Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 53
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Daga kan sawunsa take kallonsa har zuwa sama murya a sarƙafe da rawan sanyi tace.
“To me zan kiraka?â€. Yana gyara jacket É—in sa yace. “Baki san sunan da ubana ya raÉ—a min bane da zaki tambayeni me zaki kiraki, ko Mahmoud É—in sunanki ne? Ba nawa baâ€. Yayi magnar yana kallon gashin kanta dake zube kan kafaÉ—unta, kai ta sunkuyar ta tura baki tace. "Salla zan yi kuma ba hijabiâ€. Ko ta inda take bai kalla ba ya juya ya fita. Cikin sanyi ta koma bakin gadon, 3 quarter T-shirt É—in da ya bata, ta zura, gaban dressing mirror shi ta tsaya tana mai sauÆ™e numfashi saboda sassayan kanshi da kekkyawan É—akin nasa keyi wanda sai yanzu ma take iya fahimtar tsarin É—akin dan yadda ta shigo a gigice jiya bata fahimci komai ba, É—an roban da taga set É—in kum da mayykan gashisa ta jawo, taje kan tayi ta shafa manshi ta fesa turaren gashinsa sannan ta tubÆ™e gashin ta kitse jelarba ta naÉ—e.
Manshi ta É—an shafa dan rage sanyi sai kuma turarensa data fesa.
Wordrobe ta buɗe a hankali tanayi tana kallon ƙofar shigowa, hmmmm ta faɗa a fili tana mai kallon tsarin kimtsa kayan sa dake cike cib kai kace a ƙasar yake da zama din-din-dim ba zuwa yake yi ba, komai yana gefensa ido ta tsaida kan step ɗin da Socks, gloves, Scarf, caps ne kawai zalla a wurin kala da ban da ban, hulunan saƙar ulun dake wurin ta fara ɗagawa a hankali ta dauke maroom mai ɗan tambarin M a sama goshin, kai ta jinjina ganin yadda hular ta zauna cib a kanta ta ɓoye duk himilin gashin kanta da kunnenta, Scarf ta ɗauka mai ɗan girma shima maroon color ta naɗe wuyanta cib, sai kuma ta zaro Socks inrin dogayen nan farare ta saka, tsawonsu yasa suka rufe duk Gwari ta gloves ta saka a hannunta, sai kuma ta kalli kanta a jikin madumin jikin Wordrobe ɗin duk jikinta a suturce yake, sai dai 3 quarter ɗin da ya ɗan kamata sosai musamman cinyanta da mazaunenen ta. A hankali ta dawo kan salla cikin rashin gamsuwa da suturar a dole ta kabbarta sallah.
Koda ta idar zama tayi a wurin tayi Azkarul Sabah, kusan ƙarfe 8 ta koma kan gadon ta kwanta tana mai lumshe idanta lokacin ɗaya baccin da firgici da tsoro ya hanatayi a daren jiyan ya kwasheta.
Ƙarfe biyu dai-dai ya farka dan kiran Salim daya addabeshi.
“Bacci kake yi neâ€. Yana zuge zip É—in jacket É—insa yace.
“Ban sani baâ€. Yayi magnar yana kallon Æ™irjinsa tabbas fatar jikinta ya É—an manne da nashi cikin sauke numfashi yake shafawa cikin son tabbatarwa jin ba komai.
Numfashi ya ɗan sauƙe dan sanin yadda fatar jikinsa keyi in dai fatar wani ya taɓashi jin ba ƙaiƙayin ba kuma ƙarajen kuma baiyi jaba ne yasashi janye idonsa yana tuna wannan shine karo na biyu kenan jin Salim na faɗin.
“To ga Abba in ma ni bazakayi magna baâ€.
Gyara zamansa yayi yace. “Abba Barka da safiyaâ€. Abba yace.
“Barka da rana dai ko Mahmoudu ya jikin naka da sauÆ™i sosai koâ€. Cikin tabbatarwa yace.
“Alhamdulillah da sauÆ™i sosai Abba kar kace zaka zofaâ€. Cikin gamsuwa yace.
“To Alhamdulillah haka dai Saleh yace min É—azu da safe yaje kun koma kunga Doctor yace ba komai sun Æ™arasa ma alluranka. Ina iyalintaka da yarankuâ€. Yana meda zip É—insa yace.
"Suna gidan Yah Saleh wurin Sajidaâ€. Bayan sunyi sallama ne yayi al'wala ya fito yayi salla a parlour.
Kan sallayar ya jawo system nashi ya fara É—an aikin da ba'a rasa ba, kai ya jinjina cikin gamsuwa ganin tuni kamfanonin da ya bawa aikin kayansu sun gama komai har wasu sun fara loda kayan cikin tirelolin dan kai kayan bakin teku yanayi yana É—an shafa.
kekkyawan farin karensa da ke gefen yana kaÉ—an jela.
