Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 38 of 49

*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
PAGE 78
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

"Alhamdulillah jikin ya lafa ma ko har ya samu yayi bacci ko Fariyda?”. Kai ta gyaɗawa Amina murya a diririce ta gaida Abba da Goggo Dada dake riƙe da Zaitoon , Zaid kuma na hannun Sadiq.
Ido Goggo Dada ta tsaida kan fatar idon Mahmoud É—in dake nuna ba bacci yake yi ba. Salim kuwa hannunsa dake kusa da na Mahmoud yasa ya É—an mareshi haÉ—i da cewa.
"Mahmoud tashi ga Abba”. Cikin ƙurewar girma da zargi mai haɗe da kokonto Abba yace.
"A'a barshi yayi baccinsa. Kai Sadiq ɗauki Fariyda ka maida ita gida kaga har munyi sallan magrib”.
Sai kuma ya juyo yana kallon Fariyda yace.
"Karɓi Zaitoon ɗin kuje ko Allah ya kiyaye hanya, Allah yayi miki al'barka”. Ido cike da kunya tace.
"Amin Ya Allah”. Daga nan ta juya ta fita kamar kazar da ƙwai ya fashewa.
Abba ya kalli Mahmoud sai kuma ya juyo kan Amina dake ajiye musu basket É—in abincin data kawo musu.
"Mu tafi ko Dada, Salim sai da safe Allah ya sauƙawa jiki”. Amin Salim yace, yana mai zama bakin gadon ya ɓoye ribbons ɗinta da yaga Goggo Dada ta zuba wa ido.
Bayan su Abban su tafi ne. A hankali ya miƙe zaune ba tare da ya buɗe idonsa ba, Aunty Amina ta matso bakin gadon cikin kulawa tace.
“Sannu Mahmoud ya jikin da sauƙi ko? ga abinci me zan sa maka, kaci sai kayi salla ko?”. Miƙewa tsaye yayi yana zura ƙafarsa cikin takalmansa, har lau idonsa a rufe numfashi mai tafe da waraka yayi haɗi da motsa lips ɗinshi kaɗan yace.
“Nifa na warke!”. Ido Salim ya zuba mishi cikin nazartar ganin alamomin warakar da ya faɗan a fili dan tunda suka zo bai tsaya shi kaɗaiba dole sai ya riƙeshi kuma nan ma sai a ɗan sunkuye yake tsayuwar dafe da mararsa amman yanzu gashi tsaye ras.
Amina tace. "To Alhamdulillah ai haka mukeso, in lafiya taci gaba dai wata ƙil ranar Monday za'a sallameka”. Waje ya nufa yana faɗin.
"Nifa na warke kuma na gaji da Asbiti”. Daga nan ya fita tare da ja musu ƙofar, har Saida ya fita ya iya buɗe idonsa da masifar kunya ta rufeshi.
Abinci Aunty Amina ta zuba ita da Salim sukaci a tare, a zatonsu wurin likita ya tafi ko masallaci, har suka gama cin abinci bashi ba labarinsa.
“Salim wai ina Mahmoud ya tafi ne har yanzu shiru”. Miƙewa yayi ya nufi waje yana faɗin bari inje in dubashi, Jim kaɗan da fitarsa ya dawo yana faɗin. “Naje masallaci baya can naje office ɗin Dr ma baya nan fa, ina kiran layinsa kuma yana ringing baya ɗagawa”. Tana tattare plate ɗin da sukayi amfani dasu tace. “To ina ya shiga”. Dai-dai lokacin Hafiz ya shigo tare da Huzaifa zama sukayi kusa da maman nasu Hafiz na faɗin.
“Mom ina Uncle Mahmoud ɗin ya jikin nasa da sauƙi ko?”.
Amina tace.
“Muma yanzu shi muke nema baya nan baya masallaci baya wurin likita. Juyawa sukayi kan Huzaifa dake cewa.
"Uncle Mahmoud ai yana gida, ni na tsamman É—aukarsu Mom mukazoyi cike da mmki Amina ta kalli Salim da shima ita yake kallo, sai kuma kawai ya kauda kai yana danne dariyar dake taso masa kana a hankali yace.
