Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 49
Washe gari da safe waya take yi da Ummi,
Murmushin Ummi tayi tana kallon jikokin nata.
“Fariyda ina Appiy nasu suke ta kiransa, ni yau kwana uku kenan banyi magna da shibaâ€. Cikin mmki take kallon Ummi sai kuma ta É—an kalli akwatinsa zuciyar ta na harbawa tace.
"Ummi to ki kira layinsa mana, ya bar wayar Yah Amin É—in a parlour neâ€. Tana É—an kallon Amina data matso Ummi tace.
"Ai layinsa ma baya tafiya Fariydaâ€. Sai kuma tayi saurin kallon Amina da tace.
“Nima nayi ta kiransa baya shiga, kin san dama shi WhatsApp kuma yana daÉ—ewa bai leÆ™abaâ€. A hankali ta sauÆ™e nannauyan ajiyan zuciya cikin sanyi tace.
“Hummmmâ€. Daga nan bata iya Æ™ara cewa komai ba, baÆ™in da suka shigo Parlour Ummin ne yasa suka katse kiran.
Tunda ta idar da sallan magrib take zaune bisa sallayar yau dare na huɗu kenan da tafiyarsa. Zaid daya matso bakin gadon yana riƙo wuyanta da fadin Appiy. Appiy. Ammiy Appiy, Zaitoon dake kwance a ƙasa a gabanta itama ta kama Appiy. Cikin sanyi murya ido cike da tsoro tace.
"Na shiga uku naâ€. Wayarta ta jawo tare da kunna Wi-Fi Amina ta kira, cikin sa'a kuwa bugu É—aya ta É—aga. Fariyda ya daiâ€. Ta tambaya tana kallon yadda take ta kiciniya da yaran, da suke ta kuka da kiran Appiy, cikin sanyi tace. “Aunty Amina nifa ina jin tsoroâ€. Da sauri tace.
“Tsoro kuma Fariyda to ina Mahmoud É—inâ€. Kai ta sunkuyar tare da cewa.
“Yau kwana uku fa cib ban ganshi ba, gashi har yanzu bai dawoba kuma kunce bakwa samunsa a wayaâ€. Cikin tsaro Amina tace.
“Ban ganeba Fariyda kiyi min bayaniâ€. Cikin sanyi tace.
“FaÉ—a mukayi kuma ya fita yana kuka, har yanzu kuma bai dawoba, gasu Zaid nata min kuka suna kiransa, kuma bai dawoba yaumaâ€. Ta dire mgnar cikin rawan murya ido na cike da Æ™wallaâ€. Da sauri Amina tace.
“innalillahi bari in tambayi Abba ko sunyi waya dashi, dan har su Salim É—azu da suka zo É—aukan abinci sunce basa samunsa, ke kuma ki kira driver ku kiji ko akwai inda ya kaishiâ€. Daga nan ta katse kiran.
A parlour Abba ta samesu bisa alamu yanzu ya dawo sallan isha.
Ummi da Goggo Dada sai Sulaiman da tarin fufun goro a gefe da alamu na É—aurin auren Salim É—in ne gobe jumma'a. Shiru Abba yayi yana sauraron jawabin ta, kai ya jinjina cikin shiga tunani yace. Baban nawane yayi fushi ya bar gidan, yau kwana uku, hmmmm to lallai kuwa babban faÉ—ane da yafi duk faÉ—a da sukeyi, fushi har ya bar gidan ya bar su Zaidâ€. Cikin tsoro Goggo Dada tace.
"To me ya haÉ—asu?â€. Kai Amina ta jujjuya alamar bata sani ba.
Ummi kuwa ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tare da cewa.
“Lallai koma menene abu mai zafi ta gaya mishi ko tayi masa, irin zafinda bazai iya komaiba sai hawaye Mahmoud dai yayi hawaye kan abu lallai lamarin babbane kuma lamirine mai Æ™ara É“ata komai a cikin zamansu, abinda muke fata bazai taÉ“a samuwa ba, na san waye Mahmoud da irin zuciyarsa duk abinda ya sashi kuka to wlh ya barranta dashi kenanâ€. Da sauri Sulaiman dake ta gwada kiransa baya shaga yace.
