Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 44 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 83
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*
_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaÉ—en gida Shararriya kuma Æ™asaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maÉ—i, garin Hakkin mayi, garin É“elÉ—amhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar RiÉ—i wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin MaliÆ™i mai masifar Æ™arfi da matse mace, ka masin DaÉ—i har MaÉ—igan Akwai, kwanon Æ™asaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inÆ™antacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haÉ—insa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin RiÉ—i mai Æ™arfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Æaure, tuwon É“auren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin Æ™amshi kasance da Shu'umin Æ™amshi wanda ze gigita Æ™waÆ™walwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da Æ™asaitar Rayyan Naaan amma lokaci É—aya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riÆ™e ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haÉ—in da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya KaÉ—an) ko kinsan hakan nada alaÆ™a da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer É—in ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuÉ“i number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaÉ—in Nigeria harma da Æ™etare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muÉ“atawa kanmu lokaci...ðŸ¤ðŸ»ðŸ¤ðŸ»ðŸ¤ðŸ»ðŸ¤ðŸ»ðŸ¥°ðŸ˜˜sai.kunzo. sayan na gari maida kuÉ—i gida,
Baki ta tura ido cike da hawaye take watsa mishi harara cikin iyakar gaskyarta tace.
"Ni bana sonka ai kasan bana sonka, kamar yadda nima nasan baka sona kaida kankama kacemin ai dai kin san bana sonki kuma bazan sokiba har gaban abadan.
Nasan kuma haka ne kuma nima haka ne. Kasan bana sonka ko? Kuma bazan taÉ“a sonkaba har gaban abadan ka dai kasan bana sonka? Dan haka ni bazan rayu da kai ba yanzu sai ka yi min sakin kamar yadda su Abba sukace tunda ka san bana sonka ai ko?â€. Ta Æ™are maganar da alamar tambaya. Jajayen idanunsa ya zuba mata jiki na rawa yake gyaÉ—a mata kai alamar eh ido cike da wasu tsumammun hawayen da suka idanun sauya launi a take sukayi Nasir murya na rawa haÉ—i da cushewar numfashi da tunani yace.
“Eh na sani ai tunda naji labarin ranar da aka É—aura mana aure har suma kikayi nasan bakya sona tunda har suma kikayi kawai dan ance mini an aura min ke dan kin tsaneni kin maidani masifa da zama dani zai saki suma ai nasani nasan bakya son sumafa kikayi Fariyda kawai dan zaki rayu dani a matsayin miji kika sumaâ€. Cikin galabaitar gajiya da yunwa ta zuba masa ido tana jin yadda yake ta mai-maita kalmar ta sumar nan sau ba adadi yana mgnarne daga can Æ™asan zuciyarsa take fitowa da zafin, fuska a tsuÆ™e tace.
"To ni dai har abadan bazan sokaba, ka rubutamin takardata kamar yadda iyayenmu suka baka umarni, ka barni in samu in auri wanda yake sona tun ina Æ™arama. ba kai da nasan tun fil azal baka sonaba ka tsaneni kai da kanka ka bani damar kula maza da aurenka a kaina da na biye maka sai in kai kaima wutaâ€. Ta Æ™are maganar tana zubda hawaye.
Murya na rawa yace.
"Please dan girman Allah ki daina tuna min wannan jahilci da rashin sanin ciwon kai da nayi, ni da kaina inajin tsanar kaina in na tuna wannan abu Please Farriyyhah ki yarda dani nasan tabbas na Æ™iki Æ™i mafi muni da tsauri, amman wlh a yanzu duk tsaurin kiyayyar ya zama so Please ki daina cemin zakije ki auri wani wlh zuciya zata iya bugawa Please My Angelâ€.
Tureshi tayi tana faÉ—in.
"Nifa Wlh sai ka rabu dani dole ka sak...â€
Sai kuma tayi shiru ganin yadda yayi da fuska murya a kufule yace.
"Wato har kin mance sharaÉ—in Mamy har zaki cemin in sakeki ko? In kin mance na Mamy tunda Ita kin rainata ai bazaki mance na Allah ba da ya tsinewa duk matar da ta tambayi mijinta saki, wlh kika sake yimin mgnar saki ko mgnar waÉ—annan banzayen jahilan wlh yau wuni zanyi akanki har sai kin kasa magna bare ki yi min rashin kunya kin ganni nan sai in kwana ban gajiba tausayunki ne yasa na barki kuma duk abinda zan yi dake halal ne lada ma zan samuâ€. Ya Æ™are maganar yana nuna mata papi É—insa, haÉ—i da miÆ™a hannunsa ya jawo goran Admiral É—in.