A hankali ta miƙe tsaye bayan ta idar da sallan la'asar da ta haɗa da azahar data wuceta tayi ƙasarunta, cikinta ta ɗan shafa dan yunwar da taji na murɗarta rabonta da abinci tun jiya da safe a hotel.
Ta buɗe ƙofar ɗakin ta ɗan leƙo kai corridorn da yake cike da haske da sheƙin gyara sai kamshi da sanyin da yafi na jiya dake busowa, cikin ɗan ƙara leƙowa saboda tsoron cin karo da karen tace.
“Appiy! Appiyâ€. Kanshi ya É—ago yana mai rufe system nashi da tattara wayarsa da ta Yah Amin da tata wayar data wurgar garin gudu ya zurasu cikin briefcase É—insa. Igiyar jikin Chain É—in dake wuyan karen ya riÆ™e ya rataya briefcase É—in ya nufi hanyar fita yana faÉ—in.
“Ke ki fitomin a É—aki, kizo ki koma inda kika fito É—akina ba mazauninki baneâ€.
Da sauri tace.
“Ina tsoron karenkaâ€. Da sauri ta fito jin yadda ya mata magna a faÉ—ace.
“Yana hannuna in baki fitoba zan sako miki shi ya fito min dake waje, ance miki É—akina matattaran aljanuneâ€. Cikin taka tsantsan da ware ido take taku har ta fito parlour, ganin baya cikine yasa tayi saurin fitowa waje.
Da sauri ta koma da baya ganinsa tsaye shida Arda da Yah Saleh Mahmoud ɗin na riƙe da Ketra yana ta zirga-zirga a tsakaninsu, ganin yana riƙe da shine yasa tayi saurin raɓawa gefe can ta wuce da sassarfa ta nufi gidan Yah Saleh.
A parlour ta samesu kasan cewar yau ba makaranta su Imran na gida, Zaid da Zaitoon sai wasansu sukeyi a tsakanin su Sajida da su Iman. Numfashi ta fesar a hankali saboda É—umin parlour ya fara kore mata sanyin waje data É—ebo, Sajida ne ta matso kusa da ita tana jawo hannun su Zaid tace.
"Zaid ga Amminkuâ€. ko kallonta basuyi ba gwara Zaitoon ta É—anyi dariya ta rufe ido.
Aunty Maryam da Iman taje ta kirane ta fito Amira na biye da ita a baya.
Dai-dai lokacin Yah Saleh ya shigo Mahmoud na biye dashi a baya da Ketra, da gudu Imran ya rungumo karen ya fara shafa shi, ita kuwa Fariyda cikin rawan jiki ta koma can bayan kujerar Aunty Maryam tana karya kai murya a sanyaye tace.
"Appiy kallona yake yi faâ€. Igiyar ya miÆ™awa Imran sai kuma ya kalli Zaid dake ta shafa karen Zaitoon kuwa da gudu ta maÆ™ale Sajida tana nuna Ketra ganin haka ne yace.
"Imran maidashi wurin Ardaâ€. Cikin jin dadi kuwa ya nufi waje riÆ™e da igiyar yana kuma kiran Zaid.
suna fita ta dawo tsakiyar parlour ta gaida Yah Saleh dake murmushi da faÉ—in.
“Har yanzu baki dena tsoron Ketra baâ€. Mahmoud na É—an kallonta ta gefen ido a ranshi yace.
"Hmmm yarinyar da harda suma dan tsoron tsiyaâ€. Maryam ne ta É“e baki tana kallon Mahmoud É—in da ko inda take bai kalla ba bare ya gaisheta, sai Sajida daya miÆ™awa hannu alamun ta miÆ™o mashi Zaitoon, yana amsarta yace.
"Kin basu abinciâ€. Da sauri tace. “Eh Yah Mahmoud sunci sun Æ™oshiâ€. A daÆ™ile Aunty Maryam tace.
“Ni na É—auka ai suma bazasuci abincin gidanmu baâ€. Da sauri Sajida tace. “Ai su da guzurinsu suka zo ko ruwan gidana ban musu amfani da shiba ba abinda babu a babybag É—insuâ€.
Fariyda dake gaidata a karo na biyu ta kalla a yatsine tace.
“lauâ€. Yana kallon Yah Saleh yace.
“Bari mujeâ€. Cikin kulawa yace. “Bakuyi breakfast ba gashi har lokacin yin lunch ma ya wuce. Maryam ki kawo musu abinciâ€. Baki ya taÉ“e tare da jujjuya kai yace.