"To mara lfy mara mutunci in la warke ba sallama sai kawai ya tafi ya barmu kamar wasu sakarkaru to ai hike nan muma sai muyi gida muji me zai ce mana”.
Ido Ummi ta zuba musu tana kallon su Hafiz da Huzaifa dake shigo da tarkacen da suka je asibiti dashi kamarsu carpert, pillow, duvet. Kai ta juya kan Amina dake cewa Goggo Dada.
"Wlh dawowa yayi ya barmu a can, mu muna can hangame da baki a zatonmu masallaci ya tafi tunda yace mana shifa ya warke, ashe gida ya dawo, mun kirashi ya zai tafi likita bai sallameshi ba, sai ce mana yayi wai to mu zauna in ya sallameshi ma dawo”. Kwaffa Salim yayi yana miƙewa tsaye yace. “Bari inje in sameshi”. Goggo Dada na dariya tace. "Kuma kun san halin mutum tunda yace muku ya warke kuma ya fita ai zaman banza kuka tsaya yi tunda kukaji haka kun san ba wani bayani zai ƙara mukuba”. Ta ƙare maganar tana miƙe tsaye tabi bayan Salim da Ummi itama Amina tana murmushi tabi bayansu.
A hankali yake tafiya idonsa na lumshe hannunsa na kan mararsa yana shafawa haÉ—e da sauke numfashi gami da hamdalar warakar da ya samu.
Murmurshi yayi haɗi da lumshe idanunsa yana kallon yadda ta kwaɓe fuska ta tura ɗan lip ɗinta na ƙasa tana kukan ya ɓata mata jiki zai sata amai a fili yace.
“Zakiyi bayani ne”.
Yana zama kan kujerar suna shigowa, kai ya sunkuyar har suka iso bai kuma ɗago kansa ba Ummi tace. "An sallame ka ne?”. Kai a ƙasa yace. “Na warke”. Goggo Dada na murmushi mai cike da nunawa Ummi kinga gskyar abinda na gaya Miki ko tace. "To Alhamdulillah Allah ya ƙara lfy”. Amin yace yana latsa wayarsa. Salim ya watsa mishi harara yace. “Ai duk gaggawarka sai ka jira sai Dr ya sallameka kafin ka tafi”.
Da sauri Amina tace.
"Wai mutum baida lfy bazai tsaya a kula da shiba.”
Ba tare da ya kalli kowaba yace. "Lau nake, me zan tsaya sai sun sallameni dama me sukayi min”. Juyawa Ummi da Goggo Dada sukayi suka fita suna faɗin Allah ya ƙara sauƙi, Amina ta mara musu baya. Shi kuwa Salim ƙasa yayi da murya yace.
"Kai baka da mutunci ko na asi sai ka kunya mutum kai ko a jikinka”. Harara ya watsa mishi ya kishingiɗa kan kujerar yana latsa wayarsa haɗe da sauƙe ajiyan zuciya akai akai.
A can gidan Baba Malam kuwa. Tana shiga part ɗin Aunty Amarya ta wuce, cike ta samesu a parlour suna ta sallan magrib da alamun basu jima da dawowa wurin walimar ba, kai tsaye bedroom ta wuce ta faɗa kan gado. Sadiq dake biye da ita a baya kuwa Salma da ta idar da salla ya miƙawa yaran ya juya ya fita. Da sauri Saddiqa data fito daga bathroom ɗin Aunty Amarya ta zauna bakin gadon tana kallonta cikin mmki tace.
“Subahanallah Fariyda kuka kuma? Ya jikin Mahmoud ɗin ne ya rikice”. Ba magna sai sheshheƙan kukanta da yake fito mata daga ƙasan zuciyarta. Aunty Rashida dake salla a gaban Wordrobe ne tana sallamewa ta juyo kansu tana faɗin.
"Fariyda meke faruwa ne”. Kuka take ba magna, Salma ne ta shigo riƙe da yaran tana faɗin.
"Hmmm manyan ma'aurata naku salon na dabanne, wato shine kuka meda min mijina mai gadinku kuka barshi da abin kunya”. Kai ta juyo ido cike da hawayen takaici ta watsa mata harara. Dariya mai haɗe da ƴar shewa tayi ta zauna kusa da Saddiqa dake tambaya lfy kuwa.
