Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 12 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 54
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
“Gani cinyeni nima abincine ai tunda ke mayyace da kika san kina jin yunwa me ya hanaki amsar abinci a gidan Yah Saleh. Can ma Hanzade da mukaje me ya hanaki kici duk abinda kike so kikayi ta zuƙan ruwan zafi kamar mai cutar sanyi, sai yanzu da muka dawo zan kwanta inyi baccin da kika hananiyi jiya kice min zakici abinci yunwa kikeji cikinni na ciwo, to gani zo ki cinyeni.†ido cike da kwalla tace.
"Masifa take min tana min gorin Yah Amin ya rasu, shiyasa bazan iya ci ba, a Hanzade Terrace kuma sanyine ya hanani ci.†a kufule yace.
"Eh to yanzu ai gani ga zafi sai kizo ki cinyeni zaki fi samun kwanciyar hankaliâ€. A hankali ta juya ta kwanta ta kife kanta a pillow gami da jawo duvet ta rufe jikinta tana mai sakin kukan cikin sanyin da yunwa a haka bacci ya É—an saceta.
A hankali ta yunƙuro daga kwanciyar tana rumtse idonta da ƙarfi gami da fara jan duvet ɗin jiki na rawa, ta farka a firgitacin daga bacci jin ana ajan duvet ɗin, Ɗan tsaki yaja ya sunkuyo hannunsa ɗaya dafe da kan gadon ɗaya hannun da ya kai yana jan duvet ɗin dan tada ita yaci gaba ja,
Cikin sanyin bacci tasa ihun gami da faÉ—in.
“Innalillahi wayyo Allah na Appiy Ketra Appiy ka taimakeniâ€. Tana magnar ne cikin magagin bacci da rawan jiki cike da É—imuwa da tsoron karen da yasata gigicewa, shiru yayi cikin duhun da baya iya ganinta. tsaki yaja fahimtar a gigice take bata da niyar yin shiru ne yasa hannunsa ya fizgo duvet É—in.
“Yah salamâ€. Ya faÉ—a saboda jin yadda ta fara buge-bugen neman ma É“oya da auna masa kira a jere a jere da magiyar neman taimako.
“Wayyo Allah na Appiy Ketra ka taimakeni Appiyâ€. Zama yayi kan gadon ya miÆ™a hannunsa ya fara lolubo ta inda take, da Æ™arfi ya fizgota kusa dashi kafaÉ—unta ya riÆ™e da hannunsa duka biyu yace.
"Ke zan tsinka miki marifa in baki rufe min bakibaâ€. Ai bata ma jishi ba bare ta sahirta sai fizgewa take da yunÆ™urin Æ™wace wa.
“Da ƙarfi ya fizgota sabida juyawar da tayi tana tattaro duvet, kanshi ta faɗo da ƙarfi.
“Ke nine karenne ko me kike nufi?â€. Da Æ™arfi ta rungumeshi Æ™amÆ™am cikin haki da rawan jiki take Æ™ara Æ™waÆ™umeshi.
Shiru yayi tamkar ba numfashi a jikinsa, yana jin yadda jikinta ke tsuma da bugun zuciyarta dake harbawa da ƙarfi-ƙarfi. Ita kuwa Fariyda har lau tana ƙwaƙume dashi gam, a hankali ya fara janye jinsa sai kuma ya miƙe tsaye ya ɗan matsa gefen gadon da ita a jikinsa jin yadda ta ƙara shaƙo wuyansa ta maƙaleshi, hannunsa yasa ya kunna wutan ɗakin fuskarta ya ɗan leƙa idonta dake rufe gam-gam ya ɗan kalla sai kuma ya fara magna cikin shakeƙƙiyar muryarsa da ta shaƙe ta maƙale wuyansa da tayi yace.
“Ke zaki kashe ninfa ki sake min wuya, ki buÉ—e ido ki gani ba wani kare a nan sai dai ko in aljanu kike daâ€. Ya Æ™are maganar da sauÆ™e numfashi mai nauyi saboda jin ta sakeshi, gefe ta tsaya tare da fara gyara rigarta daya tattare tayi Æ™asa da kai kamar munafuka ta fara gyara Scarf É—insa dake wuyanta da hularsa. Harara ya auna mata ya tsuÆ™e fuska yace.
"Ga nan abinci sai ki É—auka kiciâ€. Ya Æ™are maganar yana komawa kan sallayar ya kwanta yana rufe idonsa da bakin Scarf É—in wuyansa alamun baya son hasken. A hankali ya lumshe idanunsa yana faÉ—in.
