Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 49
*Yau Akwai shafta a SAƘAR MAKAFI Arewapen comments kenan*
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 57
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*
Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.
Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.
Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk Æ™asar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasuneðŸ¤ðŸ»sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA
Cikin zarra yake taku tare da kutsa kanshi cikin babban hall ɗin hotel ɗin inda suke da mitting na musamman wanda zasuyi na gamayyar manyan Yan kasuwar Arewa da kudu dan kyutata mu'amala a tsakanin ɓangarori biyun da samar da sauƙin farashi wa junanmu.
Da sauri ya ƙarasa ciki tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da babban table ɗin dake ɗauke da kujeru sama da 126, babu ƙaɓilar da babu a wurin akwai wakilci dukkan 33 State da kuma wakilcin dukkan kamfanin masu zaman kansu da manya-manyan yan kasuwa.
Yana zama suka fara gabatar da manufar zaman nasu.
A ƙalla 3 hours suna tattaunawa Alhamdulillah basu tashiba har saida suka tsaida matsaya ƙarfe she ɗaya dai-dai ya shigo ɗakin bayan ya amshi jallabiyarsa da ma'aikacin ya kawo ma lokacin da ya iso bakin ƙofar.
A inda ya barta a nan ya sameta a durƙushe har yanzu ko ƙwaƙwaran motsi batayi ba, jallabiyar ya wurgar kan gado ya juyo yana kallon su Zaid da tuni sunyi bacci a kan kujerar 3 seatter ɗin numfashi mai sanyi ya tare kallonta ta gefen idonshi, hannunsa yasa ya jawo jallabiyarsa daya bari kan gadon turarukansa masu sanyin ƙamshi ya fesa tare da zura jallabiyar akan 3 quarter and shirt dake jikinsa
Wayarsa ya zira aljihunsa yana mai rataye jakar system nashi a kafaÉ—arsa na hagu ya sunkuyo ya É—aukesu duka biyu ya É—aurasu a kafaÉ—a, É—an jujjuyawa yayi ganin ba wani abu nasa daya mance, to dama da iya briefcase nasa kawai yake wanda ya kimtsa komashi a ciki kafin ya fito wanka kamar yadda itama komanta yake cikin hand bang É—inta.
Ƙofar ɗakin ya buɗe a hankali yana kallon agogon roles ɗin dake hannunsa yana gyara riƙonsu da tabs ɗinsu yace.
“Ke mu tafiâ€. Ya faÉ—a yana kallonta da dukkan idonsa dan tabbatarwa tana motsi ko dai suma tayi dan ya lura bata da wuyan suma suman daÉ—i yake mata.
A hankali take yunƙurowa tare da haɗe lips ɗinta ta matse tana mai dafa jikin wardrobe ɗin ta samu ta miƙe tsaye ba tare da ta kalli inda yake ba ko idonta nauyin ɗagosu takeji, handbag ɗinta ta ɗauka a hankali ta zura ƙafarta cikin takalmanta, duk abinda take yi idonsa na kanta har saida yaga ta nufo bakin ƙofar sannan ya juya kai ya buɗe ƙofar ya fita tana biye dashi a baya.
Tunda ya shiga motar bai juyoba kamar yadda itama bata É—ago kantaba, ganin sun shiga Airport ne yasata lumshe idonta a hankali ta fara motsa bakinta tana jin garÉ—in Grapes daya zuba mata har yanzu bai bar bakinta ba.
Ƙarfe sha biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga Lagos to Kano.
Bayan tashinsu da 36 minute ya É—an juyo ya kalleta har yanzu kanta na sunkuye idonta dake É—an kumbure alamun ta É—anyi kuka ya kalla sai lips É—inta da gogesu da tayi tayi kafin yayi mata aika-aikan yasasu yin jazir kamar an shafa mata jan jambaki.
Numfashi ya sauƙe tare da kwaɓe fuska mai haɗe da murmushin gefen baki ya maida kanshi kan su Zaid da suka farka daga baccin.
