Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 35 of 59
Chapter 34
Da daddare, kamar yadda aka saba, kowa ya hallara a dining domin cin abincin dare.
Abbah na kan kujerarsa ta gado, Mami na gefensa, Ya Umar kuwa na gefen Zahra. A ɗaya ɓangaren kuma Mummy da Batoul ne suke zaune.
Ana cikin cin abinci ne Zahra ta ɗaga kai ta kalli Abbah.
"Abbah..."
Ya ɗago yana kallonta.
"Na'am, Baby."
Ta ɗan yi murmushi.
"Yau ba? an yi mana announcement a school, an ce an buɗe registration na WAEC, NECO da JAMB ga waɗanda suke son yin jumping."
Ta ɗan dakata tana kallon reaction dinsa
"Abbah... ni ina so na yi making trial."
Lokaci guda Mummy ta ɗago ta watsa mata wani irin kallo.
Batoul ma ta taɓe baki tana kallonta.
Abbah ya ajiye cokalin hannunsa.
"Why do you want to skip SS3, Zahra? You want to write paper in SS2 instead ?”
Zahra ta ɗan yi frowning face, tana murza cokalin hannunta.
Kafin ta samu damar amsawa, Ya Umar ya yi saurin cewa,
"Abbah, ai Zahra tana da ƙoƙari” Ya yi murmushi yana kallon ƙanwarsa.
"Ka barta mana ta yi making trial. Ko da ba ta ci ba, experience ne. Though bamu fatan haka”
Abbah ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya gyada kai
"Okay." Ya kalli Zahra
"Since kina so... Gobe Ya Umar zai raka ki makarantar ya yi miki registration na komai”
Fuskar Zahra ta cika da annuri
"Thank you, Abbah naa”
Mami ta ɗan kalleta cikin kulawa.
"Zahra... ba ki yi ƙarama ba?"
Zahra ta girgiza kai da sauri
"A'a Mami Ina so."
Abbah ya yi murmushi.
"Tunda ita tana so, babu wanda zai hana ta."
Nan take Mummy ta yi ƙwafa.
"Amma ai kuna gani, a gidan nan babu wanda ya taɓa yin jumping sai ita."
Abbah ya juya ya kalleta
"Lokacin da 'ya'yanki suke secondary... kin taɓa nuna musu cewa ni ne ubansu?"
Mummy ta ɗan cije baki.
Abbah ya ci gaba da magana.
"Har gwara Umar shi a ɓoye yana zuwa wajena har daga baya ya dawo gaba daya amma ita...”
Ya nuna Batoul da kansa
"Har yau ba ta ɗauke ni a matsayin uba ba. Duk saboda abin da kika cusa mata tun tana ƙarama."
Dining ya yi tsit.
Ya ci gaba da cewa,
"Shi ya sa na mayar da hankalina kan waɗanda suka ba ni dama na kusance su."
Ya sauke numfashi.
"Ban san manufarki ba. Maybe akwai wani dalili da ya sa kika raba ta da ni”
Mummy ta zaro ido.
"Ban gane ba. Zargina kake yi?"
Abbah ya kalleta cikin nutsuwa.
"Duk yadda kika ɗauka... toh hakan ne."
Nan take ta buga tebur da hannu.
"Alhaji!" Ta kira cikin fushi
"Wannan ai zargi ne kai tsaye."
Abbah bai ko motsa ba.
Ya ci gaba da kallonta cikin ƙanƙanin lokaci, sai ya ce da murya mai nauyi,
"Hafsat..."
"Kar ki sa mu yi cacan baki a gaban yara. Saboda idan ba haka ba... wallahi za ki sha mamakina da kuma abun da zai fito daga baki na Wanda ke Baki san na sani ba” Muryarsa ta fito cike da izza da gargaɗi
Nan take Mummy ta yi shiru
Batoul ta sauke kanta ƙasa. Ya Umar kuwa ya saki numfashi a hankali.
