ga masu aiki ba? Shine sai Ni kuma na zo na tayaki girki?”

Mami ta naɗe hannayentq tana kallonta

“Eh, su na nan amma yau…Ina son ki koya wani recipe, dan ba abun da kika iya sai shopping da order online”

Zahra ta lumshe ido, ta yi kamar za ta yi kuka.

“Mami wallahi I’m tired, ki tausaya min, yanzu fah na dawo daga school”

Mami ta ƙure ta da ido

“Toh? Gidan miji idan kika je za ki ce akwai masu aiki ne tun kina amarya?”

Zahra ta dafe kanta

“Wayyo Allah na, Mami ni dai ba zan yi aure yanzu ba.”

Mami ta kasa riƙe dariyarta

“Zo nan, ki daina drama ko na saɓa miki”

Zahra ta ƙarasa tana taɓe baki

“Wallahi Mami kin fi lecturers bada wahala”

Mami ta buga bakinta, ta karɓe jakkanta ta miƙawa Anty Binta ta ce

“Ki Kai mata ɗakinta"

Ya mayar da dubanta ga Zahra

“Ke kuma ki fara yanka albasa.”

“Ni kuma zan haɗa sauran kayan.”

Zahra ta ɗauki wuƙa, ta fara yankan albasa

Bayan minti biyu…

Idanunta suka fara zubar da hawaye

Ta yi ƙara

“Mamiiii! Waiii albasa tana cutarwa, kinga har kuka na fara fah”

Mami ta yi dariya sosai

“Wannan ai ba kuka ba ne Albasa ce kawai, kuma dama haka take. Ci gaba.”

Kitchen ɗin ya cika da dariya.

Masu aikin gidan ma na ta murmushi a ɓoye suna kallon yadda Zahra ke ta ƙorafi amma tana yin abin da Mami ta ce

A hakaa dai dakyar aka samu aka gama wannan girkin, rabi da kwata ita dai bata fahimci komai ba kawai tasan duk abun da aka yanka a tukunya ake zubawa

Da daddare bayan sun gama dinner kowa ya watse

Abbah na zaune a parlonsa yana duba wasu takardu.

Zahra ta shigo a hankali

“Abbah.”

Ya ɗago kai

“My Baby.”

Ta ƙarasa ta zauna kusa da shi, ta jingina da kafadarsa.

Abbah ya shafa kanta

“Lafiya?”

Ta ɗan yi shiru, sai ta ce

“Abbah…”

“Hmm?”

“Ina son magana.”

“Ina ji Dear”

Ta ɗaga kanta

“Abbah… Ina so na koma hostel.”

Abbah ya cire gilashin karatunsa, ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kanta.

“Hostel?”

Ta gyada kai

“Eh Abbah. Firdausi za ta koma, Asiya ma haka, Saudat ma, ni kuma ba zanji daɗi ba, kar su zo performance ɗinsu yafi nawa"

Abbah ya yi shiru na wasu daƙiƙu yana kallon fuskarta

Sai ya ce cikin natsuwa

“Kin tabbatar?”

Ta gyada kai ba tare da wata-wata ba

“Yes, Abbah Ina son na gwada rayuwar hostel, Ina jin zai taimaka min sosai wajen karatu”

Abbah ya jingina da kujera, ya ɗan yi murmushi

“Toh… Ba zan ba ki amsa yanzu ba, zan fara yi wa Mami magana, sannan mu zauna mu tattauna.”

“Idan muka ga ya dace.. shikenan.”

Fuskar Zahra ta sake, nan take tayi murmushi, ta rungume hannunsa

“Thank you, Abbah.”

Ya shafa kanta

“Amma ko kin koma hostel karatunki shi ne first priority.”

Ta yi murmushi

“I promise.”

Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa

“Good girl.”

Zahra ta sumbaci hannunsa cikin girmamawa

Sannan ta miƙe cikin farin ciki…

Tana fatan wannan karon, burinta na zama tare da ƙawayenta a hostel zai cika.

