Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 48 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 87
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Shi kuwa Hadi ya shige ciki jim kaÉ—an ya fito tare da wani babban mutum gaisawa sukayi kana suka kuma fita jim kaÉ—an da fitansu suka dawo.
Ido cike da kaɗuwa take kallon Sa'ad da Faisal dake biye dasu a baya, gefe suka zauna, fuska a tsuƙe ya nuna Faisal yana faɗin.
"Ka cire idonka kan matata tunda yanzu dai ka san matar aureceâ€.
Sai kuma ya dannawa Sa'ad matsiyacin kallon yace. "Kai dama ka san matar aurece da yake mayen matane kai ba kunya ba tsoron Allah kayi ta bibiyar matataâ€. Murya cike da sanyi Sa'ad yace.
"Kayi haÆ™uri mahaifiyata na cikin damuwa kuma kaine da kanka ka bani damar nemantaâ€.
Fasal ya kalla jin yana faÉ—in. "Ni wlh ban san matar aure baceâ€. MiÆ™ewa tsaye Mahmoud É—in yayi ya jawo hannunta yana fita yace.
"Ok Barrister a medasu ciki kawaiâ€.
Daga nan ya juya ya fita Hadi É—in na biye dashi a baya.
Daga nan Maitama suka wuce gidan Aunty Kubra ƙanwar Yah Saleh, anan ya barta ya kuma fita shi da Hadi.
Abral ne yar matashiyar Aunty Kubra da bazata gaza 16 years ta zuba wa Fariyda ido bayan tayi al'walan ta fito daga bathroom tana tattare gashin kanta dan wurin shafar kai ribbons É—inta ya sule.
“Masha Allah Our Aunty kina da kyau dama Sajida ta tura min hotonki lokacin da kukaje Istanbul, itama ta kusan dawowa aiâ€. Tana tubke gashin ta amshi hijabin da Aunty Kubra ke miÆ™a mata, bayan ta idar da sallane sukayi ta hira da Abral É—in da Aunty Kubra dan itama akwaita da sauÆ™in kai.
Sai ƙarfe takwas dai-dai Mahmoud ya dawo Hadi ne ya kaisu Airport ƙarfe goma dai-dai jirkinsu ya tashi zuwa Kano.
Tunda suka shiga jirgin duk hankalinsa na kan system nashi da alamu Abu mai mahimmanci yake yi, tsakin ta É—an ja a hankali tana lumshe idonta, hannunsa yasa ya jawota jikinsa haÉ—i da É—an kissing goshinta cikin raÉ—a yace.
"Bacci ko zo nan kwanta kiyi baccinkiâ€. Ya Æ™are maganar da gyara mata kwanciya.
A can Kano kuwa Hafiz ne zaune a parlour Ummi da Sulaiman da suka iso tun ƙarfe biyar na yamma, sai Huzaifa da bayan sallan isha ne ya kawo Sulaiman abincin da Amina tayi masa, Ummi da Goggo Dada na zaune anan suna ta hira Sulaiman na basu lbrin sanyin Gembu.
Text message É—in da Mahmoud yayi masa ya duba yana faÉ—in.
“Hafiz zuwa sha É—aya ka shirya zakaje Airport ka É—auko Mahmoud sun tasoâ€. Cikin zumuÉ—in yace.
"Uncle Sulai da wacce motar zanje da prado ko Hillux tunda kuna dawowa na kai an wanketa an gyarata tsab.
Yana É—an cin snackers É—in da Amina ta turo masa yace.
“Eh kaje da Hillux É—in ga key É—inâ€.
Goggo Dada tace.
"Allah ya kawoshi lfyâ€.
Amin Ummi tace kamar basu san inda yajeba duk da dai basu san har yanzu yana tare da Fariyda ba.
Karfe sha biyu dai-dai suka iso cikin gidan, cikin sauri ta buÉ—e idon daga bacci daya saceta tunda suka fito Airport É—in.
Ido ta zuba mishi cikin mmkin ganinsu a harabar gidansu Abba suke da sauri ta ja ta tsaya murya cike da kaÉ—uwa tace.
“Appiy gidan nan kuma ba gidanmu zaka maidani baâ€. Yana kallon Hafiz da ya É—auki akwatin Fariyda ya nufi ciki Huzaifa riÆ™e da nashi jakar.