Zahra da Mami suka kalli juna na ɗan lokaci, domin sun fahimci wannan shi ne karo na farko da Abbah ya fito fili yana ƙalubalantar Mummy a gaban kowa, dan Abbah mutum ne me son yara
Da suka gama cin abincin, Zahra ta goge bakinta da tissue sannan ta miƙe tsaye.
Abbah ya ɗago yana kallonta.
"Baby."
Ta juyo tana murmushi
"Na'am, Abbah."
Ya miƙa hannu ya shafa kanta cikin kulawa irin ta uba.
"Kar ki manta idan kin shiga ɗaki ki yi alwalar barci."
Ta gyada kai
"In Sha Allah."
Ya ci gaba.
"Ki yi addu'o'in barci, sannan ki karanta Suratul Mulk kafin ki kwanta."
Murmushi ta yi.
"In Sha Allah, Abbah."
"Good girl."
Ta matsa kusa da Ya Umar.
Kafin ya ce komai, ya jawo ta kusa da shi ya yi kissing goshintanta
"Good luck, little professor."
Ta yi dariya
Sai ta sunkuya ta rada masa wani abu a kunne.
Nan take Ya Umar ya fashe da dariya.
"Wallahi kina da matsala."
Ita ma ta yi dariya tana girgiza kai.
Mummy ta bi su da wani irin kallo.
Da ace kallo na kashe mutum, da tuni su biyun sun mutu sbd irin kaifin kallon da take musu
Zahra ta ƙarasa wajen Mami.
Ta yi kissing kumatunta.
"Good night, Mami."
Mami ta shafa mata baya.
"Allah ya tashe mu Lafiya, ya kuma miki albarka"
"Ameen."
Daga nan ta sake komawa wajen Abbah.
Ta rungume shi ta baya, ta ɗora haɓarta a kafaɗarsa.
"Good night, my Abbah."
Abbah ya riƙe hannayenta yana murmushi.
"Good night, Baby. Allah ya tsare min ke."
"Ameen."
Ta sake rungume shi na ɗan lokaci kafin ta sake shi.
Daga nan ta juya ta nufi matakala tana ɗan tsalle-tsalle har ta ɓace daga ganin su.
Mami ma ta miƙe.
"Bari na shiga” Ta faɗa tana kallon Abbah.
Ta nufin ɗakinsa domin ta gyara masa ko ina tare da kunna turaren wuta kamar yadda ta saba yi masa kowace dare.
Ya Umar kuwa da sauri ya miƙe, ya san yanzu idan Abbah ya bar wajen, toh tabbas ya banunsa a wajen Mummy
Ya ƙarasa kusa da shi.
"Good night, Abbah."
Abbah ya gyada kai.
"Allah ya tashe mu lafiya."
"Ameen." Ya amsa, sai kuma ya juya yana kallon Mummy wacca ta cika take basewa ya sunkuyar da Kansa kasa ya ce a hankali
“Mummy, good night”
Ta dago ta watsa masa wani banzan kallko
Yayi saurin dauke kansa daga nan ya juya ya wuce sama.
Da Zahra ta shiga ɗakinta, ta ajiye system ɗinta gefe
Ta cire kayan jikinta, ta saka sleeping wear mai launin pink.
Kai tsaye ta shiga toilet, ta yi alwalar barci cikin nutsuwa.
Da ta fito, ta shimfiɗa sallaya tayi shafa’i da witr kamar yadda Mami ta Saba mata, Tana idarwa
Ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin kwanciya
Bayan ta gama, ta ɗauki Al-Qur'ani.
A hankali ta fara karanta Suratul Mulk kamar yadda Abbah ya umarce ta.
Da ta kammala, ta ɗaga hannayenta sama.
Ta yi addu'a ga iyayenta, Ya Umar, Mami da kuma dukkan muslumai
Sai ta tofa addu'ar a tafukan hannunta ta shafa a jikinta.
Ta koma kan gado, ta kashe fitilar ɗakin.
Ta kwanta tana murmushi.
Ta lumshe idanunta. Cikin ƴan daƙiƙu kaɗan...
Barci mai daɗi ya ɗauke ta.
Washegari tun da sassafe, bayan sun gama breakfast kamar yadda suka saba, Zahra ta fito ɗauke da school bag ɗinta, yayin da Ya Umar ya jingina da motarsa yana jiran fitowarta.