"Ni matsalata ina yake wanne hali yake ciki? Gashi har yanzu layinsa baya tafiyaâ€. Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
“Kada ku damu, duk inda Mahmoud yake a doron duniya baya wuce adadin kwana uku duk rintsin halin da yake ciki zai nemeni zamuyi magna, in dai yau kwana uku kenan in sha Allah zuwa safiya zai kiraniâ€. Daga nan yace suje suyi harkokin gabansu.
Suna fita ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, alwalar kwanciya yayi tare da yin nafila kana ya ɗau Qur'ani ya fara bita.
Hasken da wayarsa keyi ne yasa yayi saurin kai ƙarshen suratul yaseen da yake, ya jawo wayar.
Ganin kiran Mahmoud yasashi amsa kiran da sauri, cikin sauƙe numfashi yake amsa gaisuwar Mahmoud ɗin da tambayar Ummi da Goggo Dada
Gyara zama Abba yayi saboda jin Mahmoud É—in yayi shiru, cikin sanyi yace.
"Babana kayi shiru, ko bacci kakejiâ€. Cikin sanyi yace
"A'a Abba ina jinkaâ€. Cikin fahimta irin ta uba da É—ansa da yayi gadon halinsa yace.
"Nima ina jinki?â€.Cikin sanyin muryar can Æ™asan maÆ™oshinsa yace.
“Abba tambaya ce nake so inyi kuma na rasa wanda zan tambaya, dama ace da Yah Amin na raye shi zan tambayaâ€. Cikin sauri da rauni Abba yace.
“Tambaye ni Mahmoud faÉ—i ina jinka duk abinda Aminullah zai maka fiye dashi zan maka aiâ€.
Cikin ƙoƙarin danne rawar da muryarsa keyi yace.
“Abba wai menene ke sa a cewa mutum nakasashshe wanda ba cikekken mutumâ€...........
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 45
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Numfashi mai nauyi Abba ya fesar saboda jin Mahmoud yayi shiru, alamun amsa yake jira, cikin tausasa lafazi yace.
“Nakasa tana nufin mutumin da wani sashi na gangar jikinsa yake da tawaya, kamar Æ™afa! hannu! ido! kunne!â€. Murya na rawa yace.
"Abba kuma duk mai wata makamanciyar wannan ba cikekken mutum baneâ€. Da sauri Abba ya fara girgiza kai kamar suna tare yace.
“A'a Mahmoud cikekken mutum ne mana, sai dai bashida cikakkiyar halitta shi yasa za'a iya kiransa da nakasa dan tauyeyyen halittar shiâ€. Zuwa yanzu muryarsa ta fara disashewa cikin rawan da muryar tasa take yace.
“Abba kenan nima nakasashshe ne, ban cika mutum ba, tunda naksata ma ai tafi ta hannu! da Æ™afa! da ido! da kunne! tafisu illa da nakasa rayuwar mutum, amman ai Abba bani na É—aurawa kaina ba ko? Allah ne ya É—aura min duk da nasan na saÉ“a masa da lafiyar da ya bani a baya na kasance maâ€. Cikin kamala Abba ya fara jujjuya kai yana faÉ—in.
"Kul Mahmoud kada kace komai, ka tsaya iya Allah ne ya É—aura maka, kuma jarabtace zaka kuma cinyeta in sha Allah, kada kace komai kayi haÆ™uri, shi Allah gafurun ne kuma rahimunneâ€. A hankali Ummi ta zauna gefen Abba kib dashi, fahimtar da Mahmoud yake mgna ne yasata sauÆ™e numfashi mai nauyi
Shi kuwa Mahmoud Da sauri ya fara magna cikin fizgo mgnar da rawan murya yace.