“Ya za'ayi bazakiyi ta ihuba kin kwanta ba al'wala ba addu'a sai charting da Æ™attin banza, ni ki addabeni da ihun Ketra da baya nan yara Æ™anana na bacci sai ke ki buwayeniâ€. Baki ta tura ba tare da ta kalleshi ba bare tace wani abu.
Tray abinci da ya fita ya amso mata a kitchen ɗinsu ta kalla, sai kuma ta zauna a bakin gadon a ƙasa tana maida numfashi, tray ta ja ta fara cin abincin tana waige-waige tsoro, kusan rabi taci ta ɗaura da coffee sai kuma ta shiga bathroom ta wanke bakinta ta sabunta al'walan bacci ta fito ta kwanta bayan tayi addu'a. Duvet ɗin ta ƙara jawowa ta duƙunƙune a ciki har zuwa kanta a haka bacci ya ɗauketa.
A ƙalla 43 minute da kwanciyarsa amman bacci ya ƙauracewa idonsa saboda hasken dake kunne a ɗakin tsaki ya ɗan ja ya miƙe tsaye dan kashe hasken da ya hanashi baccin.
time ya kalla a wayarsa daya miÆ™e da ita. 1:00 Am. A fakaice ya É—an kalleta, sai kuma ya É—an tsaya a bakin gadon, ganin yadda take duÆ™unÆ™une cikin duvet da take rufe dashi har kanta duk da haka kuma rawan sanyi take yi, hannunsa ya miÆ™a da nufin kashe wutan sai kuma ya janye hannun gaban gadon su Zaid ya wuce gyara masu rufuwa yayi sannan ya juyo dan kashe wutan, karkarwa jikinta keyi bakin gadon ya É—an zo ya tsaya a Æ™alla 2 minute sannan ya sunkuyo ya É—an ja duvet É—in, shiru ko motsi batayi ba tabbacin bacci take yi sai karkarwar da jikinta ya Æ™ara kan lips É—in ta tsaida idonsa, ta turo É—an lip É—inta na Æ™asan kaÉ—an na saman kuma ta ritsashi da tsotso tamkar yar yayen data rasa nannan É—inta, gashinta dake baje kan pillow har zuwa kan Æ™irjinta saboda zamewa da hular tayi ne ya É—an kalla a fizge. “Hmmmmâ€. Ya sauÆ™e numfashi, sunkuyowa yayi dan ganin rawan jikin yayi yawa ya wuce ace na sanyin Istanbul ne da alamun akwai zazzaÉ“i hannunsa ya É—an matso dashi kan wuyanta zafi yaji rau har jikin Scarf din sa yaji É—umin, matssss yaja tsaki.
Briefcase nashi ya buÉ—e magungunansa dake ciki ya fara dubawa, kala biyu ya É—auke daga cikinsu kan bedside drawer ya ajiye searched É—in magungunan tare da goron bottle water É—in daya É—auka kan Tray abincin da ko rabinsa bata gama ciba.
Bakin gadon ya zauna yana mai kallon tsanantan rawan jikinta kamar wacce zata sume sai tsotsar da takeyiwa lip dinta take tana sauƙe numfashi mai zafi.
Hannu shi ya kai kan wuyanta ya fara jawo Scarf din dake zageye da wuyanta, da sauri ta buÉ—e idonta tana cewa.
“innalillahi Appiy ketraâ€. Sai kuma tayi shiru ganinsa zaune a gabanta ya tsuÆ™e fuska tana Æ™ara jawo duvet É—in tace.
"Me nayi kuma?â€. Lip É—inta na saman da yayi jazir sai sheÆ™i yake yi sabida tsotsarsa da takeyi ya É—an kalla a fakaice ya miÆ™o mata searched É—in maganin.
“Kishaâ€. Ya faÉ—a a sanyaye. Cikin tsanar shan maganin tace.
“Ni lfyta Æ™alauâ€. Juyowa yayi kan gadon da kyau yace. "Kishaâ€. Kai ta jujjya tana Æ™anÆ™ame jikinta, hannunsa ya kai da nufin jawo Scarf din da sauri ta matsa tare da cewa. "Ni ka barni inyi bacciâ€. Fuska a haÉ—e yace. "Bani abuna in ma bazaki sha mgni ba ya rage nakiâ€. Cikin muryar bacci tace.
"Wanne abun ka ni ba abunka da na É—aukaâ€. Yana kai hannunsa yace.
“Ai bazaki iya daina min sata ba, sai ranar da na karya wuyan zanga a inda zaki É—aura Scarf din harma da turarena kika Æ™ara fesawa koâ€. Tana Æ™ara ja da baya tace.
