Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 3 of 59

CHAPTER 2

Bayan fitarsu, zai wuce É—akinsa, Zahra ta ce,

"Ina wuni, ka dawo lafiya?"

Bai kulata ba, ya ci gaba da taka stairs. Ta ɗaga kai tana kallonsa da mugun mamaki har ya gama hayewa. Miƙewa tayi ta bi bayansa.

Tana isa ƙofar ɗakin, ta ga a kulle. Ta kai hannu a hankali ta buɗe ta shiga. Bin ɗakin tayi da kallo ganin ba ya ciki. Ƙofar toilet ta bi da kallo jin karar ruwa. Ta ƙarasa ciki ta zauna bakin gado tayi tagumi.

She can't believe… wai yau 15 days da aurensu, amma gaba ɗaya duk wani soyayya da komai ya riga ya fara fading

A haka ta dinga sake-sake har ya fito daga wanka. Kallo É—aya ya mata ya É—auke kansa, ya ci gaba da tafiya zuwa wajen mirror.

Ta miƙe ta shiga gabansa ta ce,

"Noory, wai wani laifin na maka ne? Idan har ma laifi na maka, ina soyayyar mu da har ba zaka iya yafe min ko ka faÉ—a min kuskure na na gyara ba?"

Wuce ta yayi, ya ƙarasa dressing mirror ya fara shafe jikinsa da mai.

Ja da baya tayi ta tsaya tana kallonsa. Har ya gama ya sanya wani kaya na daban. Ba ƙaramin kyau ya mata ba. Tuna yadda yake mata yasa a take mood ɗinta ya canza.

Ta ga ya nufi hanyar fita, ta miƙe ta ce

"Yau da ka zo da wuri ina murna… ashe fita zaka yi ka dawo yadda ka saba sai cikin dare ko?"

Sauka yake akan stairs tana binsa a baya.

Suna isa main parlour, ta sha gabansa.

"Haba Noory, wai me yasa kake min haka ne? Where is the promise? Haka muka yi da kai?"

Idonta ya cika da ƙwalla bayan ta gama maganar.

Ya tako zuwa gabanta ya tallabi fuskarta da hannayensa biyu yana kallon cikin idonta dake jike da hawaye.

Ya ce,

"Zahra… tauraruwa na" yana maganar yana tauna cingam.

Still idonsu na cikin na juna, ya ce,

"Alkawarin? FaÉ—a min, menene bana miki a gidan nan?"

Ta kwace kanta tayi baya tana masa wani mugun kallo. Ta koma ta zauna kan kujera tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.

Ya juya zai fita, ringing É—in wayarta yasa ya dakata.

Ta É—aga kiran, ganin Ya Umar ne.

A hankali ta ce,

"Hello Yaya…"

Yayi shiru kafin ya ce, "Zahra, menene?

Ta ce, "Me ka gani Yaya?"

Ya ce "Na ji muryarki wani iri ne."

Ta ce "Au ai mura nake yi"

Yayi shiru, sai kuma ya ce,

"Alright, anjima idan baki da wani abu, ki kira Abba ki masa ya jiki, dan kwana biyu bai ji daÉ—i ba"

Ta ce da sauri "What? Abbana ba shi da lafiya, shine ba a faÉ—a min ba? Noo, ba zan iya kira ba, dole zan zo gida na duba shi"

Ya Umar zai yi magana, ta katse kiran.

Ta miƙe tsaye, hanyar stairs zata yi....

Ibrahim dake bakin ƙofa ya ce,

"Kar ki kuskura ki fita ko'ina"

Ta juyo ta ce "Har kana tunanin kana da wani power ne? Kalli yadda kake magana as if kai wani ne."

Wani dariya yayi ya ce,

"Ni wani ne mana, Zahra. Ko kin manta ke ma saboda kuÉ—in kika aure ni ne?"