"Lfy lau Aunty Saddiqa ku kwantar da hankalinku Yah Salim yace min tana zuwa ma Appiy Zaid kam ya warke garau harma ya sallami kansa yanzu haka suna gida, tunda maganin cutarsa taje”. Sabon kuka ne mai cike da mololon baƙin ciki ta kuma fashewa dashi. Aunty Rashida ta zauna kusa da ita tana ɗan dafata tace.
"Fariyda me haka kefa ba yarinya bace.” murya cike da takaici tace. "Aunty Rashida ya sakeni fa kuma ya dawo yana”. Sai kuma tayi shiru tana goge lips ɗin, ganin yadda Saddiga ta zuba mata idone yasa tayi ƙasa da kanta a hankali tace.
“Aunty Saddiqa meyasa zai min haka tunda yasan ya sakeni ai ba sauran hallaci koda na kallonema a tsakaninmu kuma yasan kafin ya sakeni ba idarsa a kaina”. Da sauri Salma tace. "Wai dan Allah kinma kuwa san menene saki da kuma abinda shi ya rubuta miki”. Miƙewa zaune tayi tana faɗin. "A gaban Babanshi da Malam yace ya tura min kuma ga nan text message ɗin nasa ai yana wayar”. Aunty Saddiqa ne tace.
"To kin karantane? Waima saki nawa ne yayi miki?”. Kai ta jujjuya hawaye na zuba tace.
"Ni ban karantaba tunda dai yace musu ya tura min ai shike nan”. Rashida ne ta ɗanyi wani makirin murmushi tare da cewa.
"Ikon Allah to kuma yanzu me yayi miki kike kuka”. Cikin suɓutar baki tace. "Matseni fa yayi yasani yi masa suckin....”. sai kuma tayi saurin rufe bakinta da hannunta duka biyu ta kife kanta kan guiwowinta hawaye na silalo mata, da sauri Saddiga tasa hannu ta jawo hand bag ɗin Fariyda tana faɗin. "To wlh Mahmoud ba saki ya rubuta mikiba, tunda dai kin sani shi ba jahili bane, ke ashema duk abinda akeyi bakima karanta saƙonsaba”. Tana zaro wayar tana kallon Rashida dake cewa. “inma sakine da alamu dai ya maida ita wanima bai sani ba, lallai akwai daru tsakanin su Abba da Baba Malam da Mahmoud in basu bashi matarsaba zai kunyatan' masu kunya”. Da sauri ta miƙawa Fariyda wayar tana faɗin kinga ma gashi yana kira”. Kai ta kauda tana sauƙe ajiyan zuciya.
Amsa kiran Saddiga tayi ta manna mata wayar a kunnenta murya can ƙasa tace. "Ke kiyi magna ki saurari me zai ce miki”. Ido ta rufe tana ƙoƙarin danne kukan dake son taso mata haka yasa ta sheshheƙan.
"Farriyyha har yanzu kuka kikeyi?”. Ya faɗa da narkekkiyar muryar, cikin kubcewar kuka tace.
“Ba kai bane”. A hankali yace. "Nine me”. Tana lumshe idonta tace. “Ka sani ai, kasan abinda kasa nayi maka ba kyau, kuma bana so, kuma Wlh Allah zai saka min”. Cikin cikar kamala da darajar isasshen namiji yace.
"Farriyyha ke kin fi son in bada jikina ga wasu ƙazaman kafuran banza, suyi min abinda ke ya cancanta kiyi min duk duniya kece kika halattarmin”. Tura lip ɗinta na ƙasa tayi cikin shogoɓeɓiyar muryar kukanta tace. "Ka ɓata minjikina fuskata kamar an shafa min kunu har wuyana fa kuma kalmar zanyi amai”. Wata shegiyar kunyace ta rufe Saddiga har tasata rufe kanta dan suna ɗan jiyo mgnarsa can ƙasa yace.
"Da kin tsaya ai zan wanke miki, amman dai bakiyi aman bako”. Da sauri Salma ta koma can baya tana jijjiga Zaid ita kuwa Fariyda data mace dasu a wurin a hankali tace.