"Ni ba abinka da na É—auka wannan cikin waÉ—anda aka bani a hotel É—in nan ne, turarenka kuma ina zan ganshi maâ€. Da Æ™arfi ya fizgo Scarf din har saida ta matso kusa dashi sunsuna shi yayi yana mata kallon takaici yace.
“Ke Æ™anwar uwarsu ce ai yan hotel É—in dole su baki kaya, ba ga turaren nawa baâ€. Ya Æ™are maganar yana É“alle maganin ko wanne É—aya ya cire. "Ni dai ba barauniya baceâ€. Ta faÉ—a tana turo lip É—in Æ™asa hannunta ya jawo da Æ™arfi ta matso kusa dashi kan wuyanta ya manna hancinsa inda Æ™amshin turaren jikin Scarf din ya mamaye.
Da ƙarfi ta rumtse idonta saboda ɗumin numfashisa daya ratsa fatar wuyanta.
Da ƙarfi ya juyota ta buɗe baki da nufin yin ƙara ya afa mata maganin a bakinta cikin zare mata ido yace.
“Kina fiddashi sai na tsinka miki mariâ€. Yayi magnar da É“alle marfin goron ruwan ya sa matashi a baki, ido ta rumtse da Æ™arfi cikin tsananin sanar maganin ta fara kakarin amai, gefen tafin hannunsa ya manna kan bakin nata sai kuma yasa yatsarsa ma nuniya da babban ya matse hancinta yana zare mata ido yace.
“HaÉ—iyeâ€. Cikin rawan jiki da neman numfashi ta haÉ—iye. MiÆ™ewa tsaye yayi yana goge hannunsa da Scarf É—in ya wurga mata shi kanta, ya kashe wutan É—akin ya kwanta.
Ƙarfe biyar dai-dai ta farka daga baccin duvet ɗin da tun da zazzaɓin ta ya sauƙa ta farajin zafi ta ture gefe tayi saurin jawowa ganinsa tsaye kan sallaya yana Sallah, sai da ta gyara rigarta ta sauka ta ɗaya gefen ta wuce bathroom.
Wanka ta farayi da ruwa mai zafin gaske duk da yau sanyin bai kai na jiyaba wanke bakinta taya tare da al'wala kana ta fito, ganin baya nan ne yasa ta sake tayi salla da azkar sannan ta kimtsa, bayan su Zaid sun farka tayi musu wanka suma ta kimtsasu cikin kayan sanyi.
Jin ana buga mata ƙofane ta miƙe taje ta buɗe ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya miƙo mata Tray ɗauke da abincinta da nasu Zaid sai flacks ɗin tea amsa tayi kana ta koma ciki.
Sa'ad ne zaune gaban Mom ɗinsa da Uban riƙonsa gaba ɗaya baya cikin nitsuwarsa.
“Kayi haƙuri Sa'ad yadda Mahmoud ɗin ya faɗa shine mafi dacewa sabida kaucewa saɓawa Allah, sannan tunda har ta tabbatar maka baya sonta kuma kaiman kaga tabbacin haka tunda har shi ke bada shawarar yadda zakuyi abin a sirri ta yadda ran iyayensa bazai ɓaci a kansa ba, to ka haƙura ni da ka gayamin zaka zoma da zan hanaka. Dan nima ina bincike kan ɗan uwansa da yace yana nan Gombe kuma akwai wanda yace min ya sanshi, ita kuma Fariyda ka dena damu da ƙinn baka number da tayi, ina da baccin taƙine dan kiyaye haƙƙin igiyar auran dake kanta kuma shiyasa bata amsa kiranka, take kuma katse kiran koda shi ya ɗauka ya bata wannan shine tabbacin tasan abin da takeyi yar gidan mutuncice.†cikin ɗimuwar rashin ɗaukar wayarsa da ciwo bai bar Mahmoud ɗin ya ɗauki kiran iyayensa ba yace.
“Abba ina sonta wlh ina son Fariyda irin son da nima ban san adadinsa ba, bana son rasata domin itace kaÉ—ai matar da nakeji zan iya rayuwa da ita, ina kiran layinshi baya picking call na É—aya number da ta bani kuma ko na kira baya shiga sai WhatsApp da nayi magna yafi sau goma ba amsa, kawai dai muje Kano nan tunda ganesu bazaiyi wuyaba da sunan Al'ummah zan gano inda yakeâ€. Numfashi mai sanyi Mom da son da Sa'ad É—in ke yiwa Fariyda yasata jin Æ™aunar ta tamkar ranta tace.