Ita kuwa tunda ya fara magna tayi shiru haɗi da tura baki ido na cikowa da sabbin hawaye ganin Papi ɗinsa kuma yasata rufe ido tana matsawa gefe, jin ya manna mata bakin gorar Admiral ɗin ne yasa ta buɗe idonta dake cike da hawaye, fuska a tsuƙe yace.
"BuÉ—e baki ki shanye duka, bazaki cutar min da kanki da yunwabaâ€. A hankali ta fa Sipping Admiral É—in tanayi tana zubda Æ™wallan har saida tasha kusan rabi ta janye kai a hankali tace.
"Ni na Æ™oshi ka buÉ—e min zan tafi gidan Hajja Innaâ€.
Maltina ya ɗauka ya ɓalle marfin yasa mata shi a baki, yadda ya tsareta ne da yadda ya kamo hannunta ya ɗaura kan abinda ke sa hanjin cikinta hautsinewa yasata sha fiye da rabi.
Miƙewa yayi ya kamo hannunta ya miƙar da ita bakin gado ya kawota ya kwantar da ita haɗe da jan duvet ya rufeta. Guntun Admiral ɗin data bari yasha da ƙarin gora ɗaya.
Kan gadon yazo ya kwanta haɗe da jawota jikinsa yana ɗaura kanta bisa ƙirjinsa yace.
"Kiyi bacci in mun tashi zan kaiki, kinga har yanzu maganin murar nan bai gama sakeki baâ€. Shiru tayi tana jin yadda yake shafa bayanta, a hankali kuma ya fara sauya fitar numfashi haÉ—e da fara jan jallabiyar, da sauri ta miÆ™e zaune ido na zubda wahaye murya na rawa cikin gajiya da tarin bacci tace da tsoron lamarinsa cikin rauni tace.
"Please dan Allah kayi haÆ™uri ka barni inyi bacci wlh na gaji bazan iya bafaâ€. Kai ya fara jinjina mata kamar gadangare idanunsa da suka fara sauya launi ya zuba mata yana zare jallabiyar jikinsa ya cilla gefe, da sauri ta rufe idonta jiki na rawa ya rungumeta cikin sanyi yace.
"Bazan miki komai ba, ina son samun É—umin jikin kine My Angel zamuji sauÆ™in sanyiâ€.
Ya ƙare maganar yana zare mata jallabiyarsa dake jikinta ya cillashi gefe.
Hmmmmmm suka dauƙe numfashi da ajiyan zuciya a tare lokacin da tafarsu ta mannewa juna, wani irin masifeffen kunya ne mai haɗe da takaici ya rufeta jinta ba komai a jikinta shima ba komai a nasa jikin, wai yau itace da Mahmoud a wannan yanayin mafi ƙololuwar kusancin duniya suna gari ɗaya! ɗaki ɗaya! gado ɗaya! Duvet ɗaya! Pillow ɗaya! Fatarta manne da tasa fatar a yanayin da babu wani sutura a tsakaninsu sai duvet ɗin daya rufesu.
Juya kanta tayi jin yana ƙara ƙwaƙwumeta a jikinsa kamar zai maida ita cikin cikinsa ya ilahi wai a raye take ko a mace ido biyu take ko a mafarki ne koko farke a haka yasata rufe ido kamar yadda shima ya rufe nasa idon a haka sukayi bacci.
Ƙarfe tara dai-dai aka fara shirin fansar idon.
Raihana da saida tayi wanka akazo aka ɗauki Humaira taje gidansu ta ɗanyi mata make-up acan sannan suka dawo, har lokacin dai ba Fariyda ba dalilinta sai ƙarfe goma dai-dai aka fara fansar.
Alhamdulillah anyi fansar idon amarya lfy sha ɗaya dai-dai aka gama kamar yarda al'darsu take uwar ango ta fanshi ido amarya da saniya da shanu mafarin garke kenan sauran yan uwa duka kowa ya fanshi idon amarya kana aka fara na ango sai ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi daga fansar idon inda ango yasha ruwan kuɗi da kyautan shanaye Sulaiman kam ya zama abokin ango tuni komai dashi akeyi hakama Farooq ko ina yana maƙale da Zainab shi kuwa Sulaiman tarko nai ya kama kurciya shida Humaira sun fara zantawa bisa sahalewar Yah Farooq.
A hankali take tafiya da ka gani kasan taji jiki a hannun maza, duk da ba É—ingishi take yi ba, amman da ka gani kasan ta gurzune iya kar gurzuwa abu ya haÉ—u da yongwali sarkin raki.
Hand bang ɗinta dake hannunsa ya gyarawa riƙo haɗe da miƙa mata hannunsa ɗaya dan ganin kamar zata faɗi, da ɗan ƙarfi ta riƙeshi dan tabbas ta kusa faɗuwa sawunta sam ba ƙarfi sai rawa sukeyi.