“Bazan cibaâ€. Da sauri Yah Saleh yace. “Ki kawowa Fariyda ita ai zataciâ€. A faÉ—ace tace. “Ita ba mace bace ba daga gidan mijinta ta fitoba, nifa na gayama ba abinda zan basu, ta iya aure wa in ya mutu ta aure Æ™ani, amman bazata iya bashi abinda zaiciba da wanda zataci, ni ba su Ummi bane da zan Æ™are a kanta kamar yadda Ummi da Abba suka ga zasu iya su Æ´aÆ´ansu duk ita suka haifawaâ€. Wani kallon da yayi matane yasa ta haÉ—iye rogowar maganar.
“Mu tafiâ€. Ya faÉ—a yana kallon Fariyda da idanta ya cika da Æ™walla.
“Mu tafiâ€. Ya kuma faÉ—a yana kallonta, a hankali ta miÆ™e tsaye ta bi bayansa.
Binsu Yah Saleh da Sajida sukayi har waje, motarsa suka samu a waje Arda ya fito da ita, key ɗin ya karɓa ya kwantar da Zaitoon a baya inda Sajida ta ajiye bag dinsu, Zaid dake ta wasa da Ketra Fariyda tace Arda ya miƙo mata, a baya ta sashi bayan Imran da Iman sun rungumeshi Iman tace.
“Aunty yaushe zaku dawoâ€. Tana É—an shafa kanta tace. “Anjima kaÉ—an zamu dawoâ€. Sai kuma ta É—an rungume Sajida tace.
"Goggo Sajida mun gode babys naki zasuyi missing dinkiâ€. Tana murmushi tace.
“Nima na kusa zuwa Nigeria in sha Allahâ€. Hannu Yah Saleh ya miÆ™a masa yace.
“Sai ka juyoâ€.
Kai ya jinjina mishi kana ya shiga.
Ganin ya shiga motane, itama ta shiga gaba.
Tuƙi yakeyi cikin nitsuwa da sanin kan garin, tunda ta shigo bai kalli ko ta inda takeba, itama gefe ta rakuɓe ta haɗe jikinta wurin ɗaya saboda jarabebben sanyin garin da ya buwaye ta, ta mirror ya kalli su Zaid da suke wasa.
gaban motar kawai take kallo yadda garin yayi luf alamun ana iya fara Snow ako wanne lokacin.
Kusan tafiyar 38 minutes sukayi, sannan yayi parking a wani kekkyawan eatiry na alfarma, Hanzade Terrace. daga motocin dake parking space ɗin nasu kasan wurine na hamshaƙan mutane.
Su Zaid ya ɗauka ba tare da yace mata ko ƙala ba, ya juya ya nufi ciki, murɗawar da cikinta yayi shi ya sata yi masa biyayyar dole ta fito tabi bayansa tana ƙanƙame jikinta. A hankali suke taka upstairs ɗin.
Hammm taja numfashi mai tafe da rawan lips sabida sanyin garin
Wurine na alfarma dake bakin teku daga sama kana hango tekun dake shimfiɗe a ƙasa, wanda glass ne yayi musu Garkuwa tsakaninsu da ruwan sai flowers masu kyau da aka zageye wurin dasu sai yan tables masu kyau wasu da kujeru huɗu wasu biyu, inda ya zauna ta ƙaraso ta zauna tana gyara Scarf dinta tare da haɗe hannunta duka a ƙirji manu ɗinsu ya jawo yana dubawa, ɗaya daga cikin ma'aikatansu da yazone ya faɗawa abinda yakeso da abinda su Zaid zasuci.
Tambayar ta abinda take buƙatane yasa tayi saurin cewa.
“Coffeeâ€. Duk da azabar yunwar da takeji ta zaÉ“i coffee ne saboda sanyin daya gigitata ya fara sata Æ™arÆ™arwa, baki ya taÉ“e yana dannan wayarsa.
Su Zaid ya fara bawa abinci saida suka ƙoshi ya goge musu baki sannan ya gyara zamansa ya fara cin abinda suka kawo mishi. Flacks ɗin coffee ta buɗe a karo na uku ta sa a ɗan ƙaramin mug ɗin da baya wuce kurɓa biyar, zuƙeshi tayi tana mai ɗan jin rawan sanyin da lips ɗin ta keyi na raguwa, sau huɗu tasha kana ta gyara zamanta tana mai longwaɓar da kai tace.
“Ayyah zan tafi cikin mota sanyi kamar zai kasheniâ€. Tayi mgnar tana É—aukan Zaid da shima yake takure duk da Sweater dake cikinsa.
Zaitoon kuwa yar son sanyi harkokinta takeyi daga nan zuwa can. Car key É—in ya ajiye a kan table É—in ta É—auka da sauri ta juya ta fita.