Yana gyara riƙo hannunta da take ƙwaceea yace.
"Angle kin dawo gidanki ne ai can kuma gidan Baba Malam ne.†ya ƙare maganar tare da ƙara jawato da sauri, ido cike da hawayen tace.
"Ni kam wlh bazan shigaba gidanmu zan komaâ€.
Abba dake kallonsu ta window bedroom nashi ne ya kafe idonsa akanta yadda take janye hannunta daga gareshi da yadda fuskar ke nuni da bata son shiga cikin gidan duk da baya iya jiyo mai take faÉ—a shiyasa yake ganin kamar kuka takeyi kuma a dole ya kawota.
Haka yasashi jan wani irin fusataccen numfashi fuska cike da fushi yace.
“Tabbas zanyi maganinka in kai ɗan yau ne nima tsowon yau ne, ba yadda za'ayi in zuba maka ido ka mulki rayuwar yarinya dan tana yiwa iyayenta biyayya su kuma suna maka kara, yadda take nuna bata son shigowa kaɗai ya tabbatar da gudun kasancewa da kai da takeyi, dan haka dole ka sake ta, ta samu mai sonta ya aureta bazan zuba ido kana cutar da ita da mari da duka harda targaɗata da karya ɗan ƴan uwnta, zanga ni da kai waye zaiyiwa wani biyayya!
Sake labulen yayi ganin ya É—agata cak ya shiga ciki da ita duk da tureshi da takeyi.
A hankali ya zauna bakin gadonsa yana fesar da zazzafan numfashi.
A can wurin su Mahmoud ɗin kuwa a parlournsa ya direta nan ma dan kiciɓis da sukayi da Huzaifa da Hafiz ne, a hankali suka raɓa gefe suka wuce ba tare da sun kuma ɗago kansu ba.
Ita kuwa Fariydan can nesa dashi ta matsa tana bubbuga sawunta kaÉ—an haÉ—e da yarfa hannunta murya na rawa ido cike da bacci da hawaye tace.
"Ni wlh bana so ka maidani gidanmu ba zan kwana anan baâ€.
Da sauri ya nufi inda take bayan ya ajiye briefcase nashi kan Centre table, cikin bubbuga sawunta ta koma can gefe tana yarfa hannunta haÉ—i da cewa. “Ni dai ka maidani gidanmuâ€. Da sauri ya jawota jikinsa haÉ—i da faÉ—awa kan kujerar dake bayansa da ita murya a sanyaye yace.
"Angle nan nefa gidanki É—akin mijinki uban Æ´aÆ´anki ina kike dashi a duniya da yafi nan, Please ki daina cewa in medake nifa mijinki neâ€. Tana Æ™oÆ™arin zillewa tace.
"Kowa fa yasan ka sakeniâ€. Da sauri yace.
"Amman ai ke kin san ba haka bane, kin san da igiyoyin aurena uku ras a kankiâ€. Tana tureshi tace.
“To ai babu wanda yasan da hakan sai ni da kai, kuma Mahaiafina da Mahaifiyata basu saniba ba izininsu ba komai kawai sai ka dawo dani nan nidai bazan iyabaâ€. Yana Æ™ara matseta yace.
"Ba abinda Malam zaice in ma yayi magna ni zan faÉ—a masa ba sakinki nayi ba, kuma zan nuna masa hujjataâ€. Murya na rawa tace. "Koma menene sai ka bari sai kayi magna dasu ka nuna musu hujjar taka su yanke hukuncin da sukaga ya dace akaina dole zan musu biyayya kamar yadda nayi musu a bayaâ€. Tallabe kanta yayi yana kallon idonta dake sheÆ™in hawaye a hankali yace.
"Karkiyi musu biyayya in dai hukuncin rabamu suka yanke Please My Angel karkiyi nesa dani duk rintsi wlh bazan iya rayuwa ba tare da kebaâ€.
Tana ɗan bubbuge ƙirjinsa tace.
"Ni dai ka maidani gidanmu wlh bazan kwana a nan ba, me zancewa Mamy na yanzuma duk sun koma saura ni kaÉ—ai in naje ince mata ina na tsaya ni da wayeâ€. Yana jawota jikinsa da kyau yace.