“Eh banyi ba”. A hankali yace mata. "Ai ya shiga kenan yarinya bazai fitaba, kin samu tabaraki ai ga lada”. Fuska a kwaɓe tace. “Harda rigata fa sabuwa duk sun ɓaci”. Kai ta jujjuya kamar tana gabanshi jin yana faɗin.
"Kin yi sallane”. Murya can ƙasa har suma basa jinta tace. "A'a ai sai nayi wanka na canza kaya”. Cikin bada umarni yace.
"Okay to tashi kije kiyi wanka kincanza kaya kiyi salla ko”. A hankali tace.
"Toh”. Jin ya katse kirane yasa Saddiga cewa.
"To mu dai ƴan kallo tun yanzu mun fara ji da ganin abinda ya girmewa tunaninmu da alama kuwa wlh Abba da Malam da nufi sukayi horaku sukeso suyi kusan darajar junanku dan haka bakinmu alekum”.
Bathroom ta wuce ba tare da tace musu komai ba.
Su kuwa dariya sukayi tayi suna kitsima ya lamarin ya kasance.
Washe gari ranar jumma'a aka É—aura auren Raihana da Bashir É—inta.
Ranar kam gidan yafi kullum cika, bayan an ɗaura auren ne yan uwa maza na jiki suka rinƙa shigowa sunayi wa Mamy Allah sanya alkhairi ya bada zaman lfy ango da abokansa ma suka shigo akayi ta hotuna. Kusan a tare Yah Farooq da Yah Muhajid suka shigo, sosai hannunsa yayi sauƙe duk kumburin ya ɓace sai dai hannun ba ƙarfi, sai bakinsa da har yanzu yake kumbure kuma har lau da wawulumon sa giɓin ahoƙara biyu na gaba, da ba'a saba dan raunin da bai gama warkewaba.
Hotuna sukayi tayi su yasu cousins mazansu da matansu anan Mujahid ɗin ke ce mata in sha Allah dashi za'aje Taraba zai samu driver shi da ita da yara zasu tafi a sake. Cikin kwaɓe fuska tace.
"Yah Mujahid baka gama warkewa bafa, kuma ni da Aunty Saddiqa da Rashida da Salma muna son mota ɗaya”. Ta ƙare maganar tana kallon hannunsa cikin tausayawa. Yana kallon Salma da Rashida dake kwashewa da dariya duk san da yayi magna suna hango wawulumon sa yace. "Sai kuyi ai”. Sai kuma ya maida kansa kanta yace. “Ai yadda kikeso haka za'ayi zan nemi babbar motar da zata ɗaukemu sai mu tafi dasu, muje suyi ta dariya har cikinsu ya ƙulle”.
Wuraren ƙarfe sha biyu na dare hira suke yi suna shirya kayan da zasu tafi dasu Taraba.
Saddiqa ne ta miƙawa Raihana mug ɗin damu hakama Fariyda.
"Ni fa wlh na gaji da wannan shaye-shayen”. Fuska a haɗe Saddiqa tace. "Kuma wlh sai kun ƙarasa shan dan bazanyi asarar kuɗina ba.”
Ajiye mug ɗin tayi tana faɗin. "Ni baku san matsalata ba, bare ace mgninta aka bani, ni da ace ana zuwa asibiti a buɗa mutum da shi zanje amin”. Ledan da duk abubuwan cikin sun ƙare dan ta zage da naci tasa duk sunci su sha daka da gumbuna da dahuwa da su tsumi duk kaɗan kaɗan ya rage, ɗan guntun ta miƙawa Salam haɗe da cewa.
"Gashi ke ki ƙarasa wannan ko kina da guntun naki”. Amsa tayi haɗi da cewa.
"Eh ina da ɗan saura kaɗan wannan fari mai kamar suger nan menene ma sunanshi”. Adda Nana da itama ta tura kuɗin an mata haɗine tace.
"Daɗi har maɗiga ko”. Da sauri Salma tace.
"Eh shi ni nawa ya kare dan ya zubene garin buɗewa kuma ina jin dadinsa dan wlh tun ran forko da nasha wahala ban kuma jin zafiba da ina amfani dashi”.
Saddiga ne ta fito da Æ´an robobin guda biyu tana faÉ—in.
