Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel
Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx
Chapter 48 of 59
Chapter 46
Bayan ɗan lokaci suka isa gida.
Mai gadi ya buɗe gate Ya Umar ya shigar da motar compound.
Yana parking, Zahra ta buɗe ƙofar motar.
Kafin ta fita sai ta waiwayo.
“Thank you once again.”
Ya Umar ya girgiza kai yana murmushi
“Go inside.”
Ta gyada kai, ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakin Mami ta nufa, ta tura ƙofar tana sallama.
Mami na zaune tana karanta Al-Qur’ani.
Da ta ga Zahra… Ta yi murmushi
“Kin dawo?”
“Eh Mami” Ta zauna kusa da ita.
Ba tare da ta jira an tambayeta ba… ta fara ba ta labarin komai.
“Mami da muka fita… Ban ma bari ta buɗe bag ɗin a gabana ba.”
“Muna kan hanya, sai ta kira ni. Kuka take yi wallahi har na tsorata.”
Ta yi dariya.
“Mami… Kin ji yadda take min addu’a kuwa?”
Mami ta yi murmushi.
“Allah Ya karɓa.”
“Ameen, amm Mami na ji daɗi sosai, na fi jin daɗin farin cikinta fiye da kayan da na ba ta.”
Mami ta shafa kanta.
“Allah Ya ƙara miki wannan zuciyar.”
“Ameen.”
Daga haka ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce
“Mami lemme rest” tana faɗin haka ta wuce zuwa ɗakinta
Ana dab da kiran sallar Magrib, sai aka yi sallama daga kofar parlour, kuma babu kowa a parlon sai masu aiki dake girka diner a kitchen
Mama Ladi ta yi saurin zuwa, tana buɗe entrance door taga mutane tsaye, murmushi ɗayan tayi ta ce
“Mami fah?”
“Bari na kirata, ku shigo” ta fad’a daga haka ta nufi sama su kuma suka shigo parlon
Ɗakin Mami ta shiga da sallama
“Hajiya kinyi baƙi.”
Mami ta ɗago kai
“Su waye?”
“Wata yarinya ce da wata dattijuwa, daga gani kamar mahaifiyarta ce, amma ita yarinyar ina ganinta wani lokacin anan”
Mami ta miƙe daga kishingiɗin da take
“Toh gani zuwa" Ta miƙe tsaye
Ita kuma Mama Ladi ta fita
Bayan Mami ta sauko ƙasa, da ta isa parlour…
Sai ta ga Saudat ce.
A gefenta kuma wata dattijuwa mai kamala, sanye cikin tsaftatacciyar atamfa duk da tsufarta
Da suka ga Mami Nan take suka miƙe “Barka Hajiya”
“Yauwa, Barkan mu” Mami ta amsa da fara’a
“Sannu da zuwa! Bismillah, ku zauna mana”
Suka sake zama, Mami ta kalli Mama Ladi
“Je ki kira Zahra, ki ce ta sauko”
“Toh Hajiya.”
Zahra na gyara hijabinta bayan ta yi alwala, Mama Ladi ta turo ƙofa.
“Zahra, Mami na kiranki.”
“Toh.”
Daga haka ta ajiye hijab ɗinta
Ta sauko cikin sauri.
Da ta shiga parlour…
Idanunta suka sauka kan Saudat, sai kuma mahaifiyarta, ta yi mamaki sosai
“Mama?”
Saudat ta yi murmushi cikin kunya.
Mahaifiyarta ta miƙe tsaye, Kafin Zahra ta ƙarasa…
Sai ta kama hannunta
“’Yata Allah Ya saka miki da alkhairi.”
Zahra ta ji kunya ya kamata
Ta yi saurin riƙe hannunta.
“Mama don Allah kiyi shiru, ba komai na yi ba.”
Mama ta girgiza kai
“A’a ’yata, a wajenmu ba ƙaramin abu ba ne.”
“Kin faranta wa ɗiyata rai Allah Ya faranta miki.”
Saudat ma ta yi shiru
Sai murmushi take yi, idanunta cike da ƙwalla.