"Kice mata wurin mijinki kika tsaya tare dashiâ€. Kuka ta saka a sakalce cikin iyakar gaskyarta da tsanar kwana a nan É—in murya na rawa tace. “Abba nefa da kanshi ya maida ni ta yaya kuma zan dawo gaba gaÉ—i, ni bana son gidan nanâ€. Cikin fargaba yace.
"To naji zan maidake amman kingafa yanzu har sha biyu ta gota, kiyi haÆ™uri da asuba zan maidaki ko su Abba bazasu san nan muka dawo baâ€. Kai ta rinka jujjuyawa cikin gajiyar wuni zirga-zirga Taraba to Abuja, Abuja to Kano, a hankali ta fara sassayan kuka mai haÉ—e da É—an dukan Æ™irjinsa tana faÉ—in.
"Ni dai yanzu, ka maidani gidanmu, bana son Mamy na ta gane tare da kai muka tafi, bazan iya kallon su Ummi ba, me zan cewa Malam da Abba da ya maidani gida da kansaâ€. Ta Æ™are maganar da alamun bacci ya fara danne kuzarinta dan muryarta tayi Æ™asa, cikin hikima yake É—an jijjigata yana lilata haÉ—e da shafa bayanta a hankali yake faÉ—in.
"Naji ni zan medake da kaina da asubaâ€.
A hankali tace.
"Ni dai yanzu..â€. sai kuma tayi shiru alamun bacci ya kwasheta.
Ajiyan zuciya ya sauƙe haɗe da gyara zamansa, yana kallon fuskarta, murmushi mai cike da shauƙine ya subce masa tuno daren da sukaje Gembu yadda ta rinƙa yi masa abubuwa cikin maye, ta bashi dukkan farin cikin da yake buƙata a hankali yace.
"Yau É—inma da na É—ura miki maganin murar ai ki bani kakan daÉ—i naâ€.
Sai wuraren ƙarfe ɗaya ya miƙe da ita caɗak bedroom nasa ya nufa da ita, kan ƙasaitaccen gadonsa, numfashi mai sanyi ta fesar lokacin daya kwantar da ita, duvet ya jawo ya ɗan rugeta zuwa ƙirjinta, a hankali ya ɗan zauna gefe hannunsa ya ɗaga ya Azkarul Naum ya tofa a hannunsa ya shafa mata, idonsa ya tsaida kan lips ɗinta yana ganin yadda takeyin kamar wacce ta samu sweet haka take tsotsan lip ɗinta na saman a hankali yace.
"Shi yasa kika ƙware a iya tsotso duk abinda kika ritsa da tsotso sai kin masa irin tsotsar da bai taɓa jiba.
A hankali ya yunƙura ya shiga bathroom, wanka yayi gami da al'wala yana fotowa ya zira 3 quarter irin mai laushin nan, a hankali ya dawo kan gadon ya kwanta haɗi da jawo ta ya ɗaura kan ƙirjinsa yana mai yin Azkarul Naum.
A can gidansu kuwa tunda suka iso duk sukayi wanka suka cicci abinci sai kuma aka dasa hira.
Mamy ne ta kalli Saddiga data shigo goye da Zaitoon tana faÉ—in.
"Mamy bari in kwantar miki da princess anan É—akin mamanta yana cike surutun su Salma da Rashida ya hanata bacciâ€.
Kwaffa Mamy tayi kana tace.
"Ai sai ki kira Æ™anwar taki ki gaya mata su zo su É—auki yaransu, kuma suyiwa mutane bayanin munafurcin me suke É“oyewa ni dai nasan in dai Mahmoud ya saketane kuma babu idarsa akanta kamar yadda ta faÉ—a bazai je ya É—auketa suyi ta yawon hotel ba, dan haka ki gaya mata duk inda suke suzo su É—auÆ™i yaransu danni ba Æ´ar raino bace tasan dai Raihana tayi aure yanzu ni kaÉ—aice anan in kun koma Khadijah da Nana da suke garinma ba kullum suke zuwaba bare ita da kullum suna cikin yawon Æ™asashe tun Aminullah É—inma bare shi wannan Yaron Mahmoud yafi Aminullah É—in fita waje, dole suzo suyi mana bayani musan matsayin aurensu dan ba É—aukar sakarcin zamuyiwa baâ€. Ita dai Saddiqa tunda Mamy ta fara magna batace komai ba tana kwantar da Zaitoon ta koma gefe ta É—an zauna a hankali tace.
