Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 56 of 59

Chapter 54

Kusan rabin ranar suka shafe suna yawon shakatawa

Suka shiga wani babban shopping mall, suka yi window shopping, suka shiga game arcade inda Firdausi da Aasiya suka dage sai an gwada wasu games

Suhaima da Saudat kuwa suka dage sai an ɗauki hotunan duk wani move nasu a wajen

Zahra ce ta riƙa musu dariya

“Wallahi ku huɗun nan ba za ku taɓa girma ba.”

Firdausi ta harare ta

“Kamar ke ɗinma wata babba ce”

Daga nan suka wuce wani restaurant mai kyau, suka ci abinci cikin nishaɗi, suna ta hira da dariya.

Kafin su tafi, suka ɗauki group pictures da selfies na short vid masu yawa

“Today’s memories are worth keeping,” Zahra ta faɗa tana kallon hotunan.

Da yamma ta yi, suka yanke shawarar komawa gida.

Da suka isa parking lot, Zahra ta latsa remote, motarta ta yi ƙarar buɗewa.

Ta yi wa ƙawayenta murmushi

“Ku shiga mana.”

Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat suka shiga motar.

Zahra kuma ta zagaya zuwa gefen direba, ta kama handle ɗin motar ta buɗe ƙofar

Daidai lokacin… Wani hannu ya riƙe ƙofar kafin ta shiga

Ta ɗago kai.

Wani matashi ne tsaye gabanta.

Dogon saurayi ne, cikin baƙar shirt da jeans, fuskarsa cike da damuwa amma idanunsa na nuna ƙarfin hali.

Ya haɗa ido da ita

“Hey… excuse me, please.”

Zahra ta kalle shi daga sama har ƙasa, sannan ta haɗe fuska.

“A taƙaice… are you mad?”

Ta nuna inda yake tsaye

“Za ka tsaya min a kai haka?”

Saurayin ya yi murmushin da bai rasa kunya ba

“Eh… gaskiya I’m mad… a kanki Fatima Zahra”

Ya ɗan sauke numfashi.

“Har mutane suna kallona kamar wani psycho.”

Ya yi murmushi kaɗan “Idan kin ce no, zan ji zafi… amma ba zan ji wani iri ba.”

Zahra ta ji ranta ya fara ɓaci, ta matso kusa da shi.

“Za ka matsa min ne, malam, ko yaya?”

Ya ɗan sunkuyar da kansa

“Please, Zahra… one minute”

“Ki tausaya min.”

Ta yi wata ’yar dariyar raini

“Fuck you.”

Ta nuna shi da yatsa

“Who are you?”

Ya yi shiru na ɗan lokaci

Sannan ya amsa cikin nutsuwa.

“I’m nobody…”

Ya ɗan yi murmushin gefen baki

“But hoping to be somebody… one day.”

Zahra ta girgiza kai cikin rashin jin daɗi

“Congratulations.”

Ta ture hannunsa daga ƙofar motar

“Yanzu ka gama? Saboda ni kam ban zo nan don sauraron speeches ba.”

Ta shiga motar ba tare da ta sake kallonsa ba, ta ufe ƙofar.

Saurayin ya tsaya yana kallon motar cikin rashin abun yi

Firdausi, Aasiya, Suhaima da Saudat kuwa suka yi shiru gaba ɗaya, suna kallon Zahra da saurayin, sun kasa cewa komai.

Zahra ta kunna motar, ba tare da ta waiwaya ba, ta fice daga parking lot, ta bar saurayin tsaye a wurin yana kallon motar har sai da ta ɓace.

Su kuwa har suka fara tafiya, babu wanda ya yi magana na wasu daƙiƙu.

Sai ƙarar AC da waƙar da ke tashi a hankali kawai ake ji

Firdausi ce ta fara karya shirun, ta juya ta kalli Zahra

“Baby…”

Zahra na kallon hanya ta ce

“Hmm?”

“Me ya faru ne tsakanin ki da guy ɗin nan?”

“Nothing.”