Mami ta yi murmushi tana kallonsu
“Ai da baku wahalar da kan ku na zuwa ba, duk yiwa Kai ne. Dama kuma Zahra tun tana ƙarama.. tana da son taimakon mutane.”
“Idan ta ga wani cikin buƙata… Ba ta samun natsuwa har sai ta taimaka masa”
Mama ta kalli Zahra da wata irin ƙauna.
“Allah yayi mata fiye da zato”
“Ameen.”
Mami ta amsa.
Mama kam sai addua take
Zahra kuma sai jin kunyar irin yabon da ake mata take yi, tana ta ƙoƙarin sauya zancen saboda ba ta son a riƙa ɗaukar abin da ta yi tamkar wani babban alheri ne.
Sun ɗan zauna na wasu mintuna suna hira cikin girmamawa.
Sai Mama Ladi ta kawo musu lemo da snacks
Mahaifiyar Saudat ta ɗan kurɓa kaɗan kawai, ta mayar da cup ɗin a hankali ta ajiye
Daga haka ta miƙe tsaye
Saudat ma ta miƙe tare da ita.
Mami ta ce,
“Haba, ai da kun ƙara zama mana.”
Mahaifiyar Saudat ta yi murmushi.
“A’a Hajiya. Kar dare ya yi mana. In shaa Allah wata rana za mu sake zuwa.”
Mami ta gyada kai.
“Toh shikenan! Allah Ya kai ku lafiya.”
“Ameen.”
Zahra ta ƙarasa kusa da Saudat.
Ta kamo hannunta
“Shine sai kin fito da Mama a wannan Magrib din”
Saudat ta yi murmushi cikin kunya.
“Wallahi Mama ce ta ce sai mun zo. Ni ma na ce ai ba sai mun wahalar da ku ba, amma ta ƙi.”
Mahaifiyarta ta yi dariya.
“Toh ai dole ne, ba za a yi mana irin wannan alkhairin mu zauna a gida ba.”
Zahra ta yi murmushi.
“Nagode da zuwa.”
Saudat ta matso kusa da ita, ta rungume ta a hankali.
“Allah Ya saka miki.”
Zahra ta maida rungumar.
“Ameen! Hope yanzu kin daina kuka?”
Saudat ta yi dariya.
“In shaa Allah.”
Daga haka suka nufi kofa
Mami da Zahra suka raka su har bakin gate.
Suna isa bakin gate…
Mai gadi ya riga ya buɗe musu.
Mahaifiyar Saudat ta sake juyowa, ta ɗaga hannayenta.
“Allah Ya albarkaci wannan gida. Ya haɗa ku da alkhairi, ya kare ku daga dukkan sharri.”
“Ameen.”
Mami da Zahra suka amsa tare.
Saudat ta yi wa Zahra wani kallon godiya.
Zahra ta ɗaga mata hannu tana murmushi.
“See you tomorrow.”
Saudat ta yi murmushi.
“In shaa Allah.”
Daga haka su Saudat suka fita daga gidan, Mai gadi ya rufe gate
A hanyar su ta komawa cikin gidan Zahra ta sauke numfashi a hankali
Mami ta kalleta ta yi murmushi.
“Kin ga dai wani lokaci ƙaramin alkhairi da mutum yake ganin bai kai komai ba… a wajen wani shi ne mafi girman farin cikin rayuwarsa.”
Zahra ta lumshe ido kaɗan, ta gyada kai cikin natsuwa.
“Kin yi gaskiya, Mami.”
Washegari…
Tun kafin ƙarfe shida na safe…Alarm ɗin Zahra ya fara ringing
Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta kashe alarm ɗin
Miƙe wa tayi zaune tana murza idanunta, sai kuma kai tsaye ta nufi banɗaki.
Ta yi alwala tare da brush, tana fitowa ta shimfiɗa sallaya sannan ta tayar da Sallah cikin nutsuwa.
Bayan ta idar tare da addu’o’in safe da maraice ta fara shiryawa domin makaranta.
