Sakar Makafi Littafi Na 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 35 of 49
By
*GARKUWAR MARUBUUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 75
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Suna Ina? A wani Hali suke ciki? Me sukeyi musu a can? Sunacin Abinci? Wanne irin fargaba zuÆ™atansu keciki?, ya iyayensu da Yan uwansu keji?. Allah yasa basu haiÆ™ewa budurcinsu ba. Tabbas ma kuka sukeyi Wlhi Akwai tashin hankali ka Auna hakan akanka ya hayyu ya qayyum Allah ka kubutar dasu cikin Amincinka ya rabbi ba iyayensu kadaiba da yan uwansu harmu munaji ajiki da zuÆ™atanmu Allah ka duba bayinka mu bazamu iya ba Amma Allah kana ganinsu Allah ka shiga lamarinsu ya Ubangiji Annabi Muhammad SAW Allah ka kare rayukansu da lfyarsu da budurcinsu da natsuwarsu da imaninsu!!! Allah ka hana waÉ—annan azzaluman samun damar cutar da WaÉ—annan yaran mata bayinka masu rauniðŸ™ðŸ»ðŸ™ðŸ»ðŸ™ðŸ»ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜
“Salma jikin nasa har haka yayi tsananin da Abba da Ummi ma suke kuka, to yaushe ya fara mishi?â€. Sai kuma ta É—anyi jim tana sauraronta fuska cike da kaÉ—uwa tace.
"To Allah ya kawoki lfy, Salman É—in ya isone ko dai in turi Sadiq yazo ya É—aukeki tunda kince Salim É—in ne tare dashi, ba yadda za'ayi ya bar wurinâ€.
Sai kuma ta É—anyi shiru na seconds kana tace.
“To Allah ya kawoku lfyâ€. Daga nan ta katse kiran. Fariyda da har lau idanta ke kafe a kanta tace.
“Meke faruwa meya sameshi?â€. Juyawa tayi tana kallon Saddiqa dake cewa. “Yanzu fa kafin inzo Aunty ta dawo daga parlour Malam tace wai baya nan akwai mara lfy da aka gaya masa jikin yayi tsananin a rikice ya tafi baima gaya mata wayeba to ko dai Mahmoud É—in neâ€. Adda Nana tace. “Shine ma dan Salma tace min ga Malam ya iso tun É—azu jikin fa yayi tsanani sosai tace har Umminsa da Goggo kuka suke yi, Abba ma yana zubda Æ™wallaâ€. Ido ta juyo tana kallon Raihana dake cewa, ai É—azu da na fita na samu Mamy ma sun fita da Sadiq da Aunty Amarya.
Irin abinda zuciyarta yayi mata ranar da akace Yah Amin yayi acsident shine taji sak irinsa ya rufe mata zuciya da jiki, haka yasa ta kasa ƙara cewa komai sai tsuma da jikinta keyi ta ciki, idonta kuma har lau ta kasa koda ƙebtasu.
Saddiqa tace.
"Adda ko zamu jeneâ€. Cikin sanyi Adda Nana tace.
"To ai su Salma ma da suke can. tace Malam yace duk mata sun tafi, yanzu itama dasu Mamy Salmanu na dawo dasu gida, su Ummi ma Malam yasa Hafiz ya medasu gida dan kukan da suke yi sun rikita ko ina.â€
Zuru sukayi cikin sanyin jiki, ita kuwa Fariyda a hankali take motsa lips ɗinta bayan taja numfashi mai ƙarfi sai kuma tayi shiru bata ce komai.
Dai-dai lokacin sukaji shigowar su Mamy, da sauri duk suka nufi parlour banda ita da ƙafafunta suka kasa miƙewa.
Adda Nana ta kalli Mamy dake zaune kan kujera tallaÉ“e da kuncinta. Aunty Amarya na gefe zaune a hannun kujerar Mamy Salma kuwa na zaune a Æ™asa Salmanu Æ™aninta aune a gefenta. "Mamy ashe Mahmoud ne ba lfy ya jikin nasaâ€. Ido na cikowa da Æ™walla Mamy tace.
"Nana Mahmoud najin jiki, yaron nan ya bamu tsoroâ€. Da sauri Aunty Saddiqa tace.
"Mamy meke damushi? Yanzu ya jikin nasaâ€
Ta ƙare tambayar tana kallon Aunty Amarya dake cewa.
