Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 27 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 67
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Fusataccen numfashi ya sauƙe haɗe da buɗe idanunsa daya rumtse da ƙarfi, ganin Faisal ɗin na ƙara kirane ya sashi damƙe tafin hannunsa da masifar ƙarfi.
Suna isowa ta buɗe ta shiga ido na zubda ƙwallan. Su Zainab kuwa a baya suka ajiyesu su Zaitoon.
Cikin kulawa Dr Nasir da Mujahid ke biye dashi a baya, ya buɗe marfin motar ya miƙawa Mahmoud hannu gami da cewa.
“Kayi haÆ™uri Mahmoud, zamuyi magna in kun koma, Allah ya kiyaye hanya zan É—auki mataki in sha Allahâ€. Yafa É—a yana Æ™ara miÆ™o masa hannun da nazartarsa da gane wutan kishi dake ci a zuciyarsa.
Ba tare da ya ɗago kansaba ya miƙawa Dr Nasir din hannu hannu yana mai ɗan jinjina masa kai.
Sake hannun Dr Nasir yayi lokacin da Fariyda ta jawo marfi motar tana mai zubda ƙwalla tace.
“Ni ina son zama tare da iyayena da Æ´an uwana, sune masu sona da bazasu taÉ“a jifata da kalmar maita har yan uwansu suji suma su kamabaâ€.
Idonshi na kan Dr Nasir da ya juya tuni ya shiga motarsa yaja ya tafi, dan baima lura da Mujahid da ya nufi gefen da Fariyda take ba.
Zainab da Raihana ma sun koma cikin gida.
“innalillahi Babe kiyi haÆ™uri ki bar zubda hayen nan a banza dan hawayenki masu daraja ne, Please kada ki cutar min da kyawawan idanun nanki, hakan zai sa zuciyata fashewa faâ€. ya Æ™are maganar cikin muryar dake nuna so, idonsa na kan Mahmoud da yayi kamar bai san da zamansa a wurinba bai kashe motarba, kuma bai ja sun tafi ba, gefen da Mahmoud É—in yake ya zagoyo ya buÉ—e marfin motar yamatso kusa dashi sosai ya miÆ™a masa hannu yace.
“Ya kake? Ko dai baka magna ne? Please ni dai a barmin sanyin idaniyata mu wuni tare ko dan inji muryarta in samu natsuwa kasan abincin wani gubar wani, lokacin da baka damu da ita da farin cikintaba a lokacin nake jin zan iya sadaukar da komai na rayuwata dan farin cikinta.â€
Tunda ya iso wurinsu ya fara magna ko sau ɗaya bata daga ido ta kalleshi ba, sai hawayen dake ta sintiri a fuskantar, kanta a sunkuye tana ƙoƙarin danne sheshheƙan kukanta da yaƙi dannuwa.
Shi kuwa Mahmoud numfashi mai nauyin gaske ya fesar tare da miƙawa Mujahid hannu lokacin da yake ci gaba da cewa.
"Kukanta na tayar min da hankali saboda ina son t.....†da sauri ya zazzaro idonsa waje lokacin da yaji Mahmoud ɗin ya haɗe tafin hannunsu wuri daya gami da yi masa wani irin azabebben matsa tare da murɗa hannun duk in one second, gigitaccen ihu mai firgita duk wanda yaji Yah Mujahid ɗin ya kurma da azaɓan ƙarfi jin yadda Mahmoud ya murɗa hannun nasa haɗe da matsewa ɓas sharaɓansa ya bada sautin dake nuna tabbacin karaya mai cikekken dafi.
Ihun da ya kurma da ƙaran karyewan wannun ne suka sa Fariyda dago kanta ido ta zuba wa Yah Mujahid ɗin da jikinsa ke wani irin ƙarƙarwa mai haɗe da zufa mai tsiyaya
Innalillahi tace da karfi tana maida kallonta kan Mahmoud dake zaune tamkar ba shi ba har yanzu hannun Mujahid ɗin na hannunsa yatsunsa ya sarƙafe cikin na Muhajid yayi musu murɗar da yasasu targaɗewa baki ɗayansu.