Ta zaɓo wata doguwar abaya mai launin navy blue, Ƙaramin bracelet a hannunta. Black handbag ɗinta. Da flat shoes baƙaƙe masu kyau
Ta kalli kanta a mirror bayan ta gama saka kayan, ta gyara veil ɗinta. Sai ta sauko ƙasa.
Ta yi breakfast cikin gaggawa. Ta yi sallama da Mami, ta gaisa da Abbah.
Daga haka ta ɗauki mukullin motarta ta fita
Mai gadi ya buɗe mata gate. A hankali ta ja motarta ta fice daga gidan….
Saudat bayan tayi sallah ta fita compound kafin karfe 7 ta gama Duk wani abu da zata yi na taimakon gida
Mama ta shiga daki tana kallon Saudat ta ce
“Saudatu ba zaki shirya ba kar ki makkara?”
Saudat ta gyaɗa Kai ta ce
“Mama Kaya zan saka ai nayi wanka”
Kaii ta gyada mata hadi da barin bakin kofar
Saudat ta jawo babban fancy bag ɗin da Zahra ta ba ta, ta buɗe shi, ta ɗan tsaya tana kallon kayan.
Har yanzu ba ta saba da ganin su ba, sai ta zaɓi wata doguwar abaya mai launin olive green mai musulmin kyau, ta saka ta a hankali, ta dade tana kallon kanta harta manta da wani boko
Ta ɗaura veil, haɗi da shafa lip-balm, ta sake tsayawa a gaban mirror, ta kasa gane kanta
Kamar ba ita ba. Mama ta fito daga ɗayan ɗakin
Da idanunta suka sauka kan Saudat… sai ta dafe ƙirjinta da sauri tana kallonta
“Ehyee! Saude? Kin ganki kuwa? Allah kinyi kyau sosai”
Aliyu ma ya shigo daga tsakar gida, da ya ga yayarsa, sai ya zaro ido
“Yaya Saudat? Allah kin yi kamar wata Hajiya”
Saudat ta yi dariya
“Aliyu ka cika surutu.”
Mama ta ƙarasa ta shafa stones dake jikin veil din, sannan ta shafa kumatunta
“Allah Ya saka wa Zahra.”
Saudat ta sauke kai.
“Allah Ya saka mata da aljannah.”
Mama ta gyada kai
“Ameen.”
“Yanzu ki je ki yi karatunki, Allah Ya ba ki sa’a.”
“Ameen.”
Saudat ta ɗauki jakarta, ta i musu sallama daga haka ta fita
A makaranta…
Students na ta shigowa ɗaya bayan ɗaya, wasu una hira, wasu suna sauri zuwa lecture hall, wasu kuma suna zaune ƙarƙashin bishiyoyi
Saudat ta shiga campus tana tafiya cikin nutsuwa.
Sai dai…
Yau ba kamar kullum ba. Mutane da dama na waigowa suna kallonta, not like before data zama kamar ghost
Ita kuwa…
Sai ta ƙara gyara veil dinta cikin jin kunya
A can parking lot… Zahra ta faka motarta, ta ɗauki handbag ɗinta, ta fito
Da zarar ta shiga faculty…
Sai idanunta suka sauka kan wata da ke tsaye tare da Firdausi da Asiya.
Ta tsaya cak
Murmushi ya mamaye fuskarta
“Saudaty!” Ta kira da ƙarfi
Saudat ta waigo.
Da idanunta suka sauka kan Zahra…Ita ma ta yi murmushi
Zahra ta ƙarasa da sauri, ta tsaya tana kallonta daga sama har ƙasa
Sai ta haɗe hannayenta.
“Woooow.Look at you, I like ur Abaya, zan saya irinsa gaskiya dan yayi min kyau”
Saudat ta yi ƙasa da kai saboda kunya
Zahra ta girgiza kai
“Wallahi kayan sun yi miki kyau sosai.”
Firdausi ta yi dariya.
“Ni ma, daga nesa ban gane Saudat ba.”
Aasiya ta gyada kai
“Wallahi ta canza.”
Saudat ta yi murmushi tana jin kunya. Idanunta suka koma kan Zahra.