Kusan 42 minute tayi a zaune kafin ya fito tuni magrib ta ƙarato, daga nan Homey Airport hotel ɗin suka wuce tafiyar 26 minute suka isa.
Suna shiga ta sauƙe Zaid kan babban gadon, shi kuma bathroom ya wuce al'wala yayi yana fita ya nufi ƙofar ɗakin a hankali tace.
“Tafiya zakayi ne?â€. Tsayawa yayi ba tare da ya fitaba kuma bai tankanata ba tana É—an kallonsa tace.
“Ina zaka je?â€. Tayi tambayar dan son cemasan ta manta wayarta a gidansa.
“inda kika aikeniâ€. Ya bata amsa tare da fita.
A hankali ta sauƙe numfashi tana mai jin sauƙin sanyin saboda ɗumin ɗakin.
Wanka tayi da ruwa mai ɗan karen zafi haɗi da al'wala tana fitowa ta kimtsa cikin tattausar Turkish jallabiya mai sulɓi da ɗumin gaske, turarenta mai sanyin ƙamshin ta fesa, tana zura ɗan hijjab ɗin jallabiyar ya shigo riƙe da sallaya da briefcase ɗinsa.
Yana shimfiÉ—a sallaya ya kabbarta sallan magrib da tuni ana ta kiran salla, Itama gefenshi ta koma ta kabbarta sallah.
Bayan sun idar ne, ta miƙe ta gyarawa su Zaid kwanciya dan tuni sunyi bacci.
Shi kuwa waya yake yi da Sulaiman dake tambayarsa ya jiki da kuma abinda ya shafi kasuwancinsu.
Koda suka gama waya isha tayi. Bayan ya idar ne ya jawo pillow yasa akan tattausan sallayarsa daya shimfiÉ—a kan Turkesh carpert É—insu mai masifar laushi gaske, É—an kishin giÉ—a yayi ta sa system nashi a gaba yana aiki da Yah Ahmad ya tura masa.
A hankali tace.
"Appiy wayata na bari aâ€. Cikin tsareta da ido da takaicin umarnin da Abba ya bashi na cewa kar ya sake kwana shi kaÉ—ai saboda jikinsa ya kwana da ita, ganin yadda ta addabi rayuwarsa daren jiya akan kare harda suma ta kwana iface-iface ta hanasa bacci ne yasa dole ya taho nan É—in da shirin kwana.
“Appiyâ€. Ta kuma kiransa cikin sanyi. A daÆ™ile yace.
"Kika sake cemin Appiy sai na baki marin da zai makantakiâ€. A hankali tace. “To ince ma Mudyâ€.
Wani irin kallon takaici ya watsa mata a kufule yace.
“Nine ma Mudy, Mudy to ma a gidan uwar wa kika samo wannan sunan zaki labta min shi Mudy me Mudyâ€.
Cikin sanyi tace.
"To incema Papi?â€. Wani irin juyowa yayi ya mata kallon da bata taÉ“a ganin makamancinsa ba a rayuwarta, rawa lips É—inshi suka farayi kamar maijin sanyi yana nunata da yatsarsan ido cike da yanayin da yafi kama da nadama sai kuma kawai yayi Æ™asa da kanshi
“Ina son magna da Mamy nane kuma wayata na canâ€. Wayarta ya zato ya cilla mata kan gadon.
Ya maida kanshi yaci gaba da abinda yake yi.
Da sauri ta É—aga kanta ganin ya kashe wutan É—akin duhu ya mamaye É—akin. Kwanciya yayi kan sallayar ya lumshe idanunsa saboda baccin da ya fara fizgarsa.
Voice É—in da Mami tayi mata ta bata amsa kana ta ji na Aunty Saddiqa sai na Amina sai Zainab, É—an gajeren tsaki taja ta juyawa gefen hagu sai ta kuma juyowa dama, hannunta ta É—aura kan cikinta da yake É—akale kamar ba hanji É—an coffee É—in da tasha fitsari É—aya da tayi ya tafi.
Zama tayi a tsakiyar gadon tana É—an tunanin cikin É—akin ba wani abu na ci haka ne yasa ta É—an kwaÉ“e fuska, sai kuma ta kwanta 2 minute tsakani ta tashi zaune, saboda murÉ—ar yunwa tun jiya da safe. Cikin rawan murya tace. “Appiyâ€.. Shiru bai amsa ba baiyi masifa ba shi yasa ta Æ™ara cewa.
“Appiy!â€. Cikin baccin yaji muryarta dan ta sunkuyo ta inda yake kwance a Æ™asan. “Appiy yunwa nakeji cikina ciwoâ€.
Da sauri ta dawo tsakiyar gadon jin ya buge hannunta da ta kai da niyar tadashi hasken wayarsa ya kunna tare da cewa.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.