Suna sauƙa a Kano Ana ana kiraye-kirayen sallan azahar wasu masallatanma tuni sunyi salla.
A hankali take biye dashi a baya, tamkar wacce bata da laka a jikinta. Suna fitowa Arrivals ta ɗago kanta a hankali jin anyi mata rungumar da tasa ɗan kuzarinta dawowa, Hafiza da Samira ne da Raihana sukayi mata rungumar da tasata dariyar Farin ciki Hafiz kuwa da sauri ya amshi Zaitoon Huzaifa kuwa Zaid ya karɓa sai kuma Sulaiman da yayiwa Mahmoud ɗin side hug tare da ɗan sakeshi sai ya kuma rungumeshi yana murmurshi mai haɗe da jin daɗi ganin yadda su zama tamkar taurarine sa ƙyalli suke shi yasa suke ta kallonsu.
Sadiq na sauri ya miƙawa Mahmoud hannu tare da gaidashi cikin girmamawa.
Sulaiman na amsar su Zaid a hannun Huzaifa dake gaida Mahmoud É—in yace.
“Welcome back my son.†sai kuma suka kalli Raihana dake cewa.
"Yah Salam Zaid haka ka girmaâ€. Samira na amsar Zaitoon tace.
“Yanzufa ya danne Zaitoonâ€. Murmurshi mai cike da jin daÉ—i tayi tace.
“Ai kuwa kamar ta fishi tsowoâ€. Da sauri Huzaifa yace. "A'a fa Aunty Fariyda mace bata taÉ“a fin namiji tsawo ko yaya in dai za'a godasu sai anga na mijin yafi tsawo, nimafa nafi Aunty Hafiza tsawoâ€. Mare Æ™eyarsa Hafiza tayi tace. “Dama ai nasan haka zaka ceâ€. Sai kuma duk suka haÉ—a baki wurin gaida Mahmud É—in da tuni ya nufi motar shi da Sulaiman yazo dashi, ba yabo ba fallasa ya amsa musu gsisuwar ba tare da ya juyo ba.
Haka yasa suma duk suka biyo bayansa
Hafiza da Samira motar Hafiz suka shiga, Fariyda da Raihana da Huzaifa kuwa motar Sadiq suka shiga. Huzaifa ne a gaba riƙe da Zaid, Zaitoon kuwa tana can hannun Samira, ba tare da ya janye idonsa daga bayan motarsa da Sulaiman ya ɗauko yazo ɗaukrsa da shiba ya ɗan ɗaga hannunsa yayiwa su Hafiz da Sadiq alamun su tsaya, haka yasa duk suka tsaya ba tare da sun kashe motocinba suka maida hankalinsu kanshi shi kuwa Mahmoud juyowa yana kallon Sulaiman da ya iso kusa dashi.
“Shiga mu tafi manaâ€. Da hannu ya masa nuni daya buÉ—e bayan motar. Kai Sulaiman É—in ya jinnina cikin jin karsashi da fatan cikawa Jidda dake baya burinta na samun kusanci da shaÆ™uwa da Mahmoud wanda suke fatan ya kaisu ga aure, yana buÉ—e marfin motar ya watsa mata kallon da yasa ta saurin yin Æ™asa da kanta tace.
“Yayah barka da dawowaâ€. TsuÆ™e fuska yayi yana mai watsa mata kallon takaici ya nuna mata hanyar fita sai kuma ya juyo yana kallon Sulaiman.
“Akan me zaka kwaso ko wanne irin tarkace ka cusa min cikin motata kasan ba kowa yake shiga min mota bako, ke fice min da gani kar in Æ™waÆ™wali indon kallon mayun nan da kasan kowa ka samu zaka kwaso da sai ka É—auko motarka aiâ€. Ya Æ™are maganar ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta fito tana kwÉ“e fuska motar Hafiz dake bayansu ta buÉ—e ta shiga baya kusa da Hafiza, ita kuwa Fariyda baki ta taÉ“e tana mai Æ™ara yin Æ™asa da kanta don har yanzu bata bari sunyi ido biyu ba shayin haÉ—a ido dashi ma take yi.