“Me za ki ce min? Na ce miki ai, ke kyakkyawa ce.”
Saudat ta yi murmushi, ba don kayan da ke jikinta ba.
Sai don ta ji akwai mutanen da suke ganin darajarta fiye da yadda ita kanta take ganin kanta.
Zahra kuwa…
Ta ci gaba da kallon ƙawarta cikin farin ciki. Kamar ita ce ta saka kayan.
Domin babu abin da ya fi faranta mata rai…
Kamar ganin murmushi ya a kan fuskar Saudat….
Lecture ɗinsu na farko ya ƙare kusan lokacin azahar ne, da lecturer ya fita…
Students suka fara ficewa daga hall ɗin, wasu library, wasu cafeteria, wasu kuma kai tsaye masallaci
Zahra ta rufe notebook ɗinta, ta saka shi cikin handbag, ta kalli ƙawayenta.
“Mu je sallah.”
“Let’s go.”
Duk suka nufi masallacin mata..
Bayan sun yi alwala.. suka shiga mallaci suka yi sallar Azahar cikin nutsuwa
Bayan an idar…
Zahra ta zauna na ɗan lokaci tana addu’a Saudat na gefenta.
Firdausi da Asiya kuma na ɗayan gefen, da suka gama… Suka fito daga masallacin a hankali
Iskar rana na kaɗawa
Students na ta wucewa suna hira.
Firdausi ta sauke ajiyar zuciya
“Wallahi ni kam na gaji.”
Aasiya ta yi dariya.
“Da me kuma?”
Firdausi ta ɗan taɓe baki.
“Mama ta ce na dawo hostel kawai, ta ce ta gaji da cacan ƙudin mota.”
Asiya ta yi dariya.
“Ni ma fa jiya Baba ya tambaye ni… ‘Ke ba ku da hostel ne?’”
Duk suka yi dariya.
Zahra ta kalli su.
“Toh…Idan duk za ku dawo hostel Ni ma zan dawo.”
Firdausi ta tsaya cak.
“Da gaske?”
Zahra ta gyada kai.
“Eh mana, ba zaku bar ni Ni kaɗai ba.”
Sai ta juya ta kalli Saudat
“Ke fa? Mama za ta barki?”
Saudat ta yi murmushi
“Eh Na taɓa yi mata maganar.”
“Ta ce idan na samu kuɗi kuma na ga ya dace… ba ta da matsala.”
Firdausi ta tafa hannu
“Perfect.”
Asiya ta yi dariya.
“Shi kenan, zamu haɗe abun mu”
Zahra ta gyada kai
“Da yamma zan yi wa Abbah magana. Na san ba zai hana ni ba.”
“Allah Ya sa.”
Firdausi ta faɗa cikin farin ciki.
Can kuma Zahra ta ce,
“Come on! Mu je cafeteria, uunwa nake ji.”
Asiya ta yi dariya
“Ni ma.”
Cafeteria ɗin faculty ɗinsu cike yake da ɗalibai
Wajan ya gama gaurewa da aroma
Daga shigarsu Idanu suka dawo kansu, wasu suka gaisa da Zahra.
Wasu kuma idan suka hada ido sai su mata mutmushi
Suka samu wani tebur a gefe, suka zauna
Firdausi ta ɗauki menu.
“Toh Madam Zahra. Me za ki siya mana yau?”
Zahra ta yi dariya
“Ke dai kullum ni.”
Firdausi ta ɗaga kafaɗa
“Ke ce mai mota, ke ce kuma mai kuɗi, ashe ba ke za ki biya ba?”
Duk suka yi dariya.
Zahra ta girgiza kai
“Okay! Order whatever you want.”
Firdausi ta yi wata irin dariya
“Na san za ki faɗi haka.”
Asiya ta ce,
“Ni fried rice da chicken.”
Firdausi ta ce,
“Ni jollof rice da chicken “
Saudat kuwa ta yi shiru.
Zahra ta lura, ta kalleta.
“Ke fa?”
Saudat ta yi murmushi.
“Ko ruwa ma ya isa.”
Firdausi ta buga hannunta.