"Eh ai gana Raihana gana Fariyda ke Fariyda nakinma shine wannan mai yawar sai ki ɗan ɗibawa Salma”. Ta ƙare maganar tana miƙa mata robar, amsa tayi tana kallon Raihana ma data amshi wanda aka miƙa mata a hankali tace.
"Masu maganin mata suyi ta cin kuɗinku a banza”. Da sauri Salma tace. "Ke wlh zakisha mmki kin san Allah wannan yar robar da abu kamar sugar nan ki adanashi zai miki amfani musamman ke da kike da matsalar tsukewa kuma ga sanyi nan kin san lokacin sanyi jikin mata na bushewa na rantse miki da Allah in kin sashi bazaki ƙara jin zafiba bare ki kuji mijinki ke keda kankifa zakiga sauyi kuma wlh ɗan mitsilili zakisa yana da masifar sauƙar da ni'ima sha yanzu magani yanzu ni bani in ɗibi nawa”. Adda Nana tace.
"Sosai ma kuwa dan wlh nima kusan irin kine kuma wlh tunda na fara aiki dashi lfy lau”.
Aunty Rashida tace.
“Ke wandafa yace babu wlh ƙaryane bai nema bane, na rantse miki da Allah daɗi har maɗiga duniya ne in dai matsalarki jin zafi sabida a tsuke kike ko rashin ni'ima to kina sashi irin kamar bayan sallan la'asar wlh ranar ke kanki zakiji abinda baki taɓa jiba”
Aunty Aisha ne tace.
"Wai dan Allah nawane ni dai nasan banda juriyar shan magani amman shi tunda matsine kuma na ni'imane zan saya nawane”. Adda Nana tace. "10k kacal fa yar robar, kuma sai ki kusan shekara kina aiki dashi”. Fariyda tace.
"Toni fa ta ya zan sashi”. Adda Nana tace.
"Tashi zo nan in gaya miki yadda zakisa ki saka yanzu wlh ke da kanki zakisha mmki zaki gaskata mgnarmu”.
Ido ta zuba mata har ta gama mata bayani yadda zata sashi sai kuma ta kalli Saddiqa dake cewa.
"Tashi kije ki saka zaki tabbatar maganin mata ba ƙarya bane yarinya gata nake miki kuma sai kunmi godiya da addu'a daku da mazanku”. Cikin son tabbatar da yadda suke koɗa kayan ne ta shiga bathroom tana tunanin eh jiya mafa tasha mmki da abinda Mahmoud yace mata pompo kuma tabbas data dawo tada pants ɗinta na tabbar mata da abinda yace mata waima yarinya kamar ƙworama numfashi ta fesar a hankali tana tuna baya ko da Yah Amin wani lokacin sai da taimakon yawunsa daga baya wani abun ya saya yake sa mata shine take ɗan iya jurewa taji ba zafi amman kwanan duk in ta cire pants sai taga fanshi a fili tace.
"Shine duk maganin ya jamin shi kuma harda cemin ƙworama ya ɗauka ni jarabebbiyace irinshi to ni mema ruwana dashi”.
A nan cikin É—akin kuma
Aunty Kubra ne tace.
"To mufa da girma da yawan haihuwa yasa muka fara ɗan sakewa me zamu saya”.
Aunty Sadiya tace.
"Ciccibi yana haɗe mace sannan kaca-kaca shima na tsuke macene ci akaye da dabino, akwai kuma garin maɗi shima na tsukewane akwai gumar cikowa akwai dahuwar kaza da akeyi itama ta tsuke macene ke dai in kin mata bayani iya kuɗinki iya shagalinki”. Ta dire mgnar tana kallon Fariyda data fito bathroom tana ɗan yamutsa fuska tace.
“Ni ko yatsarma da zafi na dai sa kam”. Salma tayi kwaffa haɗe da cewa.
"Inama Allah zai kawo Appiyn Zaid yau zuwa gobe ko jibi zaki san maganin mata ba ƙarya bane gashi kin tsumu kuma ga wannan da kikasa Allah zafi dai kam zakiji babu sai d...” dukan da Adda Nana ta kaimata ne yasa tayi shiru tana rufe ido. Nan dai suka fara shirin bacci ganin har ƙarfe biyu tayi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.