"Wlh har yanzu jikina rawa yake yi, Mahmoud yana cikin wani yanayi, Amman yanzu kam da sauÆ™i Sadik yace dan na kirashi kafin mu shigoâ€. Raihana tace.
"Mamy Accident yayi ne?â€. Tana sharce hawayenta tace.
"Ba Accident bane, ciwon cikine ya murÉ—esa lokaci É—aya ya galabaitar da shi tamkar zai É—auke rayuwarsa, wlh Hajia Fatima ta bani tausayi ta kiÉ—ime sosai sai kuka takeyi Goggonsu har suma tayi lokacin da cikin yayi masa murÉ—ar da tasa maza zubda Æ™wallanâ€. Ido na cikowa da hawaye Salma tace.
"Ni tunda naga Yah Salim na kuka nasan abin nan babbane.†kiran Salim ɗin da ya shiga wayarta ne yasa ta sauri amsawa, yadda taji muryasa ne yasa ta sauƙe numfashi da sauri tace.
"Babe ya jikin Appiyn Zaidâ€. Sai kuma duk suka kalleta jin tana hamdala tare da addu'ar Allah ya Æ™ara masa sauÆ™i ta É—aura da cewa,
“Babe ina gidan Baba Malam mun dawo dasu Mamyâ€.
Bayan ta katse kiran ne tana kallonsu tace.
"Alhamdulillah Yah Salim yace yanzu jikin da sauÆ™i har sun samu yayi bacciâ€. A tare sukayi ta hamdala, Mamy ne ta mike ta nufi bedroom É—in Fariyda yadda su Raihana suka barta haka Mamy ta sameta kamar mutum mutumi, sai dai yanzu numfashinta ya dai-dai tun da ta jiyo duk abinda suke tattaunawa a parlour har da abinda Salma ta faÉ—a.
Haka yasa ta rungume su Zaid a jikinta irin yadda Mahmoud ke rungumesu kansu take shafawa kanta na sunye a kansu. Fuska a haÉ—e Mamy tace.
"Ke baki ji Mahmoud ba lfy baneâ€. A hankali a É—ago kanta sai kuma tayi Æ™asa da kanta a hankali ganin kallon da Mamy ke watsa mata, ita kuwa Mamy cikin takaici tace.
"Koma baki masa fatan samun lfy a kan komai ba a duniya kyayi masa fatan samun lfy ko saboda yaranki da in babu shi a duniya sun tabbata marayu, amman da yake zuciyar dutse gareki kin É—aurawa kanki tsanar mutumin da yake son yaranki tamkar ranshi kowa ya fito amman banda ke wato ke farin cikima kikeyi ko?â€. A hankali ta fara jujjuya kai alamun a'a.
Saddiqa da Adda Nana ne suka shigo Salma na bayansu Mamy taci gaba da cewa. "A'a wlh farin ciki kikeyi tunda ko ki fito ki jajanta kiji me ya sameshi kin gaza, bare aje ga babin kiyi masa addu'ar samun lfyâ€. A hankali tace. "Allah Ubangijin talikai ya bashi lfy dashi da dukkan Æ´an uwa musulmai baki É—ayaâ€. A faÉ—ace Mamy tace.
"Amin Yah Allah in ma da gatse kikayi masa uwarsa kam da ubansa suna can sunayi masa addu'a suna kai kukansu wurin Allah kuma zai amsasu, muma kuma da duk masoyansa muna masa addu'aâ€. Daga nan ta juya ta fita Aunty Amarya dake bakin Æ™ofa nace mata.
"Yi haÆ™uri dare yayi fa ana jinki har wajeâ€.
Gefenta Salma ta zauna tana amsar Zaitoon tace.
"Wlh naji tsoro sosai shiyasa na kiraki, Fariyda naga su Ummi ma sai kuka suke Abba ma da kansa da Bappa Lawan hawaye suke yi, Yah Salim kamar macefa yake kuka yana rungume da Appiy Zaid. Amman Alhamdulillah yanzu kam yace da sauÆ™i sosai har yana min tsiya wai na gudu na barshi yau da wa zai kwana kinga kenan ai jikin Appiyn Zaid da sauÆ™i kenanâ€. Kai ta jinjina tare da cewa.