Aasiya ta haɗe gira

“Nothing? Kin san shi ne?”

“No.”

“Toh me ya sa ya kira ki da sunanki?”

Zahra ta yi ɗan tsaki

“Wallahi ban sani ba.”

Suhaima ta ce

“Amma kamar ya san ki sosai.”

“Ya sani mana,” Zahra ta amsa ba tare da ta juya baya ba. “Mutane da yawa sun san ni.”

Saudat ta yi murmushi

“Ba wannan nake nufi ba. Kamar… ya san wani abu game da ke.”

Zahra ta girgiza kai

“I don’t care.”

Firdausi ta ce

“Amma kin yi masa zafi fa.”

Zahra ta ɗan kalleta.

“Yanzu idan ke ce wani ya zo ya tare ki haka fa?”

Firdausi ta yi dariya

“Ni zan tsaya na ji abin da zai ce.”

“Ni kuma ba zan tsaya ba” ta mayar mata amsa ba tare data ko kalleta ba

Aasiya ta ce,

“Wallahi ya yi magana cikin mutunci. Ban ga ya yi rashin kunya ba.”

“Mutunci?” Zahra ta ɗan yi dariyar raini. “Riƙe ƙofar motar mutum ba tare da izininsa ba ai ba rashin mutunci ba ne.”

Suhaima ta gyada kai

“Hakan ma gaskiya ne.”

Saudat ta ce cikin sanyin murya

“Amma… na ji tausayinsa.”

Zahra ta kalleta ta mirro da mamaki

“Tausayinsa?”

“Eh. Yadda ya ce, ‘I’m nobody… but hoping to be somebody one day.’ Ban san dalili ba, amma maganar ta taɓa ni.”

Na ɗan lokaci motar ta yi sit

Firdausi ta ce,

“Ni dai ina jin ba zai ƙara hakura ba.”

Zahra ta ɗan yi murmushi ba tare da ta kalli kowa ba.

“Toh ni kuma ina fatan ya yi hakuri. Saboda idan ya sake tare ni… wannan karon ma ba zai ji abin da zai so ba.”

Dukkansu suka yi shiru

Sai dai kowacce na da abin da take tunani.

Saudat na tunanin kalaman saurayin ta rasa dalilin daya sa maganarsa ta bugeta

Ita kuwa Zahra… Ta mayar da hankalinta kan tuƙi, kamar abin da ya faru bai da wata muhimmanci a gare ta

Suna isa School Villa, Zahra ta faka motar a parking space ɗinsu.

Ta kashe motar sannan ta cire seat belt.

“Finally… home.”

Firdausi ta miƙa hannayenta tana jan numfashi.

“Wallahi na ji daɗin outing ɗin nan.”

“Same here,” Aasiya ta amsa.

Suhaima ta ce

“Ya kamata mu riƙa yin haka ko sau ɗaya a wata.”

Saudat ta yi murmushi

“In Sha Allah.”

Suka fito daga motar suna ɗauke da shopping bags ɗinsu.

Kafin su shiga block ɗinsu, Firdausi ta ce,

“Girls, ice cream fa! Na manta mun saya.”

Zahra ta kalli ledar da ke hannunta

“Oh… gaskiya.”

Aasiya ta yi dariya

“Ke dai idan ba mu tuna ba, da kin manta da rabin kayan da kika saya.”

Zahra ta ɗan harare ta

“Whatever.”

Da dariya suka shiga cikin gidan.

Da suka shiga falo, kowacce ta ajiye kayan da ta saya.

Firdausi ta cire hijabinta ta zauna a kujera

“Wallahi ƙafafuna sun gaji.”

“Ke kuma?” Zahra ta yi dariya. “Ai ba trekking muka yi ba yau.”

“Shopping ma exercise ne fa.”

Dukkansu suka yi dariya.

Suhaima ta buɗe ledarta

“Guys, ku zo ku ga turaren da na saya.”

Nan take suka zagaye ta

“Wow!”

“Smells so nice.”

“Try this one.”

Kowacce ta fara gwadawa a wuyanta da hannunta.