"Abba dan an min gorin banda lfy bazan haihuba ni ba cikekken mutum bane bazai sa in butul cewa Allah ba na godewa Allah a hakama da ya bani rai da lfy, Allah ne kaÉ—ai fa yasan adadin mutum nawane suka mutu a wannan iftila'in ni kuwa ya barni da rai da ji da gani da tafiya, kawai dan ya nakasa min sashin da rasashi ya zame min al'khairi ya hanani saÉ“a masa ai bazanyi kuka ko Æ™orafi ba. Matsalata É—aya ce da kuka Æ™i yarda da mgna ta, kuka bi ta Yah Amin da yafaÉ—a cikin zafin fitan rai kuka haÉ—ani da abinda zai iya sawa inji cewa Allah ya tauye min halitta taâ€. Cikin cushewar tunani Abba yace. “Mahmoud ka raunata min zuciya zaka sani hawaye, yanzu kana inaneâ€. A hankali yace.
“Kayi haÆ™uri Abba kada kayi min kuka, ina Kerala ne naje ganin Dr Avinashâ€. Cikin sanyi Abba yace.
"Yaushe zaka koma, dan hankalin Fariyda ya tashi itace ta gayawa Amina bata san inda kake ba, ga can su Zaid nata kuka da kiranka, tace baka gaya mata ina zakaje?â€.
Cikin danne zuciyarsa yace.
"Eh gobe zan je dan zan maida Zaid wurin Dr Imran Patel zai Æ™ara dubashiâ€. Cikin taussa lafazi Abba yace.
"Allah yayi maka al'barka, ya rufa maka asiri duniya da Æ™iyama, Allah ya raya maka yaranka yayi musu al'barkaâ€. A sanyaye yace Amin kana daga nan sukayi sallama.
Da sauri Ummi tace.
“Yana ina ne wai? Me yake gaya makaâ€. Cikin girma Abba yayi mata bayanin yadda sukayi dashi, A sanyaye tace.
“Yanzu dai na gama gamsuwa Mahmoud bai samu lfy ba, kuma bazai iya zaman aureba, tunda aka fara wannan ta Æ™addamar a tsakaninsu bamu da wata madogara a haÉ—asu zaman aureâ€.
Cikin karaya Abba yace.
"Shike nan ni kuma haka Allah ya Æ™addara min kan yarana. Allah na tuba ban butulce maba wanima bai taÉ“a haihuwar baâ€.
Ahmedabad.
Cikin sanyi take kallon Amina murya a sanyaye ido cike da hawaye tace.
“Driver yace min Airport ya kaishi Amman bai san jirgin ina ya shigaba, kuma shima tun ranar basu sake yin mgna da shibaâ€.
Shigowar Ummi É—akin Goggo Dada inda Amina ke zaune tace.
“Da Fariyda ne kuke mgnaâ€. Da sauri ta miÆ™a mata waya tare da cewa.
“Eh Ummi itace gata taÆ™i bacci ita kuka su Zaid kukaâ€.
Da sauri ta saki wani raunataccen kuka murya na rawa tace.
"Ummi ban san inda ya tafi ba, kuma har yanzu bai dawoba, gasu Zaid ma sunÆ™i bacci sai kuka sukeyi suna kiransa, ni kuma bansan inda yajeba, ba kowa sai ni dasu tsoro nakeji ban san ina zanje in nemoshi baâ€. Cikin mmki Ummin ke kallon yadda take sheshheÆ™an da zubda Æ™walla cikin murmushi tace.
“Ba komai Fariyda yanzu yayi waya da Abbanku, yana lfy ba abinda ya sameshi K...â€. maganarce ta maÆ™ale mata a maÆ™oshi jin sautin nannauyar ajiyar zuciya da Fariyda ta sauÆ™e ta lumshe idonta ta buÉ—e gami da cewa.
“Alhamdulillahâ€. Aminace tayi dariya gami da cewa.
“To sai a bar ni inyi bacci a lallaÉ“a min yara tunda anji labarin inda Habibi da'iman yakeâ€.
Baki ta taɓe tare da yin ƙasa da murya yadda Ummi da Goggo Dada da suka nufi parlour bazasu jiba tace.
“To ni me gamina dashi, yaje yayi ta yajinsa mana in yaga dama kar ya dawo ya jira ayi bikonsa, tunda yaji yayi, ni tausayin Ummi da Abba ne ya hanani nitsuwa Yah Amin ya tafi shima É—an bala'in sarkin faÉ—a ace babu shi ai zuciyar Umminmu zata tsaya, ga kuma su Zaid suna damuna da kiransa, in babushi zasu zama marayun gaske shiyasa hankalina ya tashi ina tsoron su rasashiâ€. Da sauri ta katse kiran jin Goggo Dada na cewa.