"Allah ya Æ™ara sauÆ™iâ€. Amin sukace a tare. Daga nan kuma suka É—an fara hira, Raihana ta shimfiÉ—a katifa a can gefe ita da Adda Nana da Salma suka kwanta a kan katifan Anuty Saddiqa da Fariyda dasu Zaid suna kan gadon hira suke yi sosai Raihana da Bashir É—inta ya turo mata videos É—in gidansu dasu Aunty Jamila da matar kawunsu da Æ™awar Mamynsu sukaje suka yi jeren yau É—in ne ta kalla tare da miÆ™awa Aunty Saddiqa wayar.
“Wowâ€. Tace lokacin da ta fara kallon tsarin farfajiyar gidan har zuwa cikin parlour bedroom kitchen da ko wani saÆ™o na gidan. Salma da Adda Nana suka amsa suma suka gani, sosai kyau da tsarin gidan yayi kyau duk da gidan ba irin Æ™ato É—in nan bane.
Ido Adda Nana ta zuba wa Fariyda dake zaune jingine da kan gadon idonta a buÉ—e Amman kamar bata É—akin duk abinda suke faÉ—a shiru.
Salma tace.
"Dama fa nima gobe talata zanzo tunda goben za'ayi sisters day, jibi laraba kamu ko, ranar Alhamis kuma wali jumma'a É—aurin aure asabar zamu tafi taraba koâ€. Saddiqa tace.
"Wai kin tambaya an barkin neâ€. Da sauri tace.
"Wallahi ya barni da kanshima fa ya tayani shirya akwati da zanzo dashi É—azu muna cikin shiryawan ne aka kirashi Appiyn Zaid ba lfyâ€. Kai Adda Nana ta jinjina tana kallon Fariyda data zame ta kwanta ta rungume su Zaid haÉ—i da lumshe idonta tayi shiru.
Da ido Adda Nana ta nunawa su Saddiqa ita, a hankali Raihana tace.
"Mamy ta mata faÉ—a ta É“ata mata farin cikintaâ€. A hankali Salma tace.
"Ko dai ciwon mijinta baâ€.
Tsaki ta ɗan ja tare da taɓe baki tana hararan Salma tace.
“Bani da mijinma bare yayi ciwo bare ciwonsa ya tsaya min a raiâ€. Ta Æ™are maganar tana jan wayar taci gaba da karatun littafin Garkuwa, 2 minute tayi da farawa sai kuma ta juya É—aya gefen tare da kifi wayar bayan kamar 10 minute ta kuma jawo wayar ta ci gaba da karatun tsaki ta É—an ja ta kuma kife wayar.
Su kuwa sai hira suke tayi Ameera ne ta shigo da trayn a hannnuta ta dafa musu indomie sai tururi yake yi yaji kifi da albasa taruhu.
Salma tace.
"Kai yar Æ™anwata Allah yayi miki al'barka dama yunwa nakejiâ€. Aunty Saddiqa tace.
“Ai mu mun saba cimar tsakiyar dare, don bama bacci da wuri shiyasa in gari ya waye yara sun tafi school mu biya bashin baccin itama Amiran da yake zuwan rana takeyiâ€.
A hankali Fariyda ta juyo tare da jawo wayarta tana duba Time ƙarfe biyu saura, bathroom ta wuce alwala ta fito. Saddiqa na kallonta tace.
"Kizo muci yayi yaji sosai yadda kikesoâ€. Kai ta jujjuyawa a hankali tace.
"Bana jin yunwaâ€. Ta Æ™are maganar tana shimfiÉ—a darduma ta kabbarta sallah, kusan duk a tare suka É—aga gira kana sukaci gaba da hira da cin indomie, nafila tayi tayi daga bisani ta fara karatun Alqur'ani.
Ƙarfe huɗu baccin shaiɗan ya kwashe su, har lau tana kan sallaya Saida tayi sallan asuba ta tashesu, kana ta koma ta kwanta tana cewa Raihana.
"Dan Allah in su Zaid sun farka ki tafi dasu part É—in Aunty Amarya ki musu wanka acan ki basu abinci kar su hanani bacciâ€. Kai Raihana ta gyaÉ—a mata.
A tare suka shiga parlour Baba Malam dan gaisheshi. Aunty Amarya suka samu a parlour nashi tana shirya masa kayan tea, bayan sun gaisa ne Adda Nana tace.
“Aunty Malam faâ€. Tana ninke dardumarsa tace.
“Tunda ya fita masallaci bai dawoba dama yace zasu wuce asibiti shida Safiq zasuje su duba Mahmoud da jiniâ€. A tare sukace. Ayyah to Allah dai ya bashi lfy. Amin tace tana kallon Salma dake cewa. "Nayi magna da Yah Salim dai yace, har yanzu yana bacciâ€. Aunty Amarya tace.