Da ta ƙaraso, ya buɗe mata front seat.
“Princess.” Ya faɗa yana murmushi.
Ta yi dariya.
“Thank you, Yaya.”
Ta shiga ya rufe mata ƙofar sannan shi ma ya shiga ya tada motar.
A hanya Zahra ta riƙa ba shi labarin test ɗin da suka yi makon da ya gabata da kuma yadda take sa ran za ta ci su dukka
Ya Umar yana saurarenta lokaci-lokaci yana jinjina kai.
“Kin yi karatu kuwa?” Ya tambaya.
Ta taɓe baki
“Yaya kenan, ai ka san ni.”
Ya yi dariya.
“Na sani. Amma WAEC, NECO da JAMB ba wasan yara ba ne, ba wai Baki karatu bane just that zaki sake dagewa ne”
Ta gyada kai.
“Shi ya sa nake son in gwada tun yanzu.”
Ya yi murmushi cikin jin daɗin yadda take da himma.
Da suka isa makarantar, tare suka fita daga motar, ya bi bayanta suka shiga admin block.
A reception suka tarar da wasu iyaye da ɗalibai suma sun zo saboda registration.
Bayan sun jira na ɗan lokaci, aka kira su ciki.
Class mistress ɗinta ta yi murmushi da ganin Zahra.
“Oh, Zahra! So you’ve finally decided?”
Zahra ta gyada kai.
“Yes, Ma.”
Ta juya ta nuna Ya Umar.
“My elder brother.”
Ya Umar ya gaishe ta cikin girmamawa.
Ta amsa tana murmushi.
Nan ta yi musu bayanin abubuwan da ake buƙata.
Ya Umar ya karɓi form ɗin registration ya zauna yana cikewa cikin nutsuwa, Inda bai gane ba sai ya tambayi Zahra.
Da ya gama, ya miƙa mata, ta duba komai.
“Everything is correct.”
Ta nuna cashier.
Ya Umar ya nufi cashier ya biya kuɗin registration ba tare da wata-wata ba.
Bayan an ba shi receipt, aka sake ba su wasu takardu da za a adana.
Class mistress ta ce,
“Ki tabbatar kin ƙara dagewa da karatu Zahra, na san wacece ke, but ki sake d’aura d’ammara’’
Zahra ta gyada kai.
“I’ll do my best, Ma.”
Ta yi murmushi.
“I know you will.”
Da suka fito daga office ɗin, Ya Umar ya miƙa mata envelope ɗin.
“Ki riƙe shi da kyau, kar naje na bar miki shi a offic
Ta karɓa tana murmushi.
“Thank you, Yaya.”
Ya shafa kanta.
“Abin da nake so da ke kawai shi ne ki yi iya ƙoƙarinki, don’t stress yourself too much”
Zahra ta yi murmushi mai cike da kwarin gwiwa
“In shaa Allah.”
Ya raka ta har ƙofar ajinsu.Kafin ya juya zai tafi, ya ce,
“Zan karaso In shaa Allah kafin ku tashi”
“Okay, Yaya.”
Ta yi masa waving da hannu.
Shi ma ya daga mata hannu yana murmushi kafin ya juya ya fita daga harabar makarantar.
Zahra ta tsaya tana kallonsa har sai da motarsa ta ɓace daga ganinta, sannan ta yi murmushi ta shiga aji, tana jin wata sabuwar ƙwarin gwiwa ta cika zuciyarta, zata bawa Abbah mamaki wannan karon ma…
Da aka tashi daga makaranta, Zahra ta fito tana tafiya a hankali. Ko daga kallonta ka san ta gaji matuƙa
Registration, classes da test ɗin da suka yi sun ɗauke mata ƙarfi tass haka take ji
Da Ya Umar ya zo ɗaukarta ma, ko magana sosai ba ta yi ba, kamar yadda ta saba cikasa da surutu. Ta jingina da seat tana kallon titi ta window, lokaci-lokaci idanunta na lumshewa saboda gajiya.