Bayan Zahra ta fita zuwa makaranta… Gidan ya yi tsit

Abbah ya dawo daga office ɗinsa na cikin gidan bayan ya gama duba wasu takardu.

Ya shiga ɗakinsa, ya zauna kan sofa yana huta wa, bayan wasu mintuna…

Mami ta shigo ɗakin, a hannunta akwai turaren wuta

Da ƙamshinsa ya fara bazuwa a cikin ɗakin tun kafin ta shiga

Ta fara zagayawa tana ƙona shi a sasanninta, nan ɗakin yayi wani iron cool kamshi

Sannan ta gyara kan gadon haɗi pillow ɗin kan gado

Ta daidaita duvet, ta ɗauki wasu rigunan Abbah da aka ajiye kan kujera ta ninke su.

Abbah kuwa…

Tun shigowarta yake kallonta cikin murmushi, ita ɗin tabbas peace ɗinsa ne

Da ta gama komai ta sake masa murmushi, ta nufi ƙofa.

“Na gama” Zata fita…

Sai ya kira ta

“My peace”

Ta waigo haɗi da murmushinta dake kashe shi

“Na’am?”

“Zo mana”

Murmushi ta yi ta ƙarasa

Ta zauna a kujerar da ke gabansa.

“Lafiya dai?”

Abbah ya ɗan yi shiru, sannan ya ce

“Maganar Zahra ce.”

Mami ta gyara zamanta

“Na san za ka yi maganarta idan Baby ce”

Abbah ya ɗan yi murmushi

“Kin san tana son komawa hostel?”

“A’a gaskiya bamu yi magana ba, amma tunda ta maka magana tana son komawa ne”

Abbah ya gyada kai

“Ni ma na lura.”

Ya jingina da kujera

“My dear, Ke me kike gani?”

Mami ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa.

“Da farko da ace ta ce Nile University take so kaga ai dole a hostel dama zata zauna, ko ma Pen resource da kake so”

Abbah ya gyada kai.

“Haka ne.”

Mami ta ci gaba

“Amma yanzu dan tana KASU zata iya zama, kuma idan aka yi la’akari da zirga-zirga… Lectures, Assignments, Group discussions.”

“Wani lokaci ma practical. Hostel zai fi mata sauƙi.”

Abbah ya yi shiru yana sauraronta.

Mami ta ce

“Amma ba za mu tura ta hostel kawai mu ce shi kenan ba”

Abbah ya ɗaga kai

“Me kike nufi?”

“Za mu zauna da ita, mu yi mata nasiha. Rayuwar hostel ba kamar rayuwar gida ba ce, ba kowa ne irin wanda kika saba gani a gida ba.”

“Akwai nagari, akwai kuma marasa tarbiyya, akwai masu son karatu, akwai masu son ɓata lokaci. Saboda haka dole ta san abin daya kai ta”

Abbah ya yi murmushi

“Wannan maganar taki ce”

Mami ta yi murmushi ita ma

“Ni dai abin da nake so ko ta je hostel, kar ta manta tarbiyyar da aka raineta da ita, kar ta shiga rayuwar kwaikwayo. Kar ta yarda matsi ko ƙawaye su canja mata halinta”

Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa

“Dear wallahi kin faɗi abin da ke raina.”

Sannan ya ce cikin natsuwa

“Ni ma ban damu da zamanta a hostel ba. Abin da na damu da shi ne ta ci gaba da kasancewa Zahra ɗin da muka sani.”

“Mai mutunci, mai kunya, mai son addini, mai sanin darajar kanta.”

Mami ta yi murmushi

Abbah ya ɗan yi shiru sai ya ce,

“Toh idan haka ne, yau da dare idan ta dawo zamu zauna da ita muyi magana sosai, sannan mu yi mata duk abin da ya kamata.”

Mami ta gyada kai

“In shaa Allah.”