“Nima ina sonta Sa'ad kuma in sha Allah sai ka sameta bi'izinillahi ta ala burinka zai cika domin inayi maka addu'a, amman gskyar Fariyda da take kinyin mgna da kai kuyi ta istigfari na mgna da kayi da ita lokacin da kaje na tunda da aurenta ka daure mu kara sati uku zuwa wata É—aya muga in har bai kiraka ba, kuma ba amsa a WhatsApp sai muje Kanoâ€.
Cikin gamsuwa da hakan Alaji Usman É—in yace.
"Yauwa hakan shi yafiâ€.
Istanbul
Tunda ya fita bai dawo ba, itama bata sa ran dawowarsa ba dan tunda suka zo Istanbul in ba jiyaba bai kwana anan ba kai ko awa biyu ma baiyi ba.
Shi kuwa Mahmoud tunda ya fita bai zauna ba, aikin haɗa kan kayyakinsu da yayi kwanaki yana duba aikin da ake yi musu da hada kayansu kafin ciwon yaci ƙarfinsa ya kwantar dashi, komai ya haɗu kama daga carperts darduma blankets da labulayen yan gaske da shi ya bada samfurin ko wanne aka buga musu, Alhamdulillah kuwa ko wanne Company sun gama hada dukkan abin da ya nema har an fara parking na kayyakin ana libgawa a manyan kontenoni dake bakin tekun da sakasu cikin jirgin ruwa zuwa Lagos. Gab da magrib ya baro bakin tekun dan tirelan takalma da rigunan da akayi musu ya iso har an gama sasu a kontenarsu an sa a jirgin ruwan har ta kama hanya ne yasa ya fito cikin gamsuwa da kammala komai da yake da nufin yi a Istanbul ɗin gidansu ya wuce kai tsaye .
Bayan sallan isha kwance take tana lulluɓe da duvet ɗin iya kantane kaɗai a waje waya da ke kan kunnenta ta gyara riƙewa tana kallon su Zaid da keta harkokinsu a kan gadonsu.
"Nima ban san yaushe zamu dawoba Yah Mujahid amman in sha Allah mun kusaâ€. Ta faÉ—a cikin jin gamsuwa da magna dashi a tudu biyu É—an uwa kuma miji a gare ta in Allah yasa sun koma. Kai ta É—an É—ago jin an tura Æ™ofar É—akin an shigo. Wurin su Zaid dake ta É—aga hannu suna haÉ—a bakin faÉ—in.
"Owo Appiy! Appiy!!â€. Ya nufa tare da buÉ—e musu hannu rungumesu yayi a jikinsa yana kissing neck É—insu dariyar da sukeyi ne yasa ta É—an kallesu ta gefen ido, sanye yake cikin tattausar Turkish jallabiya maroon color mai masifar kyau da Æ™elli tayi cib da jikinsa hulÉ—ar dake haÉ—e da jallabiyar na kwance kan kafaÉ—unsa sai takalmi sauci milk color da hular saÆ™a shima milk color da yasa a kansa, hakama Scarf din wuyansa shima milk ne, Æ™amshi yake zubawa tamkar fure flower, baki ta taÉ“e ta maida hankalinta kan wayar da take yi murya can Æ™asa tace.
“Yah Mujahid nima nayi missing É—inkufa, ina son ganin Mamy na dasu Ummiâ€. ÆŠauke kunnensa yayi daga jin maganar da take yi É—in, ya ajiye su Zaid É—in bakin gadon travelling luggage dinsa dake can gefe ya kalla komai a kimtse yake wuri É—aya sai jakar dake gefe na kayan da yasa Arda ya kawo musu ya bada a Reception aka kawo mata, wayarshi ya zaro time ya É—an duba takwas harda kwata na dare.
Knocking ɗin da ake yi ne yashi juyawa dan zuwa buɗe ƙofar.
"To Yah Mujahid karka manta faâ€. Ta faÉ—a cikin muryar dake nuna jin dadi. Ko ta inda take bai kuma kai idonsa ba, tray abincin da aka kawo musu ya amsa.
Kan table ɗin dake gaban kujera ya ajiye tare da miƙawa su Zaid hannu da gudu suka zo. Su ya fara bawa saida sukaci ya goge musu baki sannan ya jawo plate ɗin fruits, ya fara sha.
Ita kuwa Fariyda a hankali ta juya ɗaya gefen taci gaba da wayarta. Bayan kamar 46 minute ta juyo da kanta tsaye ta hangoshi rungume dasu a bakin ƙofar, baki ta ɗan taɓe bayan ya fita, plate ɗin fruits da ya rage ta jawo ta fara shan strawberry and Apple da ya rage, tana cikin sha ne taji ana Knocking tasan ba shi bane dan in shine sai dai ya shigo kawai dan shima da card a hannunsa cikin mamaki ta zuba mishi ido tare da cewa.
“A...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.