Da sauri Samira ta fito tana miƙo mishi Zaitoon, amsarta yayi yana mai kallon Huzaifa yace.
“Huzy kawo Zaidâ€. Cikin sanyi Huzaifa y fito tare da miÆ™awa Raihana hannu ya amshi Zaid É—in tafiyar Huzaifa ta lukutayen yara yake kallo haka nan ya É—anyi murmushi gefen baki cikin son É—an yayartasa da Æ™aunarsa da yadda lukutancinsa ke sashi nishaÉ—i yace.
“Kacewa Farriyyhah tazo nanâ€. Fuska Huzaifa ya É—an kwaÉ“e cikin alamun É—an shaÆ™uwarsa dashi yace. “Our Uncle wacece hakaâ€. Ido ya zubawa Fariyda dake jin duk abinda suke cewa kamar yadda duk sauranma keji saboda kusancin su da ida yake da kuma sauÆ™e glass da sukayi dan jin dalilin tsaidasu da yayi.
“Farriyyhah zo nanâ€. Ya faÉ—a yana shiga gaba rungume dasu Zaid.
Jidda kuwa kai ta jinjina cikin fusatar zuciya da zafin kishi da ƙara kafa zuƙar cimma burinta ita ta koreta wannan yar girman kan kuma ya kirata.
“Aunty Fariyda kije sai mun haÉ—u a gidaâ€. Sadiq da Raihana suka haÉ—a bakin faÉ—a, ido cike da yanani na sanyi tace.
“Sadiq mu tafi kawai ni fa ta gida nake son mu fara ina son ganin Baba Malam dasu Mamiâ€. Da sauri Sadiq yace.
“To ai ko a mota tane ma ni bazan biya dake can ba saida sanin Yah Mahmoud É—in in ya baki izi kafin in kaiki in dai ba so kike malam yayi fushi da nibaâ€.
Sulaiman da tunda yasashi buÉ—e mota ya kori Jidda ya zuba mishi ido har yanzu bai É—auke kallonsa a kansa ba da mmki mai tafe da nazari.
“Madam ke muke jiraâ€. Ya faÉ—a yana kallon Fariyda, a hankali ta shiga bayan motarsa Prado ce baÆ™a, bata taÉ“a ko taÉ“ata ba kai ko tsayuwa kusa da itama bata taÉ“ayi ba sabida sanin halin masifarsa yo ko Hafiz ma bai taÉ“a shigarta ba, Amina sau É—aya taÉ“a shiga, wacce yaje da ita gaida Baba Malam ta shiga Benz ce, duk motocinsa baÆ™aÆ™ene masu sheÆ™in sabunta da gyara tana shiga Sulaiman ya rufe Æ™ofar.
Tunda ta shiga taji alamun an buÉ—e but da alamun ana sassaka kaya a ciki, kusan 13 minute ana shirya kaya a ciki kafin ya maida marfin but É—in rufe, ya juya ya shiga gaba driver seat yaja motar. Yayin da Hafiz dake bayan Sadiq kuwa tuni sunyi gaba.
Tunda suka shiga motar ko tari bata ƙara yi ba, sai wayarta da take ta jujjuyawa kanta a sunkuye duk sanda ta tuna abinda yayi mata sai tayi saurin rumtse idonta tana mai tsumashi matsayin ƙanin miji bata taɓa zato ko tsammanin wannan tijarar ba daga gareshi, lallai ta yarda Mahmoud ya ƙware a tijara da iya iskanci na gasken gaske.
Shi da Sulaiman kuwa suna hira duk da ƙarfin hirar Sulaiman ne yake yi da dariya harda ƙyaƙyata shi kuwa sai ɗan murmushi dake nuna eh sosai yake jin daɗin hirar.