“Ke fah ki daina wannan halin.”
Zahra ta kalli Saudat da ido mai nuna rashin Jin dadi
“Saudaty! Order what you want.”
Saudat ta ɗan yi shiru. Sai ta ce a hankali,
“Toh… Fried rice da chicken.”
Zahra ta yi murmushi cikin gamsuwa
“That’s my girl.”
Bayan ɗan lokaci
Waiter ya kawo musu abincin, aka jera plates huɗu.
Drinks da bottled water.
Firdausi ta ɗauki spoon
Ta ce,
“Wallahi idan hostel ya haɗa mu…Faculty ɗin nan za ta sha labari.”
Asiya ta yi dariya.
“Musamman idan Zahra na tare da mu.”
Zahra ta ɗaga gira.
“Me ya sa?”
Firdausi ta ce cikin wasa
“Saboda ke ce za ki riƙa feeding ɗinmu.”
Nan take… Duk teburin ya kaure da dariya, har Saudat…
Wadda a baya ba kasafai take yin dariya da ƙarfi ba…
Sai da ta riƙe cikinta tana dariya.
Zahra ta kalle ta cikin farin ciki. A zuciyarta ta ce,
“Alhamdulillah…”
Suka fara cin abinci cikin nutsuwa
Firdausi ce ta fi kowa surutu.
Asiya na biye mata da dariya.
Saudat kuwa yau ta fi kowace rana sakin jiki a cikinsu
Bayan da suka gama cin abincin…Waiter ya zo ya kwashe plates ɗin.
Zahra ta ciro wayarta daga handbag, ta kunna data
Nan take notifications suka fara shigowa.
Course rep taga yayi sending message, ta shiga class group ɗin
Daidai lokacin wani sabon saƙo ya shigo
Course Rep:
“Attention everyone, all afternoon lectures have been cancelled due to an emergency meeting involving the lecturers. Students are advised to return to their hostels or homes. Thank you.”
Zahra ta sake karantawa don tabbatarwa. Sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
Ta ɗaga kai, ta kalli ƙawayenta
“Guess what?”
Firdausi ta yi saurin cewa,
“Abbah ya ce ki kai mu shopping.”
Aasiya ta girgiza kai tana dariya
“Wataƙila result ɗin assignment ya fito.”
Saudat ta ce
“Ko an canja venue lecture.”
Firdausi ta ƙara cewa,
“Ko kuma yau za ki biya da mu ki saya mana ice cream.”
Zahra ta yi dariya, ta girgiza kai
“Nope.”
Ta ɗauki handbag ɗinta, ta rataya a kafaɗarta, sannan ta miƙe tsaye
“Afternoon lectures…”
“…have been cancelled.”
Ta fada tana murmushi
“Whattttt?!” Firdausi ta yi tsalle
“Da gaske?”
Zahra ta juya wayarta ta nuna musu saƙon.
Asiya ta karanta.
“Innalillahi, wallahi da gaske ne”
Saudat ta yi murmushi
“Alhamdulillah, dama I’m tired”
Firdausi ta tafa hannu
“Best news of the day” Ta yi dariya tana ɗaukar jakarta.
“Allah ya albarkaci Course Rep.”
Aasiya ta buga mata kafaɗa
“Ke ma dai.”
Duk suka yi dariya.
Zahra ta saka wayarta cikin handbag.
“Come on! Mu tafi.”
Suka fito daga cafeteria tare
Suna tafiya a harabar makarantar cikin hira da dariya.
Students ma da dama suna ta duba wayoyinsu.
Wasu kuma suna murna bayan sun ga irin wannan saƙon.
Harabar makarantar ta fara watsewa a hankali…
Saboda kusan kowa ya fara shirin komawa gida ko hostel, yayin da Zahra da ƙawayenta ke tafiya tare, kowacce na ba da shawarar abin da za su yi da wannan lokacin da suka samu ba zato ba tsammani.
500 ne, a biya ta wannann acc din 7084571222, Hauwa Jibrin Opay
Shaidar biya ta wannan 08110615256_ Hauwajay writes
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.