Sai ɗakin ya cika da ƙamshi.

Saudat kuwa tana zaune tana kallonsu tana murmushi.

Zahra ta lura, ta auki wata ƙaramar leda ta miƙa mata.

“Open it.”

Saudat ta karɓa cikin mamaki

“Mine?”

“Of course.”

Da ta buɗe… Wani elegant perfume ne da kuma wristwatch mai kyau

Ta zaro Idanunta waje

“Zahra… wannan fa…”

“It’s yours.”

“A’a, wannan ya yi yawa gaskiya”

“No, it isn’t.” Zahra ta amsa

Saudat ta girgiza kai

“Wallahi ba zan karɓa ba.”

Zahra ta haɗe fuska

“Saudat!!!”

Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba

“Kin taɓa barina na wanke kaya na?”

Saudat ta yi murmushi

“Ai wannan ba komai ba ne.”

“Toh ni ma wannan ba komai ba ne.”

Firdausi ta yi dariya

“Please karɓa kawai. Kin san halinta.”

Aasiya ta gyada kai

“Otherwise ba za ta sake fita shopping da ke ba”

Dukkansu suka yi dariya.

Saudat ta sauke numfashi

“Thank you… Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen,” suka amsa gaba ɗaya.

A daidai lokacin…

Knock! Knock!

Kowa ya waiga zuwa ƙofar.

Firdausi ta miƙe

“Wa zai zo mana wannan lokacin?”

Ta nufi ƙofar ta buɗe, wani matashi ne tsaye a waje.

Sanye da uniform na dispatch rider.

Ya kalli Firdausi

“Assalamu alaikum.”

“Waalaikumus salam.”

“A nan ne Zahra Fatima take?”

Firdausi ta juya ta kalli Zahra

“Baby… ana nemanki.”

Zahra ta ƙaraso

“Ga ni”

Dispatch rider ɗin ya miƙo mata wani ƙaramin box da aka naɗe da golden ribbon.

“An ce a ba ki wannan.”

Ta karɓa cikin mamaki

“Wa ya aiko?”

Ya girgiza kai

“Ban sani ba, an biya komai tun da farko.”

Ya yi musu sallama ya tafi.

Dukkansu suka taru suna kallon box ɗin.

Firdausi ta ce da sauri

“Open it!”

Zahra ta kalli box ɗin na wasu daƙiƙu.

Sai wani tunani ya faɗo mata…

Unknown Number.

Da kuma… Saurayin nan na parking lot

Ta haɗe gira

“Who exactly is this?”

ta ci gaba da kallon ƙaramin gift box ɗin da ke hannunta.

Firdausi ta kasa haƙuri

“Baby, open it manaa!”

Aasiya ta matsa kusa

“I’m curious.”

Suhaima ta ce

“Kar dai ki ce ba za ki buɗe ba.”

Saudat ma ta gyada kai

“Mu gani mana.”

Zahra ta sauke numfashi

“Okay.”

Ta fara cire golden ribbon ɗin a hankali, ta buɗe murfin box ɗin.

Cikin box ɗin…

Wata ƙaramar rose mai launin fari ce, tare da wani folded note

“Flowers?” Firdausi ta faɗa da mamaki

Zahra ta ɗauki note ɗin

Kafin ta buɗe shi, Aasiya ta ce,

“Read it aloud plsss!”

Ta buɗe takardar

Rubutun hannu ne mai kyau..

“You don’t know me… and maybe you don’t want to. But I just wanted to say thank you… for unknowingly teaching me that some people are worth respecting from afar. Have a beautiful day, Zahra.”

Ba suna, ba number, bakomai da zai yi indicating ɗinsa

Shiru ya ratsa falon.

Firdausi ce ta fara magana.

“Wallahi… wannan ba irin letter ɗin soyayya da muka saba gani ba ne, iyyeee this guy sabi love”

Suhaima ta gyada kai

“It’s… different.”

Saudat ta ce a hankali,

“Ya rubuta cikin girmamawa.”