Wani ihun da yafi na farkon Mujahid ya danna cikin rawan jiki da murya da shiÉ—ewa.
Kuka tasa ta riƙo hannunsa dake kusa da ita tana faɗin.
“ innalillahi Appiy ka sakeshi, zaka kasheshi fa wayyo Mamy kuzoâ€. Ta Æ™ira sunan Mamy da Æ™arfi.
Ba tare da ya kalleta ba yayi saurin sakin hannun Mujahid ɗin, sai kuma ya danna masa naushi a kan muƙamuƙinsa kafin ya ɗago hannunsama haƙora biyu na gaban nan da jini sunyi ƙasa ƙafarsa ya ware ya zurota waje, lips ɗinshi duka ya haɗe ya taune da ƙarfe ya danna mishi naushi a ƙugunsa hakan yasashi tafiya taga taga ya faɗin ƙasa rim. Da faɗuwarsa da ihunsa da zubewar haƙorinsa duk a tare.
Shi kuwa Mahmoud a 360 yayi figi motar, cikin tsananin kiɗima ta rumtse idonta da ƙarfi ta ɗaura hannunta duka biya ta riƙe kanta dan ganin yadda ya figi motar yayi kwana dai-dai kan Mujahid ɗin, bata buɗe idonta ba har saida taji sun bar gidan hannunsa data rike take ta jijjigawa tana kuka haɗi da yarfa hannunta ɗaya tana cewa.
“Shike nan ka kasheshi Wayyo Allah Yah Muhajid na me yayi maka zaka kasheshi?â€. Bai gama fita gidanba Mamy Aunty Amarya Saddiqa da Maigadin dasu Raihana duk suka iso farfajiyar gidansu cikin tsaro Mamy suka Æ™araso wurinsu da sassarfa sabida hago yadda yake wani irin burbuwa da ihu jiki duk na mazari....
Sadiq dake jan motar Baba Malam na gefenshi ne ya É—an juyo ya kalli mahaifin nasu yace.
“Malam gida zamuyi ko akwai inda zamujeâ€. Yana buÉ—e wani shafi daga cikin shafukan littafin Kulasatul norul yaÆ™in Yace.
“Ka mance nace ma in mun gama dubiyar marasa lafiya daga hospital É—in gidan Abbanku Alhaji Umar zamujeâ€. Da sauri yace.
"Afwan Malam wlh na mancene, ai mun kusa ma, da banyi mgnaba zamu wuce naga kai hankalinka na kan karatuâ€. Malam yace.
"Abubakar ka daina yawan rantsuwa a cikin dukkan mgnarka dan yawan rantsu alamice ta makaryataâ€. Cikin girmamawa yace.
“In sha Allah Malam zan kiyayeâ€......
Dai-dai lokacin kuwa Mahmoud yayi parking a harabar gidansun, yadda ya shigo a guje da yadda yayi parking É—in ne yasa. Hafiz juyawa da sauri ya nufesu, Baba idi ma dasauri ya maida gate É—in ya rufe ya nufasa.
Da sauri Hafiz ya ja da baya ya tsaya, shima Baba idi tsayawa yayi ba tare da ya ƙaraso ba, hakama Sulaiman da ya fito daga part ɗin Yah Amin. Duk ido suka zubawa Mahmoud ganin yadda ya fito cikin motar fuskar nan babu annuri ko salama, tayi masifar ja sabida fushi da fusata jikinsa duk rawa yake yi har lips ɗin sa.
Inda take ya zagoyo ya buÉ—e Æ™ofar cikin wani irin kallo yasa hannunsa ya kamo nata ya fizgota waje, sautin kukan da tunda ya É“alla hannun Muhajid takeyi tana faÉ—in “Ka kasheshi fa, ka takashi da motafa Appiy me yayi makaâ€.