Tafiya mai tsawo sukayi wacce bata san ina sukeba saboda kanta dake sunkuye jin an buɗe gate ne yasa ta ɗan ɗago kanta, numfashi mai cike da farin ciki jin dadi ta sauƙe ganin sun kutsa kai cikin farfajiyar gidansu, ido ta lumshe tare da ɗaukar hand bag dinta ganin sunyi parking ne yasa ta buɗe marfin motar da sauri ta fara kiciniyar sauƙowa dan tudun motar yasata ɗan riƙe gefen ta fito dai-dai lokacin Dr Nasir ya fito part ɗin Mami da nufin shi ga part ɗin Baba Malam cikin sauri ya juyo kanta da sassarfa ta nufeshi tana isa inda yake ta rungumeshi.
Mami dake biye dashi a bayane ta tsaya cikin mmkin ganin Mahmoud da Sulaiman da suka fito cikin motar shi kuwa Mahmoud tunda ta abka jikin Dr Nasir ya kauda kanshi daga kansu.
“A'a ikon Allah mutanen India barka da isowa, sauÆ™ar yaushe?â€. Sai kuma ta meda hankali kan Fariyda data rungumata ta baya tana faÉ—in.
"Mami i miss uâ€. Ta Æ™are maganar cikin zubda Æ™wallan farin ciki.
Tana ɗan murmushi mai cike da jin daɗin ganin yar tata ta shafa kafaɗarta tare da ɗan janyeta daga jikinta kallon sama da ƙasa tayi mata cikin mmkin ganin wani irin mashahurin kyau da sheƙi mai haɗe da ƙyallin da ɗiyartata keyi war wani yellow ta surka a farinta, tana ƙara tureta ganin zata kuma rungumata tace.
“Ke bakya girma fa to me kuma na kukanâ€.
Sai kuma ta kalli Dr Nasir da ya bawa su Mahmoud hannu tare da yi musu iso tana gyara mayafin jikinta tace.
“Mahmoud Barka da dawo ku isa ciki yanzu Malam ya dawo masallaciâ€. Cikin girmamawa Mahmoud yace.
“Mami barka da ranaâ€. Tana nuna musu hanya tace. “Ku isaâ€. Suna gaba tana biye dasu a baya riÆ™e da hannun Fariyda dataÆ™i saketa.
Da sauri Baba Malam ya miƙe tsaye cikin jin dadi mai bayyana akan fuskarsa ya warewa Mahmoud ɗin hannu cike da kunya da jin nauyi ya iso gareshi haɗesu yayi dasu Zaid ya rungume tare da cewa.
“Kai Alhamdulillah Mahmoud nayi farin cikin ganin kuâ€. Sai kuma ya sake shi ya koma ya zauna bayan ya amshi Zaid. Mami kuwa da Aunty Amarya da Dr Nasir ido suka zubawa Malam É—in da soyayyarsa akan Mahmoud da su Zaitoon a fili ya bayyana farin cikin da ya basu mmki.
Gefensa ya nuna Mahmoud É—in da Sulaiman, sai kuma ya kalli Fariyda da Aunty Amarya ta rungumeta tana ce mata
“Daga ina haka yan uwanki duk yau suna gidankiâ€. Cikin muryar kukan jin dadi tace.
"Daga Airport nan muka fara zuwaâ€. Cikin so Malam yace.
"Zo nan mana Mamanaâ€. Da sauri ta sake Aunty Amarya gabanshi ta durÆ™usa gafen Mahmoud É—in hannun sa yasa ya jawo kanta ya É—aura kan guiwowinsa yana shafawa yace.
“Barka da dawowa Mamana Allah yayi muku al'barka dake da yaranki da mijinki dama mu baki É—ayaâ€. Da Amin suka amsa baki É—ayansu sai kuma suka kalli Mami dake cewa.
“Mahmoud barka da dawowa lfy, Alhamdulillah anyi farar jinya ga yadda Zaid ya murje ya zama Æ™ato abinsaâ€. Yana kallon Zaid É—in dake ta miÆ™o masa hannu alamun zai dawo wurinsa yace.