Zahra ta sake baki tana kallonsa ta ce

"Wai tunani kake yi kai wani ne a hakan? Thank God ka san waye ubana. Kafin ka aure ni, ko motar da nake hawa baka taɓa hawa irin ta ba. Don haka baka isa kayi min gorin arziki ba, dan a cikinta na taso"

Ta É—an dakata sannan ta ce,

"Fita kuma, idan har ka isa ka dakile fitan nawa, nagaji… nagaji da wannan halin naka. Idan da na san haka kake, wallahi da ba zan taɓa aureka ba, ko da kuwa a mafarki ne"

Daga haka ta juya zuwa sama da gudu tana hawaye.

Ibrahim ya juya ya nufi ƙofa. Direct inda motarsa yake ya nufa, ya buɗe, yana shiga ya fice daga gidan.

Tana shiga ɗakinta, ta zube a ƙasa tayi kukanta mai isarta. Sannan ta tashi ta wuce toilet. Wanka tayi, ba ta wani daɗe ba ta fito ta sa kaya.

Ta fito ta kulle ko'ina sannan ta wuce compound. Gun motarta ta tafi, tana shiga ta kwantar da kanta a jikin steering motar ta fara rera kuka.

"Wannan wani irin rayuwa ce…"

Sai da ta yi mai isarta sannan ta tada motar, tayi wa mai gadi horn ya buÉ—e mata.

Bayan ta yi tafiya sosai, sai ga shi ta isa unguwarsu. Tana horn, mai gadi ya leko, ganin itace ya buÉ—e gate É—in yana mika gaisuwa. Ta amsa masa da fara'a sannan ta shiga ciki tayi parking.

Kofar parlour ta buÉ—e da sallama a bakinta.

Mummy ce kaɗai a parlour, tana shan fruits ta ɗora ƙafarta akan stool.

Tayi sallama ta shiga.

Mummy ta É—aga kanta tana kallonta da murmushi a fuska ta ce

"Waiiii, yau kuma Zahra ce a gidan namu?"

Zahra tayi murmushi ta shiga tayi hugging É—inta ta ce,

"Mummy, ya naga ke kaÉ—ai ce anan? Ba kowa ne a gidan?"

Mummy na kallonta ta ce,

"Duk ba su nan. Kin baro gida lafiya?"

Zahra ta ce "Lafiya kalau"

Zahra ta ce,

"Mummy, ya jikin Abbana?"

Mummy ta riƙe haba ta ce,

"Wa ya ce miki Abbanku ba lafiya?"

Ta ce, "Yaya Umar ne."

Mummy tayi tsaki ta ce,

"Allah, ban san yaushe Umar zai girma ba. Ace yarinya ko wata bata yi da aure ba, ya wani ce miki Abbanku ba lafiya ki zo gida"

Zahra ta yi murmushi ta ce,

"A'a fah Mummy, ba cewa yayi na zo ba, kawai cewa yayi na kira shi"

Mummy ta kwala ma mai aiki kira, sai ga Zulai ta fito da ladabi.

Ta kalli Zahra da har ta kwanta ta lumshe ido ta ce,

"Kije ki kawo wa Zahra ruwa, naga kamar ta gaji."

Zulai da ladabi ta amsa wa Mummy sannan ta juya ta tafi.

Mummy ta jima tana kallon Zahra dake kwance, idonta a lumshe.

Bata wani daɗe ba sai ga Zulai ta fito da ruwa a hannunta. Ta duƙa ta ajiye a gaban Zahra.

Mummy na kallonta ta ce,

"Zahra, tashi ki sha ruwa."

Zahra ta buɗe ido tana kallonta, sai kuma a hankali ta miƙe ta zauna.

Mummy ta ce xZahra, me ke damunki?"

Zahra tayi murmushi ta ce,

"Babu komai fah, Mummy."

Mummy ta mata wani kallo ta ce,

"Boye min damuwarki zaki yi? Gashi duk kin rame, kin yi duhu… anya lafiya kuwa?"

Zahra ta ce,

"Babu komai fah…"

Ta ƙarasa maganar trying hard not to cry

Mummy ta ce "ko baki jin daÉ—in gidan naki ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Kawai dai kwana biyu bana jin daÉ—i ne, Mummy."

Daga haka ta kyale ta, amma ba wai don ta yarda cewa babu komai É—in bane...