"Bacci ai alamun lfy neâ€. Sai ta kuma kalli Saddiqa da Adda Nana tace.
"Zakuje kitchen kunsan sai an sawa Lami hannu a aikin, yanzu Kahdija ma ke cemin anjima kaÉ—an zata isoâ€. To sukace, ina Fariyda ta tambaya,
Raihana tace.
“Tana bacciâ€. Daga nan suka fito suka nufi kitchen É—in tsakar gida inda ake aikin biki.
Ƙarfe tara da rabi Mamy dake tare da Khadija da bata daɗe da isaba, ta miƙe ta nufi daƙin Fariyda zaune ta sameta gaban dressing mirror, tana fesa turare da alamun ta ɗan jima da tashi tayi wankanta tayi kimtsa cikin doguwar rigar material mai taushin gaske milk color and yellow sai ɗan purple jersey veil purple color tayi rolin kanta dashi fuskarta ta fito ras sai kamshi take bazawa tayi ras da ita, da sauri ta juyo ganin Mamy ta cikin madubi tana ɗan yin ƙasa da kanta tace.
"Mamy ina kwanaâ€. A takaice tace. “Alhamdulillahâ€. Shiru tayi kanta a Æ™asa tana jiran me Mamy zatace.
“Kin kira Mahmoud kinji ya jikinsa ne?â€. Mamy ta katse shirun, kai ta jujjuya alamar a'a, fuska a haÉ—e tace.
"Shima sai nace zan ja miki Allah ya isa ne in baki kira É—inba kafin zaki kira!?â€. Da sauri ta fara jujjuya kanta ido na cike da Æ™walla tace. “Kiyi haÆ™uri Mamy kar kim Allah ya isa, bani da number shi faâ€. Harara ta danna mata tace.
"Wayar Aminullah da take wurinsan zaki kira, tunda ke dai baki cika maceba, number mijinki ce baki da ita sabida isa ke sai dai a biki kikeso ba ke zaki bishiba tunda kece aljannarki ke Æ™arÆ™ashin digadiginsa ai dolene ma yasa Mahmoud ya sakeki to me ma zai yi da mace mai taurin kan tsiya, zaki kira ki tambayi ya jikinsa ki masa addu'a ko sai na saÉ“a miki tunda ke baki da kara ai ko dan su Zaid Mahmoud ya cancanci kulawa a wurinki mu samman irin halin da ya shiga jiyan nanâ€. A hankali tace. "Mamy zan kiraâ€. Kwaffa tayi ta juya har taje bakin Æ™ofa tace.
"Idan kin kirasa ki kira Abbansu da Umminsa ki tambayi ya jikinsa, har Amina ki kirata ki tambayi jikin É—an uwantaâ€. Daga nan ta juya ta fita.
A bakin gadon ta zauna ta jingine kanta da allon kan gadon tare da miƙar da sawunta ta jawo pillow ta ɗaura kan cinyarta haɗe da jawo wayar ta, a ƙalla 6 minute tana riƙe da wayar, jin kamar Muryar Mamy na tahowa inda take ne tayi saurin lallatsa numbersa ɗin Yah Amin ɗin tayi dailing tare da ƙara wayar a kunne.
Shiru tayi tana jin yadda wayar ke bada sautin É—ut-É—ut numfashi ta fesar a hankali lokacin da taji an amsa kiran sai kuma taji shiru ba'ayi magna ba, haka yasa ta É—an motsa lips É—in ta a hankali tace.
"Assalamu alaikum Appiy!â€. Ta faÉ—a can Æ™asan maÆ™oshinta, cikin wata iriyar galabaitacciyar murya mai sanyi yace.
“Hmmmmmâ€. Shiru tayi tana jin sautin yadda yaja numfashi a kunnenta, murya can Æ™asa ya kuma cewa.
“Ke baki iya gaisuwa bako!?â€. Baki ta É—an tura like tana gabansa cikin sanyi tace.
"To ba kai baneâ€. Murya cike da alamun ciwo yace. “Nine me? Me kuma nayi?â€. Tana kwaÉ“e fuska tace. “Kayi shiru kaÆ™i mgnaâ€. A taÆ™aice yace. "To ina jinki!â€. Kamar cikin raÉ—a tace.
“Ina kwana ya jikinkaâ€. Cikin muryar raÉ—ar da tasata lumshe idonta yace. “Kinyi farin ciki ai ko?â€. A hankali tace.