Ta miƙe tsaye

“Toh bari na je kitchen.”

Abbah ya bi ta da kallo har ta kai ƙofa.

Sai ya kira ta

“My dear”

Ta waiwayo

“Na’am?”

Ya yi murmushi.

“Nagode.”

Ta ɗan yi dariya.

“Na me?”

“Saboda yadda kike kula da yaran nan.”

Mami ta sauke idonta tana murmushi

“Allah Ya sa mu sauke amanar da Ya ɗora mana.”

“Ameen.”

Daga haka ta fita daga ɗakin…

Ƙamshin turaren wutar da ta bari na ci gaba da sanyaya ɗakin, yayin da Abbah ya jingina da kujera, yana jin kwanciyar hankali cewa shi da Mami suna tafiya a hanya ɗaya wajen tarbiyyar Zahra

Da yamma…

Bayan Zahra ta yi sallar La’asar, ta ɗauki laptop ɗinta da physics notebook, sai assignment sheet ɗin da lecturer ya ba su

Kai tsaye ta nufi ɗakin Ya Umar, ta yi knocking sau biyu.

“Come in.”

Ta tura ƙofar

Ya Umar na zaune a kan study table ɗinsa Laptop a gabansa, wasu files da takardu suna warwatse

Ya ɗago kai

“My Baby.”

Ta yi murmushi

“Yaya Busy?”

Ya ɗan kalli agogon hannunsa

“Not really. Lafiya?”

Ta ƙarasa ciki, ta ɗaga assignment paper ɗin

“Please help me.”

Ya ɗan yi dariya

“Physics again?”

Ta turo baki

“Wallahi lecturer ɗin nan baya tausayinmu.”

Ya miƙa hannu

“Zo gani.”

Ta zauna a kujerar da ke gefensa, taba shi paper ɗin, ya fara karantawa

Sai ya gyada kai

“Hmm ba shi da wahala, amma ina son ki fara solving ɗinIdan kin makale…”

“Sai na taimaka miki.”

Zahra ta yi wani iri da fuska.

“Yaya please ka sani ai.”

Ya harare ta da wasa

“A’a ba zan miki assignment ba, ni zan koya miki ne sai Ke kuma ki yi da hannunki”

Ta sauke ajiyar zuciya

“Okay.”

Ta buɗe notebook ɗinta, ta fara rubutu, kamar abun arziki ta fara, sai kuma ta tsaya.

Ta cije bakin biro

“Yaya…”

“Hmm?”

“Na makale.”

Ya ɗan matsa kusa da ita, ya ɗauki biro

Ya nuna mata inda ta yi kuskure

“Ki duba nan.”

“Kin rikita formula, shi ya sa answer ɗin ya ki fitowa.”

Ta ɗan karkata kanta tana kallon yadda yake rubutawa.

“Oooh… Ashe haka ne”

Ya gyada kai

“Eh, kada ki yi saurin solving.”

“Ki fara fahimtar question ɗin.”

Ta sake gwadawa, a wannan karon… ta samu answer ɗin, nan take ta yi murmushi

“Yesss! I got it.”

Ya Umar ya yi murmushi cikin gamsuwa.

“Good, na san za ki iya.”

Ta ci gaba da solving sauran questions. Duk lokacin da ta makale… Sai ya bata hint kaɗan ba tare da ya ba ta answer kai tsaye ba.

Bayan kusan awa ɗaya… Ta sauke biro

Ta miƙa notebook ɗin

“Done.”

Ya karɓa, ya duba ɗaya bayan ɗaya. Sai ya gyada kai

“Excellent Question ɗaya ne kawai kina da ɗa mistake.”

Ta yi saurin matsowa kusa

“Ina?”

Ya nuna mata, ta gyara

Sannan ya mayar mata da notebook.

“Now It’s perfect.”

Zahra ta yi wani irin murmushin nasara, ta haɗa littattafanta.