Ido Hajja inna ta zuba musu kamar ta samu TV har Saida suka iso tsakiyar parlour ArÉ—o Habu kakansu sannan tace.
"To saketa mu ga uwar yauÆ™i ke ko yaushe aka ganki largi-largi kamar bulala sai raki yanzu haka zatace yunwa takeji ko shi yasata wannan narkewarâ€.
Murmurshi ArÉ—o Habu yayi haÉ—i da nunawa Mahmoud wurin zama kusa dashi.
Zama yayi tare da jawo hannunta ya zaunar da ita gefe yana kallonta yess tana da longomi kam dan yasan yayiwa idaya abinda yafi haka da yake ita jakace gar zaka ganta, baima yi zaton ritsawar da yayi matan nan zata iya tashi ta tafi da sawuntaba.
Hannu ya bawa Ardo Habu suka gaisa sai kuma ya É—an gyara zamansa ya matso kusa da ita sosai kanta ya jawo ya manna da kafaÉ—arsa a hankali yace.
"Bacci ko yunwaâ€. Lip É—inta na Æ™asa ta tura murya na rawa tace.
"Duka biyuâ€.
Hajja inna ya zuba wa ido sai kuma ya kwaɓe fuska yace.
"Tace bazataci komai ba sai abincinki zataci Bashir da kanshi ya kaimana abinci taÆ™i ci wai naki zataciâ€.
Ya ƙare maganar yana ƙara sunkuyo da kanshi ya manna lips ɗinshi a goshinta.
Worman dake jere gaban dattijon Hajja Inna ta jawo haÉ—e da fara zuba musu zazzafan dandarerun naman zabbi da tayi, ganin ta jawo wani bowl É—in zata sane yace. "Bari haka wannan ya isaâ€. Tana kallonshi tace. "To kai É—infaâ€. Gyara zamansa yayi yana gyara mata jinginar, idonsa na kan É—aya kular da Hajja inna ta buÉ—e wanda yake cike da chips soye plate ta jawo ta zuba mata kana ta gyara zamanta ta jawo mug ta fara haÉ—a mata tea. Fork ya É—auka yana gyara zamansa ya soÆ™o tsakar dandarerun haÉ—e da chips É—in ya kai mata baki yana faÉ—in.
"Ha buÉ—e bakiâ€. Cikin kasalar rashin bacci da uban gajiyar daya tara mata da sauran É—an ragowar aikin maganin muran da rashin bacci hanata janye jukinta a hankali ta buÉ—e baki, cikin kulawa yasa mata.
Murmurshi ArÉ—o Habu yayi haÉ—i da cewa.
"Sannu tattabara uwar Æ™oto dan sakalci sai ka bata a bakiâ€. Idonshi na kanta yace. "ArÉ—o ta gajine shiyasaâ€. Baki Hajja inna ta taÉ“e haÉ—e da cewa.
"Me tayi da zata gaji yarinya ko yaushe lagwai-lagwai kamar ganye ba auki sai raki yar tafiya daga Kano zuwa nan ai nima tsohuwa ina yinta kuma bana jemewa haka in narke kamar zan suma bare ita yarinyaâ€. Girarsa É—aya ya É—an É—aga mata yana kuma kai mata sokar naman, ko taunawar a kasalance take taunawa a hankali.
Jin sallamar su Adda Nana ne yasa Hajja inna cewa. "Ai na zata bazaku isoni ba, tun jiya nake tsammanin nan zakuzo mu kwana nayi muku girki ba wanda yazo sai su Farooq da Sulaiman da Mujahid, sai yau da safe su Abu su kam duk sunzo tunda ni uwarsuceâ€.
Kusan a tare suka shigo da sallama a bakinsu sai kuma duk suka É—an kalli juna haÉ—i da zama kan kujerun.
Saddiga ne ta kalli Mahmoud da yayi tamkar baishi shigowar suba, sai tea da ya fara bawa Fariyda dake kiciniyar tashi cikin raÉ—a yace. "Angel tsaya ki sha teaâ€. Tana kwaÉ“e fuska ta turo É—an baki a hankali tace. "Appiyn Alhamdulillah I'm full.†Kai ya É—an jujjuya mata, yana Æ™ara manna kanta da kafadarsa, kusan a tare da Khadija Aunty Rashida sukace.
"Appaiyn Zaid kun rigamu isowa kenan ina kwanaâ€.
ba tare da ya kallesu ba yace.
"Our Auntys ina kwanaâ€. Ya faÉ—i yana lumshe idanunsa jin Zaid ya rungumeshi ta baya.
Adda Nana Aunty Saddiqa da Sadiya ne suka amsa suna cire idonsu daga kanshi ganin yadda yake ƙara sa Fariyda mug ɗin a bakinta.