Suna zaune, sai ga su Mami da Abbah, sai Umar dake gefensa yana masa sannu suka shigo parlour.

Zahra ta miƙe tsaye ta ƙarasa wajen Abbah da gudu ta rungume shi.

Mami sai kallonta take da mamaki ta ce,

"Ke kuma, daga yanzu har kin fara fita?"

Zahra dai tana rungume da Abbah, wanda babu wani ƙarfi tattare da shi, har ma ya kasa magana.

Mami ta ce "Ki sake shi mana, baki ganin ba lafiya gare shi ba?"

Ta sake shi tana murmushi mai haÉ—e da hawaye.

Abbah ya ce "Zahra, yaushe kika zo? Ina mai gidan naki?"

Zahra ta ce "Abbah, ya jikin naka? Fatan baka jin komai ko?"

Ya ce "Da sauƙi"

Ta kama hannunsa zata kaisa É—akinsa, duk suka bisu a baya.

Suna zagaye da shi suna É—an hira sama-sama.

Mami sai satan kallon Zahra take yi, haka ma Abbah. Umar kam ya gagara É—auke kansa akanta....

Gyangyadi ta fara.

Mummy ta ce,

"Zahra, ki shiga ciki ki kwanta mana, naga kamar bacci kike ji ko?"

Ta buÉ—e ido, sai kuma ta make kafaÉ—a ta ce,

"Ina gefen Abbah na."

Abbah ya ce,

"Toh kwanta anan ki yi baccin tunda har yana son sace ki."

Tana kwanciya kuwa, nan da nan numfashinta ya canza alamar bacci ya É—auke ta.

Abbah yana kallonsu ya ce,

"Ko ido na ne, naga Zahra ta canza… kamar tana cikin damuwa sosai.*

Mami ma tayi shiru, don abin dake ranta kenan.

Mummy ta ce "Ai Alhaji, ina jin kamar albarkar aure ce fah"

A É—an fusace ya ce

"Ban gane ba. Haka kawai sai ’yar tawa ta dinga ramewa ace albarkar aure? Ina albarka anan?"

Mami tayi murmushi.

Mummy ta ce

"Toh ai albarkar aure ina nufin ka kusa samun jika ne. Baka gani ba, tun da tazo take ta faman bacci? Wannan ramewan a cikin laulayi ne"

Mami ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya. Sai yanzu ta ji hankalinta ya É—an kwanta ganin kamshin gaskiya a maganar Mummy.

Abbah yayi murmushi, amma har yanzu Umar bai daina kallonta ba......

Bayan Magrib, Zahra ta fito daga toilet zata hau kan sallaya, sai ga Mami ta shigo ta ce,

"Zahra, ki yi sallah ki É—an ci abinci, ki samu ki tafi kafin dare ya yi."

Sai da gabanta ya faÉ—i jin maganar.

A hankali ta ce

"Toh, Shikenan"

Daga haka Mami ta fita kawo mata abinci.

Bayan Mami ta dawo, ta same ta ta idar amma tana kwance kan darduma.

Ta duƙa tana kallonta ta ce,

"Baby, me ke damunki ne?"

Zahra ta ce,

"Menene Mami?"

Mami ta ce,

"Duk kin canza ne Zahra… ba Baby na dana sani bane a baya. Ko akwai wata matsala ne?"

Zahra tayi dariya ta ce,

"Babu komai fah, Mami."

Mami ta ce

"Toh Shikenan… amma bayan bikin ki kin yi period ne?"

Zahra tayi shiru tana kallon Mami, dan bata san ma’anar tambayar ba.

A hankali ta ce

"A'a, ban yi ba"

Nan take Mami ta yi murmushi.

Sai da gaban Zahra ya faÉ—i saboda abinda kwakwalwarta ta hasko mata game da tambayar da Mami ta mata...

Umar ne yayi sallama a ƙofar ɗakin.

Mami ta amsa ya shiga yana kallon Zahra da har ta gama shiri.

Ya ɗauki jakkanta tare da riƙo mata hannu ya ce,

"Mu je, mijinki ma yana downstairs."