Figota da yayi ne yasa takalminta saluɓewa, a fusace yake janta, da ido kawai su Hafiz suka bishi. Barin motar da yayi a buɗene ya bawa Hafiz damar ɗaukar su Zaid ya nufi cikin gida bayan Mahmoud ya shige da Fariyda.
A hankali Sulaiman ma ya mara masa baya, Baba idi kuwa bakin gade ya koma ya zauna cike da nazari da tsoron ganin wannan mugun fusatar da bai taɓa ganinta tare da Mahmoud iya zamansa dasu tun suna yara.
A parlour suka samu Ummi da Goggo Dada.
“A'a har sun dawo neâ€. Goggo Dada ta faÉ—a tana amsar Zaitoon.
Hafiz yana kallon Ummi cikin tsoro murya a saɓule yace.
"Sun dawo kuma Aunty Fariyda nata kuka tana cewa Uncle Mahmoud shike nan ka kasheshi ya mutufa ka takashi.†cikin tsanin tsinkewar zuciya Ummi ta miÆ™e tsaye tare da kallon Goggo Dada dake cewa. "Innalillahi kai Hafiz kisa kuma a ina É—inâ€. Sulaiman ne ya kamo hannun Ummi yana faÉ—in.
"Ummi muje sun haura samaâ€. Cikin kiÉ—ima Ummi ta fara É—aga Æ™afafunta dake rawa da barazanar kasa riÆ™e jikinta. Goggo Dada da Hafiz kuwa parlour Abba suka nufa.
Daga kan upstairs suka fara jiyo muryarsa haka yasa su sauri ƙarasawa cikin parlour dai-dai lokacin.
Yayiwa Fariyda wani irin gigitaccen marin da yasata ganin stars sun cika parlour sai gilmawa sukeyiwa ganinta.
Wayar Yah Amin da kiran Faisal ya kuma shigowa ne. Yayi sauri sa hannunsa ya riƙo wuyanta tare da nuna mata fuskar wayar cikin rawan jiki ya danna mata tsawa da ɗimautacciyar muryasa da kaji kasan baya cikin natsuwa da hayyacinsa yace.
"Wai kasheni kike son yine Farriyyha nace kasheni kike son yine, ki gani fa kiran da tsinannun Allah ta alan nan ke min Sa'ad ya kira shima wannan mayen ya kira, kin san irin azabar saÆ™ar makafin da suke yiwa zuciyata kuwa sun sarÆ™afemin zuciya da numfashi suna son kasheni.â€
Cikin karkarwa da tsananin tsoronsa da bata taɓajin tsoron wani ɗan adam hakaba a doron duniya, take jujjuya mishi kai ido na kwaranyar da hawaye murya da jiki na rawa take cewa.
“Appiy ka kasheshi fa dan Allah kayi hakuri ni ban san me nayi makaba, dan Allah karka kasheni Pleaseâ€. Wani irin nannauyan kuka ne ya taso masa haka yasa ya fara dukan Æ™irjinsa da hannunsa na dama na hagun kuwa ginin da ya haÉ—ata dashi ya fara duka da Æ™arfi yana haÉ—awa da gwara kanshi cikin fitar hayyaci da Æ™arfi ya fara faÉ—in.
"Farriyyha zuciyata zata fashe, zan mutufa!!! meyasa bakya tausayina ne me nayi miki kika tsaneni, koda bakya sona kiji tausayina mana, zasu kasheni fa zuciyata zata fashe in baki daina kuka da kiran sunan wancan karenba ya mutu mana sai me dan ya mutu, ni so nake ya mutufa ya barmin ke a duniyarâ€. Ya Æ™are maganar cikin karkarwa ido na kwaranyo da hawaye har lau yana dukan Æ™irjinsa da masifan Æ™arfi kamar yadda yake dukan jikin katangar da É—aya hannun.
Takure jikinta tayi cikin tsananin kiÉ—ima firgici da tashin hankali da tsananin tsoronsa take kuka mai raunata zuciya.
Da gudu Sulaiman ya iso inda suke ya kamosa, Ummi kuwa cikin tashin hankali ta rungumo Fariyda da ta iso gabanta da gudu.