“Oh wato ke banda ke a damuwar rashinsaâ€.
Anan akan sallayar ta kwanta kusa da su Zaitoon da ta samu bacci yayi gaba dasu.
Kano
Washe gari da safe Ummi zaune dasu Mamy a parlour ta, Aunty Amarya ce tace.
"Mu ai tun jiyan mukaso zuwa, ganin dare yayine yasa muka haÆ™ura, to ta kira Saddiqa ita kuka su Zaitoon kuka wai kwana hudufa ba'a ga Mahmoud ba sannan kuma bakwa samunsa a waya, harda cewa wai kada ace ita ta batar dashiâ€. Dariya Amina tayi tare da cewa.
“Yoh in dai bai badda ita ba ai bata badda shi baâ€.
Nan dai sukayi yar hira kana Dr Nasir ya tafi dasu.
Ahmedabad
Harara ta liƙawa akwatinsa sai kuma ta ɗan jawoshi gabanta, buɗe zip ɗin tayi.
“Shmhummmâ€. Taja dogon numfashi sabida Æ™amshi turarensa daya buÉ—e mata hanci ido ta zuwa kayan saboda ganin zip box hawa-hawa a cikin akwatin da alamu komai da wurin zamansa, box na firÆ™o ta buÉ—e kaya baccinsa dake jere a ciki wanda suke a wanke a goge, É—agawa ta farayi a hankali tana ajiyewa kan kujera, wasu tattausan gajeren wondo da yar top É—insa mai guntun hannu nevy blue masu masifar kyau da taushi ta É—an ware tare da, sunsunarsu ta mannasu kan fuskarta Æ™amshinsu da laushinsu yasata warware su, a fili tace.
“Wlhi É—aukesu zanyi duk abinda zai faru ya faruâ€.
Sai kuma ta buɗe ɗaya zip box boxers ɗinsane da singlet ɗinsa suma wanke ƙal a goge sai dai su ƙamshisu ba irin na jikin kayan baccinsa bane, wani irin sassayan ƙamshine mai shiga zuciya sukeyi.
É—aya ta kuma buÉ—ewa glass's É—insa ne da agogonshi da ring sai car keys guda biyu. Da sauri ta buÉ—e na kusa dashi, turarukan sane da man shafawansa na jiki da kai kusan kala uku-uku, sai kum É—insa da suke cikin paket É—insu
gefenshi kaɗa taga ƙaramin box ta buɗe brush da Makilin ɗin one family na yayan strawberry. Sai sabulun guda uku da ba'a buɗeba komai masu masifar tsadar gaskene a ciki.
Manyan ta fara buÉ—ewa ganin kayan sawansa ne a ciki É—aya wondunan jeans ne na kansa rigunan É—aya kuma jompa ne guda biyu sai suit kusan uku, sai É—aya kuma 3 quarter ne a ciki da rigunansu, da pajamas fara maidawa tayi bayan ta cire turarukan nasa biyu ta bar mai É—aya.
“Mutum sai Æ™a'ida komai da Æ™a'idar wurin zamansaâ€. Rufe wa tayi gami da maidashi wurin zamansa.
Kan gado ta ajiye riga da wondon, da turarukan wanka ta shiga, tana fitowa tayi sallan azahar, mai kawai ta ɗan shafa ta gyara gashin kanta ta tubkeshi da ribbon ɗin ba ta kitse jelarba, ta fara saka kayan, murmushi mai sauti tayi lokacin da ta tsaya gaba dressing mirror, ganin yadda rigar tayi mata ruwa-ruwa sai wondon kuma da ya cika cib da hips ɗinta, wondon iya karsa guiwowinta, wuyan rigar da yayi mata sakayau da faɗin rigar ya taimaka wurin bayyana ƙirjinta dake tsaye, haka kuma yasata jinta so Comfortable sosai kayan suka mata daɗi a jikinta turarensa ta fesa a karo na uku dan ƙamshinsa da yake ƙara sata fesawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.