Aasiya ta kalli Zahra

“Toh… yanzu fa?”

Zahra ta sake ninke takardar, ta mayar da ita cikin box

Ta ɗauki rose ɗin ta kalla na wasu daƙiƙu sai ta nufi dustbin.

Firdausi ta zaro ido

“Baby… me kike yi?”

Ba tare da ta ce komai ba…

Ta jefa gift box ɗin gaba ɗaya cikin dustbin.

Firdausi ta riƙe kanta

“No way!”

Aasiya ta ce,

“Haba Zahra”

Suhaima ta yi shiru tana kallonta,

Saudat ma haka

Zahra ta tafa hannunta

“Unknown people don’t deserve a place in my life.”

Ta juya ta nufi ɗakinsu. Ba wanda ya sake magana

A waje, a cikin wata baƙar mota da ke ajiye nesa da gate ɗin School Villa…

Mutumin ya hango dispatch rider yana fitowa.

Ya ɗan yi murmushi

“That’s good!”

Ya kunna motar a hankali

“The Game is just beginning.

Washegari….

Karfe bakwai da rabi na safe.

School Villa ta cika da ɗalibai masu shirin fita lectures

A kitchen kuma…

Firdausi na frying pancakes.

Aasiya na haɗa tea

Suhaima na shirya lunch warmers

Saudat kuma tana goge kitchen

Zahra ta fito daga ɗaki cikin wani elegant milk-colored abaya da premium silk veil. A hannunta akwai mug ɗin coffee.

Ta tsaya bakin kitchen tana kallonsu

“My God… ku huɗun nan ba ku gajiya ne?”

Firdausi ta waiwayo tana dariya.

“Madam, idan muka jira ki, ai yunwa za ta kashe mu.”

Dukkansu suka yi dariya.

Zahra ta zauna a dining chair

“Seriously, Saudat… na fa ce ki daina yi mana komai ke kaɗai.”

Saudat ta yi murmushi

“Na kusa gamawa ai.”

“Exactly! Shi ya sa nake magana.”

Aasiya ta kawo mata plate

“Princess, eat first before your daily speech.”

Ta karɓa tana murmushi

“Thank you.”

Bayan sun gama breakfast, suka fito compound.

Motar Zahra na sheki, Firdausi ta yi whistle.

“Driver madam… your chariot is ready.” Zahra ta jefa mata key.

“Since kina surutu, ke za ki tuƙa?”

Firdausi ta cafke key ɗin da sauri.

“God forbid! Idan na yi scratching ɗin motar nan, Ya Umar zai kashe ni.”

Dariya suka yi gaba ɗaya! Suka shiga motar.

A hanya, karatu ne ke tashi a motar

Suna hira cike da annashuwa a haka suka isa cikin university…

Parking area ta cika da motoci. Zahra ta faka motar cikin nutsuwa.

Kafin su fito…

Sai Firdausi ta dafa hannunta.

“Baby…”

“What?”

Firdausi ta nuna da idanunta zuwa wani gefe

“Don’t look immediately.”

Zahra ta ɗaga gira

“Why?”

“Because… he’s here.”

Zahra ta juya kai a hankali.

Can ƙarƙashin wata bishiya… saurayin nan ne, sanye cikin farar shirt da black trousers.

Ba ya kallon wayarsa baya tare da wani balle yayi magana da shi

Idanunsa kawai suna kan motar Zahra.

Da idanunsu suka haɗu…

Bai yi murmushi ba.

Sai kawai ya ɗaga hannu kaɗan cikin girmamawa, kamar yana yi mata sallama daga nesa

Zahra ta haɗe fuska, ta buɗe ƙofar motar ta sauka

“Let’s go.”

Duk sauka suka yi suna mamakin nacin mutumin nan, suka fara tafiya.

Firdausi ta yi ƙasa da murya.

“Wallahi… yau bai zo ya dame ki ba, just to see yhu”

Aasiya ta gyada kai

“Maybe ya fahimci message ɗin da kika ba shi.”