Ya Umar ya kalleta yana murmushi
“Exhausted?”
Ta ɗan buɗe ido
“So much.”
Ya girgiza kai.
“Kin ce kina son jumping, a haka ne zaki fara university Baki son stress?”
Ta taɓe baki
“Na sani… amma ban yi tunanin zai gajiyar da ni haka ba.”
Ya yi dariya
“Wannan fa farkonsa ne.”
Da suka isa gida, Zahra ta sauko daga motar tana jan ƙafafunta a hankali.
Tana shiga parlour, kai tsaye ta nufi inda Abbah yake zaune yana karanta wasu files. Ko kula da Mummy bata ma yi ba
Ba tare da ta ce komai ba ta zauna a gefensa, ta jingina da kafaɗarsa.
Abbah ya ajiye files ɗin yana kallonta.
“My Baby… Ya school?”
Ta sauke ajiyar zuciya.
“Alhamdulillah.”
Sai ta fara ba shi labarin komai dalla-dalla.
Yadda registration ya kasance, yadda aka cika forms, yadda class mistress ta yi musu nasiha, da kuma yadda malamai suka ce rubuta paper ba abu ne mai sauƙi ba.
Abbah yana saurarenta yana gyada kai lokaci-lokaci. Da ta gama, ya yi murmushi
“I’m proud of you.”
Ta yi dariya.
“Thank you, Abbah.”
Sai ta ɗan matsa kusa da shi.
“Abbah…”
“Hmm?”
Ta ɗan marairaice fuska.
“Please… Ka siya min waya mana”
Ya Umar da ke zaune kusa da su ya yi saurin cewa,
“Wannan dai kin dan responsibility nane ko?”
Mummy ta ɗaga kai ta watsa masa wani irin kallo. Karaf Ya Umar idanunsa ya fada cikin nata wanda shima bai yi noticing ba
Ya Umar ya haɗiye sauran maganar da zai yi. Sai ya yi saurin ɗaukar remote.
“Abbah… wai match ɗin Arsenal yaushe ne?”
Abbah ya ɗan kalle shi, ya san sarai dalilin canja maganar, amma bai ce komai ba.
Sai ya juya wajen Zahra.
“Waya ba za ta gudu ba.Ki fara mayar da hankalinki kan karatu. Ki nuna min cewa kin shirya wannan jumping ɗin. In sha Allah, idan lokaci ya yi, zan saya miki wadda za ki so. Kai ba waya ba ko duniya kike so idan Ina da shi Zahra ni me baki ne”
Fuskar Zahra ta sake, ta yi murmushi.
“Promise?”
Ya ɗan ja hancinta.
“Promise.”
Ta yi dariya
“Thank you, Abbah.”
Can da yamma, Duk suna zaune, Mami Tana mamakin yawan ganin Mami a parlon na kwana biyu, amma bata cr komai ba, game take bugawa a wayanta
Mummy ta zauna tana latsa wayarta itama amma sauran ba wanda ya kula da ita
Sai dai fuskarta ta nuna ba ta cikin nutsuwa, ta buɗe WhatsApp
Wani sabon saƙo ya shigo, ta duba sunan wanda ya aiko…
Nan take murmushin da bata shirya yin sa bane ya bayyana a fuskanta, ta ɗan waiwaya ta tabbatar babu mai kallonta
Sai ta buɗe saƙon.
Da ta karanta layi na farko…
Murmushinta ya ɓace gaba ɗaya, fuskarta ta sauya.
Ta ɗaga kai a hankali ta kalli Zahra da ke dariya tare da Abbah.
Sai ta sake kallon wayarta, ta matse ta da ƙarfi a hannunta…
A hankali ta furta cikin ƙasa-ƙasa,
“Fuck you…”
“Wannan ai shirme ne, Abu daban ace kuyi daban?…”
Sai ta kashe screen ɗin wayar, ta miƙe ba tare da ta ce wa kowa komai ba, ta nufi ɗakinta
Mami ta d’aga kanta ta bita sa kallo sai kuma ta girgiza Kai kawai ta cigaba da game dinta
#FARASHIN IZZAH
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.