Ta kalleshi ta ce

"Yaushe ya shigo kuma?

Ya ce,

"Not long ago"

Daga haka ta yi wa Mami sallama suka fita.

A corridor, ya tsaya ya ce,

"Baby, me ke damunki?"

Ta yi shiru.

Ya ce "Baby talk… akwai matsala ne a zamantakewar ku?*

Ta ce,

"Nope."

Ya ce,

"Ƙarya kike, shine zaki lalace har haka?"

Ta yi shiru ta ce,

"Yaya, babu komai fah. Ka bari idan na tafi gida zan kira ka na sanar maka abin dake damuna.*

Ya ce,

"Kin yi alkawari?"

Ta ce

"Eh, nayi"

Daga haka suka fara sauka.

Tun a kan stairs Ibrahim ya É—aga kai yana kallonsu.

Satan kallon Abbah yayi, ya É—auke kansa, ya ci gaba da kallonsu har suka sauka.

Ko kaÉ—an Zahra bata kalleshi ba.

Gefen Abbah ta ƙarasa ta zauna ta ɗora kanta a faɗarsa.

A hankali ta ce,

"Abbah, ya jikin?"

Ya ce

"Da sauƙi, Baby"

Ya ce

"Yaushe zaki koma school? Ban ji kina labarin komawarki ba"

Ta ce,

"This coming Monday nake son na fara zuwa."

Ya ce,

"Good. Ki fara saboda final year ba shekarar wasa bane."

Ta yi shiru.

Ibrahim kam ya kasa É—auke idonsa akanta.

Abbah ya ce,

"Tashi ku tafi, sai da safe."

Umar ya É—auka mata jakkanta.

Abbah ya ce,

"A'a, ajiye mata. Ai tare da mijinta zata koma."

Zahra ta miƙe tsaye ta ce,

"No Abbah, da mota nazo ai"

Daga haka tayi hanyar ƙofa.

Ibrahim yayi wa Abbah sallama ya bita a baya.

Wani kallo Umar ya bishi da shi.

Tana isa jikin motarta zata buÉ—e kenan, ya ce,

"Wani irin rashin tarbiyya ne wannan? Baki ganni bane? Ko gaishe ni ba zaki yi ba? Wani zindikin kato zai riƙe hannunki ku fito kamar baki san ina existing a wajen ba…"

Ta juyo ta masa wani kallo ta ce,

"Dama zama tare da kai akwai wani alkhairi ne? Ko ba matsala muke samu ba?"

Ta numfasa ta ce

"Abeg ka matsa min a hanya kafin nayi calling attention na mutane."

Ta shige motarta ta fita.

Shi ma ya bi ta a baya da nasa motar.

Tana shiga gida, ta sauka ta wuce É—akinta direct.

Tana cikin toilet, ta ji karar buɗe ƙofa.

Tana fitowa, ko kallon inda yake bata yi ba.

Ya ce

"Gobe after Magrib ina so ki shirya, zamu tafi wani taro. Kuma na san zaki cire ni a kunya. Dan wannan abun zai iya trending sosai, so dan Allah be ready, bana son ki bani kunya."

Ta yi banza da shi.

Ya ce "Baby, magana fah nake miki."

Ta ce "Na ji."

Ya ce,

"What?" Ya ƙarasa inda take.

Ta ja baya ta ce,

"Na ji, Allah ya kaimu."

Ya ce,

"Ameen."

Ta kalleshi ta ce,

"Khalil, me yasa kake min abubuwan da suke kona min rai? Baka so na shine zaka aure ni? Baka so na shine zamu yi wannan deal É—in? Ko dai ka manta alkawarin mu ne? Ko wani laifin na maka da zaka ke min haka?"

Ya ce,

"Calm down… zan canza, baby. Wallahi babu abin da kika min. Sorry kinji."

Ta rungume shi tayi lamo a kirjinsa…

tana jin yadda zuciyarta ke bugawa.

#08110615256

*FARASHIN IZZAH*

Jiddatulkhayr writes

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)

Book 1

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.