"To Mamy zan gaya mata, ni É—azuma na kirata Mahmoud É—in ne ya É—agaâ€. A kufule Mamy tace.
"Nima da na kira jiya shi ya É—aga yana ta min kame-kame, kawai ki gaya mata malam ne ke son ganintaâ€. Tana gyada kai tace. "Toâ€. kana ta juya ta fita, a bakin Æ™ofa sukayi kiciÉ“is da Mimy maman Salam kenan da Matar Uncle Muhd suna shiga É—akin Mamy suna faÉ—in.
"In mun biyewa hirar Fariyda da Mahmoud da Raihana da Bashir sai muyi kwanan zaune, mazane Allah ya basu Æ´an soyayyaâ€.
Dariya tayi ta wuce tana faÉ—in.
"Ina kuka manta Rashida ita da mijinta soyayyarsu bata tsufa, gacan Salma da Salim wlh har tausayi wayarsu nakeji wuni da kwana fa sukeyin magna a waya na rasa me suke faÉ—awa junaâ€. Dariya sukayi suka wuce riÆ™e da tray abincin da Amira tayi musu.
Anan gidan Abba kuwa.
Ido Ummi ta zuba wa Goggo Dada bayan Sulaiman ya tasa ƙeyarsu Hafiz da Huzaifa sun tafi part ɗin da suke.
"Hmmm Mahmoud yana son takalo fushin Abbansa ne, ya jamin É“acin rai dan yanzu gani zaiyi kamar da sanina ya tafi Taraba ya kuma kwaso yarinya ya dawo da ita bayan ya saketa gaban su yanzu kuma ace yayi gaban kansa ya dawo da itane ko kuma ya haukacene so yake ya lalata mata tarbiyaâ€. Numfashi mai nauyi Goggo Dada ta sauke haÉ—i da cewa.
"Ai kina da shaidu baki saniba, kuma kinji Sulaiman fa cewa yayi to ba matarsa bane mene dan ya dawo da ita, nifa ina ji a jikina wlh Mahmoud baiyi sakin nanba, tunda dama kawai ce masu yayi na tura mataâ€.
Kwaffa tayi haɗi da miƙewa tace.
"Saida safe zamuga iya gudun ruwansa da iyakar tsaurin idonsa.â€
Daga nan sukayi saida safe.
5:48 Am ta fito parlour da sassarfa tana gyara mayafin ta, tana taka Downstairs a hankali gudun kar a jita tafiyar take tana mgnar zuci.
"Yah Allah kasa har in haÉ—u da kowa har in fita, kafin ma su dawo masallaci na isa gidanmuâ€.
Ta ƙare maganar zucin tana yin ƙonon sauƙowar.
Dai-dai lokacin kuma Samira da Mamanta ke tsaye bakin Æ™ofar parlour Ummi dake cikin corridorn inda zatabi ta wucen Knocking Maman Samira takeyi Samiran na gefenta dan saboda Hafiz yace yana da lectures 7:00 Am shiyasa suka shigo da wuri dan É—aura kari, Ummi ne ta buÉ—e musu Æ™ofar haÉ—i da É—an ja da baya tana faÉ—in. “Hafiz ya saku tasowa da wuri ai da kun barshi yasa tea ya tafiâ€.
Maman Samira na shiga, sai kuma duk suka juyo ita da Ummi jin Samira ta saki É—an sautin jin daÉ—i haÉ—e da cewa.
"Oyoyo Aunty Fariyda kai Alhamdulillahâ€. Sai kuma kawai ta Æ™arasa gaban Fariyda data Æ™arasa sauÆ™owa tana karkaÉ—awa mata kai haÉ—i da mata alamun tayi shiru, rungume Fariyda tayi tana faÉ—in.
"Kai naji daÉ—i Hafiz ina kuke gidanmu zaiyi daÉ—i Our Aunty ina twins?â€. Jin haka ne yasa Ummi da Maman Samira fitowa, Ita kam Fariyda shiru tayi kamar bata wurin sai kanta data sunkuyar cike da tsananin kunya mai kashe jiki da ido ta kasa koda É—aga idon ta bare Æ™afarta.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.