Best / Popular Hausa Novels

Farashin Izzah Littafi Na 1 Compplete Hausa Novel

Reading file: FARASHIN IZZAH- Hauwajay, -1semi cmplt.docx

Chapter 38 of 59

Shafin ya ɗauki wasu daƙiƙu kafin ya buɗe.

Sai…

Idanunta suka fara sauka a hankali.

English Language A1, Ta yi shiru

Mathematics A1.

Hannunta ya fara rawa, ta ci gaba.

Biology A1, Chemistry A1

Har zuwa ƙarshe…

Nine Subjects… Nine Distinctions.

“Allahu Akbar…”

Shi kaɗai ta iya furtawa, sai ga hawaye sun fara tsintiri a fuskanta

Abbah da Ya Umar suka shigo saboda jin shirun da ya yi tsawo

“Baby?”

Abbah ya kira.

Ta juya, Idanunta cike da hawaye, ba ta iya magana ba, sai ta miƙa masa laptop ɗin.

Ya karɓa, ya fara dubawa

Lokaci guda murmushi ya cika fuskarsa.

“My daughter… you did it”

Ya rungume ta.

Ya Umar ya karɓi laptop ɗin.

Da ya gani…

Sai ya yi wata irin ihu.

“Nine A1! Baby ta kashe su!”

Dawowa Parlourn suka yi, Duk fuskokinsu dauke da murmushi

Anty Binta har gudu ta yi zuwa kitchen.

“Hajiya! Zahra ta samu Nine A1!”

Mami ta fito da sauri, ganin fuskokinsu kadai ya isa ya sanar mata,

Sai ta rungume Zahra.

“Ma shaa Allah Baby”

Mummy dake tsaye daga sama tana kallonsu, ta taɓe baki.

“Hmm!! Da alama yau ma gidan nan ba za a kwana lafiya ba”

Batoul ta yi murmushin gefen baki.

“Dama ai… Princess ce fah, ko kin manta ne?”

Abbah ya ɗago ya kalle su.

Sai dai bai ce musu komai ba

Maimakon haka…

Ya juya ya kalli Zahra.

“My Baby dole na miki kyauta.”

Ta yi murmushi

“Wace irin kyauta?”

Ya girgiza kai

“Not now! Amma kafin hakan…”

“Ina son ki je ki yi weekend a gidan Uncle Moh”

Ta haɗe gira

“Weekend?”

“Eh Ki je ki huta, kin cancanci hutun.”

Ta yi dariya

“Toh Abbah.”

Juma’a da safe…

Tun bayan ta idar da sallarta, Zahra ta fara shiryawa.

Ba ta yi wani kwalliya mai yawa ba

Doguwar abaya ce mai launin light purple ta saka, haɗe da veil dinsa purple color mai laushi. Sneakers purple ta sanya a ƙafarta, handbag ɗinta kuma ta rataya a kafaɗa

Da ta sauko ƙasa…

Ta tarar da Abbah, Mami da Ya Umar suna kammala breakfast

Mami ta ɗaga kai ta kalleta

“Kin shirya kenan?”

Ta gyada kai tana murmushi

“Na shirya.”

Abbah ya ce,

“Weekend kawai, that’s kwana biyu kawai fa.”

Ta yi dariya

“Abbah kamar zan yi wata ɗaya”

Ya Umar ya taɓe baki.

“Da kin san Uncle Moh, sai ya ƙi sako ki ki dawowa.”

Dariya suka yi gaba ɗaya.

Mami ta miƙa mata wata ƙaramar basket

“Na saka miki wasu fruits da snacks a ciki, ki bawa Anty Maryam na Babban roban

Ta karɓa

“Na gode, Mami” Ta rungume ta

Sannan ta nufi Abbah

Ta rungume shi kamar yadda ta saba.

“Allah ya kiyaye hanya.” Ya ce

“Ameen.”

Ya shafa kanta

“Ki gaida Uncle Moh da Aunty Maryam.”

“In shaa Allah.”

Ya Umar ya ɗauki ƙaramar travelling bag ɗinta

“Mu tafi, Baby.”

Bayan kusan mintuna arba’in da biyar suna tafiya…

Motar ta tsaya a gaban wani katafaren gida, ba shi da irin girman gidan Abbah…

Sai dai yana da wani irin tsari da nutsuwa. Flowers masu kyau sun zagaye compound ɗin.

Da motar ta shiga…

Mai gadi ya yi saurin buɗe musu

Parking yayi, tun kafin su shiga ciki…

Ƙofar parlour aka buɗe

Wata mata fara ce mai cike da fara’a ta fito da sauri.

“Zahra!” Ta yi ihu.

Zahra ma ta fashe da dariya

“Aunty Maryam!”

Da gudu ta ƙarasa ta rungume ta.

Aunty Maryam ta sumbaci goshinta.

“Allah! Kin ƙara kyau, Daughter”

Ta yi dariya

“Aunty… Kullum haka kike faɗa fah

“Kuma kullum gaskiya nake yi” Anty Maryam ta bata amsa

Karasa cikin parlon suka yi… daga ciki kuma wani mutum mai matsakaicin tsufa ya fito yana dariya.

“Toh wai ni fa? Ni ba za a rungume ni ba?”

Da jin muryarsa… Zahra ta saki Aunty Maryam

“Uncle Moh!” Da gudu ta nufe shi, ta rungume shi

Shi ma ya rungume ta yana dariya.

“My princess! How are you?”

“I’m fine, Uncle.”

“Ya Abbah?” Ya tambaya

“He’s fine.” Ta basa amsa

Ya Umar ya yi sallama, ya shiga yana gaishe su da ladabi

Uncle Moh ya rungume shi shima

“Umar tuzuru, gaskiya aurar da Kai zamu yi tunda kaki fito da Mata”

Murmushi kawai Ya Umar yayi, Uncle Moh ya ce

“Sai Yau zaka zo?”

Ya yi murmushi

“Work, Uncle.”

“IKLIMATYYYYYY!”

Zahra ta yi wata irin ƙara

Wata kyakkyawar budurwa mai kusan shekarunta ta fito da gudu daga staircase

Da ganin Zahra… ta yi ihu.

“ZAHRAAAAA!”

Dukansu suka yi gudu suka rungume juna, suna dariya, suna tsalle

Aunty Maryam ta riƙe hab’a

“Waɗannan yaran ko Yaushe zasu girma oho “

Iklima ta riƙe hannun Zahra

“Wallahi na yi missing ɗinki.”

“Nima” ta fad’a

Sai kuma wata murya ta fito daga sama

“Hmm… Ni kuma fa?”

Zahra ta ɗaga kai, jin Muryan Ya Imran ne

Ta ga wani dogon saurayi cikin farin T-shirt da black joggers yana saukowa staircase, da zarar ta gan shi… ta yi murmushi

“Ya Ims!”

Shi ma ya yi murmushi.

“Baby Zahra.”

Da ya ƙaraso wajensu… Ya buɗe hannuwansa

Ta rungume shi, ya ɗan bubbuga bayanta.

“Kin manta da mu.”

Ta taɓe baki

“Exams ne fa.”

Ya yi dariya

“Excuses kullum haka kike

Sai kuma idonsa ya fada kan na Ya Umar dake kallonsa fuskansa cike da murmushi ya ce…..

#Farashin izzah

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.