Ta kalli Ya Umar

“Nagode sosai.”

Ya ɗan taɓe baki.

“Da kin ce ba za ki iya ba, Ashe kawai rashin sa kai ne”

Ta yi dariya

“Saboda kana kusa da ni ne. Shi ya sa”

Ya girgiza kai yana murmushi.

“Ki je ki sake karantawa kafin ki kwanta, kada ki dogara da abin da muka yi yanzu kawai.”

Ta yi salute da hannu cikin wasa

“Yes sir.”

Ya Umar ya yi dariya

“Get out.”

Ta yi dariya ita ma

Ta rungume notebook ɗinta ta fita daga ɗakin cikin farin ciki…

Tana jin wani irin ƙwarin gwiwa cewa physics, wadda ta fi ba ta wahala, yanzu ta fara samun sauƙin fahimta saboda yadda Ya Umar yake koya mata cikin haƙuri ba tare da ya gaji da tambayoyinta ba….

Zahra na zaune a kan gadonta

Assignment ɗin physics na gabanta.

Tana sake karanta answers ɗin da ita da Ya Umar suka gyara.

Lokaci zuwa lokaci sai ta yi murmushi idan ta tuna yadda ya riƙa ce mata,

“Think first before solving.”

A dai-dai lokacin…

Aka yi knocking a ƙofar ɗakinta.

“Come in.”

Mama Ladi ce ta turo ƙofar.

“Zahrau.”

Zahra ta ɗago kai

“Na’am Mama Ladi.”

“Hajiya Mami na kiranki.”

Zahra ta haɗe gira

“Ni?”

“Eh.”

Ta ɗora biro a kan notebook

“Lafiya dai ko?”

Mama Ladi ta ce da wata fuskar da take ƙoƙarin ɓoye dariya,

“Ban sani ba, kawai ta ce na kira ki.”

Zahra ta miƙe daga kan gado

Tana saka slippers ɗinta ta tambaya,

“Mama Ladi… Ina take?”

Mama Ladi ta amsa ba tare da wata-wata ba,

“Kitchen.”

Da zarar kalmar kitchen ta fita daga bakinta… Zahra ta tsaya cak, ta lumshe ido sai ta dafe goshinta.

“Wayyo Allah…”

Ta fara bubbuga ƙafa kamar ƙaramar yarinya.

“Kaiii!”

“Mama Ladi! Yanzu shikenan zata sake cewa girki wallahi Mami ta dai na tausayi a”

Mama Ladi ta kasa riƙe dariyarta.

Ta juya tana dariya,

“Ni ban ce komai ba fa.” daga haka ta bar wajen

Ita kuma Zahra…

Ta ɗaga murya tun kafin ta isa kitchen.

“Mamiiiiii! Wai kin ƙi yafe min ne idan ma laifi na miki?”

Daga cikin kitchen

Mami ta amsa tana dariya.

“Zo mana my love”

Zahra ta ƙaraso bakin ƙofa ta tsaya, ta haɗe hannaye a ƙirji ta turo baki gaba.

“Mami… Don Allah wai yau ma?”

Mami ta nuna mata chopping board

“Eh, yau ma.”

Zahra ta dafe ƙirji

“Wayyo ni, Mami wallahi na yi assignment na gaji.”

Mami ta ɗaga gira

“Toh? Ni kuma ban gaji ba ne?”

Zahra ta yi shiru

Sai ta ƙarasa a hankali.

Ta tsaya kusa da Mami, ta kalli kayan girkin da ke kan kitchen island

“Kaiii duk wannan?”

Mami ta yi murmushi.

“Duk wannan, za mu yi.”

Zahra ta wani marairaice fuska

“Please ki kira Mama Ladi mana.”

Mami ta girgiza kai

“A’a dole ki koya fah, dan yanzu kin girma.”

“Gobe idan kina gidanki…Ba za ki ce Mami ta zo ta dafa miki ba.”

FARASHIN IZZAH

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.