Suhaima ta ce

“Ko kuma yana son ya nuna cewa ba zai matsa mata ba ba”

Zahra ba ta ce komai ba.. sai dai kafin su shiga faculty…

Ta ji wata murya daga bayanta, a sanyaye… cikin girmamawa…

“Have a nice day… Zahra.”

Ba ta waiwaya ba, ta ci gaba da tafiya kamar ba ta ji komai ba

Ranar ta ci gaba da tafiya kamar kowacce rana, sosai yau suka wuni a makarantar saboda lectures

Ga lots of Assignments da aka basu, Class discussions da suka yi, Short tests ma, har yamma suna school suka yi ƙarshen lectures na ranar

“I’m starving,” Firdausi ta faɗa tana riƙe cikinta

Aasiya ta yi dariya

“Same here. Cafeteria?”

“Definitely!”

Kowa ya amince.

Su biyar suka nufi cafeteria cike da hayaniyar ɗalibai

Bayan sun yi order, suka zauna a wani table da ke gefen window.

Firdausi na ta ba da labari

Suhaima da Aasiya na dariya.

Saudat na cin abinci a hankali.

Zahra kuwa tana sipping juice ɗinta kafin ta fara cin fried rice ɗin da ke gabanta.

Sai kwatsam…

Wata inuwa ta tsaya kusa da table ɗinsu.

Firdausi ta ɗago kai

“Oh no…”

Saurayin nan ne, ya na tsaya cikin natsuwa

Ya kalli Zahra kawai

“Excuse me…”

Zahra ko kallonsa ba ta yi ba, ta ci gaba da cin abincinta.

Ya sake magana cikin ladabi

“Can I have just one minute?”

Still…

No response.

Ya sauke numfashi

“Okay… I’m sorry for disturbing your peace.”

Zahra ta miƙe tsaye ta ɗauki jakkanta ta juya zata tafi.

Yayi saurin shan gabanta

“Dan Allah ki saurare ni zahra… kar ki tafi”

Ta fara tafiya a zuciye, jakar da ke rataye a kafaɗarta ta fara zamewa saboda ba ta rufe zip ɗinta sosai ba.

Without thinking…

Ya miƙa hannu ya riƙe jakar kafin ta faɗi ƙasa.

Cikin daƙiƙa guda…

PAA!

Wani irin mari Zahra ta wanke shi da shi.

Sautin marin ya amsa cikin cafeteria.

Hayaniya ta tsaya cak. Cokula suka tsaya a sama.

Wasu ɗalibai suka miƙe tsaye, kowa ya waigo

Zahra ta zuba masa ido cike da ɓacin rai

“How dare you?”

“Wa ya ba ka izinin taɓa ni?”

“How dare you hold my bag?”

Saurayin ya dafe kumatunsa

Ya kalleta cikin nutsuwa.

“It’s not my fault, Zahra.”

Ya ɗan nuna jakar

“It was falling.”

Na ɗan lokaci… Idanunsu suka haɗu

Sai ya yi wani ƙaramin murmushi mai cike da takaici

“But… have a nice day.”

Ya juya ya fara tafiya.

Cafeteria gaba ɗaya ta yi tsit. Har sai da ya fita.

Firdausi ta kalli Zahra

“Baby…”

Aasiya ta kasa magana. Suhaima ta haɗe gira

Saudat kuwa ta kalli ƙofar da ya fita, sannan ta sake kallon Zahra.

Wasu ɗaliban da ke kusa suka fara raɗe-raɗi.

“Wallahi bai yi mata komai ba.”

“Jakar ta zai faɗi ne ya tare ta.”

“Amma marin nan ya yi zafi.”

“Poor guy…”

Zahra ta ji kalamansu.

Ba ta ce uffan ba

“Ina waje, if you’re done, sai ku same ni” Ba tare da ta kalli kowa ba, ta gyara jakarta ta fita daga cafeteria

Ƙawayenta suka mike suma, suka bi bayanta cikin shiru.

Kowa na jin cewa… Wannan karon, abin da ya faru ya fi kowanne rikitarwa

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.