"Mukuma bama ganin ya girma fa Mamiâ€. Aunty Amarya tace.
"Saboda kuna tare dashi neâ€. Mami ta miÆ™a masa hannu alamun ya bata Zaitoon da sauri ya miÆ™a mata ita yana faÉ—in.
“Zaitoon je ki gaida Mami koâ€. Da É—an sassarfa ta faÉ—a jikin Mami dariya sukayi ganin shima Zaid ya tafi wurin Mami.
“Baku isa gida bako Mahmoud?â€. Malam ya tambaya cikin kulawa.
Yana É—an yin Æ™asa da kai yace. “Eh Malam ta nan muka fara dan munyi miss addu'arkaâ€. Yana shafa kanshi yace.
“Ai duk inada kuke kuna tare da addu'a ta, Asma'u a kawo musu abinciâ€. Tana É—an gyara zama ta kalleshi a fakaice yo ai duk wannan munafurcin gaisuwar da nuna shi ba Allah ne iya karta a nan ne ko ruwan gidanma ya taÉ“a shane bare abinci.
Shi kuwa Mahmoud cikin girmamawa ya kalli Mami da ta É—auko tray wormas É—in da ta shiryawa Malam É—in lunch a hankali yace.
"Mami Alhamdulillah munyi lunch a Lagos maâ€. Tana kallon Sulaiman da Malam ke ce masa. “Sulaimanu yanzu fa saura kai, yaushe zamu yi maka aure kada lokacin ya Æ™ureâ€. Cikin sanyi Sulaiman yace.
“Malam ai ba wacce ke sona shiyasaâ€. Dariya sukayi baki É—ayansu sai kuma duk suka kalli Malam É—in dake cewa.
“To ba matsala zan sama maka mai sonka, yanzu dai Mahmoud ku isa gida nasan Abbanka yana nan ya zaÆ™u ya ganku, Nasir samusu abincin su tafi dashiâ€.
Daga nan duk suka fito, suna shiga mota kiran Amina na shiga wayar Fariyda.
"Wai dan Allah ina kuka tsaya ne? Su Hafiz sun inso tun tuni ba ku ba labarinku, wata nawa kuna tare har yanzu baku gaji da juna bane dan naga alamun wani zango kuke son yadawa a hotel kuma koâ€. Amina ta faÉ—a tana kallon Aunty Saddiqa dake sa turaren wuta a parlour, da sauri sukayi dariya jin tana faÉ—in.
"Allah ya kiyaye, gidafa muka zo wurin Malam gamu mun fito yanzuâ€. Murmushin Aunty Saddiqa tayi tana kallon Sadiya matar Dr Nasir ta gama karantunta a Misra ta dawo tace.
“Allah sarki bawan Allah kamar yasan Malam yayi kewarku cewa yake har mafarkinku yake yi, ya kyauta da ya fara kaiki can, Allah ya kawoku lfyâ€. Amin tace tana kallon layin unguwar tasu suna isa bakin gate É—in gidan kiran Faisal na shigowa wayar Yah Amin, yana kallon number har kiran ya katse bai É—aukaba sai kuma ya kalli wayarsa ganin sakon ne yasa ya É—an buÉ—e saÆ™o Idaya ce.
“Barka da dawo, ka huta gajia zanzo har gida yima sannu da hanya da duba jikin Zaidâ€. Shine abinda ta rubuta mishi wanda ya bashi tabbacin tana sane da duk motsinsa da kuma tabbacin tana cikin kano lip É—inshi na Æ™asa ya datse da karfi sai kuma ya kalli kiran Faisal daya kuma shigowa a kufule ya amsa kiran.
Juyowa yayi yana mata kallon da yasata yin ƙasa da kanta, kusan 3 minute wayar na maƙale a kunensa kuma bai ce ko ƙalaba bai kuma katse kiranba sai kuma duk suka kalleshi dai-dai lokacin da suka kutsa kai cikin gidan jin yadda ya......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.