Cikin tsoro take kuka da yarfa hannunta murya na rawa take jan hannun Ummi tana faÉ—in.
"Ummi mu gudu! dan Allah Ummi ki É“oyeni!! zai kashenifa Ummi mu gudu!!!â€. Jin hakane yasa Ummi jan hannunta ta suka fita, kai tsaye parlour Abba ta wuce da ita, da da sauri ta kwace hannunta daga riÆ™on da Ummi tayi mata, gaban Baba Malam da yanzu ya iso kenan.
Ta durƙushe kan guiwowinta tana kuka haɗi da riƙo hannunsa tana faɗin.
“Malam Yah Mujahid Malam ya mutu ko?â€. Cike da mmki Malam da Abba suke sauraron abinda Ummi ke gaya musu na yadda suka samu Mahmoud É—in yana yiwa Fariyda da dukan kansa da yake yi, da kuma kalaman da su Hafiz sukaji Fariyda tana faÉ—a kamar yadda yanzu take mai-maitawa wanda sune suka hanasu fahimtar manufar kalaman Mahmoud É—in. Da sauri Baba Malam ya miÆ™e ya nufi parlour Mahmoud É—in.
Shi kuwa Abba hannunsa yasa ya jawo hannun Fariyda tare da cewa.
"Yi shiru Fariyda ba abinda zai miki. Kwantar da hankalinki kinji ko in sha Allah Mujahid bai mutubaâ€. Dai dai lokacin Baba Malam ya shigo riÆ™e da hannun Mahmoud É—in da jikinsa yake tsuma, idanunsa da sukayi tamkar zasuyi Aman wuta Goggo Dada ta zuba wa ido. Hafiz kuwa da sauri ya miÆ™a ya fita. Ajiye shi Baba Malam yayi tare da bugawa Fariyda tsawa.
"Ke ki natsu wai me ya samu Mujahid É—in ne? A ina kuka haÉ—u ki daina wannan kukan ki min bayaniâ€. Jiki na karkarwa tace. "Malam Appiy ya takashi da mota da mukaje gidanmu ya mutu koâ€. Da sauri Sadiq ya zaro wayarsa Mamy ya kira. Shi kuwa Malam Mahmoud da ya zauna gefen Abba da yake yi masa wani irin kallon yanke hukunci, Æ™asa yayi da kansa har yanzu jikinsa Æ™arÆ™arwa yake yi sai wasu irin tagwayen fusatattun numfarfashi yake fesarwa yana taune lip inshi babu Æ™aƙƙautawa.
Ummi na zama gefen Abba cikin tsoro da tashin hankali tace.
"Shike nan ai in wannan zazzafar zuciyar tasa yasa ya kasheshi shima É—in ai ba tsira zaiyibaâ€. Da sauri Sadiq da ya gama waya da Mamy yace.
"A'a fa Ummi bai mutu bafa, bai takashi bafa, Mamy tace dai an kaishi asbitiâ€. Cikin kulawa Abba yace.
"Fariyda me ya faru neâ€. Jiki da murya na rawa tana Æ™ara matsawa baya kusa da Abba tayi nesa da Mahmoud É—in dan masifar tsoronsa tace.
"Abba ni dai ina tsoronsa wlh zai shaÆ™eni Abba dukana yakeyi faâ€. Numfashi mai nauyi Abba ya fesar tare da kallon Mahmoud cikin Murya mafi Æ™ololuwar fusata da bada umarnin kai tsaye yace.
"Mahmoud yanzu nan ba sai anjima ba yanzu yanzun nan ka saki Fariyda ka saketa yanzuâ€. Tunda ya zauna yayi Æ™asa da kansa bai É—ago kaiba sai yanzu ido cikin ido sukayi da Abba mari Abba ya yarfa mishi tare da cewa.
“Cire idonka cikin nawa mara kunya tsaurin ido maza saketa nace ko yanzu-yanzun nan!!!!â€.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.