"Kamar yaya?â€. Murya sarÆ™afe da sautin da ke bayyana raÉ—aÉ—in ciwon da yake ciki yace.
"Wanda bakya so bashi da lfy, wanda kikeyiwa fatan mutuwa sauran Æ™iris ya mutuwaâ€. Ido na cike da Æ™walla tab a hankali tace. "Ni wa nakeyiwa fatan mutuwaâ€. Ta Æ™are maganar murya na rawa.
Yana jan numfashi da rumtse idanunsa yace.
"Wanda kikafi tsana fiye da komai na duniya, wanda da kikaji an aura mikishi kika Sumaâ€. Dire mgnar murya can Æ™asan maÆ™oshinsa yaja kalmar suman cikin Æ™ahon zuciyarsa. Murya a sanyaye tace.
"Appiy ya jikinka da sauÆ™i ko? Tunda har ka fara neman faÉ—a da masifaâ€.
Numfashi mai nauyi ya fesar cikin muryar raÉ—a yace.
"Alhamdulillah da sauÆ™i ina su Zaidâ€. Tana É—an kallon kofar shiga tace. "Suna wurin Raihanaâ€. Hmmmm yace tare da yin shiru, itama shiru tayi tana sauraron sautin sauÆ™an numfashinda, a Æ™alla 4 minutes baice komai ba wayar ta É—an É—ago ta duba dan ta fara zaton ko kiran ya katse ne duk da tana jin alamun numfashinsa, ras bai katseba harara wayar tayi ta É—aura da cewa.
“Allah ya kara sauki sai anjimaâ€. Da sauri yace.
“Ke karki kuskura ki katse min kiraâ€. Tana kallon Aunty Saddiqa data shigo tana cewa.
"Fariyda har yanzu baki farkaba, Malam ya dawo munje mun gaisa yana tambayar ina kike ke bai ganki baâ€. Da sauri ta nuna mata fuskar wayar alamun tana waya ne.
“Waceceâ€. Ya tambaya a hankali. Tana kwaÉ“e fuska tace.
“Aunty Saddiqa ceâ€. Ta bashi amsa. Murya na Æ™arfi yace.
“Bata wayaâ€. Wayar ta miÆ™awa Aunty Saddiqa, a Æ™alla 3 minute suna magna haka yasa Fariyda zuba mata ido ganin yadda take magna dashi da jera masa addu'a a ranta tace. Mutumin da ko an gaidashi an mishi addu'a baya cewa Amin.
Bayan ta miƙawa Fariyda wayar ne ta juya ta fita tana faɗin in kin gama Malam na kira.
Kai ta gyaÉ—a tana ce masa. “Sai anjimaâ€. Shiru tayi jin yadda yake mgnar da kyar kamar a fizge yace.
“Ke karki katse min kira faâ€. Baki ta tura tace.
“To katina zai Æ™are aiâ€.
A hankali yace.
“Ni ba'a katse min kiraâ€.
Ya faÉ—a gami da yin shiru, a hankali tace.
"Appiy Baba Malam yana kiranaâ€.
Murya na rawa alamun ciwon ya yunƙuro kishi a hankali yace.
"Ba nace daina kirana Appiyn baâ€.
Baki ta É—an turo a hankali tace.
"Toh Moudy yayi aiâ€.
Numfashi ta fesar jin ya katse kiran miƙewa tayi ta fito parlour a tare suka wuce parlour Baba Malam ita da Khadija suna zama gaban Baba Malam wayarta na ɗan yin ƙara alamun shigowar saƙo cikin mmki take kallon saƙon ganin ya yasa mata katin waya har na 100k cikin ranta tace.
“in ance mai bai san zafin kuÉ—i ba yace an rainashi ko uwar me zanyi da wannan uban katinâ€. A fili kuwa Baba Malam ta gaida bayan sun gaisa ne ya kalli Sadiq dake gefensa wanda tare sukayi breakfast cikin bada umarni yace.
“Fariyda tashi kuje asbitinsu Nasir ke da Saddiqa da Nana da Khadija kuje ku duba Mahmoud da jiki, dan ɗazuma ina can abin ya ƙara tashi, sai dai Alhamdulillah kafin in fito ya lafa tashi ka kaisu yanzu. Ya ƙare maganar yana kallon Adda Nana da Saddiqa da suka shigo cikin shirin fita.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.