Ita kuwa Fariyda cike da kunya take ɗan matsawa daga jikinsa haɗi da jawo Zaitoon ta rungumeta tana mai sauƙe numfashi ta ajiyeta a tsakaninsu.
dai dai lokacin kuma Su Farooq suka shiga
Sulaiman dake bayan Mujahid da ya ja ya tsaya haɗe da yin ƙasa da kanshi cikin tsoron hango Mahmoud da ya kasa dannewa yace.
"Innalillahiâ€. Gefensa Sulaiman ya raÉ“a yabi bayan Farooq da Sadiq Humaira na biye dashi a baya Zainab na gefen Farooq É—in.
Zama sukayi gaba ArÉ—o Habu, bayan sun gaisane Sulaiman da har lau idonsa na kan Mahmoud ne hannu ya bashi yana faÉ—in.
“Ina ka maÆ™aleneâ€. Yana amsar Zaitoon daga hannun Fariyda yace.
"Sama na maÆ™aleâ€. yayi mgnar da murya can Æ™asa yadda Sulaiman É—in ne kaÉ—ai zai iya ji.
Hannu ya ɗan miƙawa Ardo Habu yana faɗin.
"Mu zamu wuceâ€. Yana bashi hannu yace.
"Zamu É—an kwana biyu ai ko kaji kalar sanyin garinmuâ€. Fuska ba walwala yace.
"In sha Allah zamu sake zuwa na musamman zamuyi gida anan dan kuâ€. Ya Æ™are maganar yana dire masa rafan kuÉ—i yan dube-dube guda biyar, sai kuma ya ajiye biyu gaban Hajji Inna ya miÆ™e Zaid da Zaitoon na maÆ™ale da wuyansa.
Miƙewar da yayi da juyowan da yayi haɗi da ido biyu da sukayi da Mujahid, da murɗawar da cikinsa yayi da bugun zuciyarsa duk a tare suka kasance, da sauri yayi ƙasa da kansa haka kawai yaji Mahmoud ya masifar bashi tsoro, idonsa har kamar wuta yake feso masa shi yasa yayi ƙasa da kai, shi kuwa Mahmoud tunda yaji an ambaci sunan Mujahid ɗin ƴar guntuwar fara'rsa ta ɓace ɓat.
ÆŠan juyowa yayi ya kalleta murya a daÆ™ile yace. "Mu tafiâ€. Fuska a kwaÉ“e ta zuba mishi ido ta buÉ—e baki da nufin magna taga ya juya ya nufi hanyar fita yana faÉ—in. "Taso mu tafiâ€. Gefen Mujahid É—in ya É—an tsaya yana masa wani irin kallo haÉ—i da hucin numfashi mai zafi wanda sautinsa yasa Mujahid É—in da tuni jikinsa yake rawa far-far a tsorace ya kare fuskarsa da hannunsa mai lafiyar É—aya hannun da Mahmoud ya karya kuwa yayi saurin karkacewa jiki na rawa tsoro ya juya a saba'in ya fita. Kwaffa yayi haÉ—i da mara masa baya.
Haka ne da Sulaiman ya gani yayi saurin miƙewa yabi bayan Mahmoud ɗin.
Ita kuwa Fariyda dariyar dasu Aunty Rashida suka farayine ya ankarar da ita, cikin dariya harda riƙe ciki Khadijah tace.
"Hege mai wuya kamar lagoni yaga maza wlh duk jikinsa rawa yakeyiâ€.
Aunty ta dafe cikinta tana kallon Fariyda data haÉ—e fuska cikin dariya tace.
“Da shegen Æ™ugu kamar na buzuzu ya wani É—amare kamar gangan yana ganin Mahmoud fa ya kasa Æ™arasowa wlh duk jikinsa tsuma yakeyiâ€. Adda Nana dake danne dariyarta tace.
"Yo gskyarsa ai gwara ya gudu ko ya samu ya tsira da sauran haÆ™oransaâ€. Cikin dariya Aunty Saddiqa tace. "Yo zai bari kansa yayi murfune yasan karonsa dashi na farko yadda abun ya kaya masa haÆ™ora biyu babu har yanzu sai wawulumon baki ga hannu a karye ina zai tsaya a Æ™ara masa wani karayanâ€.
Aunty Sadiya tace.
"Kai wlh ya bada maza da gudu ya fita faâ€.
ArÉ—o Habu ne ya kalli Salma dake cewa.
“Hege yaga maza bisa kansa dole ya tsere, kuma fa Appiy ya bishi karfa yaje ya masa wani abunâ€.
Jin haka ne yasa Fariyda miƙewa tayi wajen da ɗan sauri cike da tsoro kar yaje ya illatashi, Arɗo Habu kuma Farooq da Sadiq dake zaune gabansa ya zubawa ido haɗi da cewa....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.